tabbatar masa da gaskiyar abunda sukai, kallansu d’aya bayan d’aya uncle yayi” daga kallan fuskar ku nasan yarana sunyi lefi, oya lefin me kukai ban sani ba “, d’an shagwa’be masa fuska little yayi zaiyi magana uncle ya d’auke kansa , “ ni zaka yaudara ka wani karya mun wuya ? Toh bari na barku tare dashi”, da sauri little ya mike cikin dariya kirjinsa har sama yake ya furta “ Haba uncle d’ina kayi hakuri….”, bai ‘Karasa maganar da zaiyi ba ya fad’i ‘kasa sumammme, gabaki d’ayanxu nufar inda yake sukai cikin tsananin tashin hankali, cikin wani irin zafin nama bobo ya d’aukesa kamar ya d’auki ‘karamin yaro ya nufi sama dashi , suma hankali a tashe suke binsa a baya gabaki d’aya shi prince ya rud’e jikinsa sai faman rawa yake sai da uncle ya ri’keshi, cikin wani babban waje da aka rubuta Lab a jiki suka shiga , komai cikin zafin nawa bobo yake yinsa , yadda lab din ya tsaru mutum sai ya d’auka wani shahararran d’akin asibitine ga wasu irin na’u rori aiki da suke ciki, wani gado me d’auke da na’urori bobo ya shin fid’a little , hannu biyu ya saka ya ‘barka rigar little take wajan farar singlet d’insa ta bayyana , itama hannu biyu bobo ya saka ya ‘barkata, da Sauri ya cire jigar jikinsa ya bar guntuwar ciki, hannunsa duka biyu ya had’a ya soma danna kirjin little da baya motsi kamar matacce, “ get the x-ray “ cewar bobo da karfi, da Sauri , yadda yake dannan kirjin little sai ka d’auka zai balla masa jiki Dan da iya karfinsa yake danna kirjin little amma ko motsi little beyi ba , cikin karaji bobo ya furta “ uncle Defibrillator “, cikin Sauri uncle ya matso dashi kusa da bobo, da Sauri bobo ya karbi defibrillator paddles din da uncle ya mi’ko masa , a chest din little ya saka guda d’aya daga ‘bangaran dama , daga ‘bangaran hagu kuma ya saka masa a ‘kasan nipples Ninsa ba hagu,” charge 200”, shine abunda bobo ya furta , da Sauri bobo ya d’auki defibrillator uncle ya dannan charge 200 bobo ya dora masa defibrillator din hannunsa , wani irin d’agowa jikin little yayi ya koma ,” one more time “ cewar bobo, ta jikin abunda uncle ya janyo ya kara danna charge 200 din , yana dannawa ya ajje ya dora hanka a Daidai saitin zuciyar little sai da yaji bugun zuciyarsa ya daidaita kafun ya sauke a jiyar zuciya , gabaki d’aya kana kallansu zaka ga damuwa tattare da su, intubation d’in da bobo ya saka masa na nunfashi ya gyara masa , a gefen gadon bobo ya zauna tare da rike hannun little sosai yana runtse idanuwansa , yadda prince yake ganin little na shiga irin wannan yanayin sosai yake bashi tsoro, duk da girman shekarun sa hakan ba ya hana duk lokacin da yaga little d’insu a cikin irin wannan condition din yayi kuka , yanxu ma uncle ya rungume yana fashewa da kuka , shi kansa uncle daurewa kawai yake , muryar bobo har ta d’an canza ya furta “ karku fad’a masa komai , I will take care of him for now “, no ya kamata ya sani , dole a fad’a masa halin da little yake ciki karka manta , sabida rashin lapiyar little ya karanci ‘bangaran zuciya ,” hannun little bobo ya damke cikin tashin hankali, dan ya sani dole ya fad’a wa big boss tunda shine likitansa , da ace yana kasar ne ma da da sauki amma yadda baya ‘kasar yaji halin da little yake ciki kome zai iya faruwa “, yadda kukan prince yacika masa kunne yasa ya kallesa “ it’s okay , zuwa da safe zai tashi ? Okay ?”, amma yaya bobo me yasa yake suma haka ? Inajin tsoro sosai “, nuni bobo yayi masa da ya matso, yana matsowa yayi hugging d’insa, ganin yadda prince da uncle suka tayar da hankalinsu yasa yake ‘ko’karin danne nasa tashin hankalin Sabida ya kwantar musu da hankali “ karka damu zuwa safiya little dinka zai tashi kaji? Yanxu dare yayi ya kamata kuje ku kwanta , ni zan zauna dashi, da Sauri prince ya girgiza masa kai hawaye na sakko masa a fuska “ No yaya bobo bazan iya tafiya ni kadai ba, zan zauna anan tare da ku”. No prince “ shima da sauri prince ya furta Dan Allah yaya bobo” , jin jina masa kai bobo yayi yana kallan uncle “ kadena kallona Nima anan zan kwana, ka zauna zanje na kula da komai kamar yadda kasava “, kansa kawai bobo ya d’aga masa dan ya kasa bud’e bakinsa sai kallan little da yake kawai “ I will never forgive you ! Sabida ku little dinmu yake cikin wannan condition din, I so much hate you with passion “, cewar bobo yana lumshe idanuwansa, wani red button ya danna a jikin gadan little yake jikin bangon dake facing d’insu ya rabe gida biyu wata ‘kofa ta bayyana , da ido ya nuna prince alamar ya tafi , zaiyi magana bobo ya furta “ No complain “ jiki a sanye ya furta “ good night yaya bobo “, murmushi bobo ya sakar masa yana jinjina masa kansa , har uncle ya dawo yana zaune kusa little , wayarsa uncle ya mi’ka masa , “ he called you ! Nasan tunda be sameka ba yasa ayi masa binciken abunda yake faruwa , try to explain everything to him “, okay uncle cewar bobo, uncle yana nufar d’akin da prince ya shiga ya d’ago wayar hannunsa “ Big Boss “ shine abunda ya Fito ‘baro ‘baro a jikin wayar “ besan ta yadda zai fara masa bayani ba , shiyasa ya kashe wayan gabaki d’aya . Yanda gashinn little ya rufe masa fuska ya gara masa take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana kamar me bacci duk yadda ya motsa dimple dinsa sai ya motsa .
Har wajan karfe 3:30 idan bobo biyu bai runtsaba , sai a lokacin yayi tunanin kunna wayarsa , har yanxu sunan big boss ne rad’o rad’o a jiki, shiga wajan calls yayi daniyar kiransa amma ya dakata, sau biyu yana kokarin kiran sa amma yana dakatawa sai ana ukun ya danna sunansa amma ko ringing batayi ba ta katse , sau biyu yana kara kwada kira Amma still yadda yayi a farko hakan ne ya ‘kara faruwa . Wani irin lallausan murmushi yasaki da ya ‘kara masa kyau, kallan fuskar little da yake bacci hankali kwance yayi, ganin dare na ‘karayi yasa shi kwanta wa akan sofa din da yake zaune, be jimaba bacci ya d’aukesa.
5:30 yaji ana ta’basa, kyawawan idanuwansa bobo ya bude ya saukesu akan little, “ yaya bobo”, uhm d’an langwabe masa kai little yayi “nifa banasan wannan abun da ake Samun hanani bacci yake ba “, hararar sa bobo yayi kafun ya ciccire masa defibrillators d’in, “ yaya bobo “little “ cewar bobo” lokacin sallah yayi bari naje na taso su yaya prince kaji”, kanshi bobo ya jinjina masa yana nuna masa dakin da suke da d’an yatsa , har ya nufi kofar sai kuma ya dawo inda bobo yake yayi hugging d’insa “ am sorry yaya bobo, idan aka idar da sallah sai muyi bacci ko?”murmushi bobo ya sakar masa , “ sure in aka idar da sallah yau ba training bacci zamuyi “, da murya little ya nufi d’akin , sosai d’akin ya’ke da girma komai na anfani akwia shi a ciki , da gudun sa ya d’ane gadon ya shiga tsakiyarsu, cikin bacci prince ya furta “ little “ daman da shi ya kwana aransa , Daidai kunnansa little ya furta “ na’am yaya prince “, da Sauri prince ya ware idanuwansa yana mikewa zaune , beyi wata wata ba yayi hugging d’in little , cike da mugunta little ya muntsinesa, zaburar da yayi ne ya farkar da uncle , “ Wallhi little baka da mutum ci , me nayi maka yanxu?” Gwalo little yayi masa yana kallan uncle da shima shi yake kallo “ uncle ka dena kallona Haka , lapiya ta ‘kalau fa “, ka tabbata ?yess uncle nifa lapiya ta kalau , lokacin sallah yayi fa , karmu makara” uncle be ce masa komai ba shima yayi hugging d’insa .
Atare suka nufa masallaci , yadda little ya rike hannun bobo da prince sai abun ya baka dariya , adawowa ma haka ya rike musu hannu suka koma gida , hannun prince kawai ya saki ya rike na bobo “ uncle ni yau yaya bobo yace bazanyi training ba , bacci zamuyi ko ?” Kansa ya Jinjina masa “ Nima bacci zanyi “, kallan da bobo ya bishi da shine ysa ya hadiye maganarsa , dariya little ya saki , ya rike hannun bobo suka soma tafiya sai da sukazo hawa lifter little ya d’aga muryarsa da d’an karfi yadda prince zaiji” yaya prince kai ma kaje kayi bacci “, talle masa ‘ke ya bobo yayi , da Sauri ya turo bakinsa se kace wani ‘karamun yaro , suna shiga part d’in bobo har da wani tsalle little ya saka ya d’ane bed din bobo , girgiza kai Kawai bobo yayi ya kwanta ,yana kashe musu light, nan danan bacci ya d’aukesu. Bobo ne ya fara farkawa duk da baccin da yayi befi na 1 hour ba , fuskar little ya kalla da yake bacci hankali kwance , kafun ya mayar da idanuwansa kan agogon side bed d’insa. 8:01am , “ shitt “ ya fad’a da d’an karfi yana nausar iska , shaf shaf ya shiga wanka , be wani jima ba sosai , gabaki d’aya 30 minutes yayi , kamshin turaran Roja ya cika d’akin, yadda yayi shigarsa ba ‘karamin kyau yayi ba , ‘kananan kaya ne a jikinsa black colour , tundaga wandon jikinsa har zuwa rigar jikinsa me dogon hannu ‘kirar kanfanin versace, ba karamin kyau yayi acikin kayan ba , sai kalar fatarsa ta ‘kara haska ba’kin kayan jikinsa, yau hatta gyaran gashin kansa na asalin sojoji ne yayi,bakin agogon hannunsa kirar kanfanin Rolex ya kalla yaga har yanxu 9 batayi ba , gyarawa little kwanciya kawai yayi ya bar d’akin. Yana sakkowa yaga uncle da prince ko wannansu ya shirya suna shirin yin breakfast, suna ganinsa gabaki d’aya suka mike tare da nufar dinning, kamar kullum James ne da wasu sojoji guda uku, suna zama james ya fara serving din ko wannansu abunda zai ci , zai juya bobo ya dakatar dashi ,!da Sauri su james suka tsaya cike da girmamawa, a gogon hannunsa bobo ya ‘kara kalla , kafun ya soma magana “ make Avocado toast, hash browns,Belgian waffles “, gabaki d’aya kallansa sukai “ na little ne uncle wannan kallanfa “, hatta prince sai da ya saki ajiyar zuciya ya d’auka yaya big boss ne zai dawo”. 9 Daidai bobo yabar gidan a Daidai lokacin da little yatashi, breakfast din da bobo Yasa ayi masa akai serving din sa, yau hatta abincin abaki prince ya bashi Sabida gata.
✨✨✨✨✨✨
KANO
NASARAWA G.R.A
Eshaal ba ‘karamin aikatuwa tayi ba a kitchen , ita kadai sai faman aikin girkin baby take , sallah ne kawai ki dakatar da ita , lokacin da ta kammala girki a gajiye ta fito falon, yanxu babu momcy a falon sai baby ita kadai da take kallo, tayi crossing legs dinta ga wani d’an iskan cingum da take ci sai faman bada sautin kas kas kas , tana ganin shigowar Eshaal ta ja dogon tsaki, “Abincin suna dinning “, abunda Eshaal tace mata kenan tana kokarin juyawa , “ ke “ cewar baby, d’an juyowa tayi tana kallan baby, “ haka aka koya miki? Ko uwarki da take kabari haka ta koya miki idan aka saki abu”. Rai a’bace Eshaal ta kalleta , amma bata ce mata komai ba sai danne abun da tayi a zuciyar ta , sau dayawa tana jin zafin maganganun Baby amma tana rabuwa da ita ne sabida a zauna lapiya tasan yanxu tace zata biye mata itace a ruwa , ita zata wahala , a gadarance baby ta furta “ biyoni” tana nufar dinning din da Eshaal ta cika ga kamshi sai faman Tashi yake , amma baby na zuwa sai ta fara toshe hanci wai bata san warin aroma din be mata va ,kallanta kawai Eshaal tayi har ta Bud’e pepper chicken din da yasha kayan had’i sai faman tashin ‘kamshi yake , duk Wanda yaga kazar nan sai ransa ya biya sabida yadda ta had’u, ta’be baki baby tayi kafun ta bud’e next warmer din da kamshin fried rice ke tashi ga veggies din da ya kara ‘kawata shi, gefe d’aya ga coslow da lemukan da Eshaal ta had’a, a yangance baby ta furta “ serve Allah yasa na iyacin ‘kazantar nan “, anan ma Eshaal ta so ya ‘ba mata magana amma ta rabu da ita tasan tana tankamata baby ba akanta zata huce ba akan Amma zata huce shiyasa take shanye duk abunda baby take mata sabida Amma, ba musu Eshaal tayi serving din baby in a unique way duk da ashekaru Eshaal zata iya girman baby da watannin da bazasu Gaza uku ba . Spoon d’in farko baby ta kai bakinta duk da abincin yayi mata dadi sai tayi saurin furzarwa tana wurgar da plate din ‘kasa gabaki d’aya abincin sai yazu , “wannan Wana irin dabbancine zaki yi mun wannan abinci sai kace wata dabba irin ki? Haka uwarki ta koya miki?” Tass Eshaal ta d’auke fuskar baby da mari, itama bata sauke hannuntaba taji saukar mari dama da hagu, a gigice Eshaal ta dafe kumatunta, tana d’ago da kyakkyawar face d’inta da Tasha mari , Dadynsu ne ya mareta , yadda taga ya had’e rai ne yasa tasha Jinin jikinta , ko kallo be isheta ba sai ma baby da ya kalla, itama tana ganin abunda yayi wa Eshaal ta shagwa’be fuska har da fashewa da kukan ‘karya , lokaci d’aya dadyn su ya rud’e ganin baby na kuka , ashagwa’be ta turo masa d’an karamin bakinta ,” Dady daman sai da na fad’a maka Eshaal ba ‘kaunata take ba ka kalli yadda ta mareni dan kawai nace bazan iyacin abincin da ta dafa ba , gaskiya dady shiyasa nace bazan koma u.s tare da ita ba Sabida zata zubarmun da class, in karatun kake so tayi kasamo mata ko makarantar kwana ce ta gwamnati dan dashi ta fi dacewa “, amaimakon yayi mata fad’a sai ma murmushi da ya sakar mata “ don’t worry my dear, ko me kikeso shi za’ayi miki ai , ina momcy dinki take ban ganta ba “ ta’be masa baki Baby tayi tare da ware masa hannu alamar ita ma bata sani ba “ tace na fad’a maka ta fita ,so ni kuma na gaji bazan iya zuwa part d’inka ba shiyasa ban fad’a maka ba “, cewar baby sai faman ya tsine take , yanxu ma wani murmushin ya saki “ Toh ba komai ai bansan ma tafita ba , amma ai duk yadda tayi shine Daidai , yanxu kishirya ni sai na kaishi shopping da kaina “, duk abunda suke Eshaal na tsaye dafe da kuncinta tana binsu da kallo , babu abunda ya fi tsaya mata arai kamar yadda Dadynsu ya nuna rashin wanzuwarta a wajan , gabaki d’aya hankalinsa kaco kam yana kan baby” Dady give me some minutes bari na shirya sai mu tafi”, okay my dear cewar kyakkyawan Bafullatanin da akallan farko zakaga tsantsan kamanninsa da Eshaal, Baby na barin wajan shima dady ya juya zai bar wajan, murya a sha’ke Eshaal ta furta “ Dady “, wani irin kallan tsana dady ya bita dashi tare da jan wani dogon tsaki yana barin wajan, yadda yayi mata beyi mata dadi ba dukda ta saba da irin wad’annan abubuwan ko ma fiye da haka amma yanda yake nuna mata tsantsan tsana kamar bashi ya haifeta ba , wani lokaci har tanbayar kanta take Anya shine mahaifinta na gaskiya ko kuma wanine mari’kinta , tana tsaye a wajan baby ta fito cikin shigar ‘kananan yana da suka matse ta Amma ko a jikinta , d’an ‘karamin mayafin da ta d’akko a hannu ta ri’kesa , sai kantamemiyar wayar ta d’aya rike a hannu cike da yanga, tana fito wa dadynta ya fara tafa mata , fuskar sa d’auke da murmushi “ my daughter kinyi kyau “,Thanks kawai tace masa , suna had’a ido da Eshaal ta kashe mata ido d’aya tare da kama hannun dads dinta , sunzo zasu fita baby ta juyo tana kallan Eshaal da tun d’azu bata motsa daga inda take ba “kishiga ki gyaramun d’akina kafun mu dawo, sannan kada ki kuskura wata ‘kazama tashigar mun d’akin har ta cika mun d’aki da warin jikinta , and lastly Kema ba yadda nayi dake ba sabida duk lokacin da na saki aiki sai na nemi abu na rasa , so be careful “, ta karasa tana jan hannun mahaifinta da sai murmushi yake sakar mata . Tana ganin fitarsu ta juya a guje ta nufi d’akinta, dakin da ko kwatan na Baby be kai ba , bayan set din gado babu wani abu na ado a cikin d’akin akwai da haduwa kwata kwata bazaka had’a shi da na Baby ba dan d’akin baby dakin yan gata ne da kome take so ake zuba mata sabo.
Kan gadanta ta fad’a tana fashewa da kuka me ta’ba zuciya , sallamar da akai ne yasa tayi saurin goge face d’inta tana share hawayen da suke ‘ko’karin zubo mata , yar aikin da tashi ga d’akin baby ce , da Sauri Eshaal ta saka murmushi akan face d’inta “ Amma sannu da zuwa , aikine yayi mun yawa shiyasa kika ga d’azu banzo kinyi mun kitsan ba “, murmushi Amma ta sakar mata , cikin sanyayyiyar murya ta furta “ kiyi hakuri, komai me wucewa ne “ sai alokacin wasu hawaye Suka sake zubo mata “ Amma nagaji da gidan