tsaftace yake .
Basu zauna a cikin d’akin ba sai takalmi kawai da Abla ta canza suka sakko, ATM d’insa bobo ya mika wa little “ oya ayi mata gyaran da ya fi nakowa and karku dad’e okay ?” Okay ya’ya kawai little yace masa suka kama hanyar fita , yau bala’I little yasaka akan babu me bunsu har saida bobo ya dakatar Dashi motoci biyu kawai suka tafi da ita .
Mintuna 34 ya kawo su Heena’s saloon, tundaga wajan saloon d’in mutum zai san ba na ‘kananan yara ba , saloon ne da manya mata masu ji da naira , ta’kama da tun’kawo suke zuwa saloon d’in sabida yadda ake kashe ma’kudan kudi a wajan dan sosai kayan wajan suke da tsad’a . Cikin harabar filin da manya manyan motoci sukai parking suka shiga amma tun kafin su ‘karasa wajan motocin su Robert sukai parking, little , prince da Abla suka fito, suna tafiya suna hira abunsu kwanin burgewa , Robert da captain kuma suna bunsu a bayan , sauran sojojin kuma suka tsaya a wajan motocinsu.
Suna shiga wata ma’aciyar Wajan ta ‘karasa inda suke da murmushi akan face d’inta ta furta “ how can I help?” Tanayi tana bin ko wannansu da kallo , sabida wani irin masifaffen kyau da sukai mata kamar karta dena kallansu “ da hannu little ya nuna mata kan Abla kafun ya furta “ Munasan saloon ne “ da Sauri ta nuna musu hanya tana furta “ this way “ tana gama suna binta a baya , tun farkon shigarsu wajan yan mata suka dunga bin su little da kallo , ko waccen su sai farii take yi ko zasu kulasu amma ko kallo basu ishesu ba shiyasa wasu daga cikinsu cike jin dole su samu hanyar yi wa Abla magana Sabida su sami damar yiwa su little magana , mata uku da ga cikin yan wajan ganin su Abla sun nufi ‘bangaran saloon yasa suma gabaki d’aya suka fasa abunda ya kawosu suka bi bayansu , acewarsu suma saloon za’ayi musu, wata matace ta fito daga office da alama Babbace a wajan ta kalli su Abla tana sakar musu murmushi dan sosai itama sukai mata kyau , duk da ashekaru zatayi 43 amma lokaci d’aya taji soyayyar little ta shigar mata zuciya , shiyasa ta sallami ma’aikaciyar ita kuma ta bud’e musu wani vip rom, sai faman gyara rigar jikinta take sabida ya kalleta , amma da ita da matacciya haka little ya d’auketa dan ko uppan be ce ba , apart from his family bakowa yake wa magana ba, hatta yan school d’insu kuwa , dan kwanda prince wani lokaci idan aka masa magana yana amsawa sama sama , amma banda little da ya koyo halin rashin kula bare a wajan big boss .
Inda suka shiga kamar vip haka wajan yake dan sosai wajan yake da kyau , yan mata ne guda 5 a Wajan sai wasu ma’aikata , komai na wajan a tsare yake cikin yanga matar ta nuna musu waje su zauna duk da yan matan da suke wajan , babu Wanda ya bi ta kanta sai Abla da Prince ya nuna mata , “ ayi mata da most expensive gyaran gashi , in ba damuwa zamu dawo nan da 1 hour in Angama mata “ cikin washe baki jin abinda prince yace matar tace “bakomai ko yanxu kuka ce ayi muku ma za’ayi muku” su kuma ragowar yan matan Wajan Abla suka zubawa ido Sabida gabaki d’ayansu ta karesu a kyau bazasu ta’ba had’awa ba , duk cikinsu kuma jikinta ya fi nasu gogewa dukda uban mayukan bleaching da suke anfani dashi , ga mamakin maganganun prince . Hannu little ya d’aga mata “ Lil zamu dawo okay ?” Itama hannu ta d’aga musu tare da furta “ Byee “ little har zai tafi sai kuma ya dawo bayan ya ciro phone d’insa a aljihu “ oya kiyi game or anything karki zauna so boring okay ?” Kanta tayi knodding tana furta “ thank you yaya little ,” shima prince hannu ya d’aga mata “ bye lil” itama “ bye yaya Prince tace masa “ tana juyowa bayan sun fita taga gabaki d’aya kusan hankalin yan matan suna kanta tunda Suka shigo hatta fitan su little akan idanuwansu.
Babu Wanda ta kula a cikinsu dukda yadda suka so na ni’ke mata amma ta d’aure face d’inta , tana har kar gabanta har akazo kanta , yadda suka ga gashin kanta sai da Suka kusan sakin baki , itama ma’aikaciyar wajan sosai ta yaba da yawan gashin Abla , cikin kware da sanin aikinsu ta fara gyarawa Abla gashinta , ko cikakkiyar 1 hour din ma ba’ayi ba aka kammala mata , ga wani ado da akai mata da gashin, ita kadai sai murmushi take wa kanta dan sosai kanta yayi kyau har wani iska iska takeji a kanta . ‘Daya daga cikin matan taso kar ‘bar number Abla wai zatayi ‘kawance da ita amma ganin babu fuska yasa ta waske amma duk da haka lokaci zuwa lokaci tana satar kallan Abla . Bata ‘kara 10 minutes a zaune ba su little suka dawo yanxu sun canza shiyar jikinsu , wasu kud’i prince ya d’auko a pocket dinsa masu yawa ko irgawa be yiba ya mi’ka musu , cikin Sauri Matar takar’ba dan kudin ya ninka kudin gyara Abla sosai.
Basu ‘bata lokaci ba suka bar saloon d’in , kai tsaye gida suka nufa , itama Abla d’akı ta koma tayi wanka sai bin dogon gashinta da aka gyara mata take da kallo ga yadda suka nannad’e mata gashi sosai yayi kyau , wani baby link d’in riga da wando ta saka sai top din ma pink sai rigar jiki da ta kasance white hatta wandan jikinta ma pink ne , wani baby pink d’in mayafi ta d’aura akanta bayan tayi sallar azahar d’inta, ta yi mamakin yadda period d’inta be zoba tuntuni sai yanxu da take jin alamun kamar ya kusa zuwa . Tana sakko ‘kasa lokacin da su little zasuci lunch, gabaki d’ayansu suka ci abin su , cikin rarrashi little ya furta “ Sis can you do me a favor plx ?” Da Sauri Abla ta jinjina masa kai dan ko me suka ce mata indai zata iyayinsa tayi wa kanta al’kawari zatayi dan bata da kamar su “ please zaki gyara mun part din yaya ?” Yadda ta zaro eyes d’inta ne cike da tsoro yayi saurin cewa “ yaya baya gida ai, please kinji ? Kafun ya dawo ai kin gama gyarawa , please “, murmushi ta sakar masa tana mi’kewa tsaye “ toh bari na fara kai wa simba abincinsa “, girgiza mata kai little yayi “ No karki damu da wannan already an kaiwa simba abincinsa , kawai part d’in yaya zaki gyara fa” , Tom shikenan cewar Abla, yau duk gabaki d’aya bata sanyashi cikin idanuwanta ba , jinta take kamar wata mara lapiya dan har cikin zuciyarta take san ‘kara sanyasa cikin idanuwanta.
Ta elevator su kahau har suwa part d’in Big boss, tun kafin ta shiga ciki taji wani irin daddad’an sanyi da kamshin turaran da ko a mafarki tajisa ta san mamallakin wanene , suna zuwa floor d’insa zuciyar ta cigaba da tsananta har wajan door d’in part d’insa sa Little yasaka turn print d’insa , lokaci d’aya gabaki d’aya ’kofar wajan ta bud’e , saurin lumshe idanu Abla Sabida wani irin abu da taji yana tsagar mata tun daga ‘kafarta har zuwa kwakwalwarta, lokaci d’aya wani irin dad’i ya ziyarceta duk yadda takeji d’azu sai taji komai ya tafi. Tunda Suka shigo cikin corridor d’insa take bin ko ina da kallo dukda ba wasu abubuwane Wajan ba amma sai da ta ‘karewa kowa ina kallo , d’akin da su little suka shigo kwana bin baya nan ya ‘kara bud’ewa bakinshi d’auke da sallama , itama Abla sallaman tayi lokacin da take shigowa ciki, a hankali bakinta ya fara furta “wow wow wow”Sabida yadda taga kyan falourn , sai take ga kamar yafi ko wana falo kyau a duniya duk da falourn ‘kasa ta sani amma sosai take bin tsarin wajan da kallo, “ let’s go” cewar little , ‘kofar next door da ya bud’e sai ta kasa tantance Wanda ya fi kyau tsakanin Wanda ta baro da wannan dan bil hakkı ta zama yar kauyen gaske ,abubuwa anfani little ya d’auko mata kafun ya nuna mata ‘kofar d’akin big boss “ sorry Little sister ! Idan kingama sai cikin bedroom d’in yaya “ murmushi ta sakar masa da har saida dimples dinta ya lotsa “ babu komai ai “ daga haka little ya bar falourn gabaki d’aya , ‘kugu Abla ta ri’ke Tanabin tsarin ko ina da falourn da kallo , sosai ta bawa idan ta abinci , gashi falourn gabaki d’aya babu datti , tass tass yake , a haka ta fara komawa falourn farko , shima saida ta bawa idanuwansa abinci sannan ta gyara ko ina , tsabar karanbani irin nata duk abunda taga be mata ba sai ta canza masa waje , cikin ‘kan’kanin lokaci ta canza tsarin gabaki d’aya falourn ya fito tass da dashi kwanin burgewa , d’ayar falourn ta koma shima ta gyara sa tasss kafun ta canza komai da ya dangance sa , shima bata d’au wani dogon lokaci ba ta gyara sosai , wani burder turare ta kunna ga sanyin Ac da yake ratsa ko ina , sai yake bata wani irin daddad’an ’kamshi me ‘kyatarwa .
Sanin cewa Big boss baya cikin gidan ne yasa ta nufi cikin bedroom d’insa Kai tsaye , mamaki da shock ne ya kamata lokaci d’aya dataga dan ‘kareran dakin Big boss da yayi biyar d’in nata , duk yadda take ganin kyaun d’akinta sai taga wanda ya ci uwan wancan a komi , hatta kayan cikin d’akin kowa ya gansu ya san ba ‘karamun nairace tayi kuka ba ,sai faman waigawa take tana kallan ko ina cike da ‘kauyanci, da ta juya wannan Side d’in sai ta juya wannan d’in ta kara kallansa , a maimakon ta gyara d’akin sai ta tsaya bin ko ina da kallo, tafi tsawan 10 minutes tana ‘karewa d’akin kallo musamman king side bed dinsa da komai na kai ya kasance white colour , a gyare tass dashi ji take kamar ta je ta d’ane kan gadon taji yadda laushin sa yake , ganin mayafin ta na ‘ko’karin damunta yasa ta ciresa gabaki d’aya ,lokaci d’aya dogon tulin gashinta da ya zo mata har wajan kwankwasanta sabida yadda yasha gyara sai roto yake dan hatta nad’in da akai mata ya warware, top d’in rigar ta ma cireta tayi sabida taji dad’in yin aikin da kyau , yadda kayan jikinta suka fito da ita sosai Coca Cola shape d’inta ya fito dukda Wandan jikinta be matse ta ba , ga baiwar gashi da Allah ya bata , ga hasken fatarta da akullum ‘kara murjewa take , lokaci d’aya farinciki ya mamaye zuciyarta, cikin nishad’i ta gyara d’akin gabaki d’aya , da karan baninta ta d’auko wani turaren da ta gani ta geffesa a d’akin cikin ‘kan’kanin lokaci wani irin kamshi ya karad’e d’akin dukda lokacin da ta shigo cikin d’akin a gyara yake hakan be sa da ‘kara gyaramasa ya banbanta ba , duk Wanda yaga gyaran d’akin yasan kwararriyace ta gyara sa dan sosai tagyarasa, ‘kofar da ta gani ta nufa acewarta zata le’ka taga yadda toilet d’insa yake , amma tana bud’e ‘kofar bakin ya soma rawa dan sosai cikin wajan yayi bala’in tsaruwa , gabaki d’aya sip sip ne a ciki na jerun kayan sawarsa da yayi mugun kyau, ga ‘bangaran takalma daban, suits daban , belet da ban hatta hat d’in da yake sawa kowa da abun sawarsa, d’akin ba ‘karamin girmane dashi ba amma duk gabaki d’aya kayan Big boss ne a ciki masu kyau da tafiya da hankalin mutum, duk da hakan Abla daddara ta shigo cikin d’akin yadda zata kyan sa sosai sai kace wani Wajan saida kayan sa wa , da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai take bin kayan tana kallansu dan gabaki d’aya hankalinta ya karkata kan hatan sawarsa , Daidai wani gaban mudibi da yake tsa’ke da turaruka kala kala ta nufa, wani kwalbar turaran Dior ne ya d’au hankalinta shiyasa ta d’akkosa tanasan jin kamshin sa,ba zato ba tsammani aka bud’e kofar cikin wajan , a firgice Abla ta saki kwalbar turaren Dior d’in hannunta tana juyowa .
MANAGE 👏👏👏👏….
https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨
🦅🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅🦅
M.W.A
AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.
S____28💞
Wanda ta ganine yasa lokaci d’aya ta saka ihun da ya ‘kara razanata , cike da rud’u jikinta ya soma rawa musamman yadda taga Babu kaya a jikinsa sai farar rigar wanka da ya saka , mamakin ganin sa ne yasa lokaci d’aya wani irin shock ya kamata har ta kasa motsa ko da finger d’inta ne , bakinta yayi mata nauyin da bazata iya furta ko kalma d’aya ba ,sai zuciyarta da take harbawa cikin sauri kamar zata tsaga ‘kirjinta ta fito waje , “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Kawai take maimaitawa cikin zuciyarta “, sosai ‘kafafuwanta suka sage kamar me shirin fad’uwa ‘kas , dan wani irin jiri jiri ne take ji kamar yake ‘ko’karin kayar da ita .
A hankali ya d’an lumshe eyes d’insa Sabida ihun da tayi har cikin kunnansa da ya ‘Kara tunzurashi, amma ko kad’an babu me fahimtar hakan Sabida yadda face d’insa take kullum babu fara’a sai damshi damshin ruwa da yake sakkowa tundaga kan ba’kar sumar gashin kansa da ta sakko masa har wajan kafad’unsa .
A hankali ya nufi right side d’in d’akin , inda wasu jerun wasu white towels suke da yawa ya nufa , guda d’aya ya d’auko , lokaci d’aya ya soma goge kansa a hankali kamar Wanda aka saka dole , ko cikakken mintuna 3 beyiba ya fara takawa a hankali cikin takun izzarsa kamar kullum da ya saba , cikin nutsuwa da kwarjini ya nufi gaban mirror Inda Abla take tsaye a wajan, har Lokacin kuma be nuna yasan da wata halitta a cikin d’akin ba , yadda taga yana nufo gaban mirror d’innan ne ya ‘kara haushina mata ciki, wani irin fitsarine ya kamata lokaci d’aya , da ‘kyar ta iya jan zuciyarta lokacin da tayi Sauri barin gaban mudubin. Cikin rawar murya da take shirin saka kuka soma magana a rarrabe “ Dan Allah kayi hakuri , wallahi su’bucemun yayi dan Allah kayi hakuri ,” kamar wacce tayi magana da gunki dan gabaki d’aya idan ka kalli face d’insa sai ka rantse babu kowa a jikinsa , ko nuni da alamar da zai nuna yasan da mutum a cikin d’akin babu , komai cikin nutsuwa yake yin abubuwansa , kuka ne ya zo wa Abla amma tayi saurin had’iyeshi cikin yar fa hannu ta ‘kara maimaita wa “ Dan Allah kayi hakuri…” bata kai ga ‘Karshen maganar da take so tayi ba taga Big boss yana ‘ko’karin kwance whiterobe d’in jikinsa . Cikin wani irin zabura Abla ta ‘kara sakin kukan da ya saka ya d’an d’ago da kansa dukda be kalli side d’inta ba amma yadda idanuwansa lokaci d’aya ya soma ja zaka gane ba ‘karamin baci ransa yayi ba . Abla kuwa tunda ta ‘kara sakin ‘karar nan bata dira a ko ina ba sai bakin ‘kofa , ganin ta samu damar barin d’akin yasa cikin azama ta bud’e ta saka gudu da iya ‘karfinta . Tana fitowa mayafinta kawai ta d’aura a rud’e sai Top d’in rigar ta da ta d’ora ko damu da yadda ta saka a bai bai batayi ba , hatta mayafin kanta kawai yafawa tayi shima , cikin Sauri ta nufi ‘kofar fita daga cikin d’akin tajira a rufe gam , a fili ta furta “ na shiga uku ni Abla , wani karan banine ya sa na shigar masa cikin d’aki , nasan yau shikenan, shikenan na mutu na lalace “ ita kanta wasu maganganun batasan tana furta suba , sabida yadda ta rud’e so take Kawai taga ta fita daga cikin d’akin dan any moment fıtsarin da take ji zai iya kwace mata . Hankalinta gabaki d’aya baya jikinta , password d’in bud’e d’akin take ta gwadawa amma da ta saka wani red d’in na’ura xai bada Sauri “ No” , tun tana tunanin bud’e kofar me sauki ne har ta fashe da kuka tana zamewa ‘kasa ganin yanxu gabaki d’aya bata da wata hanyar tsira ta sani yau me kwatanta a wajan sa sai Allah , musamman idan ta turo simba sai taji wani saban kukan yana ‘kara mata , yadda ta zama a ‘kasa haka ta had’e waje d’aya ta ‘kara ta kure jikinta ga kukan da ta soma tun kafin yayi mata komai, fuskarta harta soma komawa red colour , batasan lokacin da ta kwanta a Wajan ba , tun tana kukan kad’an kad’an har nunfashinta ya fara canzawa alamar bacci ya d’auketa.