da wanzuwar wani ba a Wajan , sai da Eshaal ta maimaita kalmarta sau uku kafun baby ta d’ago fuska a ya mutse “ ki tashi ki had’a mun rich friedrice da coslow sannan ki had’amun farfesun rago, nasa, da kuma na kaza , ko wanne daban daban ,sannan sai strawberry milkshake da banana milk shake da nake so,kallanta sosai Eshaal tayi jin abubuwan da baby ta lissafa Wanda tasan idan za’a kasheta ba lallaine taci abincin ba wahala kawai take san sakata “ kin dai ji abunda ta lissafa, ki tashi ki bani waje “ cewar momcy tana binta da wani kallan tsana, jiki a sanyaye Eshaal ta mi’ke jikinta duk a sanyaye hawayen da suke sakko mata ta share , yadda momcy da baby hatta dady da bayansa ra’barta suke mata abubuwa abun na tsaya mata a zuciya shiyasa kullum cikin adduar Allah yajikan ammeyta take ,duk lokacin da zatayi sallah sai tayi addua wa mahaifiyarta sabida ji take kamar bata da kowa a duniya, mutum d’aya ce take ‘ko’karin kwantar mata da hankali a duk lokacin da take cikin kunci ko tashiga maraicin uwa , AMMA ce kad’ai ke share mata hawayenta duk da yadda itama bata tsiraba Wajan baby da momcy kasancewarta yar aiki kuma a ‘kar’kashinsu. Tasan yanxu tana komawa Amma zatace zaka temaka mata , ita kuma batasan abunda zaisa Baby ta wulakanta ta shiyasa bata tsaya a ko ina ba sai kitchen , ita kadai sai tunanin ta inda zafa fara uban abincin da baby ta tula mata take .
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
ABUJA
ADEMOLA ADETOKUMBO STREETS _!
Karfe 2:30am ‘kishir ruwa ya farkar da Abla , Allah ya temaketa akwai haske har lokacin ba’a d’auke wuta ba , bakinta d’auke da addua ta farka , mamakin ganin ‘kofar d’akinsu abud’e ne ya kamata , wai gawa Abla tayi taga Arwa na baccin hankali kwance, inda Aneesa take a kwance ta kalla , babu kowa akan katifar daman batasa ran ganin Ilham da husna ba , a hankali ta fito daga cikin d’akin cikin tafiya a hankali da ‘yar fargabarta ta fito falourn ,still shima falourn fitilarsa a kunne yake , shiyasa wani tsoran ya ‘kara kamata , ita tsorantama kar ace wasu ne suka shigo suna bacci suka d’auke Aneesa ganin bata cikin d’akin,bata gama shiga cikin mamakiba sai lokacin da taga ‘kofar falourn abud’e ga hasken fitula da Alama wanine ya fita , cikin sand’a yanxu ma ta nufi ‘kofar wajan, da Sauri tayi ‘ko’karin janyo ‘kofar falourn Amma motsin da taji a wajane yasa ta ja burki, ga tsoro tana ji amma zuciyar ta tana san ganin su wanene a wajan , waige waige ta fara idanuwanta suka sauka kan sandar data hango , cikin sand’a ta rarrafa a hankali kada suji motsinta ta d’akko sandar ta kara rarrfawa ta koma bakin kofar, a tsugunne ta fito waje tana sand’a a hankali a hankali, Inda taji motsin ta nufa tare da rike sandarta gam a hannu, ga addua da take cikin zuciyar ta hannunta data ri’ke sandar shima sai rawa yake a hankali ta soma jin magana kad’an kad’an, cikin dabara ta ‘karasa wajan mata biyu ta gani akan wani dakali ga kwalba kamar ta magani a kusa da su , mamaki ne ya kama Abla “ idan basu da lapiya Menene na ‘buya cikin dare kafin su sha maganin “ tana cikin maganar zuci taga kamar za’a juyo da sauri ta ‘kara buya gudun karsuganta, muryar Aneesa da taji kamar me magagin bacci ne ya bata mamaki “ toh me take Anan ? Baccin ne be ishetaba ? Ko bata san ta fito ba ? Ita kadai Abla take maganarta cikin zuciyarta bata gasgata muryar Aneesa ba sai da ta ‘kara le’kowa taga ta d’aga wani kwalbar magani tana kwankwad’a , abla bata san lokacin da ta karasa ta warce kwalbar ta yar a kas ba ,” Aneesa baki da hankali ne zaki dauki magani haka kiyi Tasha ? In baki da lapiya ki fad’a mana Amma bawai ki dinga shan magani ba batare da kin aunaba, a zuciye Aneesa ta d’ago da idanuwanta tana kallan Abla sai faman lumshe idanuwatake kamar me jin bacci, cikin wata iriyar murya ta furta “ uban wa yace ki yardar mun dashi , eh ? “ yar shila dake gefenta ma sai faman lumshe ido take , shurun da abla tayi tana kallanta da mamakine yasa Aneesa tayi kokarin tashi Amma ta kasa sai faduwa da tayi , cike da maye yar shila ta ‘kyalkyale da dariya “ rabu da ita bata san duniyar da muke ba , barta yar wahala , karki damu zan baki wani gobe kinji”, cewar shila yadda take magana zakasan abuge take , itama Aneesa dariya ta saka “ shikenan toh na hakura Amma duk lokacin da ta kara yi mun haka sai na ‘bata mata “, tana magana tana tafiya ta jikin bango sabida yadda ta kasa tafiya sai da ta jin gina da bango a haka tana layi ta wuce Abla da shock ya kamata , ita yar shila tana tangad’i ta wuce Abla , kwalbar da tayar ta kalla kafun ta karasa wajanta “BRONCLEER “shine sunan da yake jikin maganin, d’an shin shina wa tayi sai tayi saurin yar darwa tana toshe hancinta , fasa shan ruwan tayi ta koma d’aki har yanxu mamakin ganin Aneesa na drug abuse ya ‘ki wuce mata arai, tana shiga d’aki ta tarar da ita kwance tana bacci kamar ba Itace ta shigo ba “, kulle d’akin tayi ta kwanta itama , ruwan da bata sha ba kenan .
4:30am ta farka yau ta d’an makara tayi mamakin rashin tashin ta da su debeka basuyi ba , bata damu da hakan ba itama , shaf shaf ta soma share Fallon da kullum yake cikin ‘kazanta tana gamawa tayi mopping ta gyara d’akunan da babu kowa a ciki da toilet d’insu , tana gamawa ta had’a wanke wanke Amma bata fara ba sabida sallar da take san tayi, tana idar da sallar ta soma wanke wankenta har lokacin kuma babu wanda yafito , sai da ta kammala gabaki d’aya aikinta tukunna ta samu tayi wanka duk da bata da sabulun wanka haka tayi wankanta sannan ta sa’ba kayanta ba ko omo sai tsofaffin ragowar ko d’ad’d’en kayanta da tasaka , Arwa ce ta bude idanuwanta ganin Abla na shiryawa , itama mi’kewa tayi tayo alwala Abla ta Ara mata hijab dinta zatayi sallah, sai alokacin uban tulun gashin Abla ya fito duk da yana cikin d’an kwalunta amma yayi wa gashinta kad’an ga kwantaccen gashin ta daya kwanta , tanasan wanke shi amma bata da abun wanke wa shiyasa take hakura . Arwa na idar da sallah suka fita , cikin kudin Abla suka siya kosan hamsin suka ci duk da beje musu ko ina ba Amma haka suka hakura tunda basu da kudin siyan me yawa , yanxu ma gidan ruwa suka nufa ga rana haka suka jira a kazo har kanzu, rana na dukansu haka suka dunga siyar da ruwansu , yau ko cinikin arziki basuyi ba ga gajiya da sukai , ba yadda suka iya haka suka Zara cikin kudin suka siya rogon saba’in sukaji sabida yunwa , har akai sallar la’asar suna abu d’aya sallah ne kadai ke tsayar dasu yau ma ko makarantar allo bata samu taje ba haka ta hakura zuciyarta fal tunanin yadda zata biya uwar karuwai kudin ta. Har suka koma gida wannan tunaninne fal cikin ranta.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
UNITED STATES 🇺🇸
Yau little ne ya fara farkawa daga bacci , agogon d’akin ya kalla yaga da sauran mintuna kafun ayi kiran sallah, wanka yayi cikin shigar jallabiya da wani rawani fari irin na larabawa , yadda ya d’aura abun sai ya zama kamar cikakken balarabe , kadan ya fesa turare gudun kar ya Tashi prince dake bacci ya bude kofa a hankali ya futa , kai tsaye part din bobo ya nufa ko tsoran duhu bayayi , be tsaya a ko ina ba sai d’akin bobo, da wani dum light green yake haskawa , a hankali little ya salalla’ba ya nufi gadon bobo, baiyi wata wata ba Kawai ya d’ane jikin bobo, cikin wani irin zafin nawa bobo ya juya little dake jikinsa hannusa d’aya akan ma’kogaran little , d’ayan hannunsa kuma ya saita kan little da bunduga, murya a shake little ya furta “ yaya bobo “, da Sauri bobo ya sake sa yana d’aga sa, fitular d’akin ya kunna gabaki d’aya haske ya Haska ko ina na d’akin , ruwa bobo ya mika matsa yana shafa wuyarsa “ are you okay ?”kansa kawai little ya jinjina masa , hugging d’insa bobo yayi thank god beyi garajen sakin bullet ba ,” me yasa ka d’ane jikina ? Da nayi maka wani abun fa ?”, cewar bobo “ sorry yaya bobo nazo tashin Kane fa , sai kawai naji kajuyani kamar a mafarki”, keyarsa bobo ya talle “ babu kyau ka bari, idan ni kasamu ban saki bullet dina ba , duk ranar da kayi wa yayanka sai ya tarwatsa maka kai da bullet “, dariya little ya saki, ganin yadda yake dariya ne yasa bobo yaji dad’in hakan .” Oya kaje ka tashi su uncle ma nasan ni kadai ka tasa “ Tom yaya “ cewar little yana barin d’akin , d’akinsu ya koma ya tarar prince na bacci har yanxu wani abun d’awisu ya dakko guda d’aya yazo Daidai saitin kafarsa yana masa tafiyar tsutsa, mutsu mutsu prince ya soma Amma be bude idanuwansa ba , toshe bakinsa little yayi kar dariyar da yake dannewa ta fito waje ,kara sa masa d’awisun yayi Amma still be tashi ba , sai Tin hancinsa little ya dawo , da ya saka masa prince Zai sosa hancin, sai kuma ya koma kunnansa wani irin jutt da prince yaji ne yasa lokaci d’aya ya ware idanuwansa akan little, dariya little ya kyal’kyale Dashi yana ja baya, ganin yadda prince ya za bura rai a bace , “ sorry yaya prince , yaya bobo ne yace na tashe ka kuma Allah ka ta’bani sai na fad’a masa “, yana kaiwa nan ya bar d’akin ya nufi d’akin uncle , shima lokacin be farkava ahankali little ya Karasa inda yake Daidai kunnan uncle ya furta “ meow meow “, bashiri uncle ya ware idanuwansa , yanxu ma little dariya ya saka ganin yadda uncle ya ware idanuwansa, girgixa kai Kawai uncle yayi “ sorry uncle lokacin sallah yayi “, be jira cewar uncle ya yayi saurin barin d’akin dan yasan idan ya tsaya uncle zai iya ja masa kunne.
**** suna idar da sallah kamar kullum motsa jikin da ya zamar muku ‘ka’ida sukai, sai da Suka kammala motsa jikinsu sannan sukai breakfast tare , bobo be dad’e a gida ba ya fita,gidan yayi saura su uku.
Karfe 3:00 na rana wasu friends din prince suka zo gidan daman basu ta’ba zuwa ba sai yau da Suka dami prince akan suna san zuwa gidan su , yadda suka matsa masane yasa yace musu zasu iya zuwa , koda suka zo ba a barsu sunshiga ba saida akai musu full check up sannan d’aya daga cikin soldier ya kira cikin gidan , yadda suka ga sojoji ta ko ina na cikin gidan sai da ya rudar Musu da ciki, shima prince da biyu ya bari suka zo dan yasan daga yau ko mafarkin sake zuwa bazasuyi ba ,sai da prince ya basu umarnin shigowa sannan aka barsu, still sai da suka ajje motarsu a gate din farko d’aya daga cikin motocin sojojin ta karasar dasu, yadda suka ga sojoji duk inda Suka waiga yasa kowa ya kara shiga taitayinsa ga uban bundugogin da yake hannunsu, duk da suma ba talakawa bane amma yadda Suka ga gidan su prince sai da ya sace musu gwiwa d’aya daga cikin su da basu fiya magana sosai ba aranshi tunanin yadda zai kulla abota da prince Sosai yadda zatafi ta kowa yake , Daidai wani wajan shakatawa sojan ya kaisu dan ko yana shan giya bazai tunkare cikin gidan dasu ba , suna zuwan suka tarar da little da prince a tsaye, ri’ke kugu little yayi yana bunsu da kallo yadda yaga shigarsu ma kadai saida ta bashi haushi hatta prince sai da ya ta’be baki musamman colour da suka feffesa a kansu ga wasu uwan sarka da zai nuna maka lallai turawan ne na gaske , suna ganin prince cike suka nufeshi suna kokarin rungumesa ya dakatar dasu , kan little suka nufa ya zuba musu eyes dinsa , take a Wajan suka shiga taitayinsu, James ne da wani soja cikin kaki suka yi serving d’insu , shidai little yana tsaye yana binsu da kallo , tunanin yadda zaiyi maganinsu kawai yake cikin zuciyarsa , suma abokanan prince lokaci zuwa lokaci suna dago da kansu gudun kar wani soja ya nufosu dan lokacin dasu James suka zo wjan saura kadan d’aya ya saki futsari, wata irin dariya little ya kwashe da ita lokaci d’aya Sabida idea din da yazo masa , gabaki d’aya cike da tsarguwa suka kallesa , gira prince ya d’aga masa shi kuma little ya lumshe masa ido yana barin Wajan , kara bin babban wajan shakatawar sukai da kallo da sai faman tashin kamshi yake , da flower da suke kada iska me dadi, d’aya daga cikin friends din prince mesuna john ya dago wani pizza zai saka a baki yaji kamar ‘kara , be kawo komai a ransaba ya saka pizza dinsa a baki , wani karan ya kumaji hakan yasashi ya d’an waiga be san lokacin da ya kifa kan center din da akai serving d’insu ba ,fitsarin da sukaga ya sakine yasa suka tsaya kallansa ga wani farfadiya da suka ga yana kokarin yi , suma juyawar da zasuyi suka hango simba bakinsa abude sai faman jijjiga jikinsa yake , gabaki d’aya rud’ewa suma sukai jikinsu ya soma rawa, Aushe lokacin da little ya bar Wajan , simba yaje ya dakko musu, yadda suka ga simba na tunkarosune ya kara hautsina musu ciki gabaki d’aya sun rude, a fakaice little da ya la’be ya sakar masa fito, wani irin zabura da simba yayi ya nufesu a guje suma haka suka saka gudu suna ihun neman a gaji, john dake karshe simba ya tarfa, fashewa da kuka john yayi yana ihu, cikin zabura simba ya janyo wandansa ya kifar dashi take a Wajan john ya suma lokacin da simba ya dora masa kafarsa d’aya a ciki. Thomas da mark da suka arta kuwa basu tsaya a ko ina ba sai wajan da su bruno suke zama , sai faman sauke ajiyar zuciyar ta shin hankali suke , bombom dinsa mark ya taba kafun ya kai hanci da Sauri ya cire sabida warin kashin da ya fara, Thomas na mi’kewa tsaye yaga su bruno tsats tsaye Suna kallansu, shima Thomas kashi yaji yana zubo masa daman tun haduwarsa da simba ya saki nashi futsarin tashin hankali , suma bruno gadan gadan suka nufosu take a Wajan suka soma haushi da karfi, duk wnda ya kallesu sai ya zabura musamman ydda suka samu horo gasu manya , suma ja da baya suka somayi hankali a tashe bakin marks sai motsi yake ko magana ya kasa , Thomas kuwa karamar bishiyar dake wajan yake kokarin d’anewa , ai kafin kace me su Bruno sun biyo su abaya , abun mamaki ko ta ‘basu basuyi ba sai gudu da Suke ta sasu cikin gidan ,iya jigata kam sun jigata basu san ya akai ba sai ganinsu sukai kusa da john simba na zaune a wajan, ga su bruno da suka zagaye su ba shiru suma kowannansu ya sume , wata iriyar shegiyar dariya little da bobo Suka saki har da tafawa , sun tabbata ko amafarki bazasu kara gigin tunanin zuwa koda hanyar nan bace , Dan ruwa little ya fesa musu take suka farka , ko kallan inda prince yake basuyiba Suka nufi babban gate din gidan a guje duk da Nisan wajan kosu basusan inda suke takawaba, prince sai faman kwalla muku kira yake akan su dawo amma ko wai waye babu Wanda yayi , little da prince tsabar mugunta har da zama” yan iskan karya “ cewar little , hatta sojojin da suke wajan duk abunda yake faruwa sun gani amma tsabar mugunta babu Wanda ya temakawa su john. Sai da Suka tsagaita kafun little ya mayar da simba, saida suka tabbatar sun saita nutsuwarsu sannan suka shiga cikin gida sabida fadan uncle da zasu sha idan ya samu labarin abunda sukai.
IBTISSAM YA DAWO 300 yanxu , pay your money into 2681892316 Aisha umar , zenith bank sai a turo shedar biya ta wannan number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨
Littafin IBTISSAM is now 300 instead of 500 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar sa, to a rashi sani ne .
💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
Season__12
Karfe 9:30 gabaki d’aya suna zaune , sai alokacin suka had’u da bobo , yadda suka ga yana binsu da kallo ne yasa suka sha Jinin jikinsu “ me kuka aikata ?”, girgiza kai little ya soma , shima prince kallansa yayi yana sosa ‘ke ya “ yaya bobo babu fa abunda mukayi “, fear god prince “,kun tabbata? “ bobo ya ‘kara tanbayarsu, kallan juna sukai sabida sunsan bazasu iya yimasa karya ba, and suna gudun fad’a masa gaskiya karya hukunta su , shurun da sukaine ya ‘kara