x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 205

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
aiki kuwa kallo suka bi su da shi, ganin mutane biyu masu kammani kuma halayensu ba irin na wancan ba, anan suka yi tunanin ko ƴan uku ne domin kamannin ya ɓaci...

Kwantar da Amaar suka yi akan gadon sa har ya suma sakamakon jinin da ya zubar, kuma wurin da aka harbe shi wuri ne mai hatsarin gaske duk da ba'a wurin saitin zuciyar sa aka harbe shi ba, a ruɗe Nasreen ta riƙo hannun Abeesh tana kuka ta ce "Ya Abeesh ya ƙi a kai shi hospital sannan ya ce kar a kawo masa ko wani doctor, shin haka zamu zuba masa ido ya mutu?..."

Asmeen ta ce "dan Allah mu ceci rayuwar sa, kun ga idan ya mutu fa dole sai an kama Tasleem, kuma prison za'a kaita..."

Nasreen ta ce "idan aka kaita prison ma ita ta jawo tinda bata da hankali, ciwon hauka ke damun ta, girman kanta da baƙar zuciyar ta zai jawo mata komai, ni yanzu damuwa ta shine naga mun taimaki Ɗan uwa, nayi matuƙar tausaya masa a halin da yake ciki, yana son bayar da rayuwar sa saboda Tasleem amma ita kuma mai banzar zuciya, ina jin haushin ta sosai akan irin waɗannan abubuwan da take aikata wa ba tinani da lissafi...."

Nasreen zama tayi a bakin gado tana sharar kuka..

Asmeen zama tayi a kusa da ita tare da da fa kafaɗarta tana faɗin "Nasreen ki daina kuka dan Allah, ita ɗin ƴar uwar mu ce ba yanda zamu yi da ita sai dai mu tayata da addu'a, dole ita ɗin ta mu ce..."

Abeesh dake tsaye ya rasa abun cewa sai sauƙar da numfashi ya yi tare da faɗin "yanzu ya zamu yi da shi?..."

A zabure Nasreen ta miƙe tare da faɗin "yawwa Ya Abeesh kai doctor ne dan Allah please ka yi masa magani..."

Abeesh girgiza kai ya yi yana faɗin "no bazai yu ba saboda doka ce a taɓa majinyaci irin wannan ba tare da sa hannu a takarda ba, dole sai ƴan uwansa sun yi signing tukun..."

Nasreen sake baki tayi tana kallon sa cike da mamaki ta ce "Ya Abeesh wani irin magana kake yi haka? shin baza ka iya taimaka wa ɗan uwanka Musulmi ba idan yana cikin mawuyancin hali irin haka ba?..."

Abeesh ya ce "no ki gane mana, idan ana so nayi masa aikin nan dole sai an kai shi hospital, saboda bamu san halin rayuwa ba, wata ƙil zai iya mutuwa a hannu na kinga dole za'a kama ni, wannan aikin yana da hatsari sosai...."

Asmeen ce tayi saurin riƙo hannun Nasreen tana nuna mata Amaar,
a tsorace duk suka zazzaro ido waje suna kallon yanda Amaar yake ta amar jini, jini ne yake ta ambaliya daga bakin sa gaba ɗaya ya fita hayyacin sa, duk nufan yanda yake suka yi da gudu, basu san lokacin da suka haura saman gadon sa ba, abinda suka ji yana furta wa shine "Tasleem! Tasleem!! Tasleem ina ina ƙaunar ki, meyasa kika manta Amaar ɗinki? ni ni nine fa, ni ne fa Amaar ɗin ki, meyasa zaki manta da ni, shin kin manta alƙawarin da muka yi na cewa baza mu taɓa rabuwa ba ne? Tasleem momynki bata ƙauna ta dan Allah kar ki zama kalar ta, mommin ki ta tsane ni kema so kike ki tsane ni?...."

Nasreen da Asmeen kallon juna suka yi cike da mamaki, baki a haɗe suka furta "Amaar...."

Shi kam Abeesh tinda ya ƙafe a wuri ɗaya bai ƙara motsawa ba jin sunan da yake ambata, jin sunan da yake muradin sake ji a cikin kunnuwan sa, tin yana yaro ya rubuta sunan a tafin hannunsa har yau tabon sunan bai shafe ba....

Amaar cigaba da surutan sa yake yana faɗin "Tasleem ki tuna fa mommin ki ita ce ta raba ni da kowa, ta raba ni da mahaifina sannan ta raba ni da ƙanina Abeesh, ta kuma raba ni da ke tin yarinta, meyasa baza ki tuna ba? Tasleem! Tasleem ki taimaki rayuwata, na rayu ne saboda ke Tasleem, kuma zan mutu saboda keeee...."

Aman jinin ne ya ƙaru, yana shure-shure....


Nasreen cikin ɗaga murya ta furta "Ya Abeesh taimakooooo..."

Abeesh shima bai san lokacin da ya hautsina ba haka ya fara dube-dube yana neman abinda zai taimaka masa wurin cire bullet, ita ma Asmeen dake ta karanci fannin likitanci haka ta fara danne masa ƙirji tare da hura masa iskar bakin ta duk da aman jinin da yake,
Ita kuwa Nasreen ta gagara tsayuwa bare zama sai zarya take tayi a ɗakin, ta rasa wani gudunmawa zata bayar wurin sa ma wa Amaar lafiya dake ita ɓangaren lawyer ta karanta......



NEXTT NEXTTTT


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


25 to 26




Amaar na ta aman jini yana surutai cikin fitar hayyaci, Idanunsa sun cika da hawaye, amma ba zai iya fadin kalma daya cikakke ba sai ambaton sunan Tasleem... "Tasleem... don Allah kar ki bar ni... ki dawo..."

Abeesh yana ƙoƙarin cire bullet ɗin da ke cikin ƙirjin Amaar. Hannunsa na rawa saboda jinin da ke ci gaba da fita yana ƙoƙarin dannewa da towel, amma lamarin ya fi karfinsa. Idanunsa suka ciko da hawaye, yana kallon Amaar ya rasa abinda zai yi sakamakon rashin kayan aiki.

Asmeen da Nasreen suna tsaye gefe, jikin su rawa. Nasreen ta rike hannun Asmeen tana karanta ayoyi cikin sanyin murya, amma zuciyarta na kukan "kar Amaar ya mutu".

Asmeen kuwa ta kasa daukar numfashi daidai, zuciyarta kamar zata fasa kirjinta saboda tsananin tsoro da damuwa.

“Za mu rasa shi idan muka tsaya haka!” Abeesh ne ya furta haka yana duban Nasreen

“Ina kayan taimakon gaggawa? Ina kayan dinki?”

Asmeen ta zabura kamar wadda aka tsawatawa, ta juya cikin sauri da gudu zuwa cikin gida domin kawo akwatin taimako. Abeesh ya matsa kusa yana kokarin danne raunin tare da cewa,

“Ya Amaar! Ji ni! Ka rike numfashinka, Ka tuna da Tasleem, Ka tuna cewa zata dawo gareka...”

Cikin wahala Amaar ya daure fuskarsa, sannan cikin lafazi mai rauni ya ce, “Ina... Tasleem... nace... kar ku ce mata... na mutu... nace... na... na ƙa...”

Sai kuma numfashinsa ya tsaya na dan wani lokaci.
Abeesh cikin firgici ya fara jijjiga shi. “Ya Amaar! Kar ka bar mu! Na ce za ta dawo gareka...”

A dai-dai lokacin ne Asmeen ta dawo da akwatin taimako, tana kuka tana cewa, “Na kawo... na kawo!”


Amaar yana kwance cikin rashin hayyaci, amma zuciyarsa na yawo cikin duhu da hasken rayuwar da ya shuɗe. Cikin doguwar suma yake motsa lips, sai murya tasa ta soma fita a hankali, kalmomin da suka zo kamar mafarki..

“Wannan... duk laifin Mommyn ki ce... mahaifiyar ki Tasleem ta rabani da komai... ta ce bana da amfani... ta yi amfani da ƙarfin tsafi... ta jefani cikin ƙunci...”

Abeesh ya daina motsi. Hannunsa ya tsaya saman bandejin da yake shirin manne wa. Ya kalli Nasreen da Asmeen cikin firgici ya ce “Me yake faɗa?”

Asmeen ta matso kusa da Amaar, idanunta na cike da hawaye ta ce “Kamar dai yana magana ne akan rayuwarsa...”

Amaar ya ci gaba da surutan sa, jikinsa na karkarwa, kalmomin na fita ba tare da saninsa ba.

“Tasleem... nace ki taimake ni amma ki ka bari mahaifiyarki ta raba ni da ke, ta ce banida wani amfani sai ta jefani cikin ramin ruwa cikin duhu... shekaru ashirin... ashirin...”

Abeesh ya runtse ido. Idanunsa sun cika da hawaye, zuciyarsa na harbawa kamar zai fasa ƙirjinsa. “Ashe shi ne? Ashe wannan shi ne Ya Amaar ɗinmu?”

Nasreen ta dafe baki. “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un,wannan mutumin da Tasleem ta harba shine Ya Amaar?”

Asmeen ta fashe da kuka. “Tasleem zata hallaka kanta idan ta gano gaskiyar nan... Allah ya taimake mu!”

Sai lokacin Amaar ya soma motsi, yana buɗe idanunsa a hankali, dake yanzu an tsayar da jinin da yake zuba. Abeesh ya sunkuya da sauri, yana dafa goshin sa.

“Ya Amaar... kai ne? Kai ne ɗan uwana? Ka gane ni?”

Amaar ya zuba masa ido, a hankali ya gyaɗa kansa. “Na gane ka... tun ranar farko da na ganka... Abeesh... ƙanina...”

Dukkan su suka durƙusa suna kuka. Nasreen ta tsaya gefe tana kallon Amaar, zuciyarta na bugawa da damuwa. “Ya zamu faɗa wa Tasleem? cewa ta harbi Amaar da hannunta. Ta ɗauke shi abokin gaba ba ta san cewa soyayyarta ce ta yarinta ba.”

Asmeen ta matso kusa. “Ba zamu ce mata komai yanzu ba. Sai mun tabbatar da cewa Amaar ya samu lafiya.”

Sai kuma Abeesh ya ɗaga kansa ya ce da ƙarfin zuciya, “Zan bi mahaifiyarku
sai na fallasa asirinta. Wannan ƙaryar dafin shekaru ashirin, yanzu ya kamata ta kare.”



Tasleem na zaune gefen gado tana kuka. Ta kasa kwantar da zuciyarta. Duk da ƙiyayyar da take nuna wa Amaar, zuciyarta na tsananin bugawa tun lokacin da ta harbe shi.

“Me yasa nake jin kamar... kamar na rasa wani muhimmi abu a raina?” Ta dafa kirjinta tana kallon hoto da take ajiye tun tana yarinya — hoto nata da wani yaro da ta manta sunansa.

Ba ta san cewa amaar ne ba...



A cikin wani daki mai baƙin duhu kamar bakar dare, wurin da ko iska ba ta motsawa sai hayakin da ke tashi yana lanƙwashe sararin sama, can ne Madam Nablah take tsugunne, gefen wani ƙaton kwanon tsafi da ke tashi da wuta mai launin jajaye da kore-kore.

Hayaki yana fito da irin ƙamshin da zai iya durƙusar da mai ƙarfin zuciya. Bangon ɗakin yana da rubuce-rubuce na asiri da zane-zane na tsafi – wasu kaman jinin mutane, wasu kaman rubuce-rubucen bakaken aljanu.

A gaban ta wani mutum ya bayyana – Zulqarnain, ƙaton saƙagon tsafi, wanda ba mutum ba ne cikakke, ba kuma aljani ba ne cikakke. Gaba ɗaya siffar sa na bada tsoro, jiki mai ƙiba baƙi kamar gawayi, idanunsa jajaye da ke walƙiya kamar wutar lantarki. Wani irin zafi da ɗumama ke tashi daga jikinsa.

Ya zauna cikin murhun da wuta ke ci, wutar ba ta cutar da shi ita ce ƙarfin sa.

Madam Nablah ta sunkuya, tana rarrafawa zuwa gareshi, ta durƙusa ta saki murya mai ƙarfi, kamar ba daga cikin halittu ba


"ZULQARNAIN, UBA NA TSAFI! UBA NA IKO! KAI NE MAI SARRAFAR RAI, KAI NE MAI JUYAR DA DAKKA!
Na zo... na zo neman ƙarfin da zai murƙushe wanda ya dawo daga matattu! Na zo neman ƙarfin da zai karya zuciyar Tasleem domin ta manta da ruhi... ta manta da soyayya... ta manta da gaskiya...!”



Idanunta a rufe, tafin hannayenta na ɓullo da wuta, wata wuta mai launin shudi, ba kamar kowace ba. Wutar zuciya da tsafi ne, tana ƙuna da sanyi amma tana ƙone zuciya.

Zulqarnain ya saki dariya mai amo irin na halittu na ban tsoro, Muryar tasa ta cika ko’ina

“Kin sha wahala Nablah, amma kika rasa ƙarfin zuciya. Amaar ya dawo – ruhi da haske sun motsa. Kin bar kofar zuciyarsa a buɗe.
Don haka... zan ƙara miki iko. Amma ki sani... da wannan ƙarfin sai dai ki sadaukar da ɗaya daga cikin ƴaƴanki guda uku!**”



Madam Nablah ta bude idanu da sauri tare da faɗin “A’a! Kar ka… kar ka ɗauki Nasreen! Kar ka ɗauki Asmeen! Tasleem ma... tana da amfani...”

Zulqarnain ya girgiza da ƙarfi. Wata wuta ta buge bango, ƙasa ta girgiza. “Ɗaya sai an sadaukar! Ko kuwa… ki rasa komai!”

Madam Nablah ta dafa kanta, jikinta na karkarwa. Wata zuciyar mugunta ta fara ratsa ta. Ta tuna da Amaar – wanda take tsoron dawowar sa. Tana jin wani abu na karfi yana yawo a cikin jijiyoyin ta. Wutar da ke hannunta ta kara ƙaruwa.

"Na amince... zan sadaukar... amma ku ba ni ƙarfin da zai sa Amaar ya sake ɓacewa har abada!”

A cewar Madam Nablah!

A wannan lokacin, wasu bakaken aljanu suka fito daga cikin wutar, suka nutse cikin zuciyar ta. Hannunta ne suka ƙara kyarma, idonta sun koma fari. A wannan rana… Madam Nablah ta zama abin da ba za a iya ɗauka da wasa ba.



ƁANGAREN TASLEEM…

Tana ta hawaye, ta dafe ƙirji kamar zuciyarta na wani irin tsalle. A zuciyarta, tambayoyi na ci gaba da bubbuga kamar ƙaho,

“Me yake faruwa dani? Waye wanda na harba? Waye shi da zuciyata ke motsawa idan na ganshi? Me yasa hannunsa ke yi min shocking idan ya taɓa ni? Na kashe shi ne…? Ko yana raye?”



A take ta miƙe kamar an zaro ta, zuciyarta na harbawa da ƙarfin da ta kasa iya jurewa. Ta nufi ƙofar ɗakin da take, tana bin dogon hallway har ta sauko falon gidan da ƙafa.

Ƙafarta na taka tiles ɗin falon — hayaki ya tirniƙe idonta

“Inna lillahi...! Me ke faruwa?”



Falon ya cika da hayaƙi mai ƙamshi irin na tsafi — ba turare bane, ba hayaƙin gas bane — hayaƙin mugunta ne. Ba kowa a gidan. Nasreen da Asmeen suna can wajen Amaar suna kula da shi, Ita kaɗai ce.

Tana kokarin juyawa zata koma bedroom ɗinsu cikin gaggawa,
sai taji wata dariya mai firgitarwa kamar daga sama. Duhu ya fara lullube hasken rana kamar dare ya sauka. Idonta ya ɗauki duhu.

Kyaaaaah!!!

Kamar a mafarki, robot-robot guda biyar waɗanda Madam Nablah ta ce masu aiki ne suka bayyana daga duhu. ba na’ura ba ne — aljanu ne a cikin siffar robot.

Dukansu biyar ne suka fara rawa da dariya, suna motsa hannaye da ƙafafu, suna tashi sama kamar masu fikafikai.

“Ina zaki je, Tasleem? Ina zakiii...? Gaya mana... Gaya mana!!”



Idanunsu ne suka fara walƙiya da wuta kamar bulalai. Murya kamar daga ƙasa ta fito, mai amo da cike da mugunta.

Tasleem ta saki wani irin ihu — ihu na ruɗewa da tsoro. Sai ta juya da gudu, ta nufi stairs ɗin da ke kaiwa sama. Amma kafin ta taka mataki na huɗu — ƙafarta ta dagu sama!

Ta hau tashi kamar iska kafin jikin ta ya faɗo da karfi, Ta ji kamar an juyo mata da duniya, amma duk da haka ta fara gangarowa ƙasi kamar tabarma ce ƙasa ke ja da ita, aljanun na ta bin ta da dariya da murya mai firgita

“Ki dawooo... ki dawo ki ganshi... ki dawo ki ga wanda kika kashe…!”



Hayakin ya fara shigowa hancinta, jiki na ta rawa. A daidai lokacin, ƙarar wani abu ya daki glass, ƙofar ɗakin sama da ke a buɗe ta buge da ƙarfi.

Wani irin murya mai launin jinƙai ya fara bayyana a zuciyar Tasleem, ba daga wajen aljanun ba

“Tasleem… ke kika harbe ni. Amma zuciyarki ta san ni. Cikin ki ya gane ni. Duhu baya hana haske zama gaskiya.”


Cikin tashin hankali
tayi firgigit!

Tayi gigin mikewa, tana jan jikinta — tana kallon wuta da duhu da dariya na shigowa ko’ina.

Sannu a hankali, tana fara gane zuciyarta ba komai ke dukan ta da tsoro ba — ruhin Amaar ne ke kiranta.

Zuciyarta na bugawa kamar za ta fasa ƙirji. Tana kukan ban tsoro da na rudani, amma kuma murya mai sanyi da zurfin jinƙai na ci gaba da tashi cikin zuciyarta

“Na tsaya a cikin duhu shekaru ashirin… Amma ke kika zama Hasken Ruhi na…”



Ta dafe ƙirji da hannu ɗaya, tana kukan da bata san menene ba. Ba kuka ne na jin tsoro kaɗai ba — kuka ne na wani abu mai ƙarfi a cikin jininta, wani abu da ke birkita mata tunani, yana motsa tsohuwar ƙauna da ta mantawa da shi.

Wata guguwa ce ta haura saman gidan, tagogine suka fara dukan juna da ƙarfi, duhun ya ƙara ƙamari, robot-aljanun nan guda biyar sun fara shigowa cikin hallway suna ɗauke da kayan sarƙa da karfe, suna faɗi

“Mu ne masu gadin zuciyarki… kuma ke ɗaya ce da za ta cika sadakin macen tsafi!”



Tasleem faɗuwa tayi da ƙarfi a gaban wata kujera, tana girgiza kai da karfi tana faɗin

“Ku daina… Ku daina shigowa raina! Ni ba macen tsafi bace! Ni ba zan zama rantsuwa ga muguwa ba…”



A daidai lokacin da daya daga cikin robot-aljanun ya nufi kanta da wata irin sanda mai walƙiya, wani haske mai matuƙar ƙarfi ne ya leƙo daga ƙofar gidan, hayaki ya watse gaba ɗaya, kuma dukkan aljanun sun tsaya cak kamar an tsayar da su!

Sai ta ji sautin murya daga bayan ƙofa ana furta

End Ads