An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(The light of the soul)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
The writer of
MATAR DAMISA
MY ENEMY
And now HASKEN RUHI
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
First EP 1 to 2
★ *DELHI*★
*★SHAPRIS SHATTIMA* wani hamshaƙin mutum ne wanda a ƙalla bazai wuce shekara 35 a duniya ba, yana da bala'in kuɗaɗe wanda shima kansa bai san adadin su ba, bayan mahaifinsa ya rasu ya bar masa maƙudan kuɗaɗe wanda shi kaɗai ya ci gadonsa sakamakon shi ɗaya tilo iyayensa suka haifa, iyayensa sun rasu ne sakamakon hatsarin mota da suka yi, Shaprees yana da uwar ɗaki wato shugabar sa Madam Nablah wacce ta haramta masa dukiyarsa ta hanyar sirka masa su da kuɗaɗen jini, ta rinjaye shi zuwa fadar ta wato Devil's World.
Da matarsa Sophia ƴar ƙasar Nigeria dake garin Maiduguri ƴar shuwa, ita ɗin ba kowa bace fa ce ƴar talakawa, Mahaifinta gadin maƙabarta yake, sannan ita ta kasance tallah take a bakin titi, anan Shapris ya yi ido huɗu da ita ya nace akan Auren ta ba tare da iyayenta sun so ba, domin sun san mahaifinsa ba ƙaramin mutum bane suna tsoron kar ɗiyarsu ta wulaƙanta, daƙer suka amince da Auren Shaprees da Sophiatu, daga baya ya tafi da matarsa can ƙasar Delhi dake shima ɗan Maiduguri ne, a can ya cigaba da gudanar da harƙoƙinsa na halal da kuma na haram domin ya kasance shi ɗin ɗan secret society ne....
Yau shekara goma da Auren Shaprees bai waiwaito Nigeria ba, Sophia tayi kewar iyayenta matuƙa kullum kukan ta shine Shaprees ya dawo da ita gida amma sam ya ƙi duk da yana matuƙar ƙaunar matarsa Sophia, yau suke gudanar da walimar cikar shekara goma da Auran su a ƙasar Delhi, kowa ya hallaru a wani wantalelen gidan party, abokan harƙalla duk sun hallaru.
Wata zankaɗediyar mata ne take zaune a wani tsararren kujera, kana ganinta kasan ƴar hutu ce domin ba ƙaramar Hajiya ba ce, tana sanye da kayan ƙyale-ƙyale a jikinta wanda duk ya kasance komai na gwal ne da zinare, wannan ita ake ƙira da Madam Nablah or Hajiya Nablah ita kaɗai tana zaune sai pressing phone ɗin ta take, can taji an furta *Devil Mom* kamar daga sama Madam Nablah taji maganar nan tana tunanin wani mai ƙarfin izzah ne yazo kanta yana ƙiranta da sunan nan a halin yanzu, alhalin wannan sunan ba'a furta ta sai a cikin fadar ta mai suna Devil's World....
Madam Nablah sai da ta ɗan jinkirta kafin ta ɗago da kanta a slow tana bin wanda ya ƙira ta, dara daran idanuwanta ne suka sauƙa akan wata dirarriyar mata fara tas wacce tasha makeup tana sanye da Net cloth doguwar riga har ƙasi, Madam Nablah kallon matar tayi up and down sannan tasau murmushi tare da faɗin "Happy Anniversary..."
Sophia hararar ta tayi daga bisani ta zauna a ɗaya daga cikin jerukan kujerun wurin tana faɗin "10 years married without Babies..."
Madam Nablah glass cup ta ɗauka tare da kai lemon dake cikin cup ɗin kan lips ɗin ta, sai da ta kurɓa ta ajiye kafin ta ce "Oh so sorry my daughter..."
Sophia a fusace ta ce "i am not your daughter my friend because baki cancanci ki zama uwa ba..."
Madam Nablah murmushi ta sau sannan ta ce "kamar yanda har yanzu kike zaune ba Babies..."
Sophia ta ce "Shaiɗaniya kawai ai ke kika mun sanadi, kina tunani duk abinda kika umarci mijina baya sanar mun ne? tin shekarun baya nasan da cewa ke kika haramta mun samun ƴaƴa ta hanyar yin barazana da rayuwar mijina, kin bashi zaɓi biyu rayuwarsa ko mahaifana, inason mijina shiyasa ban goyi bayan rasa rayuwarsa ba na amince akan salwartar da mahaifana, wallahi kin cuce ni, kuma bazan taɓa yafe miki ba, biyayyan da mijina yake miki bai hana ki cutar da shi ba, ke kin mallaki ƴaƴanki a hannu amma shi kina masa baƙin cikin samu nasa farin cikin..."
Zaro ido Madam Nablah tayi tare da faɗin "Keee! wa ya sanar miki cewa bazai haihu ba? shima zai samu nasa ƴaƴan amma bata tsatsonki ba..."
Girgiza kai Sophia tayi sannan ta ce "ki sa a ranki cewa babu sirrin da zaki sanar masa wanda zai ɓoye mun, duk abubuwan da kike shiryawa na makircin ki na sani..."
Madam Nablah ta ce "haka kuwa wata rana zai sanar miki cewa ina buƙatar rayuwar ki..."
A zabure Sophia ta ɗauki kwalba zata kwaɗa mata taji an riƙe hannun ta wanda take ɗauke da kwalbar, a hanzarce ta ɗaga kanta sama tana ganin wanda ya riƙe mata hannun, miƙewa tayi tana kuka ta ce "Shapris kana jin abinda take fa ɗa koh?..."
Rungumar ta yayi tare da faɗin "ki kwantar da hankali, ki daina saka abu a ranki..."
Sophia tayi saurin katse shi da cewa "taya zan kwantar da hankali na kana tare da wannan shaiɗaniyar mata marar imani..."
Shapris ya ce "Please Sophia! ki koma gida zan iso ki..."
Tana kuka ta ce "Oh kana so na tafi ta ƙara shirya maka wani makirci ko?..."
Wani irin tsawa ya daka mata tare da faɗin "Please Sophia..."
Haka tana kuka ta bar wurin da gudu,
juyawa ya yi ya bi bayanta da kallo cike da damuwa, jin an ambaci sunansa ne yasa ya juya yana kallon Madam Nablah wacce ta miƙe tana shirin tafiya ta ce "around 2am mu haɗu a Devil's World muna da meeting..." Daga nan tayi tafiyar ta, shi kuwa ya bi bayan matar sa...
Akan gado ya tarar da ita sai sharar kuka take, shima zama ya yi cikin sassanyar murya ya ƙira sunan ta tare da faɗin "meyasa kike damun kanki akan abinda ba canzuwa zai yi ba.."
Ɗagowa tayi tana kuka ta ce "meyasa bazan damu ba, bayan rabani da tayi da mahaifana yanzu kuma rayuwata take nema fa?..."
Girgiza kai yayi tare da faɗin "hakan bazai taɓa faruwa ba, ke ɗin rayuwata ce rasaki dai dai yake da rasa rayuwata Sophia, ina sonki wallahi..."
Tana sharar hawaye ta ce "amma meyasa kafi ɗaukar Madam Nablah da mahimmanci akan ni?.."
Shafrees kamar zai yi kuka ya ce "to ya zanyi Sophia? Rayuwar mu gaba ɗaya a tafin hannunta yake, a yanzu zata iya salwartar mana da rayuwa, shiyasa nake so kiyi taka tsantsan da ita, kina binta a hankali, saboda haka nake yin duk abinda ta ce nayi..."
A zabure Sophia ta miƙe tana faɗin "cab ɗin to wallahi babu wanda ya isa ya saka ni na yiwa wannan shaiɗaniyar mata biyayya, bazan bita a hankali ba sai dai ta kashe ni, ai yanzu ma ta gama da rayuwata tinda ta dishar mun da farin ciki na, wai ma Shapris meyasa bazaka fita daga shirginta ba?..."
Shapris idonsa akan Sophia ya ce "barin ta dai dai yake da barin duniyar nan, duk wanda ya shiga ƙungiyar Madam Nablah baya taɓa fita sai dai gawarsa ta fita, wani kuwa ɓatar da gawarsa take, tanada ƙarfin iko na bala'i, tsafin da Madam Nablah take da shi Allah ne kawai masani, ina cikin ƙungiyar ta ne amma zuciyata sam bata tare da ita, yanzu ta ina zan fara tinkarar barin ƙungiyar Devil's World? Sophia bazan iya ba, in har kuwa zanyi to sai dai ki nema mun gafarar Ubangiji domin zaki rasani ne, ki tayani da addu'a..."
Sophia tana kuka ta durƙusa a gaban Shapris tare da riƙo hannayensa tana faɗin "Insha Allahu babu abinda zai same ka mijina, zan cigaba da addu'a zaka bar ƙarƙashin zalunci, nidai nasan halin mijina ba azzalumi bane sannan baya cutarwa, suna ne kawai ka rataya a wuyanka amma nasan baka jan jinin kowa..."
Ya ce "ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru da ke nayi miki alƙawari bazan taɓa barin a zalunce ki ba a karo na biyu, sannan idan Allah ya kaimu gobe zaki tafi Nigeria ki je ki dubo iyayenki tsawon shekara goma rabonki da su..."
Farin ciki ta shiga yi ta rungume shi tana godiya, da haka suka sha soyayyar su har tayi bacci, shi kuwa ko rintsawa bai yi ba domin ƙarfe 2 na dare sunada meeting ɗin da zasu gudanar...
Misalin ƙarfe 2:30 na dare cikin fadar Devil's World dake can ƙasin ruwa wasu mutane ne suke tsatstsaye duk suna sanye da dogwayen riguna jajaye masu huluna wanda ya rufe musu fuskoki, da wani dogon tebur a tsakiyar su kowa da kujerar zaman sa, sun kasu part biyu ko wani layi mutum takwas ne suna facing juna a yayin da tebur yake tsakiyar su, a can ƙarshen tsakiyar tebur kuwa Shugabarsu ce wato Devil Mom ita kuma tana sanye da baƙar doguwar riga mai hula wanda ya rufe fuskar ta sai iya red lips ɗinta ne a waje wanda yasha jan baki, ita kaɗai ce a zaune akan wani tsararren kujerar ta na gwal wanda ya fita daban a cikin su, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya duk sauran fuskokin su a rufe suke amma tasan kowa a wurin, ita kaɗai ce mace kuma shugabar su mai ɗauke da ƙarfin izzah da tsafi na ban al'ajabi, lips ɗin ta ne ya fara motsi sai fararen hakwaranta kawai kake gani yanda take juyar da jan harshenta tana faɗin "ku zauna..."
Sai a yanzu ta basu umarnin zama wanda tin tinin suke tsaye, kowa yana ajiye da cup na ruwan jini a gaban sa, haka kowa yake ɗaukan glass cup mai ɗauke da jini yana sha tamkar lemo, Madam Nablah ba tare da ta buɗe fuskar ta ba ta ce "Shaprees meyasa har zuwa yanzu idan an baka jini baka sha? tsawon shekaru da dama kana cikin ƙungiyar nan why?..."
Shaprees wanda yake zaune daga Nesa-nesa shima fuska a rufe ya ce "I don't know why..."
Madam Nablah ta ce "yanzu ka ɗauka kasha jinin nan, umarni nake baka..."
Shaprees ba tare da ya motsa ba ya ce "Devil Mom I can't ..."
A fusace Madam Nablah ta dunƙule hannunta tare da bugawa akan tebur haɗe da furta "Shaprees Shattimaa babu mai ƙarfin ikon bijirewa magana ta sai kai, ba wai bazan iya ɗaukan hukunci akan ka bane, yanzu inaso kayi abinda nace now now..."
Shaprees ta cikin hula ya kanne idanuwansa cike da takaici ya ɗora hannunsa akan cup, haka hannunsa yake kakkarwa gaba ɗaya ya kasa ɗaukan cup ɗin, haka yasa hannu biyu yana ƙoƙarin ɗago da cup ɗin haka hannayensa duk suka ɗau kakkarwa, gaba ɗaya ya kasa control kansa daga ƙarshe cup ɗin ne ya kuɓuce daga hannunsa ya faɗo ƙasi duk jinin ya wantsalu, wani irin haɗiyar yawu ya yi cike da tsoro da fargaba, ya rasa gane meye matsalar a duk lokacin da aka tilasta masa shan jini sai hakan ta faru.
Madam Nablah jinjina kai tayi tare da faɗin "many times hakan yana yawan faruwa but don't worry I'll do something..."