da hankalin ki, kar kisa damuwa a ranki ko dan saboda jaririn cikin ki...."
Nasreen tana kuka tana faɗin:
"Abeesh yana duniyar Catrina? taya hakan zata faru? Shikenam na rasa shi kenan?..."
Miemie ta ce:
"Bani da ikon shiga turken su saboda doka ta haramta haske shiga sashin duhu hakanan duhu bashi da ikon shiga sashen haske......"
A hankali Miemie ta rarrashi Nasreen har zuciyata ta nutsu amma ta kasa daina tunanin Abeesh....
★★★★★
A Duniyar Aljanu...
Catrina na Ƙudirin Auren Abeesh
A lokacin da Catrina ta bayyana niyyarta na auren Abeesh, zuciyarta ta cika da buri da soyayya. Ta kwashe lokaci mai tsawo tana kallon yadda yake kula da Nasreen da tausayi, duk da cewa zuciyarsa ta fara faɗuwa gareta saboda tsafin da ta dasa masa a cikin ƙwaƙwalwa. Amma burinta ya fi abin duniya, domin burin ta shine ta zama uwar gida ga Abeesh ta har abada.
Sai dai, da ta je ƙofar Dutsen Gwal — inda manyan shuwagabannin aljanu ke taruwa — aka dakatar da ita. Murya mai ƙarfi da girgiza daga sama ta fito daga cikin wuta
Ana faɗin:
"Catrina bint Bahrul Kayan, kin saɓa doka. Bil Adama ba halittar ki ba ce. Don ki aure shi, sai kin shigar da shi cikin danginmu — ya zama Aljani!"
Hannu ya fito daga cikin haske mai ja, yana nuna mata hanya biyu:
1. "Ko ki manta da soyayyar Abeesh, ki koma duniyarki ta duhu."
2. "Ko kuma ki cigaba da tsare Abeesh a cikin duniyar aljanu, ki mayar da shi dumi-dumin aljani ta hanyar amfani da Ruwan Zuciyar Sarauta...."
wani abu da idan mutum ya sha, sai ruhinsa ya fice ya koma sabon halitta.
Ta amsa da cewa zata tsare shi domin mayar da shi halittar su na Aljan...
Catrina ta juyo daga dutsen, zuciyarta cike da ɓacin rai. Amma tunaninta bai jinkirta ba. Ta fara shiryawa don mayar da Abeesh halittar Aljani...
Zuciyarta ta yanke shawara: Abeesh zai kasance nata — ko da kuwa a sabon duniya ne...
Catrina ta dawo daga taron shuwagabannin aljanu cike da nufin aiwatar da umarni. Ta shiga cikin wani ɗaki mai duhu da aka rufe da tabarau na zinariya da zoben tambarin Naƙsar Ruhin Dan Adam. A can, a cikin ƙwarya ta zuba Ruwan Zuciyar Sarauta, ruwa mai launin shuɗi mai haske da ke janyo ruhin mutum, yana tsarkake shi daga jinin ɗan adam har ya koma sabon halitta — Aljani mai rai da ƙarfi.
"Dole ne in fara da lalata zuciyarsa gaba ɗaya," ta faɗa a hankali, tana kallon Abeesh da ke kwance akan gado...
Cikin lokaci ƙanƙani ta shige duniyar mafarki ta hanyar ruwan, inda take iya sarrafa tunanin Abeesh ba tare da ya sani ba, a cikin baccin sa...
Abeesh ne ya fara jin sauyi
Tun daga wannan rana, Abeesh ya fara fama da mafarkai masu rikitarwa. A kowanne dare, yana ganin kansa a cikin duniya marar haske, yana tafiya a ruwan duhu, tare da wata murya mai daɗin gaske tana ƙiran sunansa:
"Abeesh... zo... in nuna maka gaskiyar ka... kai ba ɗan Adam bane..."
A ɓangaren Nasreen ta kasa kwantar da hankalin ta, riƙo hannun Miemie tayi tare da faɗin:
"Miemie! Ina son magana da Abeesh, taya hakan zai faru?..."
Miemie ta girgiza kai ta ce:
"Hakan ba mai yuwa bane, domin a halin yanzu Abeesh bai farka ba amma akwai hanya guda da zaki yi magana da zuciyarsa amma sai dole Catrina idan tana kusa zata ji maganar..."
Nasreen ta ce:
"Ba damuwa Indai zai jiyo ni zanyi magana da shi..."
Miemie ce ta ɗora hannunta akan goshin ta sannan ta ce:
" Ki lumshe idanunki sannan kiyi magana tamkar kina gaban ta...."
Itama Miemie lumshe idanuwanta tayi yanda zata ji tattaunawar su...
A hankali Nasreen take faɗin:
"Ya Abeesh, kana lafiya ne? Na lura da kai yanzu ka koma kamar wani daban, baka cikin hayyacinka...."
Abeesh a cikin bacci yaji muryar Nasreen, zuciyarsa ce ta fara magana, a hankali bakinsa ya fara motsi...
"Ban sani ba, Nasreen... kullum ina mafarki da wata murya... tana cewa ni ba ɗan Adam bane. Kuma yanzu... Ina jin wani abu yana girgiza ni daga ciki."
Catrina tana zaune a gaban madubin ɗakin ta, daga sama take jin muryar Nasreen da kuma amsar da Abeesh yake bata, a hankali ta juyo tana kallonsa, idonsa a rufe sai bakinsa dake motsi...
Nasreen ta ce:
"Abeesh! Kada ka sha komai daga hannunta! Ita ba mutum bace! Ita aljana ce! Kuma tana shirin mayar da kai wani daban!"...
Sai a lokacin Catrina itama tayi magana, tana faɗin:
"Wannan ba hurumin ki bane, Nasreen. Na fi karfinku duka..!"
Nasreen bata iya mayar mata da amsar ba sai Miemie da ta karɓi maganar ta ce:
"Catrina! Kin saɓa doka. Ruhi mai tsarki ba zai shiga ƙarƙashin aljani ba — sai da izini daga Tauraron Tsarki. Ki tuba ko kuma a hallaka ruhinki har abada."
Catrina jin Muryar Miemie yasa ta firgita, domin muryar ta na daban ne a cikin taurarin mata, kuma muryar ta yana tafiya da sanyi da kuma zafi...."
A lokacin Catrina ta fusata nan ta ɗauki wani ruwa ta watsa akan fuskar Abeesh, ta ɗauke sauraro daga gare su, yanda baza su ji wani ƙarin bayani ba, kuma bazasu sake haɗa connection a tsakanin su da Abeesh ba....
A wannan dare mai ɗauke da duhu,
Abeesh yana kwance har zuwa yanzu ba ya motsi, ba ya magana. Fuskar sa mai ɗauke da nutsuwa, kamar mai mafarki mai daɗi, amma zuciyarsa a kamamme take cikin bacci mai nauyin sihiri.
Catrina tana zaune kusa da shi, tana kallonsa da idanu masu cike da raɗaɗin soyayya da nufin iko. Duk da ya kasance ba ya numfasawa kamar yadda aka saba, jikinsa yana ɗaukan ɗumi...
Catrina a fili take furta:
"Wannan shi ne mijina... Ko da kuwa bai taɓa faɗar hakan da bakinsa ba," ta ce, tana shafa sumar kansa.
"Da zarar na gama shirye-shiryen haɗuwar jinin mu da na ruwa mai rai, zai zama cikakken Aljani – naku har abada."
★★★★
Nasreen tana zaune kan ƙaton dutse mai haske a cikin ruwan lumana. Ruwa mai sanyi yana tafasa da ƙamshi, tana kwance cikin shakatawa, amma ba kwanciyar hankali ba.
A zuciyarta, tana jin wani abu yana motsawa — kamar wani abu ya tafi da wani babban sashi na rayuwarta...
Ta ce:
"Me yasa zuciyata ke kuka ne? Me yasa nake jin babu shi?"
★★★★★
A wani kogi mai zurfi, mai launin shuɗi da ja, Tasleem tana jingine a jikin wani bishiyar sihiri. Tsaron ruhohin tsafi suna kewaye da ita – ba ta da ikon fita, ba ta iya amfani da ikon zuciyarta ba,
Tana ji a ranta cewa akwai abubuwan da suke faruwa....
A Ɓangaren Su AMMAAR...
Amaar yana zaune kusa da Abul, wanda ke fama da karamin ciwon zuciya da rashin ƙarfin jiki. Basu san me ke faruwa da Tasleem ko Abeesh ba. Amma zuciyar Amaar cike take da wani abu mai nauyi – yana jin tamkar wani mai rai yana fadin:
"Ka tashi! Ka yi wani abu!"
Amaar ya kalli Abul ya ce:
"Abul, ka tabbata baka jin wani abu?"
Abul ya ce:
"A'a, Ammaar. Kai kaɗai kake jin wannan ƙiran, Ni kuma zuciyata tana girgiza kamar an ɗauke wani na kusa da mu, kamar ana shirin tabka babban kuskure a tsakanin jinsi da jinsi...."
A ɓangaren Asmeen kuwa tana kwance a gado, a wannan lokacin Shaprees baya nan, Madam Nablah ce take tare da ita....
Madam Nablah tana zaune a gefen ta tana shafa cikin Asmeen da take fama da ciwon ciki. Cikin nan shine ƙarfin ikon ta – shine zata yi sadaukarwa domin sabunta ikonta da rayuwar da ba ta gushewa...
A cikin ranta take faɗin:
"Da zarar ta haifi wannan jariri, ba wani mai iko da zai iya dakatar dani. Zan iya cinye kowace rana, da rana, da dare!"
Asmeen kuwa tana shan raɗaɗi – tana jin wani murya daga cikin iska tana cewa, "Ki farka, ki gudu!"
Amma ba ta iya motsawa – ruhohin tsafi sun daureta da sarka ta ruwa mai rai.....
______________________★
Dogon baccin da ya rufe zuciyar Abeesh kamar wata mai duhu ce da ta rufe duniya. Kamar ba zai tashi ba. Amma a yau, wani iska mai sanyi da ƙamshi ya mamaye ɗakin. Kyandir na kyalli suna lilo, ruwayen zinariya yana shawagi a iska.
Catrina na zaune kusa da shi – cikin riga mai sheƙi da haske mai kyau fiye da na duniya. Ta kai hannunta ta shafa kuncinsa cikin natsuwa.
Ta ce:
"Ka farka, masoyina..."
Abeesh ya buɗe idanuwansa a hankali, numfashinsa ya sauƙa kamar wanda ya dawo daga wata duniya.
A hankali ya furta:
"Ina... nake?"
Catrina ta ce:
"Kana tare dani, a duniyar da babu azaba. Na ce maka ba zan cutar da kai ba."
Ya kalle ta Idonta mai ƙyalli da nutsuwa. Yana jin wani abu mai daɗi yana shige masa.
Ya ce:
"Kin… kasance tare da ni? Cikin wannan tsawon lokacin?"...
Catrina ta ce:
"Eh. Na tsare ka da soyayya, ba da sarkar wuta ba. Kuma yanzu lokaci ya yi da za ka kasance dani har abada."
Abeesh ya kalli hannunsa babu rauni, babu damuwa. Amma a gefe guda, yana jin kamar wani sabon abu yana gudana cikin jijiyoyinsa. Ruwan ɗumi na hawan kansa rayuwar dan Adam tana rabuwa da shi a hankali...
Ya ce:
"Me kike nufi?"
Ta ce:
"Soyayya ta ba zata taɓa tabbata ba sai ka zama tamkar ni. Ka zama Aljani. Sai haka ne za mu yi aure cikin bin dokokin masarautar Aljanu."
Abeesh ya lumshe idonsa. Zuciyarsa tana motsi. A can ƙasan zuciyarsa, wani sashi yana jayayya tare da faɗin:
“Wannan ba Nasreen bace… Me zai hana na jira Nasreen?”
Amma wani sashi yana ɗaga murya da cewa:
“Nasreen ta bar ni... Wannan ce kawai ta tsaya tare da ni... wannan ce ke ƙaunata.”
Catrina ta kama hannunsa ta ɗora akan ƙirjinta.
Ta ce:
"Ina sonka. Kuma zan canza ka da soyayya, ba da azaba ba."
A lokacin, wani zobe na launin baƙin zinariya ya bayyana a tsakiyar tafin hannunta. Ta ɗora hannunta a saman zuciyar Abeesh. Idanunsa suka canza launi – daga fari zuwa shuɗi....
A kallo ɗaya, wani koren fure ya tsiro a gaban su. Furen aljanu – alamar an karɓi amincewa daga manyan aljanu.
Catrina ta ce:
"Zamu yi Aure nan da kwana uku."
"Ina so." Abeesh ya amsa – cikin murya mai kauri, wanda ba irin na dā ba.
Soyayya ta rufe shi, amma soyayyar da ke jujjuya ƙwaƙwalwarsa...
Acan ɓangaren Nasreen...
Nasreen ta zabura daga mafarkin da tayi a cikin baccin ta, hawaye na zuba take faɗin:
"Ina jin shi... amma ba kamar da ba. Ya canza!"
Miemie wacce ta ɓace a cikin ruwa bata ganuwa amma tana jin maganganun Nasreen, ta bata amsa da cewa:
"Yanzu me kike so ayi Nasreen?...."
Nasreen tana hawaye ta ce:
"Ina so naje yanda Abeesh yake koda bazaki je ba..."
Miemie ta ce:
"Kina hauka ne Nasreen? to ko Tasleem wacce take da ƙarfin iko bazata iya cin galaba ba idan taje duniyar Aljanu..."
Nasreen ta ce:
"Zan yi amfani da ƙarfin zuciyata koda banida iko, bazan taɓa barin Abeesh a cikin wannan halin ba, bazan taɓa barin ya zamo Aljani ba ko dan saboda jaririn cikina...."
Miemie ta ce:
"Wuri ne mai hatsarin gaske Nasreen, ba lallai ki dawo da rai ba, in ma kin dawo to wata ƙil kema su iya canza ki zuwa halittar su..."
Nasreen ta ce:
"Inada Ayar Ubangiji, yanda Allah ya yi Ni a halittar ɗan Adam haka zan cigaba da kasancewa har ƙarshen rayuwa ta...."
Miemie wacce ta bayyana lokaci guda, ta kalli Nasreen cikin tausayawa sannan ta ce:
"Idan baki hanzarta ba, ana iya rasa shi har abada. Amma ki sani, shiga duniyar aljanu ba mai sauƙi ba ce. Za ki rasa wani ɓangare na kanki."
Nasreen tana kuka ta ce:
"Ina so! Zan bi shi! Ko da kuwa zan rasa komai!"
Miemie ta ɗora hannunta a goshin Nasreen – numfashinta ya canza. Sai ga wata ƙofa ta buɗe – ƙofa mai wuta da ruwa da iska. Duniyar Catrina....
Ɓangaren Tasleem! Madam Nablah ta ɓullo mata..
Tasleem tana nan zaune, jikinta a sarkake da sarkar ruwa. Madam Nablah tana gabanta, tana karanto surorin sihiri cikin murya mai ƙarfi.
Ta ce:
"Zaki zauna a nan har sai ikonki ya kare. Ina buƙatar jinin Nasreen da Asmeen domin in cika ikon mallakar duniya!"..
Tasleem ta kalle ta da hawaye ta ce:
"Wallahi ba za ki ci nasara ba. Ko da kuwa zaki mallake duniya – ba za ki taɓa mallakar zukatan mu ba!"
Madam Nablah ta murɗa wani zobe. Ruwa ya yi ƙarfi, ya lullube Tasleem gaba ɗaya, ta ƙara tsauwala tsaro, daga nan ta bar yanda take...
____________________★★
Amaar yana zaune kusa da Abul wanda ke kallon cikin wani tsohon littafi. Abul ya dago kai yana kallon Amaar..
Murya na rawa cikin damuwa ya ce:
"Amaar, na ga wani abu… Abeesh yana cikin hatsari. Kuma wallahi ana shirin ɗaura masa aure da Catrina… kuma Catrina ba mutum ba ce...."
Amaar ya ɗago. Zuciyarsa ta tsaya cak cikin hargitsi ya ce:
"Abeesh... Aure? Catrina... ta ya ya?"
Abul ya ce:
"Muna da kwanaki uku. Idan har aka ɗaura auren nan, ba za mu iya dawo da shi ba har abada. Idan muka kuskura muka shiga duniyar Catrina ba da izini ba, za ta iya rufe rayukan mu."
Amaar ya ce:
"To ina ƙofa? Ina hanyar zuwa can! Idan har zan mutu domin in cece shi, to haka ya dace da Ni...."
Abul ya ce:
"Kayi hakuri Amaar, inaji a jikina na rasa Abeesh, kaima bazan so na rasaka ba, saboda haka ka bi umarni na ka zauna a yanda kake, bazan bar ka kaje duniyar Aljanu ba domin nasan babu mai dawowa da rai, mu dage da addu'a da yawan karatun Alqur'ani mai girma Allah yana sane da mu...."
Amaar ya ce:
"Shikenam ba komai Abul..."
---★
A lokacin da Catrina ke shirin sa zoben aurenta a yatsan Abeesh, wani ihu mai ƙarfi ya karaɗe filin wurin...
"KAR A YI AUREN NAN!!!"
Wani haske mai ƙyalli ya faɗo daga sama. Nasreen ta bayyana cikin ruwan zinariya da numfashi mai ƙarfi. Idonta na zubda hawaye, zuciyarta na huci ta ce:
"Ya Abeesh, kar ka manta da ni! Ina ƙaunarka! Wannan ba kai ba ne!"
Abeesh ya tsaya... Hannunsa ya yi sanyi... Zoben ya faɗi ƙasa....
Abeesh ya kalli Nasreen da idanuwansa masu shuɗi kamar ruwa mai duhu. Muryarsa ba kamar ta dan Adam ba, tana fito da wata murya mai cakudadden sauti – tsakanin namiji da aljani.
Cike da tsana ya ce:
"Wa ke ƙirana da suna da ba zan iya tuna shi ba? Wace ke mana cikas da auren da zai cika ni da iko?"
Nasreen ta sunkuyar da kanta, hawaye duk ya wanke mata fuska ganin halin da Abeesh yake amma zuciyarta na cika da ƙarfin hali. Ta kalle shi sannan ta ce:
"Ni ce Nasreen! Ka tuna ni! Ni ce matar ka wadda ta so ka kafin Catrina ta ɓatar da kai, sannan ina ɗauke da cikin ka a jikina...!"
Kafin ta iya ƙara wani kalma, Abeesh ya kai hannu ɗaya, ya kamota tare da shaƙo mata wuya, ya ɗagota sama, yana sakin wani irin numfashi mai ƙarfi, ya ce:
"Ke ba komai ba ce sai cikas! Cikin ki ba ni na yi ba – karya kike!"
Aljanun wurin sun zuba musu ido. Amma babu wanda ya kuskura ya motsa. Dokar manyan Aljanu ta hana shisshigi.
Nasreen tana riƙe da wuyanta, tana hawaye da numfashi mai wahalar fitarwa Abeesh ya cilla ta gefe kamar mataccen ganye. Ta buge da ƙasa da ƙarfi, jiki na karkarwa....
Catrina ta matso da murmushinta mai cike da mugunta. Ta zaro zoben aurenta, tana kallon Abeesh tare da k'yafta ido ta ce:
"Zamuyi aure yanzu, masoyi..."
Sai dai kafin ta sa zoben a yatsan Abeesh, Nasreen cikin ƙarfin hali ta taso da ƙarfi ta buga hannun Catrina, zoben ya tashi sama, ya faɗi ƙasa, ya narke cikin wata hoda ta zinariya...
"BA ZA A ƊAURA AURE BA!" Ta yi maganar da ƙarfi....
Wani guguwa ta taso ruwan wuta da kukan duhu suka gauraya. Catrina ta yi wani irin ihu cikin tsawa ta ce:
"Kin cutar da ni! Ya isa haka!"
Abeesh cikin fushi ya juyo. Idanunsa na haske da wuta. Ya nufo Nasreen, ya kai mata wani irin matsanancin naushi a cikinta, haka ta fara jin ƙugu-gugu!...
A fusace ya ce:
"ME KIKAYI MIN!? WACE CE KE!?"
Nasreen juyi kawai take tana birgima ga wani irin kukan da take na fitar hayyaci da tsantsar ciwo da cikinta ke yi, a wannan lokacin jini ne ya ɓalle mata yana zuba kamar magudana. An daɗe ba a taɓa ganin mace ta fuskanci azaba irin haka a duniya da aljanu ba..
Murya ciki Nasreen take faɗin:
"Wayyo Allah na…wannan wani irin ƙaddara ce?" ta furta a wahalai...
Catrina ta matso kusa da Abeesh, tana kokarin rungume shi. Amma idanunsa suka nuna ba a cikin hankalinsa yake ba. Ya kama kansa – yana fitar da wani murya kamar na mahaukaci...
Gaba ɗaya jikin Nasreen ya jiƙe da jini, zuciyarta na dukan ƙarshe-ƙarshe. Hankali ya gushe mata. Ta kasa miƙewa, ta kasa magana. Tana kallon Abeesh cikin tausayawa, wanda yanzu ya canza gaba ɗaya, kamar wani halitta daga ɗayan duniya.
A hankali take furta:
"Ni nake ƙaunarka… wacce ka aura… ka ce zaka zauna da ni har abada..."
Amma Abeesh ko kaɗan bai saurareta ba. Idanunsa masu shuɗi suna cike da ƙiyayya. Bai nuna tausayin komai ba. Sai da ya matsa kusa da ita, ya durƙusa kamar zai taimaka mata… sai kawai ya sake naushinta a cikinta yana faɗin:
"Ki mutu! Kin kawo tsaiko ga zubin Aljanu da bil’adama! Catrina ita ce rayuwata yanzu!"..
Nasreen birgima tayi gefe tana murtsukuku Jinin da ke fita daga gabanta ya ƙara yawanta, Sai dai hakan bai ƙare ba.
Catrina ta matso daidai lokacin da Nasreen ke ƙoƙarin numfasawa da ƙyar...
Tana sanye da farar rigar aljanu, idanunta suna kyalli da murɗaƙen tsafi ta ce:
"Kin cuci zuciyata sau ɗaya, Nasreen. Amma yanzu sai ki ji hukuncin da duk mai tsallake Aljani ke fuskanta!"
Ta ɗaga hannunta. Wani murɗaɗɗen ƙaho na wuta ya bayyana. Ta ɗaga shi, ta bugawa Nasreen a kirji da shi. Wani irin gigitaccen ihu marar misaltuwa ya fito daga bakinta. Jikinta ba ƙaramin girgiza ya yi ba, Wata murya daga cikin sararin duniyar ta ce: