ya ce "Ni ce rabin raina fatan kin wuni cikin so da ƙaunata..."
Zaro ido tayi tare da buɗe baki tana mamakin abinda ya furta..
Ayub ganin ƙaramin wushiryar haƙorin ta yasa shi toshe bakin sa da hannayensa biyu cike da jin kunya ya yi saurin sunkuyar da kan sa,
Aasmeen cikin dariya ta ce "Ayub ni fa ba...."
Yayi saurin taran maganar ta da cewa "eh eh na sa ni ke ba Nasreen ba ce domin naga wushiryar ki ita kuma bata da shi, amma tana ina ita ɗin?..."
Ta ce "i think tana library..."
Ya ce "okay Nagode sosai, ayi karatu lafiya..."
Jinjina kai tayi haɗe da sakin murmushi tana mamakin yanda Ayub yake mistake akan su har yanzu ya kasa banbance su.....
Ta gefe guda kuwa spirit ɗin Madam Nablah ce take tsaye da baƙaƙen kaya a jikin ta tana bin su Ayub da kallo, cikin fushi ta wurga kacar hannunta zuwa gare shi dake basu yi nisa sosai ba cikin ƙanƙanin lokaci kacar ta zari sawayensa sai da ya yi sama sosai kafin ya doku a ƙasi, kan sa ne ya yi wani irin mummunan buguwa akan wani ƙaton dutsen dake wurin, lokaci guda sai ga mutane sun nufo wurin wanda abokansa su ma basu san dalilin faɗuwar sa ba, kafin a ankara Madam Nablah ta zama guguwa ta yo kan Ayub dake kwance, nan ta rufe shi wanda ba'a iya ganinsa sai baƙin guguwa, a hankali Ayub yake ƙoƙarin buɗe idanuwansa ganin yana cikin ɓakin guguwa ga kan wata baƙar Aljana a sai tin fuskar sa tana furta "Tasleem! Nasreen!! Aasmeen!!!,
Tasleem, Nasreen, Aasmeen...."
Haka take ta maimaita wa, Ayub idanuwansa kamar zasu faɗo ƙasi tsabar tsoro da firgici ga hannayensa yanda ya toshe kunnuwansa da su saboda tsananin gigicewar muryar, Muryar har kasu wa bibbiyu suke ana ƙiran sunayen triplets, da haka har ya sume a wurin daga nan guguwar ta ɓace ɓatt...
Mutane kuwa har an taru kowa yana mamakin ganin abun al'ajabin nan duk da basu ji mai ake faɗi ba, su dai abinda suke iya gani shine ƙurar guguwar da ta ke wa ye shi,
Aasmeen itama tana wurin zuciyar ta ne yake wani irin bugawa kamar zai fasa ƙirjin ta, tsoron ta shine kar shima Ayub ya shiga halin da sauran suka shiga akan su,
tana cikin wannan tunanin sai ga motar Ambulance ta tafo cikin gaggawa, nan da nan aka ɗauki Ayub rai a hannun Allah aka wuce da shi hospital, ana tafiya da shi sai ga Nasreen ta tafo da gudun gaske jin labarin halin da Ayub ya shiga, tana zuwa ta nufi wurin Aasmeen tana faɗin "Meya faru da Ayub? yana ina?..."
Aasmeen tana kuka ta ce " nima ban sa ni ba yana shirin zuwa wurin ki daga nan ban sa ni ba..."
Suna cikin wannan tattaunawar sai suka ji an furta "wannan takardar fa?...."
Duk kowa ya maida hankalin sa kan mutumin da ya ɗauki wata takarda a wurin da aka ɗauki Ayub, mutumin buɗe wa ya yi cikin ɗaga murya ya fara karanta wa
"Tasleem! Nasreen!! Aasmeen!!! Whoever falls in love with them will die (duk wanda ya fara soyayya da su zai mutu) zai mutu! zai mutu!! zai mutu!!!..."
Cikin tsoro da fargaba kowa ya mai da kallon sa kan su, Nasreen da Aasmeen su na ƙarƙame da juna jikin su har rawa yake tsabar tsoro da firgici ga hawaye ya ƙi tsayuwa a idanuwan su,
Mutanen wurin kuwa tinin har wurin ya har gutse da hayaniya kowa da abinda yake faɗi ana ƙiran su da Mayu, zagi ta uwa uba haka ake musu wasu har sun tsigo bulalu zasu dake su, maza sun kai goma kowa da itacuwa a hannayen su wasu katako suka nufo yanda Nasreen da Aasmeen suke cikin zafin nama, Nasreen da Aasmeen rungumar junan su suka yi tare da sau wani irin gigitaccen ihu dai dai lokacin da matasan nan suka ɗago makaman su zasu kwaɗa musu sai ji suka yi an hankaɗa su gefe duk su biyun suka hautsina ƙasi, kafin Nasreen da Aasmeen su ɗago su ga wanda ya hankaɗa su har an rausa sanduna akan Tasleem wacce ta maye gurbin ƴan uwan natan, ihun Tasleem ne ya karaɗe ɗuk makarantar, Nasreen da Aasmeen ganin a Tasleem duk aka kwaɗa wa itacuwa yasa su ma suka fara ihu su na ƙiran sunan ta,
Tasleem lokaci guda ta faɗi sumammiya da gudu suka ƙarisa wurinta su na kuka, matasan nan har sun ƙara ɗago da makamansu zasu rausa wa sauran nan suka fara jin kukan Kura daga nesa nesa, hankalin kowa ne ya kar kata wurin da suke jin tafowar Kura, ganin wurin su ya nufo yasa kowa ya fara guduwa maza da mata kowa ta kan sa yake, masu sanduna duk jefarwa suka yi kowa ya kama gaban sa, sai Tasleem wacce take sheme a wurin da Nasreen da Aasmeen kuma su na zazzaune a wurinta su na ta jijjiga ta akan ta tashi amma ko motsi babu, iya su kaɗai aka bari a filin makarantar duk kowa ya shiga ajijjiwa sun rurrufe ko ina, wasu har murna suke Kura zai hallaka su domin su annoba ne a cikin makarantar a cewar sauran ɗaliban, Kuran nan kuwa ganin baya ganin kowa sai ƴan mata ukun nan yasa ya nufi wurin su yana huci kamar wanda ya yi shekara bai ga nama ba, Aasmeen ganin Tasleem baza ta tashi ba kuma ga Kura ta kusan isko su yasa ta fara ƙiran sunan Nasreen tana faɗin "Nasreen ki tashi mu gudu kinga Kuran nan ta kusan iso mu, Nasreen kar muyi two zero ki tashi please..."
Asmeen gani tayi Nasreen ta kifa kanta akan ƙirjin Tasleem haɗi da rungumar ta yasa itama bazata iya tafiya ta barsu ba itama durƙusawa tayi ta rungumi Nasreen da Tasleem tare da kifar da kanta akan su tana kuka,
Ga Kura yanda yake yo wa kan su ta bayan Kuran kuma wani zabgegen mutumi ne mai kyakkyawan ƙirar jiki yana sanye da wandon kakin Soldier da farar t-shirt mai gajeran hannu, fuskar sa daga nesa sai walwali yake kamar shi ya halicci kan sa, yana bin bayan Kuran ganin ya kusan isko wasu ƴan mata a wurin yasa shi ƙara ƙarfin gudun sa kafin Kuran ya yi sufa kan ƴan matan har wannan matashin shima ya yo sufa wurin su ya kwanta a gefen su tare da ɗaga hannunsa ya cabko wuyan Kuran dai dai lokacin da shima ya yi tsalle zai fa ɗa kan su, wani irin juyi matashin nan ya yi da Kuran ya doka shi a ƙasi tare da danne masa kan sa yanda bazai iya ɗago wa ba, haka Kuran yake shure-shure ya kasa ɗago wa.
Asmeen ce cikin ƙarfin hali ta ɗago a hankali jin yanda Kuran yake gurnani cikin tsoro da fargaba take kallon Kuran idanuwa kamar zasu faɗo daga nan ta sauƙar da ƙwayar idanuwanta kan matashin Sojan nan, a hankali ta fara bubbugan bayan Nasreen itama ta ɗago jin wurin ya yi tsit sai gurnanin Kuran, ganin wanda ya danne Kuran ne yasa ta zaro ido cike da mamaki, kallon juna suka yi ita da Asmeen babu wanda ya furta komai a cikin su...
Sauran ƴan makarantar kuwa su na kallon abinda yake faruwa ta window har da masu video su suka fi yawa.
Daga baya sai ga motar sojoji su biyar duk suka parker a tsakiyar filin makarantar wasu daga cikin sojoji suka fito da kaca suka ɗaɗɗaure Kuran daman su suke tafe da shi ya ƙwace musu shine dalilin da yasa Kurar ta shigo musu makaranta, bayan an shigar da Kuran cikin mota wannan matashin ne ya kalli wurin da su Nasreen suke sai da ya ƙare su da kallo sannan ya ce "A ya yin da mutane suke guduwa ku meya hana ku gudu? ko bakwa son rayuwar ku ne?..."
Nasreen tana kuka idonta akan Tasleem wacce har zuwa yanzu bata samu farfaɗowa ba.
Sojan ganin duk mutum ɗaya yake gani kuma su uku yasa ya kanne idanuwansa sannan ya buɗe su a hankali tare da maida idonsa kan su yana mamakin wannan al'amarin,
Asmeen ce ta yi ƙarfin halin cewa "Ƴar uwar mu ce take a sume kuma baza mu iya barin ta a wurin ba, gwara ko mai zai faru ya faru damu gaba ɗaya..."
Sojan ya ce "kuna nufin ku ce ku ɗin ƴan Uku ne?..."
Asmeen ta ce "eh we are triplets..."
Jinjina kai ya yi sannan ya ce "mai ya faru da ita?..."
Har Asmeen zata yi magana Nasreen tayi saurin katse ta da cewa "hatsari ne ya faru da ita, jini yana zuba sosai a kan ta..." nan ta fashe da kuka...
Lokaci guda zuciyar sa ta karye domin a rayuwarsa ya tsani ganin hawayen mace, idan kana son ganin raunin sa to ka haɗa shi da hawayen mace, jin kukan ta kuwa tamkar ana juyar masa da ƙwaƙwalwa ne tinin kansa yake hau matsanancin ciwo, jin kan sa yake tamkar mahaukaci domin akwai abubuwan da yake yawan tunawa a rayuwar sa da zaran ya ji sautin kukan mace,
A yanzun ma jin sautin kukan Nasreen yasa kan sa ya fara juyawa, cikin lokaci ƙanƙani ya dafe kan sa da hannu bibbiyu tare da rufe idanuwansa sosai shi kaɗai yake jin abinda yake ji, a gigice ya furta "please ki daina kukan nan bana so..."
Nasreen jin maganar da ya yi kamar ba'a cikin hayyacin sa yake ba yasa tayi saurin ɗagowa tana kallon sa, Asmeen ma shi ɗin take kallo bayan ya dawo dai dai ya kalle su sannan ya ce "it's okay! ku yi haƙuri ku taso zata tashi yanzu..."
Cikin kulawa ya miƙa wa Asmeen hannu itama ta ɗora nata ya miƙar da ita tsaye, itama Nasreen ɗago ta yayi yana bata haƙuri akan kar ta sake yin kuka, ya durƙusa a gaban Tasleem ya yi alama a wani daga cikin sojojin su akan ya miƙo masa akwatin maganinnuwa zai yi treat ɗin ta, har an miƙo masa komai da komai yakai hannu zai ɗago ta, yanda ya riƙo kafaɗunta guda biyu wani irin shocking ya ji ya bi jikinsa wanda tsabar ƙarfin shocking sai da ya ɗagu sama ya yi baya a gigice ya doku a ƙasi, itama Tasleem tsabar shocking ya bi jikin ta ba shiri ta farfaɗo daga doguwar suma haka jikin ta yake ta kakkarwa, lips ɗin ta ne yake motsi alamar tana so ta furta wani abu ta kasa.
Nasreen da Aasmeen ganin a halin da Tasleem ta farfaɗo yasa duk suka nufi kanta su na ambatar sunan ta....
Sojojin dake wurin ne duk su ma suka nufi wurin Matashin Sojan nan ganin abinda ya faru da shi, ɗago shi suka yi su na faɗin "Sorry Ogah! fatan babu abinda ya faru da kai..."
Shi kuwa idonsa akan Tasleem yana mamakin taya wannan al'amarin zai faru da shi haka ta silar ta, sannan yana tambayar zuciyar sa shin wacece wannan yarinyar???....
*TO MASU KARATU ANAN ZAN KAWO ƘARSHEN KASHI NA 5 DA 6 SAI MUN SAKE HAƊU WA A KASHI NA GABA*...
*NI CE ASMEETAH TAKU HAR KULLUM*...
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 7 to 8
Tasleem tana ƙoƙarin tashi wani soja yazo ya durƙusa a gabanta da boxes na magani yana faɗin "Ogah ya turo ni akan nayi treat ɗin ki..."
Daga nan ya ciro bandej da sauran maganinnuwa, ga Nasreen da Aasmeen su ma suna gefe guda.
Sojan nan tinda ya shige motar su ya kama kansa wasu abubuwa suke ta dawo masa ƙwaƙwalwa, ga wasu sojojin a gefensa,
"Amaar! Amaar!! Dan Allah kar ka tafi ka barni, dan Allah Mom ki ƙyale shi kar ki rabani da Amaar, Amaar...." Gaba ɗaya ya fita hayyacin sa sai fama cakurkuɗa sumar kan sa yake, ya kasa manta abubuwan da suka faru da shi yana yaro.
"Ta Ta Tasleem! Tasleem ki taimake ni kar Momminki ta kashe ni, ki taimake ni Tasleem, ki ce wa Mommin ki kar ta kashe ni dan Allah, Tasleem zata jefa ni a cikin ruwan nan ki taimake ni, mutuwa zanyi idan ta jefa ni a wannan ruwan wayyo Allah Mamanaa, Abbanaaa...."
A firgice ya dawo hayyacinsa yana sakin nannauyar numfashi sakamakon ruwan da ake yayyafa masa, a hankali yake furta "Tasleem! Ina zan same ta?.."
Idonsa ne ya sauƙa akan tafin hannayensa da har yanzu yake ta zogin shocking ɗin jikin Tasleem, nan da nan hannayen har sun yi jawur, wani tunani ne ya ƙara dawo masa, wannan matsalar da yake ciki yasa an nema masa wani babban malamin duba wanda ya sanar masa cewa wannan matsalar ƙwaƙwalwar bazai warke ba har sai ya haɗa ƙwayar ido huɗu da Tasleem, ma'ana su kalli juna na tsawon minti biyar babu wanda ya ƙibta a ciki, sannan alama ta farko da zai nuna masa Tasleem shine da zaran ya taɓa jikinta zasu ji shocking gaba ɗayan su, abinda zai kawo ƙarshen shocking gaba ɗaya su daina ji shine da zaran sun rungumi juna shocking ɗin ya ratsa jikinsu na tsawon minti talatin ba tare da sun rabe da juna ba Shikenam daga nan bazasu ƙara jin wani shocking ɗin ba....
Bayan ya gama wannan tunanin da aka sanar masa a ruɗe ya miƙe tare da ficewa daga