Cikin wannan rikici ne aka bar Amaar da tambayoyi...
★★★★★
A cikin wani wuri mai zurfin ruwa, inda rana ba ta taɓuka komai, kuma iska ba ta motsawa, Tasleem na zaune cikin wani irin ɗakin tsafi wanda aka gina shi da ruwan tsafi masu hasken shuɗi da kore. Hannayenta da kafafunta an daure su da sarkoki na sihiri waɗanda ke hana ta motsi da karfi. Kamar kullum, Madam Nablah ta shigo, cikin baƙar rigar tsafinta, tana murmushin mugunta.
"Kin ga yanzu kin dawo inda kika fara."
Cewar Madam Nablah tana ɗaukar wani ƙwarya.
Tasleem ta ƙafe ta da ido, cike da hawaye da ƙiyayya. Ta ce:
"Kina tunanin hakan zai hana su nemo ni? Amaar ba zai taba barina ba."
Madam Nablah tayi dariya sannan ta ce:
"Amaar…? Shi da yake neman wata hanya ta ceton kansa da mahaifinsa? Ko Shaprees da ke cikin tarkon sihiri? Ko Asmeen da zuciyarta ke da sanyi kamar dusar ƙanƙara?"
Ta yi dariya sosai har ta durƙusa a gaban Tasleem ta ce:
"Dukansu ba za su gane inda kike ba… sai na kammala abin da na fara shekaru ashirin da suka wuce."
---
A gefe guda, Shaprees yana tsaye a gefe yana karanta wani litattafan sihiri da ya mallaka tun kafin ya shiga duhun Madam Nablah. Sai kuma Asmeen ta shigo, cikin mayafinta na gida, da kallo mai cike da damuwa.
Domin tinda Amaar ya sanar mata wasu abubuwa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, sannan tana neman ƙarin bayani a gurin Shaprees...
Ta ce:
"Na gaji da zama cikin wannan gida na sirri da ƙyale-ƙyale… Ka gaya min gaskiyar zuciyarka, Shaprees." Ta faɗa cikin ƙarfi.
Shaprees ya kalle ta, ido cikin ido ya ce:
"Zuciyata... cike take da raunuka, Asmeen. Amma na rasa yadda zan yaye su ba tare da na jawo miki ciwo ba."
Asmeen ta je kusa da shi ta ce:
"Idan gaskiyar ka ce… sai mu nemo mafita tare."
Ya kalli fuskarta da ta cika da karfin hali ya ce:
"Kin cancanci gaskiya… Amma ki shirya da abin da zaki ji. Domin akwai sirrin da na ɓoye—wanda zai iya karya zuciyar ki."
---
Amaar yana zaune a ƙaramin lambu shi da Abul domin baya son barinsa shi kaɗai especially yanzu da Madam Nablah ta dawo... Abul yana jan carbi, shi kuma Amaar Zuciyarsa na can, a cikin ruwan duhu, yana ƙiran sunan Tasleem a zuciyarsa....
"Idan har zuciyar mutum biyu sun haɗu cikin gaskiya," in ji Abul ya ce:
"ko sihiri ba zai iya raba su ba. Amma sai zuciyarka ta zama daurarriya da gaskiya da himma."..
Amaar ya ɗaga kai, yana kallon rana da ke fitowa daga bayan gajimare. Wani sabon haske ya haskaka fuskarsa.
Ya ce:
"Zan nemi Tasleem ko da yaushe, ko da me zai biyo baya.....Auren zuciya ba ya mutuwa, Soyayya ta gaskiya sai da sadaukarwa.”...
Har suka ƙarashi zaman su a lambu suka tashi, don komawa cikin ɗakin su...
A koda yaushe Madam Nablah idonta akan Abul amma sai dai Amaar ya kasa barin yanda Abul yake, kamar wanda yasan ana harin sa....
Amaar ya zamo mai gadi baya bacci kullum, ga damuwar da ya sako shi a gaba, yana so ya motsa don neman ƴan uwansa amma yana fargaban barin Abul...
A Daren yau kamar kullum zuciyar Amaar ba ta da natsuwa kwata-kwata. Yana kwance kusa da mahaifinsa, wanda yanzu ya fara murmurewa daga dogon jinyar da ya shafe shekaru a ciki. Idanun Amaar sun kasa rufuwa, kalmar "Tasleem" ce kawai ke yawo a zuciyarsa kamar sautin kiɗan da ke ƙara karfi a kunne...
Yana maganar zuci:
"Me yasa kika tafi haka, Tasleem? Ina kike?" ya furta ƙasa-ƙasa, yana ƙoƙarin hana hawaye zubo masa. Bai san me yasa zuciyarsa ke masa kamar tana numfasawa da nata numfashi ba, kamar zuciyarsa da ta Tasleem sun zamo guda....
Ga damuwar rashin Abeesh duk suna cikin zuciyarsa..
Nasreen kuwa an sanar cewa ta mutu amma basu ga gawarta ba hakan yana ɗaure masa kai......
*💋HASKEN RUHI💋*
*🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀*
It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person.
*WhatsApp 09065443871*
*🌹 ASMEETAH WRITER 🌹*
*BOOK TWO__________PAID_____₦300*
Page 7 to 8
Nasreen tana zaune a gefen tekun da ke zagayen. Ruwan yana ɗan juyawa, rana na faduwa daga nesa. Gidan ruwa da Miemie ta gina mata yana nan cikin nutsuwa, duk da a zurfin ruwa ne amma ba danshi a jikinta, ba sanyi, ba tsoro, sai annuri.
Miemie tana tsaye daga nesa tana kallon ta. Ita kaɗai ce ta san hakikanin abin da ke faruwa a gidan Madam Nablah, kuma har yanzu bata ce uffan ba.
Miemie a zuciyarta take faɗin:
“Zuciyar Amaar na ƙirana kullum, zuciyar Tasleem tana kukan gajiya da tsaro, zuciyar Abeesh na nadama da kasancewa da baƙar Aljana. Amma wannan faɗan na yara ne…”
Nasreen ta lumshe ido. Ta yanke shawara: bazata dawo ba. A ganinta, komai ya ƙare kuma ta fi samun kwanciyar hankali da Miemie....
★★★★★
Amaar ya tashi daga shimfiɗar da yake a cikin ɗakin yana kallon mahaifinsu da ke numfashi cikin daidaito, amma duk da haka ba ya jin daɗin gidan da yake cike da duhun sirri, da numfashin damuwa, ya zame masa barazana. Daga kowane bango sai ya ji kamar murya ce na Tasleem tana kiransa cikin rauni, tana kiran sunansa a hankali.
Ya fita waje don samun iska, amma iska ma kamar ta ƙi karɓar shi. A hankali ya zauna bisa dutsen ƙasa kusa da wani tsohon itace yana kiran sunan da zuciyarsa ke bugawa da shi.
"Tasleem... Ina kika je? Kalli zuciyata yanzu, ta rame, ta yi ɗumi kamar asubar da ba ta da rana."
---
A can cikin wani wuri mai zurfi, ƙarƙashin ruwan sihiri wanda babu rana, babu wata, Tasleem ta buɗe idanuwanta cikin rauni. Tana kokarin tuna yanda aka kawo ta nan, amma tunaninta yana ba ta sarkakiya. A kusa da ita, wata tsohuwar ƙugiya ce ta rufe ƙofar kogon ruwan. Wani murya a cikin ranta ke faɗa mata:
"Ki dage, ki nemi mafita, saboda soyayya da kauna na gaskiya ba ta mutuwa cikin wahala."
Tasleem ta kwanta, hawaye na zubo mata. Amma zuciyarta bata yarda da duhu ba. Ta san cewa akwai wanda ke nemanta, wanda zuciyarsa zata iya bugawa da nata...
A hankali ta furta
"Ya Amaar, ka bar ni ne, ko kuwa?..." ta furta a ƙasan murya, kamar numfashinta ya ɗauke da bege.
___________________★★★
A gefe guda, Madam Nablah ta na satar kallon ruwan sihiri da ke ɗakin sihirinta. Tana murmushi a hankali tana kallon Tasleem da ke kwance cikin wancan wurin sirri.
Cikin izzah ta furta
"Kin ga yadda nake tafiyar da al’amura ko? Babu wanda zai iya gano yanda kike. Kuma kafin komai ya bayyana, zan mallaki zuciyoyin da nake buƙata.....Ba wanda zai iya shigowa, balle ya cece ki... Sai ni kadai,"
ta faɗa cikin dariyar mugunta.
"Amaar da zuciyarsa mai tsarki, ba zai taɓa gane ina ba. Kuma kafin ya gane, zan canza tafiyar duniyar nan gaba ɗaya."
Washegari, garin ya farka cikin sabuwar rana, amma zuciyar Amaar tana ci gaba da ɗauke da rana. Ya zauna kusa da mahaifinsa yana kallon fuskar tsohon cikin kwanciyar hankali.
Ya ce,:
"Abul..." Amaar ya furta cikin murya mai taushi. "Shekaru ashirin da suka gabata, ban san kana raye ba. Amma yanzu da na sanka, sai zuciyata ke so ta bayyana komai. Amma me zai faru idan sirrin nan ya ɓalle gaba ɗaya?"
Abul bai ce komai ba, sai ya ɗaga hannu a hankali, kamar yana so ya taɓa fuskarsa. Amaar ya kama hannunsa, yana jin wani sanyi mai kama da ta'aziyya ya lullube shi. Kamar hannun mahaifi yana ƙarfafa masa zuciya:
"Ka nemi abinda ya ɓace... Ka cece ta kafin dare ya mamaye komai, domin ita ɗin Hasken ruhi ce..."
Amaar ya lumshe idanuwansa yana faɗin:
"Na rantse da mahalicci na, albarkacin soyayyar mu... Zan same ki Tasleem. Ko da kuwa zan faɗa cikin ruwan da ba mai tsira."
Bayan kwana biyu....
Falon Madam Nablah ya ƙayatu da fitilun kristal masu walƙiya, kowane lungu da saƙo ya sha ado kamar ana shirin babban taro. Amma ba shagali ake ba—damuwa da shiru sun mamaye zuciyoyin kowa...
Ana Alhinin rashin ƴan uwa wato Tasleem da Abeesh da Nasreen har yanzu ba a samu labarinsu...
Amaar yana zaune da Shaprees da Asmeen a gefe guda, Abul kuma yana room ɗin sa, suna zaune cikin yanayi na ɓacin rai. Madam Nablah dai tana ta danna wayarta kamar wacce bata damu da damuwar duniya ba...
Kafin kowa ya iya sake numfashi, ƙofar babban falon ta buɗe da ƙara mai ɗaukar hankali. Kamar walkiya, wata haske mai launin ruwan sanyi ya lullube wajen na ɗan lokaci kafin ta bayyana...
Gaba ɗaya suka ɗago kansu, suka sauƙe idanunsu kan wata kyakkyawar halitta da babu kamarta.
Matar da ta shigo kyakkyawa ce tamkar ba a duniya ba, tana sanye da doguwar riga mai ƙirar gold, Sumarta doguwa ce kamar siliki tana lanƙwashe har gadon bayanta. Fuskar ta tsab ce, kamar ba'a taɓa samun ɓacin rai a rayuwarta ba. Idanunta shuɗa ne, amma suna da wata annuri da ke jan zuciya. Kamar ruwan rafi ne mai rai....
Amaar ya miƙe tsaye nan da nan. zuciyarsa ta ɗauki bugun farin ciki. A hankali, kamar yana magana da kansa ya furta:
"Miemie..."
Madam Nablah ta ɗago kai cikin tsoro. Ba kowa bace wannan da ta shigo—ita ce MIEMIE, Sarauniyar Ruwan Aljanu. Halitta mai iko da daraja a tsakanin makaman tsafi da haske. Miemie ta zauna cikin tsayin daka, tana kallon kowa cikin salama da iko.
Cikin izzah take faɗin:
"Lokaci ya yi da gaskiya za ta fara tunkarar haske,"
ta ce da murya mai laushi da raɗaɗi, kamar ana karanta waƙa a cikin ruwa.
Shaprees ya gyaɗa kai a hankali, zuciyarsa na bugawa. Ya san wannan ba ƙaramin abu bane. Idan Miemie ta bayyana, to kuwa akwai gagarumin sauyi da zai zo. Madam Nablah kuwa ta ɓoye damuwarta tana ƙoƙarin murmushi, amma Miemie ta hango ƙiyayyar da take ƙoƙarin ɓoye wa.
Miemie ta ce:
"Nazo ne domin sauƙe nauyin da nake da shi tun shekaru ashirin da suka wuce... lokacin da aka jefa ƙaramin yaro cikin ruwan halakar tsafi, na ceci shi, na bashi kariya da haske. Wanda nake magana akai, shi ne... AMAAAR."
Wata guguwa ta tashi a cikin zuciyoyin ɗakin. Kowa ya kalli Amaar, wanda yanzu yana fuskantar Miemie da idanu masu cike da alhini da tambayoyi. Miemie ta cigaba da magana:
"Kuma yanzu na dawo... domin tsare zuciyoyin da haske ya taɓa. Ku shirya, domin akwai sirrin da zai girgiza kowa nan ba da jimawa ba."
Wani irin sanyi mai daɗi ya bayyana cikin ɗakin lokacin da Miemie ta kammala maganarta. Kamar ana busa iska mai ƙamshi daga rafin aljanna, aka ji zuciya na kokuwa da ƙalubale da kuma tsoro.
Amaar ya matso kusa da ita a hankali, idanunsa cike da tambayoyi. A yau ne ya sake ganinta a zahiri bayan shekaru masu tsawo da suka gabata, lokacin da yake ƙaramin yaro, yana cikin hadarin nutsewa cikin ruwan tsafi da Madam Nablah ta jefa shi. Sai Miemie ta bayyana wancan lokacin — kamar haske cikin duhu — ta fitar da shi, ta rufe shi da sihiri mai tsabta, wanda har yanzu ke yawo a jikinsa, duk da ba shi da cikakken sani akan hakan, amma tana yawan zuwa masa a cikin mafarki...
A hankali ya furta:
"Kina da labarin komai... kin san wacece Tasleem? Kin san inda take? sannan ƙanina Abeesh shima kin san a yanda yake? shin da gaske ke Nasreen ta mutu?...."
Amaar ya tambaya da murya mai nauyin kewa.
Miemie ta dubi kowane fuska kafin ta ce,
"Duk da ikon da nake da shi a cikin ruwa da haske, ba zan iya nuna maku inda aka ɓoye Tasleem ba. Wannan sirrin na cikin zurfin duhu ne da aka ƙarfafa da jinin zuciya. Sannan Abeesh shima yana wani duniyar da banida ikon zuwa wurin Amma zan iya taimaka maku ku ji hanyarsu idan kun tsaftace zukatanku, kuma ku jure gaskiyar da zata bayyana."
A wannan lokacin ne zuciyar Madam Nablah ta fara karaya. Ta san cewa idan Miemie ta shiga cikin lamarin, ba ruwanta da tsafi ko dabara. Tana ƙoƙarin ɓoye fargaba ne, amma idon Miemie — waɗanda suka fi ruwa tsarki — sun riga sun karanto dukan damuwar da ke ɓoye a zuciyarta.
Madam Nablah ta ce:
"Kin iso ne saboda Amaar? Ko akwai wata manufa?"
Ta tambaya tana ƙoƙarin nuna ƙwarewa da sarauta....
Miemie ta ƙaraso kusa da ita, ta dubeta cikin idanunta masu ƙasaita ta ce:
"Kin shafe shekaru da dama kina amfani da duka ikon da aka baku don girbe fansa da iko, amma kin manta... da tsarkin zuciya ake buɗe ƙofofin aljanna. Kuma idan zuciya ta ƙafe da ƙiyayya — to ruwan tsarki ba zai iya wanke ta ba."
Sai ta waiwaya gun Shaprees, wanda tuni zuciyarsa ta fara kaɗawa.
Ta ce da shi
"Ka kasance kana da zaɓi: ko ka zaɓi bin gaskiya da haske, ko ka cigaba da ɓoye kanka a cikin ruwan duhu. Amma ka sani, ba za ka iya fansar matar da ka rasa ba ta hanyar cutar da wata ba."
Shaprees ya sauƙe numfashi, ya kau da kai. Kalaman Miemie sun taɓa jikin sa fiye da yanda ya zata.
A hankali ya ɗago yana kallonta— yana mamakin yanda wannan kyakkyawar halitta ke tafiya da ikon da ba mutum ke da shi ba, kuma bai taba ganin kowa yana karantar zuciya kamar yadda take ba.
MIEMIE ta matso kusa da Amaar, ta ce a hankali:
"Zan taimaka maka neman Tasleem. Komai zai iya faruwa, amma ina jin zuciyarka na ƙiranta da gaskiya. Kuma nasan duk inda take... tana fatan sake ganin ka."
Miemie ta sake juyo wa ta dube su duka, sannan ta ce da murya mai ƙarfi:
"Na bar haske a cikin ɗaya daga cikinku... wanda zai iya bayyana mafita daga duhun da Madam Nablah ta lulluɓe. Lokaci na kusa. Amma har yanzu akwai sirri mai girgiza zuciya da bai bayyana ba."
Idanunta sun ɗan tsaya kan Amaar, ta ce:
"Ka tuna hasken da ke cikinka, Amaar... shine zai tsine duhun dake kewayen zuciyarka. Kuma shine zai bayyana Tasleem."
Asmeen kallon Mahaifiyarta kawai take, ganin ko wani magana idan ya taso akanta za'ayi...
Madam Nablah, duk da tana ƙoƙarin nunawa kamar bata damu ba, amma jikinta yana rawa. Tana tsoron su sauka can inda ta ɓoye gaskiya da tarihi, inda ta adana wani sirri da zai iya rushe komai da ta gina tsawon shekaru ashirin.
Zuciya cike da mamaki da firgici kowa ya kasa motsi a cikin falon. Bayyanar Miemie ta zame musu tamkar mafarki. Amma ga Amaar, tamkar wani kaho ne aka buga masa — kaho na kiran tarihi, na farkon rayuwarsa. Wata irin sanyi da haske ya lullube zuciyarsa yayin da yake kallon Miemie...
Madam Nablah kuwa ta ƙafe Miemie da ido kamar yadda maciji ke kallon kwallon wuta. Tana jin wani iska mai sanyi yana ratsa ta, alamar cewa karfin da Miemie ke da shi yana cikin nau’in da ke rushe dukkanin duhun tsafi.
Sai kawai Miemie ta furta da muryarta mai taushi da ƙarfi,
“Lokaci ya yi.”
“Lokaci na me?” inji Madam Nablah, tana ƙoƙarin ɗaga ƙirjinta da kangararta kamar yadda take yi a duk lokacin da take son rufe laifinta da iko.
“Lokacin da gaskiya zata fara bayyana, ko da kuwa an binne ta cikin dutse tsawon shekaru.” Miemie ta ɗaga hannunta sama, sai wata iska ta kaɗa labulen falo, fitilu suka ɗan yi rawar jiki alamar wani abu mai girma yana gab da faruwa.
Amaar, wanda yake ta kallo yana ci gaba da tuna wani abu daga rayuwarsa — ya tuna da ruwan da aka jefa shi a ciki lokacin yana yaro, ya tuna da hannun da ya zame shi daga halaka, ya tuna da muryar da ta ce masa “Zaka girma, zaka fuskanci duhu, amma ka kasance da haske.”
Sai kawai ya furta, “Ke ce kika ceci rayuwata, ina matuƙar Alfahari dake…”
Miemie ta gyada kai cikin murmushi. Sai ta juya ido zuwa ga Madam Nablah, sannan ta ce:
“Na zo ne domin janye garkuwar duhu daga zuciyar ‘ya’yanki kafin abin ya kai ga wuce gona da iri.”
Sai ta juya zuwa wani ɓangaren falon. Ta danna kafarta ƙasa sau uku, sai wani ginin ƙasa ya buɗe a hankali. Duk suka zuba ido.
Akwati ne _ akwatin gawa mai ɗauke da tambarin tsafi da dutsen haske a jikin murfin sa. Kowa yayi shiru.
Miemie ta ce:
“ Madam Nablah... kin ajiye gawar mijinki shekaru da dama amma ki sani ruhi ba zai bar duniya ba, saboda tsafin da kika tofa masa kafin ki kashe shi.”
Asmeen ta rausa ihu daga gefe, zuciyarta na harbawa. Ta ce:
“Mahaifinmu? Ashe da gaske ne kina da ikon kashe shi?”
Madam Nablah ta juya da hargowa. Tana faɗin:
“Na yi hakan domin ikon da nake nema! Ku da kuke nan da babu shi, babu ni!”
Amaar ya ƙureta da ido. Shaprees ya ƙafe ta da kallon da babu wanda zai fassara...
Miemie ta durƙusa ta shafi akwatin — wani haske ya fito daga cikinsa...
Mahaifin su... yana nan, gawarsa na kwance a cikin akwatin...
Gaba ɗaya zaman falon ya koma shiru. Kamar an danna abin dakatar da lokaci, kowa na kallon akwatin gawar da Miemie ta bayyana. Haske yana ci gaba da fita daga cikin akwatin, yana fizgar zuciyoyi da nau’in sanyi wanda babu wanda ya taɓa ji.
“Wannan shi ne mijinki, Madam Nablah. Wanda kika daɗe kina ɗauke da gawarsa don ki rufe laifinki. Amma ruhi ba ya mutuwa, musamman idan aka kashe shi da zalunci,”
Miemie ta faɗi tana kallon Madam Nablah da idanuwanta masu zurfin gaskiya.
Madam Nablah ta miƙe tsaye da sauri tana faɗin:
“Ba laifi bane idan domin iko ne!” ta hargitse da murya tana kallon kowa da wani irin kallon hauka...
“daman da gaske ke kika kashe mahaifinmu?” Asmeen ta furta da kuka murya na kakkarwa domin abun ya tsaya mata a rai, ta nufi akwatin da zafin zuciya tana fadin: “Kin ɓoye wannan shekara da shekaru, kin hana mu jin ƙaunar uba..”
Shaprees ya ja baya a hankali. Ya riga ya san cewa Madam Nablah ba mace ce da za a yarda da ita ba, amma ya kasa tsammanin za ta aikata haka a mijinta, uban ‘ya’yanta!