batajin zata iya mota jikinta , hatta harshenta ta kasa d’agawa balantana tayi addua sai a cikin zuciyarta kawai take iya ambatan sunan Allah . Sai da sukayi tafiyar 2 hours daidai sunzo inda suke san zuwa wajan kamar ba a rayuwa a wajan sabida rashin mutane , parking din motar sukai d’aya daga cikinsu ta ‘kara fitowa daga cikin motar ta nufi inda Alba take , wata allurar ta ‘kara tsira mata da ko minti d’aya batayi ba jikin Abla ya saki ta fara lumshe idanuwanta Sabida ‘karfin Allurar , tana ganin Abla ta lumshe idanuwanta ta d’aga hannuta d’aya ta saki taga baya motsi , wani salatif din toshe baki ta samu ta rufewa Abla baki tare da d’aure mata hannuta duka biyun , cikin mintuna da basu wuce 5 ba wata babbar mota kamar tifa da ake fitar da rice ta karaso wajan , cikin Sauri d’ayar matar ta fito daga cikin mota lokacin da sukaga zuwar tifar nan, a cikinta wasu gandama gandaman maza ne kana ganinsu kaga yan iska ko wanne cikinsa da tattoo ga wani irin gyaran kai na tantiran yan iska a kansu amma gabaki d’aya sanye suke cikin lallabiya ga carbi da suka ri’ke a hannayensu , wani abu me kamar bokiti suka d’auko me ‘bula ‘bula a ciki me fad’in gaske , haka matannan suka kinkimi Abla suka sakata ciki tare da kulle , sannan aka sata cikin bayan motar da take da irin abubuwan kusan guda goma , suna kulle motar su suka bawa yan matan wasu card guda biyu suka canza tafiyar tasu zuwa wata hanya daban tare da nausawa cikin daji .
10: 10am suka ‘karaso inda suke san zuwa duk da kasancewar sun fita daga cikin dajin sun shiga cikin wani ‘kauye shima wajan saida suka kara tafiya sosai sunnan Sukayi parking , da d’add’e da d’add’e suka dunga shigar da kayan cikin motar suwa wani gida da duk Wanda ya gansa zaiyi mamakin ganin gıdan a kauye dan gabaki d’aya tsarin gidan ya fita daban da kauyen da suka baro, a cikin gidan kuwa cike yake da wasu maza da mata a ciki , wasu manyan mutane da kagansu kaga masu kudi ba fararan mutanen ba , hatta ba’ka’ken zaka gansu kowa cikin shigar sa , ga manyan mata suma da zaka gansu kowaccensu taci a donsu na masu kud’i , lokacin da mazan nan suka shigo ciki haka wasu mata suka bubbud’e manya manyan abubuwan, abun mamaki gabaki d’aya matane a cikin ko wana bokitin, haka a dunga fito dasu gabaki d’ayansu babu wacce take nunfashi a cikin su dan ko motsi babu wacce tayi sabida allurar da sukayi musu , da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai haka a ka dunga d’aga matan ana nunawa maza da matan , abun mamaki yadda suka fara cikin su cikin ‘kan’kanin lokaci duk wacce Akaji kudinta yafi yawa ita ake ajje wa yarinyar ko duk me kudin da yafi saka kud’i shi za’a bawa, haka aka dunga cinikin matan kamar ba mutane ba , ana zuwan kan Abla tun lokacin da sukayi arba da face dinta aka soma cinikin kud’i bana wasa ba , cikin ikona Allah kowa so yake ya d’auketa shiyasa suka dunga saka ma’kud’an kudi akan samun ta , sun jima suna fafata Wanda zai d’auketa dan kowa hassada yake da akan wani ya fishi , watace ta furta zan bada 7million , tun kafin tayi shiru wani ya furta zan bada 10 million , shima beyi shiru ba wani ya furta zan bada 12million , haka Suka dunga cacar kudin da zasu siya Abla cikin turanci , wata farar baturiya da tun d’azu take shakar shisha ta kallesu gabaki d’ayansu a gadarance ganin irin kananan kudin da suke sawa , saida ta zu’ki shishar ta iya zu’ka ta fesar da haya’ki ta hanci da ta baki kafun ta gyara zama tana ya tsine fuska “ zan bada 35 million” gabaki d’aya wajan sai suka mayar da kallansu kanta daman haka matar take duk lokacin da ta shigo kasar taga kowa yafisan ya samu wani abu sai ta saka ma’kudan kud’ad’e koda kudin ta zaiyi kasa ta mallaki abun shiyasa ko wannansu cikin jin haushi yake bunta da kallo batare da sun ‘kara furta komai ba sai harare Harare da ake bin juna dashi “ Sold out” wani mutum dake tsaye ri’ke da taba ya fad’a , babu Wanda ya sake cewa sai bin Abla da Suke da kallo su kansu sun sani ko a cikin kyawawa Abla kyakkyawa ce ga wani irin sahirtaccen kyau da take dashi dukda basu ga gyarun idanuwanta , take a wajan matar ta saka akayi musu transfer din 35million ta saka wata yarinyarta d’aukar Abla, ragowar yaranta suka d’auki matan biyun da duk natane , bata kuma zamaba ta tashi ta tafi , a cikin motar ta aka saka Abla d’aya daga cikinsune takalle ta tana washe baki “ Mah ! Wannan yarinyar ta ‘karshe ba ‘karamin kyaune da ita ba , ita wa zaki siyarwa ?” Murmushi matar ta sakar mata tana le’ken fuskar Abla da ita kanta saida kyawun Abla ya razanata, cikin wani irin murmushi da ta barwa kanta sani ta furta “ Da ita zan tafi CANADA”, Canada ? Cewar yarinyar cike da shock dan bata ta’ba ji matar ta tafi da duk Wanda take sıya ‘kasar taba sai akan Abla , gyad’a mata kan da matar tayi ne ya kara bata mamaki cikin zuciya tana Ayyana nasara da babu Wanda ya ta’ba samu a wajan matar kamar Abla tunda har zata tafi Canada da ita . “ let’s go” cewar matar tana katse mata zancan zucin da take , da Sauri yarinyar ta bud’e mata mota ta shiga suka bar wajan , sa’banin sauran motocin da batare da ita zasu tafi ba ko wacce ta nufi hanyar da zasu kai yarinyar dake cikin motar. Abun mamakin sun dad’e suna tafiya har suka ‘karaso wajan wani private jet daga wajan harda yan sanda da mutananta da ta saka , bayan ma’kudan kud’in da ta basu aka saka mata Abla a cikin jirgi kamar gawa , kasan tuwar duk lokacin da zatazo cikin private jet take zuwa shiyasa basu ‘bata lokaci ba saida tayi settling din komai tayi wayar da zatayi sabida karta samu matsala zuwan ta canada da Abla sannan suka shiga cikin jirgin, cikin ‘kan’kanin lokaci jirgin su ya Tashi zuwa Canada 🇨🇦 ✈️ .
(Abla bye bye 🥹🥹)
🍃🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*NEW YORK*
Yadda bobo yayi wa su big boss abinci kala kala sai ya burge mutum , sosai yayi abinci masu kyau babu Wanda zaiyi tunanin bobo ya iya girki haka hatta su james sai faman jinjina irin girkin bobo suke dukda shi girkawa kawai yake duk abunda ya bu’kata suna tsaye suna mi’ka masa , ba ‘karamun ‘kawata dinning din Sukai ba , ko ita sai faman d’aukar ido sabida sunsan me gayyane zai sakko duk da kullum haka wajan yake a tsaftace , yana kammala abincin ya nufi part d’insa .
11:45am prince ne ya fara sakkowa ‘kasa shima kana ganin jikinsa zaka ga alamar wanka yayi sai faman tashin ‘kamshin turare yake , yadda yake faman kulle idanuwansa zaka gane baccin da yake ji ba ishesaba yunwace ta tayar dashi shiyasa kai tsaye ya nufi dinning , yadda yaga komai a tsare ne yafi burgeshi su James na gefe ko wannansu ya canza kayan jikinsa sabida ko kad’an idan big boss ya sakko yaji jikinsu na ‘kamshin abinci sai ya sa’ba musu shiyasa suke takatsantsan sosai dashi, prince har ya bud’e wani warmer yadda yaga abincin ya ‘kawatune yasa ya bawa James umarnin yayi serving dinsa , cikin d’an girmamawa james ya furta “ sir we’re waiting for big boss”, d’an dakatawa prince yayi kafun ya furta “ Yaya big boss be sakko ba ?” Yes sir” yaya bobo fa ?” Ya Kara tanbayarsu “ shi yayi abincin”james ya bashi amsa cikin girmamawa, shima prince cike da mamaki ya furta “ yaya bobo ? Shi yayi abincin nan ?” Yanxu ma da yes sir James ya bashi amsa “ kamar zaiyi kuka ya kalli abincin “ yanxu Kenan ta tabbata bazan ci abinci da wuri ba ? Wayyo yunwa” says who?” Yaji maganar yaya bobo daga bayansa , da Sauri ya juyo yana kallan bobo da yake ‘karasowa Wajan dinning , “ wanene yace bazaka ci abinci ba ?” Gashin kansa prince ya shafa kad’an “ no yaya bobo I thought yaya big boss kawai ka dafawa shiyasa” oh really ?shine yake hana ka cin abinci Kenan ? Toh bari ya sakko” da Sauri prince ya ri’ko hannun bobo “ Dan Allah yaya bobo kayi hakuri , ni wallahi yaya big boss be hanani abinci ba , kuma yaji wannan kalmar taka sawa zawa zaiyi a kulle ni me dalili a hanani abincin , dan ‘Allah please” , harararsa bobo yayi “ sai shegen tsoro kamar kura , shiyasa little yake maka wayo idan kuka janyo rigima” murmushi prince ya saki “ no yaya bobo ba haka bane duk lefin da little zaiyi nafiso ayi mana hukunci tare banaso naga an yi masa hukunci shi kad’ai”, gashin kan prince bobo ya shafa “ good boy, haka akesan yaya ya kasance , that’s why big boss yake d’aga maka ‘kafa Sabida yadda kake kula da little d’insa”, murmushi prince ya sakar masa , cikin d’aga murya ya furta “ Yaya bobo I so much love you all , I love you , I love yaya big boss , I love little , I love uncle , you’re my family my happiness my everything…” be ‘karasa every thing d’in da yake san fad’a ba sabida ‘kamshin turaran da ko a mafarki idan yajisa yasan ko nawane, turaran da babu ma halu’kinda yake da irin ‘kamshinsa sai mutum d’aya Sabida yadda ake had’a masa turaran da ma’kudan kudi masu yawan gaske da zai baka mamaki, ta ko ina kamshin turaransa ne yake tashi, direction din da bobo yasan yake wajan ya kalla , yana tsaye hannayensa sanye cikin aljihun farin wandan jikinsa na kanfanin Gucci fari tas dashi me laushin gaske iya gwiwar ‘kafarsa fararan ‘kafarsa sosai ta fito cikin wandon jikinsa , kafarsa ma sanye take cikin farin takalmin Yeezy , yadda ‘yan yatsun ‘kafar suka fito sosai zasu baka sha’awa dogaye farare tas dasu, jikinsa sanye yake cikin farar t-shirt din Chanel da tayi mugun fito da ‘ka’k’kar far muscles dinsa , dogon hannunsa fari tass sosai suka fito musamman yadda hannunsa na dama yke d’auke da abun hannu guda biya daban daban na diamond , yadda shirt d’in jikinsa take da shape din V ga button d’aya da yake a bud’e sosai ya bawa lafiyayyar farar fatar jikinsa fitowa , daga yadda rigarsa take kana iya hango yadda siririyar sar’kar diamond dinsa take ‘kyalli, iya kyau da had’uwa big boss ya had’u sosai gyaran da gashin sa ya samu ya ‘kara ‘kawata face d’insa musamman yadda red lips dinsa yayi jaa kamar Wanda ya saka janbaki ga tsagar giransa da tafito sosai cikin cikakkiyar girarsa, bakin gashin kansa da ya’ke amurmurd’e sosai yake tasar da ‘kamshi na daba , iya kyau Allah ya zuwa big boss kyau na wuce hasashen me hasashe musamman idan mutum ya ‘kiyasta kyaun idanuwansa, daga gefensa little ne shima cikin shigar brown din Riga sai milk din wando da milk din takalmi shima da ya saka , sosai kyaun little ya fito sosai ga gyaran askinsa da kullum yake kusa da idanunsa, duk Wanda yaga little yaga big boss yasan Jini ba wasa ba , musamman yadda kalar fatarsu take kusan d’aya amma duk da haka big boss ya fisa haske , fuskarsa har yanxu akwai murmushi akan ga dimples dinsa da ya fito sosai , gabaki d’aya maganganin prince a kunnansu shiyasa yake ta sakin murmushi , a hankali ya soma taku cikin ta kunsa na kullum a nutse cikin Kamala da tsantsan izza , ga face dinsa da har yau take a had’e babu fara’a a tattare da shi amma hakan ba ‘karamin kyau yake masa ba , yadda gyaran asking kansa yake sosai zai burge musu yana tafiya murd’ad’d’un gashin kansa na motsawa , duk da be d’ago da eyes dinsa ba yaji alamar ido akansa , a hankali ya d’ago da sexy green eyes dinsa , kai tsaye direction din bobo ya kalla tare da bashi wani irin kallo da ya saka bobo d’auke eyes dinsa yana murmushi yasani big boss bayasan kallo amma shi duk lokacin da yaga big boss yayi dressing yana jin dad’i sosai da sosai hakan yake burgeshi dan yasani d’an uwansa kyakkyawa ne shiyasa mata suke mugun hauka akan sa amma shi besan sunayi ba dan samun kwanciyar hankalinki kada ya sanı idan ba Haka ba hmmm ba’a magana dan ko wana hukunci ya mike ke Kika janyo , a kan farar one sitter kamar ta sarauta ya zauna sai kayansa da kujerar suka ‘karayı masa kyau , yadda yayi crossing legs dinsa yana lumshe idanuwa sai ya burge mutum , hatta su Prince gabaki d’aya sai satar kallansa suke , hatta uncle da ya Fito shima bin big boss din yake da kallo , danshi ba kayane suke masa kyau ba , shine yake yiw kaya kyau , kasan tuwar kowa yasan baya cin abinci akan dinning yasa little da prince jera masa dishes din da bobo ya dafa masa, cikin unique way suka shirya komai dan har course suka nemo kala kala dan ba kowane irin ajje abinci yake soba ( lalle big boss wannan izza har ina 😹🚶🏻♀️) har suka kammala jera dishes din yana zaune idanuwansa a lumshe , ko sound d’in ajje abu basayi sabida kar ya bud’e eyes dinsa.
PAY YOUR 300 into 2681892316 , Aisha Umar , zenith bank sai a turo shaidar biya ta wannan Number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨
Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*
💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
S____18💞
Suna kammala jera dishes dinning suka nufa shida prince kasantuwar uncle da yaya bobo sunyi breakfast d’insu , shiyasa ba ‘bata lokaci James yayi serving d’insu abincin da zasuci. Bobo kuma falourn ya dawo akan d’aya daga cikin kujerun da suke facing big boss ya zauna , uncle na d’ayan side d’in shima hannunsa d’auke da jaridarsa. A hankali big boss ya soma bud’e eyes d’insa , yadda yake motsi dasu haka kyawawan dogayen gashin idanuwansa suke motsawa , a hankali ya ware idanuwansa gabaki d’aya , yadda little da prince suka jera center d’in da abincin yake kai ba’karamun ‘kawatuwa yayi ba , da sau d’aya ya kalli abincin ya d’auke face d’in sa , sosai abincin ya burgesa amma ko a fuska mutum bazai ga alamun hakan a tattare dashi ba , murmushi bobo ya saki tare da matsowa , da kansa yayi serving big boss abincin da zaici and everything da yasan zai bu’kata, kusan 2 minutes bai motsaba saida yaga dama dan kansa , Greek quinoa salad da bobo ya ajje masa ya d’an iba kad’an cikin spoon ya kai bakinsa , yadda yake motsi da bakinsa kad’ai abun kallone ga red lips dinsa da suke motsawa a hankali, saida ya ‘karacin second spoon sannan ya d’an d’ago side din bobo batare da ya kallesa ba ya d’an ta’be bakinsa kad’an , fuskarsa har lokacin babu fara’a akai , sosai yadda yayi ya saka bobo murmushi hatta uncle saida ya murmusa Dan kome yayi kyau yake ‘karasa, saida ya ‘karacin 3 spoon of Greek quinoa salad tukunna kafun yaci Tortilla soup d’in gabansa, komai cikin nutsuwa yake yinsa , yadda yake shan tortilla soup mutum sai ya d’auka baya san cin abinci , yadda yake yin komai cikin nutsuwa zai baka mamaki dan ko sound din plate ba’aji. Ihun da little yayi ne yasaka bobo da uncle saurin kallansa , banda big boss da ya d’an lumshe eyes d’insa sabida yadda ‘karar ta cika masa dodan kunnansa, be gama nashi ihun ba shima prince ya saka nasa ihun lokacin little ya kammala cin abincinsa, gabaki d’ayansu sabida farinciki sun manta big boss abinci yake ci sukai hugging d’insa lokaci d’aya , little har wani sound d’in dariya zakaji yanayi sabida yadda yake cikin farinciki , bobo na ‘ko’karin yin magana yaji kamar shigowar message cikin wayansa , yana dubawa ya d’an zaro eyes d’insa waje yana sakin murmushi, yadda big boss ya ‘kara shan murr ne ya ‘kara saka shi wani dariyar, uncle be gama fahimtar murnar me suke ba shima yaji sa’kon shigowar text , kamar bazai bud’e ba amma yadda yaga little da prince sun zuba masa ido ne yasaka shi bud’ewa har lokacin basu saki big boss da ya ‘kara d’aure face dinsa ba , shima uncle yana ganin alert d’in ma’kudan kudin da big boss ya tura masa bai san lokacin da wata ‘karamar dariyar farinciki ta kwace masa ba , shi kuma ba abun kayi masa Godiya ba sabida kome zai musu baya basu chance d’in su gode masa sabida yadda yake ‘kara had’e ransa shiyasa gabaki d’aya suka kasayi masa magana dan yanxu zai iya ‘bata ransu duk da ba wannan ne karo na farko da yake tura musu kud’i ba , hatta bobo murmushin kud’in da yagani yake ,