cikin zuciyarsa , bobo tsaya kallansu kawai yayi ganin farinciki shinfid’e kan fuskarsu musamman little da kullum yake so yaga murmushi akan face d’insa , girgiza mata kai little yayi “ Yaya nane fa , bayashan jini”, kanta Abla tayi knodding “ kayi hakuri , na d’auka yana shan jini”, shikenan na hakura , amma ne yasa kika ‘kinshan magani? Ko bakyaso ki warke ?” Wasu hawayene suka soma gangarowa Abla , “ zasu cutar danine kamar ydda suka kashe mun Arwa” da Sauri prince ya kalleta , little ma kallanta yayi jin kwalla na zuwar masa ganin tana kuka , shima bobo yadda yaga sun canza reaction d’in face d’insu ne yji babu dad’i cikin ransa , karki “damu babu Wanda zai miki komai kinji?” Cewar prince yana ‘karasowa kusa da little, itama kanta ta jinjina masa “ bana san nan wajan ku tafi dani” lokaci d’aya little da prince suka juya wajan bobo , harararsu yayi alamar baku da hankali, “ yaya…” cewar little , d’aga masa hannu bobo yayi , “ let go , ina da abunyi”, be basu chance d’in magana ba ya bar d’akın , kallanta prince yayi little sukai , sudai harga Allah sunji suna san tadawo gidan su amma sunsan big boss bazai ta’ba yadda ba , da Sauri little ya mike yana furta “ ina zuwa “ shima prince bayan sa yabi suka bar d’akin, suna fita Abla ta zame ta kwanta akan tiles din hawayen da take d’azu ne suka cigaba da sakko mata .
Suna fitowa falour suka tarar da Bobo yana jiransu da Sauri little ya ‘karasa inda yake “ yaya please ! Yaya please mutafi da ita gidan mu, Dan Allah” kallan baka da hankali bobo yayi masa kafun ya furta “ bansan wannan shiriritan little kasan abunda kake fad’a bazai faruba…” be ‘karasa prince ma ya furta “ Dan Allah yaya bobo, nasan zaka iya ro’kan yaya big boss”, girgiza kansa bobo yayi “ bazai ta’ba yadda ba da alama har yanxu baku san yayankuba,”Lokaci d’aya little ya soma hawaye tare da folding hannunsa “ yaya dan Allah? Just for me please, idan ta warke sai ta tafi kaji” No” cewar bobo, kafun ya kallesu rai a had’e “ stop this dramer , let’s go home” yana juyawa lokaci d’aya kamar almara jikin little ya soma jijjiga bana wasa ba, hannunsa d’aya dafe da zuciyarsa, da ‘karfi prince ya furta “ Little” , juyowar da bobo zaiyi yaga little da fe da zuciyar sa , da Sauri ya ‘karaso Inda yake , “ Little Menene haka ? Nace ka kwantar da hankalinka ko?” Amma ina little gabaki d’aya baya jin me yake cewa sabida yadda kirjinsa yake sama da kasa , abunda be ta’ba faruwa ba, hugging d’insa bobo yayi cikin cool voice ya soma magana “ calm down please zamu tafi tare da ita , just calm down” a hankali rawan jikinsa ya soma raguwa , bugun zuciyarsa ya fara daidaita , da Sauri da Sauri ya soma ajiyar zuciya , hawaye na sakko masa a ido ya kalli bobo, a hankali ya furta “ am sorry yaya bobo, ni ina daku amma ita bata da kowa , just once please mu tafi da ita”, murmushi bobo yayi masa “ zamu tafi da ita just calm down ok?” Kansa little ya jinjina masa , yana tashi zaune, shima prince hugging d’insa yayi “ calm down kaji?” Mi’kar dashi tsaye bobo yayi tare da ri’ke hannunsa shi kansa yasan abunda yake ‘ko’karin yi bame yiwuwa bane , amma kuma dole ya saka little da prince cikin farinciki, 22 years basu ta’ba ro’kon wani ya zauna da su ba sai yanxu? Bazai iya kallo ciwan little ya Tashi ba , Allah ya sani Little shine rauninsa a rayuwa , yadda yaga little ya ‘kura masa ido ne yasa ya sakar masa murmushi “ ke ka kirata” wani irin murmushi little ya saki me sauti yana nufar d’akin , tana kwance kamar d’azu , murmushi kwance akan face d’insa ya furta “ Hey !” Da Sauri Abla ta d’ago kanta , tana ganin little ta tashi zaune , murmushi ya kara sakar mata “ taho mutafi ko bakyasan zuwa gidan mu?” A hankali Abla ta furta “ zaku tafi dani?” Shima little da Sauri ya d’aga mata kai “ yanxu zamu tafi yaya yana jiran mu, taso mutafi”, da Sauri kuwa ta mike tsaye hawaye fal ranta ta nufo inda yake, suna fitowa falourn ta tarar da Dr Eli da bobo sai prince shima sai murmushi yake, fuskar bobo ma ba’a had’e ba yace musu “ Let’s go” wani Leda Dr Eli ta mi’ka wa little “ Her medicine” kar’ban ledar prince yayi tare da furta “ thank you “, dakanta tayi musu rakıyi zuwa bakin gate , Abla tana sa ‘kafarta a waje ta saka ihu tare da komawa ciki da saurin ta , kallanta little yayi tare da le’kawa waje babu kowa sai sojojinsu, ganin yadda jikinta ya d’au rawa lokaci guda “ menene?” Bobo ya tanbayeta , cikin rawa ta dunga nuna musu waje har ta soma hawaye ga wani irin Tsoro da ya bayyana akan face d’inta lokaci d’aya , “ babu kowa fa” cewar little , da Sauri ta fara girgiza musu kai hankali atashe gabaki d’aya ta birkice, dakansa bobo ya fita , sojojinsu daya gani kowa da bindiga a hannunsa ne ya fahimci tsoron su take ji , “ Babban aiki” cewar bobo cikin zuciyarsa, gabaki d’aya umarni ya bawa sojojin akan kowa ya shiga mota bayasan ganin su a waje, hakan ce kuwa ta faru hatta Robert cikin mota ya shiga , yayi saura babu kowa a waje , “ babu kowa let’s go” kanta ta soma girgiza masa , “ fine bari na kira su” da Sauri ta fito daga bayan little da ta ‘buya “ kayi hakuri” ta fad’a a sanyaye,” oya let’s go, kuma kika bud’emun baki sai na tarwatsa kanki da bindiga “cewar bobo, a hankali ta soma tafiya kamar bazata fitowa ba dan harga Allah bata san sojoji tana fitowa waje kuma ta tarar da babu har wani ajiyar zuciya tasauke, dakansa little ya bud’e mata back seat da ya zauna shi ya fara shiga sai itama ta shiga , bobo da prince suka zauna a inda suke , d’ago fuskar da zatayi kawai idanuwanta suka sauka kan kayan Robert , kuka take ‘ko’karin yi amma tana tsoran yi Sabida bobo da yake wajan , shiyasa ta takure jikinta waje d’aya ta ‘ki bari ta bud’e idanuwa, “ babu abunda zai Miki” cewar little shima ya gane tsoran so Robert take ji, ganin ta’ki sakin jikinta ne yasa ya kalli coat d’in jikinta , tun d’azu yake jin kamshin turaren big boss a ciki , kuma kamar ya ganta jiya a jikinsa shiyasa ya d’an kalleta tare da nuna coat din “ a ina kika sami wannan rigar?”itama kallan rigar tayi har wani murmushi ne ya d’an fito mata , cikin kasa kasa da murya ta furta “ Nima bansani ba , kawai ya lullu’beni da itane lokacin da wuta zai fad’o mun”, kinsan wanda ya temakekin? Little ya ‘kara tanbayar ta , kanta ta girgiza masa alamar ah ah, daga nan shima little be kuma tanbayar taba yayi mata shiru , gabaki d’aya maganar su a kunna bobo dan duk yaji me suke cewa duk da yadda sukai maganar ‘kasa ‘kasa , cikin ‘kan’kanin lokaci suka ‘karaso gida , sabida yadda ta sunkuyar da kanta ‘kasa ne yasa bata ga sojojin da suke layin ba , har suka shigo cikin gidan kuwa bata d’ago balantana taga sojojin da Suke wajan. Direct apartment d’insu sojojin nan sukai parking, lokaci d’aya suka fito gabaki d’ayansu,suka zagaye motar da su bobo suke ciki, bobo ne ya fara fitowa sai prince , sai kuma Abla da Prince ya bud’e wa ‘kofa tana fitowa little shima ya fito , d’agowar da zatayi ne taga sojojin d’azu zagaye da ita , wani irin ‘kara ta saki jikin har tsuma yake lokacin da ta gansu, fahimtar hakan yasa little ya ri’ko hannunta ganin yadda take ‘ko’karin komawa cikin motar “ babu abunda zasuyi miki” duk da haka taki tsayawa waje d’aga ga idanuwanta data kulle taki yadda ta bud’e su , alama bobo yayi musu da su bar Wajan , cikin ‘kan’kanin lokaci kuwa suka bar wajan , dukda ta ko ina akwai sojoji a cikin gidan “ shikenan karki bud’e idanuwanki yanxu zamu bar Wajan kinji?” Da Sauri ta girgiza masa kai amma har yanxu ta ‘ki bud’e idanuwanta , a haka suka nufi cikin part d’in idanuwanta a kulle , wani irin sanyi da ‘kam shine ya daki hancinta, duk da bata bud’e idanuwanta ba , laushin da taji a ‘kafarta jitake kamar kar ta dena jin sa Sabida yadda yake mata dad’i a ‘kafa , Uncle na zaune kan kujera suka shigo , mamaki ne ya kamasa ganin little tare da wata yarinya kyakkyawa ga idanuwanta a kulle ga little ya ri’ke mata hannunta har suka tsakiyar falourn, “bud’e idanuwanki babu kowa” a hankali kamar mara gaskiya ta fara bud’e idanuwanta , cikin Sauri kuma ta kulle su jikinta har rawa yake , hawayene suka soma sakko mata sosai a kan fuska , cikin rawar murya ta furta “ kace mun ku ba masu shan jini bane amma shine kuka Kaşönü Wajan yan yankan kai , dan Allah kuyi hakuri bazan kara binkuba” wani irin dariya ne ya kama Prince , kallan da bobo yayi masa ne yasa yayi saurin had’iye dariyarsa , uncle dai tsayawa kallansu yayi mamaki fal ransa , shi babban mamakinsu yadda yagansu da mace abunda bai ta’ba faruwa ba kenan “ gidan mune karki damu babu Wanda zai yanka miki kai” cewar little , cike da d’an masifa ta furta “ kayi al’kawari?” Eh nayi” cewar little cike da dan masifa Abla ta furta “ wallahi idan kayi mun karya kuma kai da Allah , Allah na yana ganin ka wallahi “ yanxu ma little amsa ya bata “ Na miki Al’kawari ai Nima Allah yana gani ba yanka mutane muke ba”, toh shiknn na yadda cewar Abla tana bud’e idanuwanta , yadda ta ga suna kallan ga tsarin gidan falourn su ne yasa ta kalli little kamar zatayi kuka hatta falourn taki yadda ta kalla “wallahi Allah sai ya kamaka , ko dai mutuwa mukai? Akasamu a aljanna?” Ba little da ya soma dariya ba hatta bobo da su uncle sai da sukayi dariya , cikin dariya little ya furta “ wallahi baki mutu ba” sai a lokacin ta d’ago kanta kad’an ta kalli falourn tare da daga hannunta sama “ Allah kana gani yace basashan Jini basa yanka mutane ,” sai kuma a karo na biyu ta ‘kara bud’e idanuwanta tana bin falourn da kallo, duk da a tsorace take kallansa sosai wajan yayi mata kallo, “ kai ta d’akin da zata zauna” cewar bobo yana zama kan kujera , “toh yaya”cewar little , itadai Abla sai binsa a baya take , duk yadda yayi su shiga elevator Abla kin shiga tayi wai zai siyar da ita , dole sai ta kan stairs suka biyu, itadai sai bin ko ina da kallo take a tsorace ta ki yadda tayi masa kallan kurinta, a 1 floor cikin wani d’an corridor little ya bud’e d’aya daga cikin doors d’in wajan da take da nata corridor d’in daban, Babban d’akine a wajan me shegen girma da ‘kayatuwa , cikin d’akin milk colour ne hatta designer din royal bed din dakin milk colour ne , ga wasu set da suke dashi da ya ‘ka wata d’akin kasan tuwar gadon d’akin me kamar shape din circle ne sai ya yiwa dakin kyau, gaban mudubin d’akin kamar ana rayuwa a ciki yadda yake cike taf da kaya a ciki, komai na set din gado kawai a ciki hatta bed side da kwaba duk a kwai a ciki ga wani medium milk carpet a cikin d’akin , daga gefensa ma doguwar sofa ce milk colour sai d’an center d’insa shima, iya haduwa d’akin ya haduwa ko wasu masu kudin albarka dan ba’karamun dukiya aka kashe wa d’akın ba , sosai Abla ta saki baki tana bin d’akin da kallo cike da tsantsan mamaki , haryanxu ba ta yadda ba mutuwa tayi ba Sabida ydda take ganin sabanin abubuwa masu kyau , shima d’akin sai tashin kamshi da sanyin Ac yake ta ko ina , murmushi little ya d’an sakar mata “ Nanne d’akin ki” kallan inda yace d’aki Abla tayi cike da mamaki , kafun ta ‘kara kallansa “ nan ne d’aki ? Kaji tsoran Allah fa” kansa ya jinjina mata “ Nanne d’akinki Dagaske , ki zauna a ciki kafun na kawo miki abinci , zo muje na nuna miki band’akin ki” yana fad’ar hakan ya nufi wata ‘kofar da Sauri ta bi bayansa suna shiga cikin ban d’akin ta kara ja baya “ nan kuma wani d’akine ?” No band’akine “ cewar little, yadda tsarin toilet din yake sosai zai bawa duk Wanda ya kalli band’akin sha’awa mutum ko yaddar da abu yayi akasa zai iya daukan kayansa Sabida yadda yake da matukar haske babu ko datti a cikin toilet , komai macikin ban d’akin na zamani ne sosai , ga wani dogon glass da yake sha’ke da sabulan wanka , sink ya kunna tare da nuna mata “ idan kina san kiyi alwala “ sannan ya nuna mata yadda zata kashe shima , sau biyu yana nuna mata , cikin toilet ma sai da ya nuna mata, hatta shaya da yadda zata shiga cikin glass wajan wanka saida ya nuna mata da sabulan wanka da shampoos gabaki d’aya sai da ya nuna mata , sosai tayi mamakin komai tunda take aiki a cikin gidan karuwai bata ta’ba ganin waje ne kyau kamar nan ba , cikin ‘kan’kanin lokaci ta fahimci duk abunda ya nuna mata , hatta mayuka da turare saida ya nuna mata , “ ki zauna anan yanxu zan kawo miki abinci “ zatayi magana yayi saurin furta “ Allah yana gani “ yana kai karshen maganarsa ya bar d’akin , sai a lokacin Abla take ‘karabin wajan da kallo , sosai ko ina tayi mata kai , tana kallan gaban mudubi ta kalli fuskarta bata san lokacin da murmushi ya kwace mata ba da har saida dimples dinta ya lo’ba , ko minti 5 little be yi ba ya dawo dauke da tray babba sha’ke da irin kayan abincinsu, sai alokacin yunwar da take ji sosai ya ‘kara tasar mata ganin Abinci , da Sauri ta saka hannu zata soma cin abincin harta manta da little da yake wajan cikin sauri ta d’aki wani samosa da gani tana sawa a baki tayi saurin futo dashi sabida bata saba cin irin abin cin ba , kamar zatayi kuka ganin ta kasa ci, fruit din da ta gani ne ta dauka, tana sawa a baki ta saki wani ajiyar zuciya , sosai ta soma cinsa , fahimtar yunwa take ji sosai ne yasa little barin mata dakin dan taci abincinta sosai.
Yana sakkowa falourn direct kujerar da uncle yake zaune akai ya zauna tare da ri’ko hannunsa “ please uncle ku Barta ta zauna “ gyara zama sosai uncle yayi yana kallansa , “ Bobo yayi mun bayanin komai little amma ko na Amince kasan yayanka bazai ta’ba amincewa ba , kasan halinsa sosai , ka bari bobo zai samar mata wani wajan da ban” bobo bai ce masa komai ba, prince shiru yayi shima , a hankali little ya furta “ please uncle just for me, mu kwada yi masa magana dan Allah “ dungure masa kai uncle yayi “ shikenan karkayi mun kuka naga kunnanta sun farayin red alamar kiris kake jira , bari ya zo amma ban maka al’kawarin zamanta ba Indai be amince ba , kansa Little ya jinjina duk da shima shi da cikakken hope d’in yaya big boss xai amince da zamanta , gabaki d’ayansu babu Wanda ya kuwa cewa komai banda bobo da ya nufi part d’insa , basu fi mintuna goma da zamaba Robert ya shigo da wasu manyan ledoji guda shida sai wata ‘karamar jakar trolley tare da ajje musu cike da girmamawa ya furta “the trolley is for madam from Dr Eli and this is for sir “ yana kai karshen zan cansa ya juya ya bar falourn , “ kayan da bobo ya sa aka wo mata ne “ cewar uncle , d’aukan kayan prince da little sukai tunda sun fahimci natane gabaki d’aya har trolley din suka nufi d’akin da take lokacin har ta gama cin abincin ta gaji da jiran dawowar little , Bakinsa d’auke da sallama suka shigo cikin d’akin shida prince , ko wannensu da murmushi kwance kan face d’insa , nuna mata kayan little yayi “ ki shirya sai ki Hutu idan , idan lokacin sallah yayi sai kiyi sallah , kinji “ wasu hawaye ne suka sakko mata “ Nagode sosai “ girgiza mata kai little yayi “ ki dena gode mana Allah zaki godewa , ki huta kinji baki da lapiya “ daga nan basu ‘kara bata chance d’in magana ba ,suka bar d’akın , sosai Abla Tasha kuka tunda take a rayuwa babu Wanda ya ta’ba kautata mata kamar yadda sukai mata , har cikin zuciyarta take jin kaunarsu, kallan kayan tayi sosai ta gane trolley din da suka shigo da ita Sabida irinta baturiyar jiya ta bata amma taki ta’bawa , kamar bazata ta’ba kayan ba sai kuma ta nufi inda trolley din take , tana bud’ewa tayi saurin rufewa sabida abinda taci karo da su, akaro na biyu ta ‘kara bud’e har kulle idanuwanta tayi sabida kunya , cikin akwatin wasu set din pant ne dayawa a ciki sai bra da ta sako mata a ciki , hatta pad