x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 64 - IBTISSAM BOOK 1

  • 189001 words
  • 192000 words
  • Out of 200864 words

Category: Romance Story +18

Views 306

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
aka dawo daka break shiyasa kowa ya nufi seat d’insa , a haka teachers suka cigaba da shigowa har zuwa time d’in short break, yanzu ma basu fita ba a class suka zauna su hud’un , yadda suke hira suna dariya kwanin burgewa lokaci zuwa zuwa lokaci sai Baby ta kalli Abla , har Abla ta lura da ita, cikin tsokana tsokana Abla ta furta “ Yan mata ko na miki kyau ne ?” Murmushi Baby tayi mata tana girgiza mata kai , batare da damuwa ba ta furta “ I just feel having talking to you “ sosai Abla ta sakar mata murmushi , “ Nima haka , I feel the same way “ da haka suka cigaba da hirarsu. Ko da aka tashi sai da Baby tasa Abla ta bata number d’inta , amma Abla tace bata haddace ba, shiyasa Ita Baby ta rubuta mata tare da fad’a mata idan ta koma gida tayi mata magana . A haka suka Abla ta nufi inda su zata sami su Sarah , suma su Fanan sukai mata sallama suka tafi. Bata san dalili ba , she just enjoyed the day with gurls , taji dad’in kasan cewa da su ko ba komai sun rage mata kewa , har ta ‘karasa gida kuma tana Tuna’nın mafarkin Baby.
Tundaga wannan lokaci wani irin ‘kawance ya shiga tsakanin su , ko ina zasuje a school suna tare da juna su hud’u, in basu da school kuma zasu hau group d’in da Fanan ta bud’e musu , sosai wani irin ‘kawance ya ‘kullu a tsakaninsu. Cikin tsawan lokacin nan kuwa gabaki d’aya Abla ta fita har kar Big Boss , ko had’uwa dashi batasan yi shiyasa da ta Daidai lokacin dawowar sa ko shigowarsa gida zata gudu d’akin, sai ya zama kamar wasa ‘buya take dashi, gabaki d’aya duk hanyar da zata had’asu ta toshe ta gabaki d’ayan ta . Har zuwa yanzu kuma a makaranta bata had’uwa da su Bad Boys , tun bayan Alkawarin wula’kanta ta da yace zai yi bata ‘kara ganin su ba , ita gabaki d’aya ta manta dasu ma .

****ABUJA , NIGERIA…

Wani irin hayaniya ne yake tashi tako ina kamar masu danbe , hakan ce kuwa ta kasance gabaki d’aya fad’a ne ake yi ga ihu da iface iface da ake ta faman yi, d’aya daga cikin ‘yan matan da ake danbe da ita ta janyo gashin attachment d’in ’yar uwar fad’an tata , itama buga tsalle tayi ta sha’ko ta wani danben ya sake ‘kauce wa a tsakaninsu, wata matace ta so ma daka musu tsawa “ ku dakata , ku dakata , bansan iskanci ‘kananan karuwai idan fad’an zakuyi ku fita waje ,” ba kowa ne yake maganar ba face Uwar karuwai ta fuskarta tayi baki da ja lokaci guda Sabida uban bleaching d’in da take yiwa kanta , kalar jikinta ta sauya zuwa kala biyu, tsaki d’aya daga cikin su taja “ Mtswww ! Malama ban saka dake ba dan haka kiyi mun shiru , na ‘kara fad’a miki kiyi min shiru idan ba haka ba muci uwar sabada dan ni ba tsoran uwar uban kowa yake jiba “, cewar İlham da take faman bankawa Uwar karuwai harara , a zuciye zinariya da Suke fad’a ta hayayya’ko mata, “ ah ah lalle gaskiya wayanki ya isa yanka , dole ki bud’e baki mana , yar iska”, dariya İlham ta saka tana tafawa da husna da itama tazama ‘kwararriyar yar hannu yanzu, ga cingum da take faman taunaya , irin taunar karuwai.” Bani da wannan lokacin yanzu, abunda na saki kawai ki bani 2k d’ina idan ba haka ba naci Uwarki wallahi babu abunda ya shafeni, karkiga ina d’aga miki ‘kafa ko uwata Dije tayi mun wallahi sai na rama balantana ke banza , ni banza, mu banzaye rainar bariki,” jijjiga jiki zinariya kawai take “ idan naki biya kuma ?” Lokaci d’aya İlham ta furta “ muci uban juna “ ai bata ‘karasa ba Zinariyya ta kawo mata duka , idan wata kujera ta dauka ta bugawa Zinariyya a baki , lokaci d’aya wani irin fad’a ya ‘kaure cikin gidan uwar karuwai , itama a Garin ta matsa da gangan ilham ta saka mata ‘kafa sai jinta tayi ragaf a ‘kasa dan yanzu gabaki d’aya basa jin maganar uwar karuwan , sai ga ta a ‘kasa tana ‘ko’karin tashi suka Yaushe ta , sai ya zama kamar da Ita aka fad’an , duk wacce aka tashi kaiwa duka sai ta kauce a doki uwar karuwai, ita kadai sai faman ihun ate maka mata take amma bata ‘karasa maganarta suke ‘kara kai mata duka .


IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee ✨


🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅


AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__


✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

NOT EDITED

S____39💞 ( second to the last free page)

ADX FLORENCE U.S.A
**PRISON**
Tsaye suke cikin babban prison d’in ADX me shegen hatsarin gaske , da ya zamto d’aya a duk duniya baki d’aya me suna ADX Florence da ke ‘kasar America , prison ne da duk Wanda yayi gigin guduwa yake fitowa a mace, har zuwa yanzu da ba a ta’ba samun koda mutum d’aya daya ta’ba tsira daga cikin saba, shiyasa gabaki d’aya prison d’in yake da manya manyan criminals masu hatsarun gaske, tare mata kan tsaro sosai , sabida hatsarun wad’an da suke cikin sa.
Ga baki d’ayansu sanye suke cikin ba’ka’ken kaya , musamman Big Boss da gabaki d’aya mutum
Bazai gane saba sabida shigarsa, hatta ‘kafarsa sanye take cikin ba’kin takalmin David stone , da duk Wanda ya duka da takalmin nan sai ya ji a jikinsa , hatta fuskarsa baka iya ganin ta sabida Black facemask d’in da ya’ke face d’insa , gashin kansa sosai ya tufkesu a bayansa , hakan ya bawa bucket hat d’in da ya saka rufe masa ido , shiyasa idan basanın shine a wajan ba , babu mahalu’kin da zai gane sa da wuri. Bobo ma sanye yake cikin ba’kaken kaya kamar Big Boss , sa’banın shi face mask Kawai ya saka a kansa , sai gyaran gashin kansa shima da ya so rufe masa ido duk da bai saka hula ba. Suna tsaye cikin wani waje da idan mutum ya kallesa bazai ta’ba tunanin a cikin prison bane , kusan mintuna 10 suna tsaye a Wajan , time to time Bobo yana duba agogon hannunsa . Yanzu ma agogon hannun sa ya kalla duk da face mask d’in dake face d’insa mutum zai gane yayi murmushi ta ciki. A hankali ya far irga ,5,4,3,2,1, yana kai wa 1 ya furta done , lokaci d’aya wani irin ‘kara ya karad’e cikin prison d’in, cikin sauri aka bud’e inda suke tare da jefowa Bobo wani black Leda me d’an kauri , zip d’inta ya bud’e tare da ciro guns d’in da suke ciki, d’aya ya mi’kawa Big Boss , shima ya saka ta sa daga bayan rigarsa kamar yadda Big Boss yayi. Cikin sauri suka bud’e ’kofar Suka futa , da Sauri Sauri gudu gudu Suka nufi inda yawanci criminals d’in suke cin abinci ga mata kan tsaro sosai a wajan ta yadda babu Wanda zai yi ‘ko’karin yin kuskure. ‘Karan da suka ji ma d’aya daga cikin prisoner d’in ne ya samu na sarar samun gun ya saita akan d’aya daga cikin masu tsaran wajan. Daga gefen sa wani mutum ne da ashekaru zai wuce shekara kamshin, jikinsa duk tatoo d’in spider ne a jiki ba’ki hatta face d’insa , gashi ya sa anyi masa surgery a fuska ta yadda aka iya ganin ‘kofofin hancin sa , bakinsa idan ya Lura sosai zai gane alamar raba lefen da yasa akayi masa . Tunda d’aya daga cikin prisoner d’in ya samu gun yake binsa da idanuwansa da shima aka canza masa zuwa ba’ki, shiyasa gabaki d’aya ya canza halitta zuwa wani abun daban sai kace ba mutum ba . “Ka ajje bindiganka”shine abunda wasu masu tsaran suke cewa , cikin zafin nawa me ri’ke da gun d’in ya ciro bindigar da ya ‘boye a bayansa ya je fawa d’aya daga cikin prisoners d’in, shima cikin sauri ya kama tare da saita ta daidai kan d’aya daga cikin masu tsaran, a daidai lokacin da su Big Boss suka shigo wajan da gun a hannun su , cikin kakkausar murya Big Boss ya furta “ ku ajje maka manku” kamar ‘kara tinzirasu yayi cikin sauri suka saka kuna ma zasu yi harbi, cikin sauri Bobo ya furta “ ya isa haka ! Me kuke bu’kata ?” Gun d’in hannun Bobo prisoner din ya kalla tare da nuna wani daga cikin d’an uwansa prisoner da gabaki d’aya aka saka su kwanta , cikin sauri ya furta “ your gun! Ko kuma na harbesa “, hannu Bobo ya d’aga sama tare da sunkuyawa ahankali zai ajje gun d’insa , akaro na biyu Big Boss ya furta “ ku ajje makamanku !” Yana furta hakan yaja kunama shima zai yi harbi , da sauri Bobo ga bangajesa Gun d’in sa shima ya fad’i ‘kasa , pito na tsayen yayi , cikin sauri d’aya daga cikin prisoner d’in ya d’auke gun d’in Big Boss tare da saitashi akanka , gabaki d’aya suma masu tsaran sai suka saita bindugogin su , cikin sauri Bobo yake musu alama da asu ajje gun d’insu, suna cikin hakan Big Boss ya shammaci na bayansa lokacin da ya kai masa irin irin Bugu da saida gun d’insa yayi ‘ko’karin fad’uwa , Big Boss ya kwace. A bazata d’aya daga cikin prisoner d’in ya harba Bullet , daidai lokacin da Bobo zai jiyo , cikin rashin sa’a Bullet d’in ya same sa , Big boss na ganin haka shima ya harbi d’aya daga cikin su a ‘kafa bindigarsa ya bawa Bobo shi kuma wani security ya jefo masa tasa , Big Boss na kama d’aya daga cikin su ya sakar masa naushi a kumatu, saura guda d’aya da yayi saurin ja baya , gabaki d’aya sai ya nemi rud’ewa ganin yadda aka saba team d’insa za’a fitar dasu , cikin kururuwa yayo kansu shima yaji saukar bayan bunguka akansa , gabaki d’aya yayi baya zai fad’i, guy d’in dasu me tanbarin spider yana ganin hakan cikin sauri ya tare sa tare da rungumesa, batare da sanin ma’aikatan wayan da suka yo kansu ba , ya saka wa guy d’in wani abu a aljihu yana ja baya , shima Big boss hannun Bobo ya ri’ke suka fita daga wajan , ga prisoners d’in dasu ma gabaki d’aya aka sa’besu akai waje dasu , Big boss na fitowa shugaban prisoner din ya sara masa , kansa kawai Big Boss yayi knodding lokacin da yake cire bucket hat d’in kansa . Har inda helicopter d’insu Big Boss suke shugaban prisoner din nan ya rakasu, ganaki d’aya prisoner guda ukun a ciki aka saka su , sai Big Boss da Bobo da suka hau wani helicopter d’in, ragowar helicopter guda biyu kuma su Victor ne a cikin ta. Cikin ‘kan’kanin lokaci jirginsu ya tashi sabida gabaki d’aya wajan prisoner d’in babu wani abu me rai ko mutane a gabaki d’aya wajan gabaki d’aya .
Cikin sauri d’aya daga cikin sojojin ya nufi Bobo lokacin da yake ‘ko’karin cire rigar jikin sa ta sama , hannu kawai Big Boss ya saka ya yaga hannun rigar inda aka harbi Bobo, lumshe eyes d’insa yayi kawai tare da matsawa gefe , shima soldier d’in ya samu yayi wa hannun Bobo dressing bayan ya cire masa Bullet d’in ciki.


**************
************************

***NYC ***

Wani littafine a hannun Abla gabaki d’aya rabun tunaninta yana kansa sabida yadda ta mayar da hankali akai , bata ankara ba taji an fuske Book d’in, cikin sauri ta d’ago da dara daran eyes dinta tana hararar Fanan ,” Kin fiya rigima fanan , bani book d’ina “ cikin tsokana fanan da ke bud’e Book din ta furta “ wallahi bazan baki ba , ki bari sai antashi wannan nasan tabbas zan iya baki , amma gabaki d’aya tun d’azu muna magana ke hankalin ki yana kan Book “ shiru Abla tayi tana ‘kara hararar ta , kallan yadda ta ‘bata face Eshaal tayi kafin ta kalli fanan itama “ kinsan Allah fanan ki fita idan mu, ina ruwanki da littafinta ? Kun bi kun ishemu da surutu salan kusa mana ciwan kai “ kallan Baby fanan tayi “ kinji fa ! Mu zasu yi wa bariki waisu best friend , ki fad’a musu mu a ‘kawancen namu ma , mu indiyawa ne “ gabaki d’ayan su kuma sai suka ‘kyal’kyale da dariya sabida jin abinda fanan tace , “ ke dai fanan kin shiga uku da surutu zanga yadda mujin ki zai yi fama dake “ cewar Baby, da sauri fanan ta mi’ke tsaye tana toshe kunnuwan ta “ Ni bana jin hausa da safe , kunga yanzu time zai wuce , ko kuma a hanyar komawarmu muga an shiga class “ cikin tsokana Eshaal ta furta “ zakiyi bayani ne ma ! Mu zakiyi wa wayo ? Amma dont worry akwai lokacin da zakiyi bayani” da haka suka mi’ke zasu koma class , kamar ance wa Baby ta juya sai taga flowers suna motsi kamar an bangaje su an wuce ta wajan , gashi gabaki d’aya su kad’ai a wajan flowers d’in “ Me kike nema ?” Cewar Abla ganin yadda Baby take zare ido , d’an jijjiga mata kai Baby tayi “ No babu komai , mu tafi” kanta Abla ta d’aga mata kafun ta furta “ Okay “ a haka suka nufi hanyar class kwajin burgewa suna tafiya suna hira abinsu , a karo na biyu Baby ta ‘kara tsayawa jin kamar anta’ba mata hannu, tana kallan side d’in kuma taga babu kowa a wajan “ Lapiya ?” Suka had’a baki a wannan karan, waigawa Baby ta soma yi lokaci zuwa lokaci kuma tana kallan hannun ta da kuma wajan flowers d’in da suka bari “ ji nake bayan mu akwai wasu anan wajan, sabida anta’ba mun hannu yanzu” d’an murmushi Abla ta saki lokacin da ta matso kusa da Baby “ ki kwantar da hankalin ki mana , wane zai ta’baki apart from us ?ki duba kiga a kusa da student meke zaune ba , kawai da kinji irin haka kiyi addua kinji ?” Okay Baby tace mata amma gabaki d’aya ta kasa sakewa sabida bugawa da taji zuciyarta ta soma ,kamar wasu yara suka ri’ke hannun juna , zasu shiga class Baby tayi saurin janye hannun daga na Abla , kallan menene Abla tayi mata suma su fanan gabaki d’aya ido suka zuba mata , hanyar da suka baro Baby ta nuna “ sorry nayi mantuwa , ku shiga class nima yanzu zan dawo “ da sauri fanan ta furta “ okay ni bari na rakaki , inyaso su sai shiga class “ da sauri Baby ta girgiza mata kai “ No no no ki shiga class d’in kema , karki damu ko 5 minutes bazan ba zan dawo “ tana kai ‘karshen maganar ta bata bari sun yi magana ba tayi saurin barin wajan , gabaki d’aya bayanta suka zubawa ido , cikin d’an tantama fanan ta furta “ anya lafiyar ta ‘kalau kuwa ?” Ajiyar zuciya Abla tayi kad’an ganin suma sun fara shiga dawuwa da reaction d’in Baby “ No karku damu , nasan yanzu zata dawo tunda ta fad’a , mushiga class kawai “ toh kawai suka furta , suna shiga ciki kuwa teacher d’in Maths ya shigo class d’in.

Direct Baby wajan flowers d’in da suka baro ta nufa , lokacin gabaki d’aya babu student sabida komawa class da akayi, tunda ta tunkaro wajan take jin ‘kafarta kamar ana tsigarta , amma duk da hakan bata dena tafiya ba ga wani irin zufa da take ji gabaki d’aya jikinta , saura kad’an ta ‘karaso wajan flowers d’in taji ‘kafafuwanta kamar ana zuba mata wani irin abu mara dadin ji , cikin sauri ta saka hannunta ta soma sosa wa , kamar wacce ake ‘karawa abu tana sosawa tana ‘karajin abun yana ‘kara yawa , tun tana d’aukan abun wasa har ta soma hawaye sabida yadda take jin ‘kafarta, da sauri ta juya zata bar wajan taji an hankad’ata , d’ago kan da zatayi kuma ta babu kowa a wajan , cikin sauri ta kuma ‘ko’karin mi’kewa ta ji kamar an ‘kara ta’ba mata ‘kafa , a razane
End Ads