ta bud’e ’kofar tana ganin baya ciki ta nufi d’ayan falourn , shima sau biyu tana knocking ba’a amsa ba , da sallama ta shiga falourn sai kuma tayi saurin Jan burki ganin sa zaune kan d’aya daga cikin kujerun falourn , ga system d’insa da yake operating akai . A nutse ta ‘karaso cikin falourn Daidai Wajan center d’in ta rankwafa kad’an “ ga coffee d’in” shiru bai kalleta ba balantana ta saka ran amsawa , a karo na biyu ta ‘kara furta “ ga coffee d’in “ nan ma shiru yayi mata kamar be san da zuwan ta ba , Yadda ya nuna kamar babu mutum a falourn ne ya ‘kular da ita , juyawa tayi da niyar komawa ya mi’ka hannunsa kad’an ba tare da ya kalle taba “ My coffee !” A fakai ce Abla ta d’an harari side din da yake kafun ta juyo ta mi’ka masa coffee d’in, yanzu ma sai da ya gama shan ‘kamshi tukunna ya saka hannu ya kar’ba , ta juya zata tafi ya ‘kara furta “ Come back “ Abla kamar zatayi kuka haka ta juyo ta tsaya batare da ta kalli side d’in da yake ba , kamar da wasa taga ya kai cup d’in bakin sa , kad’an yayi sipping kamar me tsoran sha , ta d’auka zai mata fad’a sai taga ya ‘kara kai coffee d’in bakinsa a hankali yana sipping. A hankali ta saki a jiyar zuciya ganin yau ta tsira bazai mata punishment ba , ta fi tsawan 7 minutes tana so ya gama shan coffee d’in ko zai barta ta tafi sabida gabaki d’aya ta kasa sakewa , a hankali ya ajje cup d’in batare da ya furta komai ba, itama Abla ganin ya gama sha ne yasa ta d’auka da niyar komawar ta ‘kasa , tana juyawa ta kuma jin saukar muryarta “ Coffee “,d’an ya mutsa face d’in ta Abla tayi kad’an kamar zatayi kuka dan yau sosai take jin bacci, cikin Sauri ta ‘karo had’a masa wani coffee d’in har lokacin su Little basa falourn , yanzu ma ta d’auka zai barta ta tafi sai ya ‘kara dakatar da ita , sai da ya mula dan kansa sannan yasha coffee d’in a karo na biyu, duk wannan abun Abla ta tsaye kamar zatayi kuka Sabida yadda ‘kafar ta ya gaji, a karo na uku ya ‘kara sa ta had’a wani coffee d’in , tun tana tunanin d’aukar abun da wasa har ta dena ganin sai da ta koma ta ‘kara had’a masa wasu coffee d’in, kafafuwanta gabaki d’aya ciwo suke mata sabida hawa da saukan da tayi gashi sama da awa d’aya tana tsaye ko zama be barta tayi ba , kamar ta ro’keshi akan ta tafi amma itama taurin kanta ya hanata magana yau sai kawar da face d’in ta da tayi kad’an kwalla har sun tarar mata cikin ido. Sai da ‘kara mintuna 25 a tsaye ga bacci ga cikin kafa amma ko kusa ya hana ta tafiya , Sai da ya tabbatar ya horata da tsayuwa kafun ya furta “ get out “ ko kallan inda yake yau Abla batayi ba tayi fitowar ta , “ mugu kawai” cewar Abla kafun tayi sauri barin Wajan . Tana sakkowa ta tarar da Prince da little sai kuma uncle , “ yanzu nake shirin kiranki sai gaki ma kin fito , ina kika je ?” A sanyaye ta furta “ coffee na kaiwa Yaya Big Boss “ cikin fara’a Little ya furta “ sorry Lil nasan kin gaji ko?”Girgiza kanta kad’an Abla tayi duk da ta gaji amma ko kusa bata nuna musu hakan ba “ No yaya Little ai ba wani aikin nayi ba , ko kuna bu’katar wani abune ?” Girgiza mata kai sukai “ No Lil yaka mata ki huta haka tunda gobe kina da school , okay ?” Cewar uncle , jinjina masa kai tayi kafun ta furta “ Tom uncle sai da safe “ side d’in su Little ta kalla suma tayi musu sallama kafun ta nufi part d’inta .
Tana shiga d’aki ta fad’a kan gado sabida yadda taji ‘kafafuwanta suka ri’ke, tafi tsawan 10 minutes a kwance kafun ta iya zuwa toilet ta watsa ruwa ajikinta , lokaci d’aya abubuwan da suka faru d’azu suka dunga dawo mata cikin zuciya ta, tasan baya santa , baya ‘kaunar ta , baya san ganin ta a inda yake , amma kano na farko , mutum na farko daya ta’ba kwato mata martabarta ta ‘ya mace, baza ta ta’ba mantawa da hakan ba arayuwarta,tana cikin wannan tunanin bacci ‘barawo ya d’auke ta.
12:30am aka bud’e ‘kofar d’akin horan da aka kulle su Alice ,gabaki d’aya tun suna kuka har suka dawo ajiyar zuciya dan gabaki d’ayan su sun fice daga hayyacin su. Da victor ya tashi kulle su kuma sai ya had’a ko wannan su mata da miji ko a d’aki d’aya , Alice da jabcon sai LG da mijin ita da ya kuma shan wani dukan a wajan ta , gashi daman a buge aka d’auko sa shiyasa LG taji dad’in bugun sa.
Victor ne yashigo cikin d’auki ko wannan su ya jefa musu blanket da wani Leda “ yau ne first night d’in ku , and also congratulations you guys go be zaku tafi Greenwich Village anan zakuyi honeymoon d’in ku na tsawan sati d’aya congratulations “ a haukace Alice ta mi’ke tsaye tana d’ora hannunta aka Honeymoon ? What ? Ni zanje kauye ? Bazai yuba , no dole dady ya zo bazai ha’ba faru ba , babu Wanda ya isa ya kai ni kauye balantana wannan d’an iskan kwartan da aka cewa ya zama miji na , “ kallanta Jabcon yayi daga sama har ‘kasa , “ Ni gaskiya ina san matata “ cewar sa , ai be kai ‘karshe ba Alice ta tsinka masa mari , banza Victor yayi musu ya nufi d’akin da aka kulle LG, the same abunda ya fad’a wa Alice shine abunda ya fad’a wa LG, ita LG da ta fi kowa rud’ewa ma sume wa tayi a zaune , tasan wanene Chief , tasan tunda Big boss ya yanke hukunci shikenan ta zauna musamman da shima mahaifinta ya kasance me tsauri kamar Big Boss, mijin ta da aka fi sani da Ozzy a tsorace ya kalli Victor “ kuyi hakuri , kashe ni zatayi d’azun nan ta gama Zane ne , kuyi hakuri ni bansan abunda zai faru ba kenan” sai kuma ya soma kuka kamar wani ‘karamun yaro.
‘Karfe 2:10am Abla ta farka sabida ‘kishir ruwan da ya dame ta , a hankali ta sakko daga kan gadon daga ita sai riga da wandon ta na bacci da suka fito da shape d’in ta sosai , hularta kawai ta d’auka ta fito daga cikin d’akin , har ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta ga fitilun falourn a kunne , batare da wani damuwa ba ta wuce kitchen ta d’auko babban bottle d’in ruwan ta , tun daga kitchen d’in ta soma shan abunda hankali a kwance , tana fitowa zata nufi sama kamar wacce aka tsiyaka sai kawai ta juyo bakin ‘kofa Daidai lokacin da Big Boss zai shigo cikin falourn , batasan lokacin da ta yardar da bottle d’in hannun taba , mistakenly ta tsallake step d’aya sai ‘kafarta ta zame a ‘kasa , ‘kugunta ya bugu da step d’in, da ‘karfi ta saki ‘kara Sabida zafin da tanı a kugunta, a hankali ya d’ago da idanuwansa zuwa ‘bangaran da take, ganin yadda da ri’ke ‘kugun nata ne ya d’an ta’be baki tare da d’auke idan sa ya nufi hanyar part d’insa , da harara Abla ta bisa ganin a dalilinsa taji ciwan, cikin rashin sa’a kuma lokacin da take hararar sa ya d’an jiyo sai ya sauka akan idanuwansa , kallan zaki sani ya bita dashi , kafin ya juyo zuwa side d’in da take , tun kafin ya ‘karaso ta soma yarfa hannun ta ganin ya kamata dumu dumu tana hararar sa , hannun ta d’aga ta finciko da ‘karfi Abla ta furta “ouch “ Sabida ba ‘karamun buguwa tayi ba , yadda taga yana binta da kallo ne yasa lokaci d’aya jikinta ya soma d’aukan rawa , gashi babu kowa a falourn balan tana tanemi te maka , kamar zatayi kuka ta shagwa’be masa face d’inta, zai bud’e baki Abla ta fashe masa da kukan ta’bara, kallan da ya jefa mata ne yasa tayi saurin yin shuru sai ‘kif ‘kif ta idanuwa take , “ Me kike ‘bukata? Ouh” shiru Abla tayi masa dan gabaki d’aya bata fahimci abunda yake nufi ba sai ma ‘ko’karin Jan baya da take , a zuciye ya murd’e hannun ta d’aya ga ciwan kwankwaso ga hannu duk ita kad’ai , a tsiwace Abla ta furta “ Ni kasakar mun hannu na “ d’ayan hannun ya murd’e tare d juyo da ita , yadda taga kusancin su yayi yawane yasaka jikin ta ya soma rawa lokaci d’aya , har yana jin yadda jikinta yake rawan , ga wani irin tsoro da ya bayyana akan face d’inta sosai,motsa bakin sa yayi kad’an kafun ya saka hannun sa d’aga zuwa kwankwasan nata , yadda ta kwalalo masa idanta waje ne yaso sawa bakinsa ya motsa amma sai ‘kara tsuke face d’insa da yayi “ I think shine abunda kike so ko? And “ ya ‘kara matso da ita kusa da jikin sa kad’ai , face d’inta yakalla ganin yadda tayi saurin runtse idanuwanta gagam ga bugun zuciyarta da yake d’agowa sosai , daga gefen idanuwanta wasu irin siraran hawaye ne suka kallo mata , ‘karamun tsaki yaja kad’an kafun ya saketa , a bazata Abla taji ta ‘kara fad’uwa ‘kasa , the same ta ‘kara bugewa a kugunta, kuka kawai ta fashe dashi lokaci d’aya dan ba’karamin zafi taji ba , “ You are nothing but just a pieces of mess “ cewar Big Boss lokacin da Abla ta d’ago da idanuwanta hawayen ta gabaki d’aya ya’ki tsayawa “ just because kina zaune a gidan ba , ba hakan ke nufin ke yar gidan bace, your no body , I hate to see this your ugly face , kinsan me ? From the moment kika shigo cikin gidan nan like kinyi poison d’insu ne gabaki d’aya , I seriously hate you! That’s why naso jiya harbe kanki kikai , okay ? “ d’an huci Big Boss yayi dan doguwar maganar nan da yayi har ya saka masa ciwan kai ,” Sai da ya ‘kara d’auka second 10 kafun ya ‘kara kallanta “ duk Wanda ya aiko ki , you guys both will pay, ‘kazama , Villager “ da haka ya juya ya bar wajan , wani irin kukan ba’kin cikine ya kwace wa Abla , tasan ya tsane ta amma bata ta’ba tunanin tsanar da yake mata ta kai haka ba , ya tsane ta , yaso mutuwar ta ? “ hawayenta Abla ta share lokaci gudu gabaki d’aya soyayyar da taji tana yi masa ta goge ,dukda ita Kanta batasan a wana matsayi ta d’auke saba , hatta tsoran sa da takeji gabaki d’aya ya fitar mata cikin zuciya , babu abunda yake mata yawa cikin zuciya sai “ ‘kazama , Villager “ kallan jikin ta tayi sosai kafin ta ‘karasa goge hawayen face d’inta, da ‘kyar ta iya mi’kewa tsaye , da ‘kyar ta ke taka steps Sabida yadda ‘kugunta yake mata zafi. Tana shiga d’akı gaban mudubin ta tanufa ko zata samu man zafi, cikin sa’a kuwa ta samu, a ‘kugun ta shafa sosai kafun ta kwanta bacci, kalaman sa sun dad’e suna mata yawo cikin zuciya , tsabar takaici da hawaye takwana.
Da safe da wuri ta shirya cikin uniform d’inta , tana gama shiryawa kallan kanta tayi a madubi “ ‘kazama , Villager “ shine abunda ya ‘kara yi mata yawa cikin zuciya , sosai ta ‘kurawa fuskarta ido a fili ta furta “ tabbas ni ‘kazama ce , tunda bani da gata bansan iyaye naba a ‘kazanta na taso , sannan nid’in yar ‘kauye ne , amma sai na nuna maka banbancin ‘yan ‘kauye da ‘yar burni, daga yau na tashi daga Abla ta koma asalin Ibtissam , wannan Al’kawari ne na d’auka “……….
https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨
🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅
AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__
✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨
💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus
🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.
NOT EDITED
S____36💞
‘Kasa Abla ta sakko cikin shigar uniform d’inta , bata tarar da kowa a falourn ba , shaf shaf ta shiga kitchen ta d’auko milkshake, bata damu da d’aukar cup ba ta fara sha , tun a kitchen d’in, cikin sauri ta d’auki youghurt medium size ta fito bayan ta gama shan milkshake d’in ta , yau ko Breakfast bata samu tayi ba , time ta duba ganin ta kusa makara gashi har lokacin bata ga little ba , kamar ta zauna sai ta yanke shawaran fitowa waje ko zata gansa a waje amma babu shi babu alamar sa , hatta yaya prince da take tunanin samu gabaki d’aya bata same suba , kallan motocin da suke gefe da ita kad’an , tunani ta fara ko Little yana cikin motar ne ? Ganin babu me bata amsa yasa ta juya zata koma cikin gida , da sauri wata macan soja ta ‘kara inda take tare da sara mata,” Madam sunana captain sarah , daga yau nice zan dunga rakaki makaranta “, shiru Abla tayi kamar bazata ce komai ba , sai kuma ta jinina mata kanta , cikin sauri Sarah ta ‘karasa ta bud’e mata mota , sai data tabbatar Abla ta zauna sosai sannan itama ta shiga front seat , cikin ‘kan’kanin lokaci motocin suka kama hanyar makarantar su Abla , tun kafun su ‘karasa makaranta take ganin motocin sojoji suna ta wuce wa , ta ko ina akwai mata kan tsaro a hanyar, bata kawo komai a ranta ba har suka ‘karasa makarantar, cikin Sauri Sarah ta sakko ta bud’ewa Abla mota tare da sara mata , zata bita a baya Abla tayi saurin tsayar da ita “ No please kar na wahalar dake nagode “ cikin Sauri Sarah ta furta “ thank you ma’am “, tun da Abla ta fito daga cikin mota student d’in da suke waje suke binta da kallo , babu Wanda ta kalla nufi class d’insu, tana shiga gabaki d’aya class d’in ya d’au shiru kamar Wanda ruwa ya cinye su , Eshaal da fanan ma sai binta da kallo suke har ta ‘karaso seat d’inta . Yadda taga suna kallanta ne yasa ta d’an harare su kad’an , “wannan kallan fa ? Na mene ne ?” Ajiyar zuciya Eshaal ta sauke “ ba dole mu kalle kiba ? ,ni ai har kin fara bani tsoro ma “ kara ‘kallan su Abla tayi lokacin da take zama “ da nayi muku me ?” Kusan lokaci d’aya suka had’a baki wajan furta “ su wane ne wad’an nan mutanan ?” Shiru Abla tayi musu dan ta fahimci maganar su, zasu ‘kara yi mata magana Mss Atem ta shigo class d’in, itama da kallo tabi Abla ,duk lokacin da Abla ta d’ago kuma sai Mss Atem ta sakar mata murmushi, tun Abla na tsarguwa da kallan ta har ta share ta. Sai da sukayi period biyu na English kafun Mss Atem ta fito, yanzu Biology ne dasu gashi jabcon yana hannun sojoji shiyasa kowa ya mayar da hankalinsa kan books d’inta, har zuwa time d’in break .
A hanyar zuwa capteria ma haka akan dunga bin Abla da kallo gabaki d’aya ta tsargu da irin kallan da taga ana mata , cikin tsokana fanan ta furta “ Matar soja da alama jiya kinja hankulan mutane da yawa kalli yadda kowa yake zuba miki ido , Wanda basu sanki bama yanzu sun sanki “ shiru Abla tayi mata ta’ki tanka mata , itama Eshaal d’aga wa fanan gira tayi “ karki damu fanan yanzu zamu fara gyara Matar soja ai , kınsan kamar sarauniya take dole mu tarairayeta “ harararsu Abla tayi gabaki d’ayansu ta ‘Kara sa d’aya daga cikin table d’in, anan ma kusan hankalin kowa kanta ya dawo ganin yadda ta had’e rai yasa kowa ya koma aikin gabansu. Order abinda zasu ci su fanan sukai , har suka ‘karaso seat d’in Abla “ me yayi zafi kuma matar soja ? Kırarın da mukayi miki ne ba