x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 37 - IBTISSAM BOOK 1

  • 108001 words
  • 111000 words
  • Out of 200864 words

Category: Romance Story +18

Views 283

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ya shiga d’azu , shima yanxu ya canza kayan jikinsa sai wasu Blue d’in kaya masu tausayi da d’an sanshi daya saka , gashin kansa a taje yake ya nannad’e ta baya shiyasa kyakkyawar face d’insa da babu fara’a ta fito tass da shi musamman eyes dinsa , kan gadon ya kalla ganin little yana bacci da left side d’insa shiyasa ya ‘Karasa wajan tare da jiyowa dashi ‘bangaran dama , duk da baccin sa be nisa ba a hankali ya soma magana cikin baccinsa , fasa tashi Big boss yayi yana sauraran me yake furtawa “ Dan Allah yaya ka barta ta zauna..” shine abunda ya fad’a , Dan ‘karamun tsaki ya ja kad’an yana ‘kara lullu’be little da blanket d’insa tare da rage masa ‘karfin Ac sabida kar yayi mura .

WASHE GARI

Da wari little ya farka daga bacci tun kafin Big boss ya tashesa, Lokacin da akai kira sallah tare suka jera suka fito daga part d’insa , hannunsu ri’ke da na juna sabida yadda little ya ri’ke masa hannunsa gam kamar Ance masa zai rabu dashi, suna fitowa bobo da prince ma suka fito sai uncle gabaki d’ayanxu masallaci Suka nufa… Ana idar da sallah kamar yadda suka fita tare haka suka dawo, direct Big boss part d’insa ya nufa shi , shima Bobo nasa part d’in ya koma , little kuma kai tsaye part d’in da Abla take ya nufa , yana zuba bakin ‘kofar ta yayi knocking ‘kofar, alokacin itama ta idar da sallar ta sabida tun kiran sallar farko ta farka , cike da tsoro ta furta “ wa..wanene….” Little be ce mata komai ba ya turo ‘kofar d’akin tana ganinshi ta saki ajiyar zuciya, gabaki d’aya kayan da kawo mata ta matsar dazu gefe ta gyara Inda ta ‘bata duk da bata share ba amma komai a kintse yake , “ Na d’auka bazaka dawo ba “ cewar Abla , kansa little ya d’an girgiza mata “ No zan dawo mana , yanxu ma kishirya kiyi wanka idan zamu ci abinci zamu ci a ‘kasane gabaki d’aya kinji?” A maimakon ta amsa masa sai furta “ Nagode sosai..” No karki damu kinji kinga na zama yayanki yanxu duk Wanda ya ta’baki kawai ki kira Little da d’an ‘karfi zaki ganni kinji “ da Sauri tayi knodding kanta zata ‘kara masa Godiya yayi saurin ficewa daga d’akin. Kamar yadda ya umarcetan kuwa wanka tayi kamar yadda tayi jiya har wani iskane yake shiga ‘kofofin jikinta Sabida yadda take wanka sosai take dirje jikinta ba kamar lokacin da take gidan uwar karuwai ba da sai tayi kwana biyu bata samu tayi wanka ba , ko tayi ma sai cikin dare babu sabulu ko omo sai da tayi da toka , amma daga jiya zuwa yau har wani iskace take hura ‘kofofin jikinta. Wata doguwar Riga data gani pink colour ta d’auka ta saka , kamar an auna jikinta sabida yadda kayan suka fito sukai mata kyau sosai a jikinta , kusan Daidai tsawanta gashi ko kusa jikinta be nuna ba , gaban mudubin d’akin ta nufa yadda taga wajan cike da mayuka da turare daban daban, ita kanta batasan lokacin da take sakin murmushin farin ciki ba , tun zuwan ta jiya gidan taji gabaki d’aya zuciyarta tayi mata dadi sosai , bata ta’bayin farincikin da tayi jiya ba arayuwarta , shiyasa ta saka hakan a wata ‘kila Sabida sun temaka matane. Bin gaban mudubin take da ido yadda yake sha’ke da kayayyaki a ciki, murmushi ta saki da har saida dimples d’insa suka lotsa , wani pink turarene ya burgeta shiyasa ta d’auko shi tana sakin murmushi, kad’an ta fesa ajikinta har wani lumshe idanuwa take wai Itace ta saka abu me ‘kamshi, hular kanta ta cire gashin kanta duk ya cikurkud’e ga alamar datti yana nunawa , a hankali ta mayar da turaran ta ajje ta koma inda ta d’auki rigar jikinta, white d’in veil da tagani ne ta d’auka ta yafa a kanta , ga uban tulun gashinta da ya Fito sosai ta cikin mayafin, gefe gefen fuskarta ma wasu irin kwantaccen gashine a wajan da yayi wa fuskarta kyau duk yadda ta rufeshi baya Rufuwa , Ta dad’e zaune a d’akin har ta fidda ran dawowar little sai kuma taji ya kwankwasa mata , da Sauri ta tashi da niyar bud’ewa yashigo cikin d’akin bakinsa d’auke da bismallah, gabaki d’aya little mamakin yadda ta koma yayi lokaci d’aya gabaki d’aya ta sauya kamar ba ita ba , yadda yake kallantane yasa itama ta bi jikin Nata da kallo, “ kinyi kyau “ cewar little yana sakar mata murmushi “ itama murmushin ta sakar masa jin ya yaba shigarta “ Dagaske fa amma nayi mamakin yadda kika iya hausa Sabida bakiyi kama da su ba” yadda ta waro masa eyes ne ya sashi ‘kyal’kyale wa da dariya “ wasa nake miki, taho mu tafi su yaya suna jiran mu” , kasa motsawa tayi lokaci d’aya jikinta yayi sanyi “ nace miki karki damu kin manta na zama yayanki? Babu kowa fa kar su dunga jiran mu” kanta ta d’aga masa zata biyo bayansa , ganin babu takalmi a ‘kafarta yasa ya janyo wani takalmi white colour ya mi’ka mata, duk da yayi mata yawa haka ta zurashi a ‘kafarta , duk inda suka wuce sai tabi wajan da kallo sabida tsananin mamakin wai gidane gabaki d’aya Wajan, sosai ko ina ya burgeta, ita kadai sai murmushi ta ke saki ,irin murmushi da ta manta yadda akeyinsa, suna tafiya little yana janta da dariya tun bata sakewa sosai har ta soma yi masa dariya , suna fitowa falourn gabaki d’ayan bobo, uncle , prince idanuwa suka zuba mata ganin yadda akwana d’aya tak ta canza bakamar jiya ba da fuskarta take a kunbure , yau gabaki d’aya babu kunburar fuskar ga shi sai faman murmushi take wa little , shi kansa bobo tantamar yadda akai ta iya hausa yake ga kuma tsantsan mamakin da yake akanta tun ranar farko da ya fara ganinta , amma gudun karya gayawa big boss yasa ya ajje komai a gefe har ya gano hakan da kansa , wannan shine babban dalilin da yasa ya taho da ita Us, babban dalilin da ya barwa zuciyarsa sani .
“ wow my daughter kinga yadda kikai kyau sosai “ cewar uncle yana sakar mata murmushi, saurin du’kar da kanta ‘kasa tayi kafun tayi saurin tsugunnawa har ‘kasa da gaishesa, hakan da tayi ba ‘karamun burgesu tayi ba , ko ba komai ta nuna musu daga cikin gidan tarbiya ta fito, side din bobo ta kalla shima ta gaishe da shi, hatta prince da yake tsaye sai da ta gaishesa, ko wannansu cikin sakin fuska yake amsa mata, ‘kugu little ya ri’ke ganin ta gaishe da kowa ban dashi “ Ni kuma fa ?” Komawa tayi har ‘kasa shima ta furta “ Yaya little ina kwana”, wani irin dadi little yaji karo na farko arayuwarsa da aka kirasa yaya shima , yadda yake dariya gabaki d’aya sai yasaka kowa na cikin falourn farinciki, har da tsallan sa kamar wani ‘karamin yaro wai ankirasa yaya shima , dakatar dashi uncle yayi “ kadai ji kunya kuwa , sai faman buga tsalle kake kuma a haka kake cewa kazama yaya? Let’s eat joor “ yana kai ‘karshen zancan sa little ya d’an turo bakinsa , Haba uncle please na fad’a muku yanxu na girma , I have a sister nifa zai fad’awa yaya big boss Adena cemun little , yanxu na zama Yaya Adil “ ya karasa yana kara kyal’kyale wa da dariya . “ Big Boss “ shine sunan da Abla ta maimaita cikin zuciyarta , lokaci d’aya bugun zuciyarta ya canza ya somayi da Sauri sauri , tun bataga me sunan ba lokaci d’aya taji wani irin tsoran ganinsa ya kamata , ita gabaki d’aya bata ji me little yake cewa ba tun bayan kiran suna Big Boss da yayi , lokaci d’aya taji nutsuwarta tana ‘ko’karin gudu”, Aushe tun d’azu little yake mata magana bataji harsaida ya kira sunanta da d’an ‘karfi “ Ibtissam “ da Sauri ta firgita tana amsa masa da “Na’am…” kına lapiya ?” Ya kara tanbayarta , kasa bud’e masa baki tayi sai kanta kawai da ta jinjina masa , “ okay taje muci abinci “ yanxu ma kanta ta ‘kara jinjina masa , tun kafun su ‘karasa dinning taja burgi da Sauri jikinta har ya soma rawa , gabaki d’aya dakatawa sukai da tafiya ganin lokaci d’aya ta burki ce tana ‘ko’karin Jan baya , bakinta har ya soma rawa , ba komai ne ya haifar mata da hakan ba sai james da ta gani da shigar sojoji, yadda ta ‘kura masa ido ne yasa kowa ya kalli direction d’in, da hannu bobo yayi masa alamar ya tafi, tana barin wajan kuwa ta saki wani irin ajiyar zuciya da gabaki d’ayansu sai da sukaji “ kına jin tsoronsu?” Cewar little , da Sauri ta jinjina masa , “ ya tafi ai bazai miki komai ba “ yanxu ma kanta ta jinjina masa tsoran da take ji na d’an raguwa , a haka har suka ‘karasa dinning d’in da yake cike da abinci kala kala , tun daga ido zaka san ba’kamin kud’i aka kashewa abincin ba , “ yau ni zanyi serving din kowa da kowa “ cewar little kafun ya jawa Abla kujera, a ra’be ta zauna gabaki d’aya takı sakin jikinta , da kansa little yayi serving d’in uncle favorite food d’insa , yayi serving yaya bobo da yake gefensa shima haka yayi serving dinsa shi da prince , abla kuwa mamakin Tulin abincin da aka girka take ganin uban abinci da yawa , ita a rayuwarta bata ta’ba ganin irin abincin nan ba da suke ‘ko’karin ci gashi ko wannansu kalarsa da ban shiyasa take mamakin yadda akai suke cinsa , little ya fahimci bata iya cin abincinsu ba shiyasa yayi saurin barin Wajan yana furta “ am coming “ be jima ba ya dawo hannunsa d’auke da wani kwalin yoghurt madaidaici tare da cup a hannunsa , sosai ya cika mata cup d’in sannan ya ajje mata fruit agaban ta sosai , ganin duk sun kallesa a fakaice cikin French ya furta “ bata iya cin kalar abincin muba”, daga nan babu Wanda yakuma magana , bayan little ya zuba abincinsa shima , tunda ya ajje mata cup din yoghurt din da fruit ta ke binsu da kallo batare da ta ta’ba komai ba , ji tayi hawaye na sakko mata , lokacin da ta soma shash she’kar kuka gabaki d’aya dakatawa sukai daga cikin abincinsu suna binta da kallo, “ bakyasan abincin na canza miki?” Shima little kamar me shirin yin kuka , da Sauri ta girgiza masa kai “ zan iya d’aukan guda d’aya na kaiwa Arwa ?” , ita kanta tun kafin ta ‘karasa maganar ta kuma sai kuka ya kwace mata , sosai take yin kukan little na ‘ko’karin dakatar da ita bobo ya hanashi,gabaki d’aya sai suka zuba mata idanu ganin kukan mata bame ‘karewa bane ya furta “ da alama tana bukatar masu shan jini” da Sauri Abla ta furta “Kayi hakuri na dena “abun cinta ya nuna mata “ oya cinye abincin ki “ hannunta har rawa yake lokacin da ta d’auki Youghurt din , tunda ta saka shi a bakinta bata saukeshi ba , ita gabaki d’aya ta manta da suna zaune a wajan sabida yadda zakin Youghurt din ya yi mata mugun dadi dan arayuwarta bata ta’ba Shan yoghurt ba sai yau da little ya bata , yadda Tasha Youghurt din sosai hakan yayi musu dadi dan gabaki d’aya yoghurt din ta shanye sai data ga babu tukunna ta ajje cup , sai kuma kunya ya kamata ganin lokaci d’aya ta shanye farin abunda little ya bata dan ita Batasan ma yoghurt bane , babu Wanda ya nuna mata ya ganta kowa abincinsa yake ci, hatta fruit din da suka bata shima ta shashi sosai , suna gama breakfast din suka koma falourn gabaki d’ayansu banda bobo da ya fita , little da prince sai faman janta da iri suke tun bata sakewa sosai har ta sake kamar sunyi shekara guda take sai faman dariya suke wa junansu , uncle na gefe da jarida a hannunsa sai faman murmushi yake saki shi kad’ai, sun dad’e sosai suna hira ganin almost 12 little yasan a ko wana lokaci Big Boss zai iya fitowa shiyasa ya kalli fuskar Abla yaga tana murmushi, bayaso Big boss ya sata kuka shiyasa gabaki d’aya hope dinsa ya ragu sabida besan me big boss xai mata ma idan ya ganta dukda yasan bazai ta’ba korar taba tunda yace yana san zamanta a wajan , wani idea ne ya fad’o masa ganin anytime big boss zai iya fitowa , can d’akin kifayensu little ya ja ta , yadda taga kifayen suna motsi kwanin sha’awa ita kanta bata san lokacin da ta ‘karasa jikin glasses Dinsu ba tana shafawa, yadda suke motsi cikin kaloli masu burgewa sai sun baka sha’awa itama hakance ta kasance a ‘bangaran ta batare da tsoron ganin suna motsi ba ta soma shafa glasses din , ita kadai sai faman murmushi take saki , little na tsaye shima yana bin kifayen da kallo saida sukai kusan 40 minutes a d’akin , alokacin ya d’auka big boss ya fita daga falourn shiyasa suka fito daga d’akin little sai faman labari yake bata ita kuma tana masa murmushi kawai, saida suka zo tsakiyar falourn kamshin turaransa y dokesu gabaki d’aya musamman Abla da taji bugun zuciyarta ya canza lokaci d’aya ta dunga jin wani irin fad’uwar gaba ga kamshin da take ji na shigar mata hanci , yadda kamshin yayi mugun yi mata dad’i har wani lumshe idanuwa tayi tana ‘kara sha’kar daddad’an kamshin, ga wani irin da ta faraji lokaci d’aya da taji ‘kamshin turaran ,Little kuma gabaki d’aya kasa motsawa yayi Sabida ganin baki big boss zaune akan kujera yayi crossing legs d’insa ga idanuwansa da suke a lumshe , uncle na gefensa shi da prince , a hankali little yayi sallama yana shigowa cikin falourn, ita gabaki d’aya Abla bata san da zaman Big Boss ba sabida yadda kanta yake a sunkuye har ta ‘karasa shigowa cikin falourn Sabida yadda takejin zuciyarta , little yana shiga suka da Big boss ya nufa tare da zama a kan carpet yana yiwa Abla signal akan ta matso kusa dashi amma ita gabaki d’aya bata san yanayi ba sabida yadda ta sunkuyar da hanka ‘kasa tana tafiya , a shagwa’be little ya furta “ Yaya Big boss “ wani irin bugawa zuciyar Abla tayi da ‘karfi cikin sauri ta d’ago da idanuwanta , basu sauka ko ina ba sai kan kyakkyawar face d’insa da ya lumshe , kasa sha’kar nunfashi Abla tayi sabida yadda kyan Big boss yayi mugun rud’ar da ita da Sauri sauri zuciyarta ta cigaba da tsanan ta gudu, ga wani irin rawa da jikinta ya somayi lokaci d’aga , mugun tsoransane ya kamata gashi ta kasa d’auke idanuwanta akan sa musamman red lips dinsa da yayi mugun tafiya da ita sai kuma tsagar girarsa da ta zubawa idanuwa , tunda take bata ta’ba ganin kyakkyawa kamarsa ba dukda tsananin kyan dasu little suke dashi sai taga kamar nashi kyan na dabanne, tana cikin tunanin da ta fad’a ya soma bud’e eyes
d’insa dan tun lokacin da little ya zauna a carfet yaji alamar ana kallansa , gabaki d’aya eyes d’insa ya bud’e basu sauka ko ina ba sai cikin idanuwan Abla da ta kafe shi da kallo, lokaci d’aya yayi mugun had’e ransa tare da tsuke fass d’insa sosai, wani irin kallo da ya jefa matane yasa tashiga hankalinta , cikin Sauri ta d’auke idanuwanta tana sunkuyar da kanta ‘kasa , gabaki d’aya ko d’an yatsanta ta kasa motsawa Sabida wani irin shakkarsa da ya kamata ,maida kallansa kan little da ya zauna a ‘kasa yayi , shima nasa raban kallon Big boss ya jefa masa , amaimakon ya Tashi daga ‘kasan sai ya shagwa’be masa face d’insa “ please Yaya, please”, d’auke eyes d’insa Yayi daga kan little da ya shagwa’be fuska, cute red lips d’insa Big Boss ya d’an ta’be Batare da ya ‘kara kallan Little ba ko Abla data ‘kame kamar gunki ta kasa motsawa , shi kansa prince tsoran ya ce mata ta zauna yake kar Yaya ya bashi na sa kasan, uncle kuwa da gangan ya’ki tanka musu, kowa jiran reaction dinsa akan Abla yake , gabaki d’aya idanuwa suka zuba masa suna jiran suka abunda zaiyi mata , Allah sarki little sai faman Addua yake cikin zuciyarsa, a bazata little yaji muryar Big Boss “ should I?” Da Sauri ya girgiza masa kai sai kuma ya bud’e baki “ No yaya bari na zuba maka da kaina”, da kansa little ya zubawa Big boss abinci ga Abla da tun da ta tsaya ta sunkuyar da kanta itama ta kasa d’agowa , har wani zufane ta soma ganin suma gabaki d’aya babu me magana a cikin su, ganin ya soma cin abincinsa a tsanake yasa little sakin ajiyar zuciya , da sunga yana ‘ko’karin d’ago da eyes dinsa suke saurin d’aukewa dan sosai Big Boss ya tsani kallo, yadda yake tauna abincin hankali kwance kamar be san suna wajan ba amma gabaki d’aya ya karanci ko wannan su tsaf, kad’an yaji abinci yana gyara zamansa sosai a kan kujerar da yake , yanxu kam gabaki d’aya jira Suke suji Wana hukunci zai d’auka akan Abla dan idan yace No toh tabbas No d’innance babu me canzata, amma ga mamakinsu kwata kwata be tanka musu ba, sai ma diamond watched d’in hannunsa da ya kalla sau d’aya yana mi’kewa tsaye , har yanxu Abla tana a yadda take dan Dagaske ta kasa motsawa daga inda take tun kallan da ya jefa mata . Sosai little ya zuba masa idanuwa a shagwa’be, shi kuma amaimakon ya basa amsa sai ya lumshe masa idanuwansa
End Ads