gane asalinta ba,
Yana jin sonta a cikin zuciyar sa amma yana jin hakan laifi ne, yana jin laifi ne saboda Nasreen ta nemi afuwar sa da hawaye a fuskarta, har ya haƙura da Auren ta amma saboda umarnin Abul, da kuma shawarar Yayansa Amaar, sai ya amince da wannan auren domin su gyara rayuwa.
A wunin yau kowa yana cikin shirye-shiryen gobe. Nasreen na cikin ɗaki tare da Asmeen suna shiryawa, amma zuciyarta cike take da ƙunci. Tana son zuwa ɗakin Abeesh domin ta sake magana shi — ta san ba a gama warware komai ba, har yanzu akwai dusar da bata narke ba a cikin ransa.
A gefe guda, Catrina kuwa tana zaune a wani lungu na falon gidan, cikin shiga mai zaman kansa. Bata fito fili ba, amma tunanin ta yana kan Abeesh ne — gaba ɗaya ta gama karantar zuciyarsa. Tana murmushi a hankali, tana cewa a zuciyarta:
“Zan bar ku kuyi Aure Nasreen, Amma zuciyar mijinki ba taki bace gaba ɗaya... ba sai na kwace shi daga gareki ba, tunda nayi nasarar shiga cikin ransa.”......
TSARIN BIKIN YAU
An tsara biki da sassafe. An kira limamai da shaidu, ana sa ran za a yi aure da safe kafin rana ta bayyana sosai. Ana shirin yi a cikin babban filin gida, inda aka jejjera komai na ƙayatar da bikin....
An tsara komai, an ƙawata gidan tamkar sabuwar duniya, ƙamshi na turaren wuta da na fure sun haɗu sun ba da wata irin annushuwa ta musamman. A yau ne za a ɗaura auren Abeesh da Nasreen, da kuma Asmeen da Shapreen...
A ɗakin Abeesh...
Yana zaune a gefen gado yana kallon tagar da ke fuskantar rana, yana ta tunanin yadda zuciyarsa ke cike da ruɗani. Soyayyar da yake wa Nasreen ta fara dusashewa, amma zuciyarsa baza ta iya fitar da ita gaba ɗaya ba. Har yanzu yana jin raɗaɗin mari da kalaman da ta furta masa a lokacin da ya bayyana gaskiyar halin Madam Nablah.
Kwatsam sai ga ƙofar ɗakin ta turo a hankali, Catrina ce, ta sha ado kamar bazawara daga wata masarauta. Ba ƙaramin kyau tayi ba. Rigar da ke jikinta na launin zinariya mai kyalli, tana fidda haske da kwalliyar da ta bayyanar da surar jikinta, gashinta yana yawo har gadon baya, idonta cike da kwaɗayi da nuni.
Tsaya wa tayi a bakin ƙofa sannan ta ce
“Zan iya shigowa ko?” ta faɗa cikin wata murya mai sa nutsuwa da girgiza zuciya.
Abeesh ya ɗan juyar da kansa yana kallon ta, duk da a yanzu bai da ƙarfi sosai akan Nasreen, yana jin wata ɓangare na zuciyarsa yana ja da Catrina. Ya gyara zama amma bai ce komai ba.
Catrina ta matso a hankali, kamar wacce take jin kunyarsa, amma da mugun nufi take tare dashi, ta zauna gefensa tana kallon sa kai tsaye.
Ta furta
“Na san rana mai kamar ta yau kana bukatar nutsuwa, amma na zo ne in tayaka murna.” Ta ɗan ɗora hannunta a saman kafadarsa, tana shafar sa a hankali.
Abeesh ya kama hannunta da nufin cirewa, amma sai ya tsaya. Ganin yanda zuciyarsa ke sauya yanayi, sai ya ce da ita:
“Catrina… me kike nema a wurina?”
“Ka sani ai,”
ta ce da murmushi, sannan ta kuma cewa “Ba zan tsaya ba sai na samu zuciyar da nake nema…”
Abeesh kallon ta kawai yake ba tare da ya furta komai ba, har ta gama yinta ta tashi ta fice...
---
A can ɗayan ɓangaren part ɗin su Tasleem...
Tasleem tana tare da Nasreen da Asmeen a ɗaya daga cikin ɗakunan kwana. Ta kama hannun Nasreen tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali.
Cikin kulawa ta ce
“Nasreen… ki manta da baya, ki tuna da yanda kike ƙaunar Abeesh. Na san zai dawo ya darajar ki.”
Nasreen tana hawaye ta ce “Amma Tasleem, zuciyarsa ta riga ta fita daga wurina… ina jin yana sonta… waccan Catrina.”
Tasleem ta share mata hawayen fuskarta ta ce
“Wallahi in har Catrina ba ita ce uwar ƙaunarsa ba, ba zata shige zuciyar sa ba. Ke ce ta zuciyarsa... karki bari wani ya maye miki gurbi.”
A gefe guda kuwa, Asmeen ce ta saki ajiyar zuciya tana kallon madubi wacce ata sanadiyar Auren nan Mommynsu tasa aka ɗauko ta daga part ɗin Shaprees
Tana hawaye ta ce
“Ni kuwa Tasleem, wallahi bana jin Shaprees mijina ne. In dai auren dole ne, to zuciyata ba zata taba yarda da shi ba.”
Tasleem ta matso kusa da ita tare da cewa
“Kada ki karaya, Asmeen. Kullum haske yana da hanya, har cikin duhu. Ni zan ci gaba da neman mafita, domin ku samu kuɗi, ku sami lafiya, kuma ku samu soyayya.”
'
Tasleem wuni take tare da ƴan uwanta tana basu kulawa ta musamman....
---
A yau ne za a kai Amare ɗakin mazajen su dake cikin gidan Madam Nablah saboda tsaro Kowa yana cikin girmamawa da farin ciki a zahiri, amma a zuciya akwai sirrin da bai da mafita. Kuma a gefen wannan soyayya da ƙaddara, Catrina tana ta ƙoƙarin cin nasara da kwaɗayin zuciya...
★★★★★
Daren da aka ɗaura aure, gidan Madam Nablah ya ɗauki kyan da ba a taɓa gani ba. Wutar fitilu tana haskakawa kamar taurari sun sauko ƙasa. Turaren ƙamshi ya cika ko’ina, yana yawo cikin iska kamar harshen soyayya. Amma duk wannan ƙyalli na waje bai iya ɓoye tsananin rikici da girgizar da zuciyoyi ke fama da su ba.
A ɗakin sabuwar Amarya Nasreen tana zaune a gefen gado cikin shigar bacci mai launin shudi da zinariya. Idanunta sun cika da hawaye duk da fatar da ta yi na wannan ranar, tana ƙoƙarin kare kanta tana maganar zuci
“na samu soyayyar rayuwata amma zuciyata ta san gaskiya...."
Abeesh bai zo ɗakin nata ba. Yana can a ɗakinsa yana kallon madubi, yana duban fuskar kansa da ido mai zurfi kamar yana tambayar kansa:
“Ni waye ne yanzu? Mijin Nasreen? Ko dai ƙaunataccen Catrina da zuciyata ke bugawa saboda ita?”...
Kamar daga sama, ƙamshin turaren Catrina ya karade ɗakin. Kafin ya kammala tunani, ta turo ƙofar cikin natsuwa, cikin shigar mayafi mai launin ja da zinariya. Fuskarta cike da annuri, idanunta kuwa na walƙiya da sirrin duhu.
Ta tsaya a gabansa.
“Abeesh...” ta kira sunansa da murya mai sanyi kamar ruɗin murya daga wata duniya.
“Ka yi aure yau, amma zuciyar ka har yanzu bata samu natsuwa ba. Ni na fahimta.”
Abeesh bai iya cewa uffan ba. Kamar mai shaƙuwa da ƙamshin sihiri, ya matsa kusa da ita. Ta kai hannunta ta shafa sajen fuskarsa da tausasawa, tana murmushi ta ce
“Na san baka manta da ni ba. Kuma zan kasance tare da kai — ko da ka auri Nasreen. Ba zan bar ka ba.”
Yayi ƙoƙarin cewa wani abu, amma muryarsa ta makale. Zuciyarsa a rikice — ba ƙyale Nasreen gaba ɗaya ba, amma zuciyarsa na karkata ga Catrina.
**
A part ɗin Asmeen kuwa.... Tasleem na cikin ɗakin Asmeen, tana rarrashin ta kamar yadda uwa ke rarrashin ɗa. Asmeen tana zaune da mayafi a bisa kafadarta, hawaye na sauƙa daga fuskar ta.
Asmeen tana kuka ta ce
“Tasleem, kada ki ce mun Shaprees mijina ne. Zuciyata na tsoro, kuma hankalina ba ya kwance da shi.”
Tasleem ta kamo hannunta tare da faɗin
“Na san... na san wannan auren ba shine burinki ba. Amma ki yi haƙuri. Kada ki manta da hasken da ke cikin ki. Ki riƙe shi, kada ki bar duhu ya ruguza miki rayuwa.”
Asmeen ta kalli Tasleem sannan ta ce
“Kina nufin... Shaprees ba wanda muke zato bane?”
Tasleem ta ɗan yi shiru, sannan ta ce, “Ina jin akwai abubuwa da yawa da muke buƙatar sani. Amma yanzu... ki kasance da tawakkali. Zaki buƙaci ƙarfin zuciya sosai.”
Tana cikin rarrashin Asmeen sai ga ƙiran wayan Nasreen,
Tasleem ɗaga ƙiran tayi tare da faɗin "Nasreen lafiya kuwa?..."
Nasreen tana kuka ta ce da Tasleem "Dan Allah ki zo yanda nake yanzu akwai matsala...."
Tasleem kallon Asmeen tayi sannan ta ce "Ƴar uwa Asmeen ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu babu abinda zai faru, yanzu zanje Nasreen tana ƙira na...."
Daga nan ta bar part ɗin Shaprees da Asmeen, ta koma can part ɗin su yanda Nasreen take ....
*****
A gefe guda kuwa, Nasreen ta kai karar zuciyarta wurin Tasleem tana faɗin
“Kin ga yadda yake, ko? Bai zo ba. Babu soyayya... babu daɗin aure... Catrina ce matsalar nan, ban san ko wacece ba amma... tana son ruguza ni!”
Tasleem ta rungume ta sosai tare da faɗin
“Na fahimce ki. Ki kwantar da hankalinki. Zuciyar Abeesh ba a wuri guda take ba. Amma ki sani — ke ce matar aurensa. Kuma Allah zai daidaita zuciyarsa idan kika dage da addu'a.”
**
A ɗakin duhu kuma, Madam Nablah na zaune tana juyawa a kujerar sarautarta, tana dariyar cikin zuciya. Tana jin daɗin yadda abubuwa ke tafiya dai-dai....
Kwatsam, wani hazo mai duhu ya bayyana a gabanta — Catrina ce. Tana siffar aljana yanzu, ba mutum ba. Ta sunkuyar da kai.
“Uwar Wuta, komai na tafiya daidai. Na kusa mallake zuciyar Abeesh gaba ɗaya.”
Madam Nablah ta murmusa da mugunta ta furta
“Da kyau, Catrina... Idan muka mallaki zuciyar Abeesh, za mu iya karya ruhin Abul da kuma shanye hasken da Tasleem ke ƙoƙarin kawo wa.”
★★★★★★
Falon ya ɗauki salo mai zafi, wutar fitila na haskaka fuskokin da ke cike da motsin zuciya. Amaar yana zaune cikin natsuwa, hannunsa a kan na Tasleem wacce take ta sharar hawaye cikin tausayi da ƙunci.
“Ya Amaar,” Tasleem ta ce da muryar da ke rawar zuciya, “meyasa mommyna bazata amince da kai ba? Ta Aurar da Nasreen da Asmeen amma ni... ita ce ta hana ni farin ciki na. Na gaji da jurewa.”
Amaar ya riƙo hannunta cikin tausayawa tausayi yana kallon idanunta cikin kwantar da hankali
“Tasleem,” ya ce cikin murya mai laushi, “ki kasance mai tawakkali. Allah yana jarrabar bayinsa da wanda yafi dacewa da su. Ranar aurenmu na zuwa, ko da duniya ta ƙi, sammai zasu yarda. Kin cancanci soyayya mai tsarki kuma Allah bazai bar ki ba.”
Tasleem ta sauke ajiyar zuciya, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta. Suna cikin wannan tattaunawa ne sai ga ƙofar falo ta buɗe — Catrina ta shigo.
Sai ta tsaya, a jikin lulluɓe da atamfa mai launin zinariya da baƙi, tana kallon su da wani murmushi wanda ba’a gane ko da gaske bane ko yaudara a hankali ta furta
“Masoya... sannunku da hutawa,”
ta faɗa da murya mai saukar da sanyi amma cike da nufin karya nutsuwa.
Tasleem ta ɗaga kai da sauri, kamar wata wuta ce ta kunno kai a zuciyarta. Ta miƙe tsaye cikin hanzari kamar bazata jure ganinta ba
“Kece Catrina ko?” ta ce cikin tsawa. sannan ta cigaba da faɗin
“Ke da kika zo mana a matsayin baƙuwa amma kina ƙoƙarin ruguza soyayyar ƴar uwata da mijinta? Wace irin halayya ce haka?”
Catrina ta ɗan saki dariya — wadda ke cike da wani irin kwanciyar hankali. Ta taka zuwa tsakiya cikin falo, ta tsaya gaf da gaf tana kallon Tasleem da ido masu walƙiya.
“Soyayyar Abeesh?”
Catrina ta ce.
Ta kuma cewa
“Na rigada na mallaki zuciyarsa. Kin ce Nasreen ce matar sa, amma zuciyarsa ba ta wurinta. Shi kansa yasan hakan. Ina sonsa... ko da zuciyar ku bata so...”
Amaar dai bai ce uffan ba, yana zaune yana nazari, zuciyarsa na hararar wannan sabuwar halitta da ba ya ganewa. Amma a hankali yana lura, Catrina ba kamar kowa bace. Tunaninsa na barazanar cewa akwai wani abu mai zurfi da ke ɓoye a bayanta.
Tasleem ta matso kusa da ita, fuskarta cike da haushi da taya ƴar uwarta kishi ta ce
“Abeesh ya auri Nasreen da yardar Allah. Kuma Nasreen ba ’yar kai ba ce da za ki ƙetare ka’ida. Idan da gaske kina da ƙauna, meyasa kike cutar da wasu? Wace ce ke Catrina? Ke kamar ba mutum bace — zuciyarki duhu ne!”
Catrina ta ja tsaki, idanunta suka ɗan sauya kamar na wata halitta daga wata duniya ba tare da Tasleem ta gani ba...
Ta ce
“Na san ku ba za ku fahimta ba... Amma lokaci na zuwa da kowa zai gane inda zuciyar Abeesh take. Kuma ke Tasleem,” ta ƙara matsowa kusa da ita, “wannan soyayyar da kike fata da Amaar — bazata yuwu ba. Mahaifiyarki bazata taɓa barin ki ba, idan kuwa har zaki taya ƴar uwarki kishi akan abinda nake so to ba shakka zan dawo kan ki ne....."
Tasleem ta ɗan ja baya, ba shakka zuciyarta na girgiza. ta kalli Amaar, sai kuma ta kalli Catrina cikin ƙarfi a fusace ta furta
“To ko ki kasance aljana daga ƙasan ƙasa, bazan ƙyale ki ki tarwatsa farin cikin ’yan uwana ba. Kuma ko mahaifiyata ta ki yarda da ni da Amaar, haskenmu ya fi ƙarfinku. Zamu tsaya da juna har zuwa ƙarshen ruhi.”
Catrina ta yi murmushi, ta juya kamar wacce ta gama faɗin komai ta furta
“Sai mu gani,” sannan ta bar falon....
Amaar ya matso ya rungume Tasleem daga baya, yana faɗa mata cikin ƙasa da murya:
“Ki tsaya da gaskiya. Duhu bazai taɓa cin nasara a kan haske ba. Na rantse da rayuwata, zaki zamo matata — ko da me zai faru.”
Tasleem na tsaye a tsakiyar falo tana fidda numfashi da ƙyar, zuciyarta cike da ɓacin rai da tsananin ƙishi. Catrina ta riga ta fice ta bar tashin hankali wanda ke ɗauke da ɗumbin barazana.
Amaar kamo hannun Tasleem ya yi tare da juyo da ita yana kallonta cikin kulawa ya ce
“Na san ke mace ce mai gaskiya, kuma ke ɗiya ce mai tsarki, kar ki bari cutar zuciyar wasu ta karyar da ke.”
Tasleem ta girgiza kai tana ƙoƙarin daidaita zuciyarta daƙyar ta iya furta
“ Ya Amaar... wannan baƙuwar, tana da wani abu a jikinta wanda ban fahimta ba. Ba kamar mu take ba.”
Amaar ya kalli ƙofar da Catrina ta bi, zuciyarsa na dukan wasu alamomi da ba ya iya fassara shi Amma a ransa, wata faɗakarwa tana zagaye da shi — wannan ba mace ce kamar sauran ba...
---
Washe Gari: ana hidimar walima na ƙawaye bayan biki...
Gida ya sha ƙawanya kamar na sarauta. Jikin bango ya sha ado da fitilu, furanni da zannuwan alfarma. Kowa cikin farin ciki da murna...
A ɗaya gefen gidan, Tasleem tana cikin shirin tarbar baki da shirya abinci. Fuskar ta ɗauke da murmushi, amma zuciyarta na ƙaryar fara’a, domin ana bazarana da rayuwar ta. Ta shigo ɗakin Asmeen tana riƙe da kayan ado.
“Asmeen... kin shirya?” Ta tambaya da murmushin a fuskar ta
Asmeen tana zaune a gaban madubi, idonta cike da hawayen da ke faman taruwa amma bata bar su sun zubo ba.
A hankali ta furta
“Tasleem... zuciyata na kuka, zuciyata na kirana. Na san akwai wani abu game da Shaprees da ba daidai ba.”
Tasleem ta matso, ta zauna kusa da ita sannan ta ce
“Ki yarda da zuciyarki, Asmeen. Amma yanzu ki nutsu. Lokaci yana da ikon bayyana gaskiya.”
★★★★
A ɗakin Nasreen kuwa,
Nasreen na zaune a gaban mirror tana ƙoƙarin gyara fuskarta da kwalliya. Ta ji ƙarar buɗan ƙofa, ta cikin madubi ta hango Catrina,
tana shigo ta ce
“Kin shirya?” Catrina ta tambaya tana murmushi.
Nasreen ta ɗan harareta, ta ce:
“Ko da ke wacece, ki daina kusantar mijina. Wallahi kema mace ce kamar ni, karki cutar da wata saboda ƙiyayya ko mungun nufi.”
Catrina ta yi dariya, sannan ta matso kusa ta ce
“Ni kuwa, bana faɗa da ke. Abeesh shi da kansa ya shigo raina. Ki ce masa ya fita — ni na riga na mallake shi.” Ta juya cikin jin daɗi, ta bar Nasreen da bugawar zuciya.
---
A ɗakin Abeesh kuwa
Abeesh na zaune a gaban madubi, cikin shigar ango, fuskar sa ɗauke da damuwa da rikitaccen tunani. Baya jin daɗi kwata-kwata, komai ya yi masa nauyi. Soyayyar Catrina na damun zuciyarsa — ba da gangan ba, amma kamar aljanar ƙauna ta shige shi.
Kofarsa ta buɗe a hankali. Sai ga Catrina ta shigo, cikin shigar da ba a saba gani ba, ta lulluɓe jikinta kamar matar Aure Kafin ya buɗe baki, ta matso, ta durƙusa a gabansa tana kallon idanunsa ta ce
“Abeesh... na san bana da matsayin Nasreen a gurinka. Amma na san zuciyarka na kirana. Ka ce min da gaske... baka sonta yanzu kamar yadda kake sonta a baya ....”
Abeesh ya dafe kansa tare da faɗin
“Catrina... ban san me ke faruwa da ni ba. Idan ina jin ki, da gaske ne... to, ya zanyi da Nasreen? An ɗaura mana aure... kuma ita ce matar da na faɗa mata zan bata rayuwata.”
Catrina ta lumshe ido, tana murmushi ta ce
“Zaka iya kasancewa da ita... amma ka bani zuciyarka. Shi ne kawai nake nema.”
Ta kamo hannunsa tana shafawa, ta lallaba cikin salo har ta ƙara rikita masa hankali. Abeesh ya zama kamar mai bacci da ido a buɗe....
Cikin salo da ƙwarewa a wannan lokacin har ta samu kansa, suka kasance da juna, ta samu nasarar sumbatar sa har shima ya biye mata, amma babu abinda ya faru har yanzu yana riƙe da mazantakar sa 🙈🙈🙈
---
A gefe: Madam Nablah tana kallon komai daga wata gilashi ta tsafi.
Ta murmusa, tana magana da kanta:
“Catrina... kina sauƙe nauyi. Abeesh ya fara mantawa da Nasreen. Gaba ɗaya nufin su zai rushe.”...
Sai kuma murmushinta ya koma damuwa lokaci guda, tana faɗin