x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 43 - IBTISSAM BOOK 1

  • 126001 words
  • 129000 words
  • Out of 200864 words

Category: Romance Story +18

Views 313

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads

Suna zaune har little ya d’auko wa big boss abinci ya jera masa kamar yadda suka saba , ga Abla dake facing d’in inda yake , gabaki d’aya sai taji ta ‘koshi bata jin yunwa dan ko kwakkwaran motsi ta kasa , har little ya gama serving din yaya big boss . “ Lil ya kika dena din abincin ?” Cewar bobo bayan ya kalli big boss da ya ‘kara shan kunu, yasan Sabida big boss ne ta kasa cin abincin , muryarta na rawa ta furta “ Na ‘koshi ne…” girgiza mata kai bobo yayi “ No lil ai bakici sosai ba , ko kuma kawai ki tafi dashi d’aki “ kamar jira take kuwa ta jinjina masa kai da Sauri tana d’aukan tray d’in, little zai dakatar da ita bobo ya hanasa . Big boss kuwa kamar be san me ke faruwa a falourn ba , hankali a kwance yake cin abincinsa , lokaci zuwa lokaci kuma yana danna wayar hannunsa. Cike da d’an zolaya bobo ya furta “ yaya big boss mufa yadda kake d’aure mana face d’in nan yana bamu tsoro kaga ka saka sister d’in mu guduwa”, wani irin kallo big boss ya zubawa bobo da yasa ka babu shiri bobo ya saki dariya “ maida wukar yaya bani na kar zoman bafa “, big boss be ce masa komai ba ya cigaba da cin abincinsa , saida ya gama tukunna ya mi’ke tsaye yana kallan black Rolex d’in hannunsa . Da Sauri bobo ya furta “Are you going out ?” Ba tare da ya kallesa ba big boss ya d’an yi knodding kansa , murya ciki ciki ya furta “ yeah ! See you all” yana kai ‘karshen maganarsa yayi hanyar barin falourn , da d’an ‘karfi little ya furta “ yaya please karka manta ! Love “.

Sai da prince ya ga fitar Big Boss kafin ya kalli little “ me ne ne “ d’an harararsa little yayi “ Allah yaya prince kana san jin gulma “ babu komai fa ! Lil nace asaka makaranta “ kusan lokaci d’aya prince da uncle suka furta “ ya amince ?” Kansa little ya girgiza akan Ah’ah , murmushi bobo kawai ya saki batare da yace komai ba , har ya juya sai kuma ya d’an tsaya “ I think you get some visitors may be “ cikin tsokana Uncle yace “ kodai sirikai nane?” Lokaci d’aya bobo ya d’aure face d’insa , bai bi takan maganar uncle ba ya juya ya bar wajan.

Abla tana shiga cikin d’aki ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ‘kirjinta , kamar zatayi kuka ta furta “wallahi wannan zuciyar tawa matsoraciya ce , ko uwar karuwai da take kawo mun hari bana jin wannan bugun zuciyar ! Haba fisabilillah”, gabaki d’aya sai taji abinci ya fice mata arai har ta ‘koshi , a fili kamar me magana da wani kuma ta ta’be baki “ Mutum kullum sai ‘kara kyau yake kamar wani aljani”.
Ledojin jiya ta janyo ta fara bubbud’e kayayyakin da aka siyo mata , ba’karamun kyau sukayi ba ita kad’ai sai faman dariya take . Gabaki d’aya kayan jera su tayi cikin wardrobe , ta kalmi da jaka ba gabaki d’aya kowa da inda ta saka su hatta kayan za’kin da Prince ya kwaso mata , lokaci d’aya sai d’akin ya canza ya zama na cikakkiyar budurwa me ki da gata .

✨✨✨✨✨

2:50pm ta sakko daga d’akin ta gudun kar ta sake yin wani laifin , tasan idan bata Kai wa simba abinci ba , ita big boss zai mayar simba , ga tsoro da take ji, dad’in ta tana sakkowa taga little zaune akan kujera , “ yanxu nake shirin kiranki Lil , ya kamata ki kaiwa simba Abinci kai ki sake wani laifin ko ?” Da Sauri Abla ta furta “ Eh” suna tafiya suna hira dan yanxu ta rage tsoran sojojin sosai . Suna shan hanyar da zata sadasu da d’akin simba wasu manya manya motoci suka shigo cikin gidan kusan guda takwas, cikin Sauri wasu sojojin Suka kare wata mota , kafun lokaci d’aya su bud’e musu both side , His excellency ne ya fara fitowa daga cikin motar , sai Her excelling da ta fito itama cikin shigar ‘kananan ‘kaya , a gadarance ta furta “ let’s go sweetheart” wata farar ‘kaface ta soma fitowa da ta cin red jan farce a ‘yan yatsun ‘karta , cikin iyayi ta fito daga cikin motar , ba kowa bace face Alice da taci wankan turawa hirar jikinta black colour ko cibiyarta bata rufe mata ba , sai red d’in wando da shima ko kwiwar ‘kafarta be kai ba , ga wani uban hill shoe da ta saka , sai Faman ya tsine face take , dukda kasancewar ta yar president ba ‘karamin tafiya da imaninta tsarin gidan yayi ba kasancewar wannan ne zuwanta na farko , ta ko ina kamar kiran president Jami’ai ne , Jami’an da suka ninka nasu a yawa da girma , lokaci d’aya wani murmushi ya su ‘buce mata “ soon I will be the queen of this house ! Zanyi ruling kowa ! Wow”. Sweetly let’s go “ cewar her excelling , cikin yanga Alice ta soma ta ku, so take kawai ta saka big boss cikin idanuwanta , tun accident din da ya faru har bobo ya tsinka mata mari bata sake ganin sa ba duk yadda taso hakan kuwa . Har ciki Robert yayi musu iso , lokacin uncle ya fito daga part d’insa bobo ba haka , hugging din bobo his excellency yayi “ my son how are you “ fine Kawai bobo yace masa , itama Alice ganin Dadynta na wajan ta mi’ke wai zatayi hugging d’insa , kallan da yayi mata ne yasa ta waske ta koma ta zauna sai faman zuba ido take taga ta inda Big boss zai ‘bullo .

A ‘bangaran Abla kuwa suna zuwa wajan d’akin tsoro ya kamata , dad’insu ma yau ba Victor bane dukda kusan halinsu d’aya amma Ana bud’e d’akin simba Abla ta je fa masa abinci kamar yadda suka shirya plan d’insu ita da little , suna tafiya suna dariya abunsu, a hanyar komawarsu gida sukaga manyan motocin da suka shigo , sau d’aya little ya kalli motocin ya san bana yayansa bane , suna tafiya suna hira abinsu gwanin burgewa , suna shiga cikin falourn sukai sutus Sabida mutanan da suka gani zazzaune a falourn, Lokaci d’aya Alice ta mi’ke tsaye rai a ‘bace “ me wannan ‘kazamar take anan kuma ?”kallan tara saura Abla ta bita dashi lokacin da suke shigo cikin falourn , shima little cikin ido ya kalleta “ she’s the sister of the family kinga ba ‘kazama bace “, dakatar Dashi bobo yayi “ it’s okay little calm down !” Turo bakinsa little yayi kafun ya gaishe da su mr president duk da ya sansu amma kwata kwata face d’insa ba fara dan gabaki d’aya basuyi masa ba , itama Abla gaishe dasu tayi zata juya little yayi saurin furta “ Lil ! Zo muje garden “ toh kawai Abla tace zasu juya Alice tayi Saurin furta “ sorry guys zan iya binku” little har Zaice mata ah’ah sai yaga bobo yayi knodding kansa , kamar yadda big boss yake magana a fusge shima yau haka little yayi kafin ya furta “ why not “ Abla lokaci d’aya kamar little ya rikid’e ya koma mata Big boss , suna tafiya yana janta a hira banda Alice da sukayi kamar basu san da zuwanta ba . Suna shiga cikin garden d’in Abla ta fara furta “ wow ! Wajan nan yayi kyau sosai “ murmushi little ya sakar mata “ ko muje wajan pool? Zaifi “ da Sauri ta furta yes , haka suka bi wani side duk a cikin garden d’in lokaci d’aya ya kawosu wani babban pool me shegen kyau da fad’in had’uwarsa ‘bata bakine . Wani shu’umin murmushi Alice tayi batare da tace musu komai ba , little har zai zauna a bakin pool d’in sai kuma ya dakata tare da furta “ Lil ina zuwa “ okay Abla tace masa lokacin da ya bar wajan yayi saura daga ita sai Alice , kallan ta Alice tayi daga sama har ‘kasa cikin wani irin kallan tsana ,” how dare you ? Waya baki izinin zama a cikin gidan nan ?” Kallan baki da hankali Abla ta bita dashi batare da ta tanka mata ba sai ma pool da ta zubawa ido ganin yadda yayi blue , cikin tsawa rai a ‘bace Alice ta furta “ how dare you ! Ina miki magana kin shareni? I can easy killed you ! Stupid !” Yanxu banza Abla tayi mata hakan ya ‘kara ‘bata wa Alice rai da ‘karfi ta janyo rigar Abla “ how dare you ?” Itama Abla rai a ‘bace tayi ‘ko’karin kwace rigar ta batare da ta tankawa Alice ba , ko kawa suka soma yi Abla tana ‘ko’karin kwace rigar ta Alice kuma tana ‘kara ri’keta, a zuciye Kawai ta jefa Abla cikin pool, gashi Abla bata iya ruwa ba , lokaci d’aya ta fara wutsul wutsul a cikin ruwan ta na mi’ko da hannunta, ga ruwa da ya’ke shigar mata hanci, sosai Abla ta soma ‘ko’karin fitowa Amma kamar ruwan janta yake , tsaki Alice taja ta juya tabar Abla tana wutsur wutsur gashi ko idanuwanta bata iya bud’e , lokaci d’aya nunfashinta ya soma sar tsewa sabida rashin nunfashi da bata sha’ka, tun tana ‘ko’karin cecan kanta har ta dena motsi da hannunta , gabaki d’aya jikinta ya soma nutsewa cikin ruwan.

PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.


https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee ✨

WATTPAD
https://www.wattpad.com/user/Msslee__

AREWA BOOK
https://arewabooks.com/book?id=652ff3a03fd6ffc37f68e4e2

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

NOT EDITED
S____26💞
A dai dai lokacin da Alice ta fito daga wajan , a dai dai time d’in shima Little ya nufi fool d’in, ganin yadda gabaki d’aya kamar ba’a cikin nutsuwar ta take ba yasa ya d’an ta’be bakinsa dan shi gabaki d’aya yarinyar bata yi masa ba , yana shiga ya tarar da babu Abla , da ‘karfi ya furta “ Lil sis kina Ina ? “ shiru ba’a amsa masa ba, a karo na biyu ya ‘kara furta “ Lil na dawo “ nan ma shiru babu amsa dan gabaki d’aya hankalinsa bai kai cikin ruwan ba , har ya juya zai fita yaga kamar abu ya fad’a cikin ruwa , ‘kirjinsa ne ya buga da ‘karfi lokacin da ya hango kayan Abla , da ‘karfi ya furta “ Lil? Lil? Lil?” Kusan sau uku Abla bata amsa ba gashi ta nutse cikin ruwa , hankali a tashe little yayi ‘ko’karin shiga cikin ruwan amma an hanasa sabida condition d’insa , gashi bazai ta’ba iya barin Abla a cikin ruwan ba, danger ya danna dake jikin pool d’in batare da ya damu da yadda nasa rayuwar zata kasance ba ya fad’a cikin ruwan. Cikin kwarewa yake yin iwo cikin ruwan duk da yadda shima nunfashinsa yake ‘ko’karin sar’kewa dan sosai Big boss ya hanasa shiga cikin pool yanxu sabida condition d’insa , dai dai inda Abla take little ya nufa yana ‘ko’karin zaro ta , shima lokaci d’aya nunfashinsa ya soma sar’kewa ga sanyin ruwa da bayaso yana ratsa masa jiki, amma duk da haka cikin ‘karfin hali yake janyota, at the same time shima yana ‘ko’karin fusgo nashi nunfashin da yake ‘ko’karin sar’kewa, da saurin sa yake janyo hannun ta da ko kusa babu alamar rai a tattare da ita ,Tun kafin suyi nisa shima ya saki hannun ta da ya ri’ke mata Sabida yadda nunfashinsa ya tsaya lokaci d’aya , kamar yadda ta soma nutsewa a cikin ruwa haka shima little ya soma nutsewa.

***** Lokacin da Little ya danna danger take a wajan wani jan na’ura ya karad’e gabaki d’aya cikin gidan, a zabure sojojin suka saita bullet d’in bindigogin su, Bobo na zaune akan 1 sitter lokacin da Alice ta shigo cikin falourn kamar arud’e, yana ‘ko’karin yi mata magana yaji ‘karar danger ,da wani irin mugun zafin nama ya mi’ke tsaye , lokaci d’aya kawai ya kalli direction d’in Alice , babu Wanda yayi wa magana shida uncle cikin gudu gudu su Bobo sukai ‘ko’karin fita , tun kafun ya fita shima prince da ya fito daga cikin d’aki ya ‘kwalla wa bobo ‘kara yana furta “yaya bobo suna swimming pool “, Bobo bai jira jin ‘karshen zancan saba ya saka gudu cikin mugun speed , shima prince sakkowa yayi yana bin Alice da kallo dan gabaki d’aya yaga abunda ya faru , cikin tsana ‘karara ya furta “ zaki gane kin shigo gidan da ba’a hauka “ daganan be ‘kara ce mata komai ba shima ya saka gudu yabi bayan Bobo.

Her excellency ce ta kalli Alice cikin d’an rud’u “ Sweaty me ya faru?” Ita ma Alice da jikinta ya fara rawa kallan Dad d’inta da Her excellency tayi ganin suma gabaki d’aya sun zuba mata ido suna jiran jin amsarta, bakinta har rawa yake lokacin da take magana “ Dad bansan me ya faru ba ! Bani da laifi ! Ta ri’keni da fad’a mistakenly ta fad’a ruwa , I don’t know Anything “, shi kansa His excellency be san lokacin da ya dakawa Alice tsawa ba , karo na farko a rayuwarsa ,” Are you mad ? Baki da hankali ? Kinsan Gidan suwa kika shigo? No! No!No! We have to leave now kafin Big Boss ya shigo , Let’s go”, da Sauri suka fito daga cikin falourn , Sojojinsu suka bud’e musu mota suka shiga , Allah Allah His excellency yake su fita daga cikin gidan Inya so koma menene zai yi sau’ki Amma abinda basu sani ba sun makara sabida tun kafin su fita daka gate 1 , Manya Manyan motocin Big Boss suka shigo cikin gidan da mugun speed , wani irin gefe motar Big Boss tayi har wajan garden d’in, cikin zafin nama ya nufi Pool d’in shima . Victor da Anthony da suma sam babu fara’a a tattare dasu suka shiga gaban motocin president , cikin Sauri sojojin president suka fito tare da saita su Victor da bindiga, basu ankara ba sai gani sukai gabaki d’aya sojojin Big boss sun zagayesu tare da saita ko wannansu da bindiga , umarni kawai suke jira su saki bullet uban kowa ma ya mutu.

****** Bobo na zuwa bakin pool be jira komai ba ya fad’a cikin ruwan , Little ne a farko farko cikin kwarewa Bobo yake yin iwo cikin ruwan, Little ya fara cirowa Sabida sanin halin conditions d’insa ,
Duk da shima ba kasafai yake san ruwan sanyi a jikinsa ba , haka ya koma cikin ruwan yana ‘ko’karin ciro Abla , Duk yadda yake tunanin abun ba me sau’ki bane sabida yadda Abla ta ma’kale ta hanyar da ruwan pool d’in yake tafiya , idan yace zai cirota ta ‘karfi kuma zai iya ji mata rauni, duk yadda yaso ya janyo ta abun ya ci tura shiyasa ya nutse cikin ruwan kamar wani kifi ga idanuwansa da suke a bud’e yana kallan cikin ruwan, ‘kafar Abla ce ta ma’kale , idan kuma yace zai janyo mata zai ji mata mummunan rauni, kamar daga sama suka ga Big Boss a wajan pool d’in , cikin Tashin hankali Prince ya nuna masa pool d’in “ yaya zata iya mutuwa any moment tafi 10minutes a cikin ruwan”, d’an ‘karamin tsaki Big Boss kamar bazai shiga ba , lokaci d’aya kamar wani iska ya fad’a cikin ruwan , yadda yake yawo cikin ruwan zaka tabbatar ba ‘karamun iya ruwa yayi ba ,cikin Sauri sauri ya nufi inda Bobo ya nutse , Bobo yana ganin Big Boss ya saki ‘kafar Abla da yake ‘ko’karin cirowa , cikin Sauri ya fito daga cikin ruwan ya nufi little da har uncle da prince sun fara fitar masa da ruwan da ya shigar musu ciki, batare da ‘bata lokaci ba Bobo ya sa’bi little a ka fad’arsa suka bar wajan gabaki d’aya , wajan yayi saura Abla da Big Boss .

Almost 2 minutes Big Boss yana cikin ruwan nan shida Abla , idan mutum ba lura yayi ba sai ya d’auka baya cikin ruwan sabida yadda yayi mugun nutsewa, cikin ‘yan seconds d’in da basu wuce 30 ba inda suke ya soma yin ja alamar d’aya daga cikin su ne ya ji ciwo. Ko mintuna d’aya cikakkiya basu ‘kara ba ya janyo ‘kafarta ya fito da ita daga cikin ruwan, gashi ya had’e face d’insa da tayi mugun yin ja na ‘bacin rai . Guntun tsaki yaja ganin yadda kayan jikinta suka manne mata , har yanxu face d’insa ba fara’a ya kauda kansa tare da mi’kewa batare da ya kalli side d’in da take ba ya d’auki Coat d’insa white colour xai ‘bar wajan , bayajin zai iya temaka mata amma idan ta mutu shine da lefi a Wajan Allah , wani ‘karamin tsakin ya ‘kara saki ya nufo inda take a kwance bata ko motsi, kamar zai kai
Hannu kan face d’inta ya ‘kara jan wani tsakin , gefen face d’inta ya d’an duka tare da furta “
Hey !” Shiru Abla bata motsa ba , a karo na biyu ya d’an mari d’ayan side d’inta yana furta “Hey” still ba’a amsa masa , ganin yadda ruwa ya fara fito mata daga gefen bakinta kad’an yasa ya ‘kara sakin wani gajeran taki , Hannunsa d’aya ya kai Daidai saitin cikin ta yana yatsine fuska, yana dan na mata cikin, sai ga ruwa nan ya fara fitowa
End Ads