bobo yayi tare da kallan karnukan yana tsugunnawa a inda suke , gashin Ruby ya fara shafawa , sannan ya shafa na Roxy, ko wannansu sai karka d’amasa gashi suke , yana cire hannunsa sai ya d’aura akan scout da gashinsa yake fari da baki, gabaki d’aya karnukan sun zubawa bobo ido , hatta Rosie da Bruno sai faman futo da harshensu suke “ start going “, cewar bobo , haushi suka soma yi masa na kusan 5 second kafun gabaki d’ayansu su kashi kashi biyar kowa da side d’in da ya nufa . Bobo yana d’agowa little ya ri’ke’ masa hannu “ yaya bobo yunwa nake ji , let’s it kaji “, kanshi bobo ya d’aga masa har suka ‘karaso inda prince yake , shi kad’ai sai faman hararar little yake , suna zuwa kofar shiga suka tarar da uncle , shima hannunsa little ya kama suka shiga ciki, kai tsaye dinning area suka nufa , suna shiga wasu sojoji sanye da suit d’insu suka nufi dinning area d’in,ko wanne suka ja masa kujera ya zauna sannan su james suka soma serving kowa favorite food d’inshi da yake san ci.
Tunda Suka soma cin abinci babu Wanda yayi magana har saida suka koma cikin falourn, prince da little game suka soma bugawa , bobo da uncle kuma suna zaune kan kujera suna hira , lokacin da uncle yayi maganar dawowan big boss lokaci d’aya prince da little suka ajje game d’insu , “ uncle Yaushe zai dawo plx ?”, cewar little,” kana da number d’insa ai sai ka kirashi kaji “ yaya bobo Yaushe zai dawo ?”, cewar prince , tunda yaji Ance big boss zai dawo ya shiga taitayinsa , dan duk lokacin da big boss ya dawo sai yaji ajikinsa , bobo yafahimci hakan shiyasa yace masa “ bayanxu zai dawo ba tukunna , akwai abunda zaiyi a Uk”, bakinsa little ya d’an turo “ yaya bobo toh mu muje U.K sai mu ganshi muyi masa surprise “ , ba bobo ba hatta uncle saida ya dara prince kuwa hararar little yayi “ big boss d’in zakayiwa suprise ? Little ka zama rigimamme fa , kamanta wanene big boss d’in naka da Alama sabida baka ganinsa kwana biyu” cikin pity face yace “ no yaya bobo kawai nayi kewarsane and nasan aiki ya masa yawa , and duk lokacin da ya dawo bazan bari ya tafi shi kadai ba “, shi yaya big boss din ?”, da Sauri cewar prince “ gira d’aya little ya d’aga masa , cikin kashe ido “ sannan zan fad’a masa rashin jin da kake yi “ cewar little hannu prince ya saka zai janyo sa little yayi saurin Tashi ya koma kusa da bobo “ yaya bobo kaga ya prince ko ?”, wayarsa bobo ya ciro yana mi’kawa prince “ kirawo Yayansa ka fad’a masa “, wani irin sufa little yayi ya koma wajan prince “ Haba yaya prince d’ina nifa wasa nake Kaji ,kaga yanxu dare ma yayi let’s go and sleep “, little ka fita idona fa , ka rainani “ ni wallahi ban rainaka ba , ina sankane sosai kamar yadda nake san yaya bobo, yaya big boss , uncle , kaji yaya prince d’ina “, Allah ya shiryeka cewar prince yana mikewa , gabaki d’ayansu hugging d’in bobo da uncle sukai kafun suyi musu sai da safe suka nufi d’akinsu . “ he missed him, yana missing big boss sosai and ya kamata ya dawo ko sabida little d’insa da ya bari”, shima bobo murmushi ya saki ,” Ai kwanda ya dawo ni ciwan kai suke samun ko zasu shiga taitayinsu”, cewar bobo, “ you all missed him and we all missed him, yana dawowa wannan rigimar ta little shi kadai ke iya handling d’insa “, ni uncle banyi missing dinsa ba , kawai ya dawo Sabida wannan babyn nasa yana samun ciwan kai sosai “, yanxu ma dariya uncle ya saki “ that’s why I love you all, little shine maganinku ai musamman big boss da babu me iya controlling dinsa , that’s why nake san naga auranku “, uncle plx cewar bobo yana d’an Kauda fuska “kunsan it can’t be possible kuce zaku zauna babu aure ko? Hatta yayanku, he have to get married too, duk yan matan da suke yawan sanshi kamar suyi hauka , wannan decision d’in da kuka d’aukar wa kanku bashine solution ba “, uncle “ cewar bobo tun da uncle ya soma maganar aure yake controlling kansa ,” uncle plx karka yi masa maganar aure , everything can happen , kasan zuciyar sa idan ransa ya ‘baci, controlling d’insa yana da wahalar gaske , we don’t need any person more in our life’s , mu biyar d’inmu is okay”, murmushin manya Kawai uncle ya saki “ yasani shima bobo yana da saukin kai sosai, amma yana da zafi idan akai musu maganar aure,duk da a yawan cin lokaci ya kwammace ayi masa maganar da a yiwa big boss dan ko wanene ranshi sai ya ‘baci, shiyasa uncle da yaga ran bobo yana ‘ko’karin ‘baci shima yayi shiru ya bar maganar “, mi’kewa tsaye uncle yayi “ I have to sleep early nima , good night “, bobo be ce masa komai ba sai bayansa da yabi har zuwa part d’insa , sai da ya tabbatar uncle ya kwanta kan gadonsa duk da beyi bacci ba sannan ya yun’kura zai tashi uncle ya ri’ke masa hannu “ it has been years now , bazaku yafe musu ba ? Ka fishi sau’kin kai, zuciyarsa tana da zafi sosai “ murmushin ya’ke bobo ya saki “ uncle how many years ? Duk wannan tsawan shekarun sun damu da inda muke ? Muna raye ko mun mutu sun sani ? Basu damu ba, we don’t need them all Uncle , su suka zama silar zanjawar sa , ba haka yake ba Amma ta dalilinsu komai ya canja , ya ‘bata farin cikinsa sabida yaga munyi farin ciki, ya kwana a zaune beyi bacci ba Sabida mu , prince , Little Menene laifinsu? Hatta prince bazai iya tuna komai ba , little fa? He’s so called father ko sau d’aya be ta’ba d’aukarsa ba 22 years of his life, and his so called mother ko d’uminta bai samu ba , big boss Kawai ya sani as his mother and his father , uncle shine kake so mutuna su aranmu? Please uncle stop it ! Good night”, bejira uncle ya ‘kara magana ba ya kashe masa light ya barmasa dumm light tare da kullo masa d’akin gabaki d’aya, a babban falon su ya zauna , ranshi a ‘bace sabida tuno abunda baya bu’katar turowa a rayuwar sa gaba’ki d’aya , siririyar diamond d’in wuyansa ya shafa , “ why ! Why! We don’t need you , and bazamu ta’ba zama tare ba , cire zancen yayi gabaki d’aya a ransa , saida ya tabbatar da lapiyar tsaron gidan gabaki d’aya , hatta zakin big boss , da sauran ‘bangaran zoo kullum sai an tabbatar da lapiyarsu, su Bruno kuwa gabaki d’aya an sake su sai faman shawagi suke cikin babban compound din gidan ga sojoji da suke shawagi kamar ba dare ba . Yana shiga d’akinsu little ya tarar prince yayi bacci saura little dake sanye da kayan bacci blue colour sai kuranin dake hannunsa ,yana ganin bobo ya ajje kur’anin “ little dare yayi, you have to sleep up , okay “, okay “ cewar little yana kwanta wa bayan ya ajje kur’anin a ma’a danarsa, a gefen gadan sa bobo ya zauna har saida ya tabbatar little ya kwanta sannan yayi masa addua, zai tashi little ya rike masa hannu,bobo na juyowa little ya sakar masa murmushi “ ina sanka yaya bobo “, shima bobon murmushi ya sakar masa “ Nima isan little d’ina , good night “, bobo be bar d’akin ba sai da yayiwa prince shima addua kamar yadda yayiwa little sannan ya bar musu dumm light kawai .
🍂🍂🍂🍂
✨✨✨✨✨✨
ADEMOLA ADETOKUMBO STREETS
Runtse idanuwanta Arwa tayi lokacin da Abla ta kira sunanta, ga wasu irin hawaye masu zafi da rad’ad’i da suke zubo mata cikin idanu, da Sauri Abla ta ‘karasa shigowa cikin d’akin zanin gadon da tagani a ‘kasa tayi saurin raruma ta lullu’bawa Arwa a jikinta da take faman karewa Allah ya Rufa mata asiri ma akwai under wears a jikinta, a hankali kuma ta fara tsuntar kayan arwa tana mi’ka mata, duk abun nan da take uwar karuwai na tsaye ri’ke da towel ajikinta, Zinariyya da yar shila ma kowa sanye da wani d’an iskan towel , debeka na tsaye gaban wani camera da take shirin fara d’auka , ilham nagefenta, Ko wa jira yake yaga reaction d’in Abla amma babu Wanda ta d’ago ta kalla saida ta tabbatar Arwa ta saka kayanta taja hannunta zuwa ‘kofar d’akin, cikin ‘kasa ‘kasa ta yadda bazasu jiba Abla tace Mata ta jirata a d’aki, da Sauri Abla ta d’aga mata kai tana barin Wajan , sai a lokacin abla ta kallesu idanuwanta har sun d’an canza , cikin Sauri ilham zatayi magana Abla ta dakatar da ita tana kallan uwar karuwai cikin tsana , itama uwar karuwai rai a’bace take kallan abla ganin ta ‘bata mata shirin ta , bayan vidoe d’in da zata d’auka suna lesbian da Arwa ba ‘karamun kud’i zata samu ba , amma lokaci d’aya Abla ta ‘bata mata shirin komai ,”idan kin za’bi lalata ‘ya’yan mutane kina tunanin baki da d’a ko ‘ya da za’ayi wa kwatankwacin abunda kikai karki manta kina da ahali , yadda kike ‘bata ‘yayan mutane Kema Haka za’ayi miki sabida kamatudinu tudan , ko me kukai sai anyi muku, yadda kuka ‘bata rayuwar yara da yawa ku jira sakayya wajan ubangiji, a haife gabaki d’aya zaki haife su amma duk da wannan shekarun naki kece kike ‘bata tarbiyarsu Sabida basu da gata ? Tur da halinki”, ke cewar ‘yar shila “, da ‘karfi itama Abla rai a ‘bace ta daka mata tsawan da duk na cikin d’akin saida suka d’an razana da jin sakkunta, musamman yadda take magana babu tsoro tattare da ita “kin dad’e kina yi mun abu ina kyaleki Amma gabaki d’ayanku baku san kawaici ba , duk yadda mutum Yaso ya danne abu sai kunsa ya fallasashi, daga rana irin ta yau duk Wanda ya ce zaiyi mun abu kamar yadda ya saba yimun ada Zaiga asalina , karku d’auka a Abla da kuke yiwa komai nake muku gamana , a asalin sunana ibtissam nake , shekara biyu na shanye duk ‘bacin ranku amma banda yanzu,” kuma ta juya kan ilham da take tsaye tana kallan abla da mamaki “ kin bani mamaki ilham , da hankalinki da iliminki? Agaban idanuwanki ake ‘ko’karin lalata tar biyar yar uwarki musulma amma kina gani ? Tir da irin masu halinki “, tana kai zancenta ta juya zata tafi taji saukar muryar uwar karuwai “Naji kome kika fad’a Amma karki manta gida gida nane , dole mutum ya za’ba ko ya bautamun ko ya dinga biyana kudin kwana, tunda ko uwarki da ubanki baki sansuba balantana kiyi fariya kina da gida ko ahali”, maganar uwar karuwai ya ta’ba mata zuciya har kwalla taji na ‘ko’karin sakko mata tayi saurin had’iye ta , tana jin zafi duk dokacin da aka Goranta mata ,juyowa tayi fuskarta d’auke da murmushin bakin ciki , “ Indai akan biya ne duk sati zan dunga biyanki kud’in kwanan store d’in da nake Amma daga yanxu babu duk wacce tayi ‘ko’karin tunkarata ko tunanin yimun wani abu tabbas zataga‘bacin rai na , tana kai karshen zancenta tabar d’akin ta bugo musu da ‘karfin, jikin kofar ta tsaya hawayen da take ri’ke wa ne suka soma wanke mata fuskar sosai take hawaye zuciyar ta d’aci take mata sosai, tuno arwa ysa tayi saurin nufar d’akinsu , zuciyar ta fall tunanin saba’ar da zata fara har ta biya uwar karuwai.
A cikin d’akin kuma d’an tsaki ilham ta saki “ yar shila shikenan kunja Abla ta ganeni tun farko sai da na fad’a muku kome zakuyi dani ya Xama cikin sirri amma lokaci d’aya kun ‘bata komai , yanxu bansan na zanyi ba karku manta 3million zasu samu idan mukai wa Arwa da Abla vidoe tsirara musamman yanxu da dama tazo mana ,sai da nace muku ku bari dare yayi sai ayi vidoen Arwa Amma gabaki d’aya kun bata shirin yanxu yadda kukaga Abla tayi magana babu tsoro ko shakka a cikin idanuwanta tabbas bazata ‘kara bari wani ya takataba. Nasan Arwa yanxu zata fallasa mana duk wani sirri. Kusa da ita uwar karuwai ta matso ba kunya ko ganin irin su Zinariyya tajanyo ilham jikinta “ baby karki damu duk bugace take yi , dole ta zauna damu har burin mu yacika sabida na tabbata bata da kudin da zata dunga bamu duk sati , dole kinga tayi mun bauta kicire damuwar nan aranki, kamar yadda na gur’bata Aneesa da husna suma sai na gur’batasu dan bariki shine jigon mu, me za’ayi da wad’an da basa bariki, duka ilimin ‘karya take na tabbata wajen da take zuwa taba yini kwakuleta suke suma kawai ki saki jikin ki mu shana baby, yanxu ki kwantar da hankalinki kicire zancanta mu d’an huta , kamar ki na cikin fridge na ajje mata “, gabaki d’aya sun gansu da bayanan uwar karuwai shiyasa debeka ta kashe musu fitula , dariya da cewa Suka d’auka cikin duhu sai nunfashi da Suke saki kawai.
****** Abla tana shiga d’akin ta tarar da arwa kwance tana kuka , a gefenta abla ta zauna, itama Arwa tana ganin abla ta Tashi zaune , cikin kuka ta soma magana “ Abla na gaji da wannan kuncin rayuwar da muke ciki, mutane kullum burunsu su lalata marasa gata , Menene aibun mu dan muntashi cikin maraici? Ko maraicin da muke ciki ne yasa kowa burinsa yayi lalata da mu? Dabadan kinzo da wuri ba Abla da tuni sun lalatamun martabata, kece kadai kike sona , ban sani ba kuma bansan lokacin da ilham take cikinsuba abun ya d’aure mun lokacin da na gansu tare ga Aneesa da husna suma sun lalata musu rayuwa, ji nake Abla dama wani mummunan abu zai sameni na mutu ko zan huta da wannan takaicin rayuwar”. Saurin toshe mata baki abla tayi “ inda rai ya ‘baci hankali ai be gujewa, ko Menene ya samemu jarabawace daga Allah, yana sane damu sannan yasan halin da muke ciki, wani jirkirin Alkairi, kindunga kyautata Alkairi cikin zuciyar ki”, duk yadda ran abla yake a ‘bace Hakan be hana tayiwa Arwa lallausan lafazi me kwantar da hankali ba . “Abla yunwa nake ji, ina tunanin bara zan fara ko zamu samu abinci dan bazan kara cin komai na zunubin suba . Inda ta ajje kudin ta ta shafa taji suna nan, “ zo mufita “ cewar abla tana ri’ke hannun arwa, a duniya dari biyar d’in da aka bata sadaka ce kawai tayi mata ragowa gashi tace duk sati zata dunga biyan uwar karuwai kud’in kwananta, ‘kosai ta siyowa Arwa na hamsin, ganin kudin na yin ‘kasa yasa ta hakura daci tabarwa arwa , ita kuma ta Samu gyad’ar ashirin taci , suna gama ci gidan ruwan da Abla ta ta’ba zuwa sukaje amma sosai akwai layi saida suka bari aka gama zubawa manya mota ruwan kafun azo kansu , yau ma talatin ta bayar aka bata guda 9, haka suka d’auka suka fara yawo Dashi cikin traffic ga ranar da ake me zafi ci amma haka suka shiga cikin traffic ko za a samu me shiyan ruwa , sun dad’e suna yawa daga traffic zuwa traffic kafin a siye musu ruwan , cike da farinciki suka ‘kara komawa a wannan karan na 40 aka ‘kara musu guda biyar akai , su biyu sai yawo suke cikin zafin ranar, suna cikin tafiya ko d’ad’d’an silifas din Abla da yayi mata kad’an ya tsinke, cikin da bara ta samo leda ta kulle takalmin ta mayar ‘kafarta tunda bata da kudin siyan wani , ko da tanadashi ma bazata siya ba sabida kudin da zata bawa uwar karuwai. Har wajan karfe biyu suna abu d’aya saidai su Samu waje suyi sallah kafun su cigaba , sosai rana ta dakesu amma duk da haka sun kwammace su zauna a cikinta akan su koma gidan karuwai.sai da sukai la’asar suna siyar da ruwa ‘kafafuwansu gabaki d’aya ya sage sabida gajiya , duk da bawani kudi suka samu ba Amma iya ribar da suka zamu cikin ruwan da suka siyar sosai sukai farin ciki da haka , lokacin da Abla ta bawa Arwa wani kaso a cikin kudin ‘kin kar’ba tayi , acewarta in sun samu abinci sai su siya dashi, yau ko daman zuwa makarantar allon Malam sule batayi ba, da zasu dawo gida zallan rogo suka siya na hamsin d’insu . Kamar yadda ta saba dawowa kullum Anfara tashin kid’a yau sai tayi sa’a basu kunna ba sabida itama ta dawo gida da wuri , babu Wanda yaga shigowarta ita da Arwa suka shige d’akinsu, suna shiga suka tarar da husna zaune kan katifa ga wata tanfatsetsiyar waya a hannunta tana dannawa , ga lemo da gasashshiyar kaza tana ci, da harara da Abla dashi itama Abla ko kallan inda take batayi ba ta zauna ita da Arwa akan kwalinsu suka faracin rogonsu, wata yar iskar dariya husna ta kwashe da ita “ a haka mutum zai ‘kare a tsiyace ana nuna masa gabas yana runtse ido , in banda tsiya mata da maita me mutum zai ci a rogo “, wani banzan kallo Abla tabi husna Dashi da yasa ta rufe bakinta, cike da wulakanci husna zata d’ao gashshiyar kaza ta yaga sai ta furta “ Gaza da dadi rangen rangengen “, babu Wanda ya kulata tsakanin Abla da Arwa , Aneesa ce ta Fito cikin toilet tana ganin Abla ta sakar mata murmushi “ Abla har kun dawo “, tsayawa kallanta Abla tayi ganin yadda Wajan idanuwanta sukai baki baki gata