x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 45 - IBTISSAM BOOK 1

  • 132001 words
  • 135000 words
  • Out of 200864 words

Category: Romance Story +18

Views 292

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ya bud’e masa , Victor ya shiga driver set, Anthony kuma ya shiga d’ayan side d’in suka bar gidan su kad’ai , har lokacin bobo be dawo ba kuma. Abla tana ganin ficewar sa har wani gumin bala’I take had’awa , a guje ta nufi d’aki, ko tsayawa batayi ba sabida fitsarin da ya kamata . Sai da tayi tukunna ta saki ajiyar zuciya tana safa cikinta da take ji cike taff da ruwa , ko minti goma batayi ba ta sake komawa yin fitsari, ita kad’ai sai faman zaryar yin fitsari take dan 10 cups ba wasa ba , saida tayi zaryar yin fitsari, ana biyar d’inne har da kwalla kafun ta Samu ta kwanta , cikin ‘kan’kanin lokaci bacci ya d’auketa.

🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂

KANO
Yau ya kama ranar dasu Eshaal zasu koma Us, duk hanyar da baby ta bi danganin ba’a tafi da itaba abin ya ci tura Sabida duk lokacin da zata takaleta da fad’a Eshaal bata biye mata , Musamman yau da ta sha kuka Sabida zasu rabu da Ammi, Baby kuwa tana wajan su dad sai lallashinta sukeyi akan kome take so ta saka Eshaal idan ta’kiyi mata ta kirası , bayan doğan gargad’i da Tasha wajan su dad , lokacin da zata su tafi Airport kamar karta tafi Sabida Amma , ita kanta AMMA sai da ta share ‘kwalla , baby kuwa sai faman taunar cingum take abunta su dady suna lallashinta har suka tafi Airport. Acikin Airport din ma ko kusa mutum bazai ce tare baby take da Eshaal ba Sabida yadda taja gefe wai zata bata masa class d’in ta . Acikin jirginma Baby tana ‘bangaran Business class , Eshaal kuma tana inda normal people suke , cikin ‘kan’kanin lokaci jirginsu ya tashi zuwa U.S ✈️ .


*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee ✨


KAR AMANTA AYI FOLLOWING DINA
👇👇👇👇

WATTPAD
https://www.wattpad.com/user/Msslee__

AREWA BOOK
https://arewabooks.com/book?id=652ff3a03fd6ffc37f68e4e2

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
Book 1 free ne, book 2 kuma 300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

S____27💞

Yau Abla da wuri ta farka Sabida ta sakawa kanta hakan cikin ranta , tana idar da sallar asuba d’akin ta gyara gabaki d’aya kafin ta yi wanka, yau ba lefi ta gwada wanke kanta , dan sosai ta dirje kan nata da yayi mugun datti, har wani brown brown yake tsabar datti, tana wanke wa gaban mudubin d’akin ta dawo tana bun jerun kayan wajan, d’aya daga cikin mayukan wajan me suna HEMANI ta d’akko, daga cikin oil d’in zakaga hotan Black seed a jiki. Sai data bari kanta ya bushe sosai sannan ta shafa oil d’in a kanta , binciken inda zata samu comb ta soma, cikin sau’ki kuwa ta same wani black comb , daga ‘kasa ‘kasan gashinta ta soma tajewa Sabida zafin da yake mata , tanayi tana runtse ido ga nishin da take lokaci guda sabida wahalar tajewa da take ji . Da ‘kyar ta iya taje kan shima sama sama ta tattara ta ajjesa , sabida yadda ya ‘kara cikowa ko d’aure kan ta kasa sai mayafi da ta yafa akan ta , duk Wanda ya kalli kanta sai yayi mata dariya sabida yadda gashin kanta ya ciko sosai cikin mayafin kamar wani bishiya. Cikin d’an turo bakin da ya d’an zamar mata jiki ta fito daga falourn, 7 ta kusa shiyasa bata tsaya jiran Little ba yau ta wuce kaiwa simba abinci da kanta , dukda yanxu ta d’an rage jin tsoransa ba kamar daba , hatta sojojin gidan ma yanxu ta rage jin tsoransu sosai dan yanxu ma da kanta ta wuce ga tulin gashin kanta da yake nunawa. kamar yadda Little ya koya mata , tana bud’e d’akin simba bata shiga ciki ba ta jefa masa abincinsa tayi saurin guduwa cikin gida.

Tana shiga ta tarar da su Bobo a tsats tsaye da alama daga masallaci suka dawo, sai da tabi kowannansu ta gaishesa amma bata ga Big boss ba , har cikin ranta taso ganin nasa ko saud’aya shiyasa gabaki d’aya mood d’inta ya canza . Cike da zolaya Little ya nuna Kanta “ Sister Menene a kanki haka kamar bishiya?” Kan nata ta ta’ba itama , kamar zatayi kuka ta girgiza masa Kai dan ta rasa Wana irin amsa zata bashi ma ,” oya muga bishiyan kanki “ cewar little yana ‘kara mata dariya , da Sauri Abla ta saka hannu zata kare kanta , shima little ya dage sai ya ga kan nata , ita kuma ta ‘ki barin sa ya bud’e mata kai , da ya matso zata goce masa , su Prince suna tsaye suna musu dariya , ganin Sauri zata gudu mayafin kan nata ya zame , wata iriyar shegiyar dariya prince da little suka saki lokaci d’aya sabida uban tulun Abla suka gani gashi kamar bishiyar sabida yadda ya mimm’ke tsaye, shima Bobo sosai yayi mamakin uban tulin gashin kan Abla , ydda ta sunkuyar da kai kamar zatayi kuka ne bobo ya dakatar dasu little daga dariyar da suke mata “ rabu dasu anjima zan sa akai ki saloon a wanke miki , idan angyara miki karki nuna musu kinji ?” Da Sauri ta jinjina masa kai “ Thank you so much yaya bobo” sai ta kalli side d’in su little tayi musu kwalo tare da yan kwane hannunta kamar wata horror, gabaki d’ayansu dariyar reaction d’inta suke , hira kad’an suka ta’ba ko wannansu ya koma part d’insa Sabida zuwa training . Itama Abla d’aki ta koma ganin bacci be isheta ba yasa ta fad’a kangado kamar me shirin komawa baccin , a hankali kuma ta furta “ Amma me yasa be fito ba ?” Kamar zata kawar da zancan daga zuciyarta amma hakan ya faskara , so take kawai ta saka shi cikin idanuwanta koda ace hukunta ta zaiyi , haka kawai taji tayi missing d’in ganinsa , tun tana tunanin kyakkyawar fuskar sa a zuciyar ta har bacci ya d’auketa.

10:50am Abla ta fito daga cikin d’akinta haryanxu kanta yana a yadda yake dan kuwa sosai ya tashi kamar bishiyan, prince ne kawai a falour shima lokacin game yake , batare da ya kalle taba ya furta “ sister breakfast d’inki na dinning,Little yace idan baki cıba idan ya dawo na fad’a masa “, kamar yana kallanta ta Jinjina masa kan nata tare da furta “ okay yaya “. Tana zuwa dinning d’in ma ba wani abun kirki taci ba , coffee Tasha sai waffles data gani , daganan kuma bata ‘kara cin komai ba . Tana gama wa falour ta dawo , d’an satar kallan elevator Abla tayi kamar tana jiran fitowar sa , sai kuma ta d’auke eyes d’inta “ Yaya prince ina yaya little ?”
Har yanxu game d’insa prince yake , still be kashe ba ya furta “sun fita da yaya bobo”, Tom Allah ya dawo dasu lapiya “ cewar ta , shima da kalmar Ameen prince ya bita dashi, yadda yake cin game d’in take kalla amma idan kayi mata kallan nutsuwa zakasan gabaki d’aya hankalinta baya kan game d’in prince , ta fad’a wani tunanin ne kawai daban. Lokaci d’aya taji zaman falourn ya isheta shiyasa tayi excusing kanta ta koma cikin d’akinta , a fili ta furta “ me ya hanashi fitowa ? Ko bashi da lapiya ne ?”, sosai damuwa ta hau kan fuskarta irin damuwa da bata ta’ba shiga ba na rashin ganin wani, amma yanxu gashi ta damu da sanın halin wanda ya fi tsanar ta a cikin gidan . Lokaci zuwa lokaci tana duba time , sau 2 tana sakkowa ‘kasa koza ta gansa amma still babu alamar sa , ji take kamar ta tanbayi Inda yake amma haka ta ‘kara komawa cikin d’akinta, a karo na 3 data ‘kara sakkowa bata ga prince ba shiyasa ta sauke a jiyar zuciya . Gabaki d’aya ta damu da san ganin Wanda bata ma isheshi kallo ba . Ha’kura tayi da sakkowan ta koma d’akinta ganin shirun na neman gundurarta yasa ta d’auke system d’inta da little ya bata , kamar wacce ta ‘kware a harkar computer haka take sarrafata sabida gabaki d’aya ta gane yadda ake anfani dasu.

****** Big Boss

Tunda yafita daran jira bashi ya dawo ba sai washe gari da asuba , yadda kowa ya ga face d’insa a had’e yasa suka soma kaffa kaffa dashi dan kuwa zai iya huce ‘bacin ransa idan ka kuskura ka shiga gonarsa yau , hatta little idan yagansa a irin condition d’in nan baya takura masa . Shiyasa gabaki d’aya gidan kowa ya shiga cikin hankalinsa , musamman su little akan lokaci yau suka fito training batare da sun ‘bata lokaci ba . Babu Wanda ya kalla yayi wucewarsa part d’insa . Direct toilet ya nufa ya sakar wa kansa ruwa me mugun sanyi, ya dad’e a cikin ruwan kafin ya danna wani button da glass in wajan ya zama kamar tinted , mutum bazai ta’ba ganin me ke faruwa ba sai dai shi da yake ciki yaga abunda akeyi.
Be d’au dogon lokaci ba ya fito daga cikin toilet d’in d’aure da wani white d’in rigar wanka sai gashin kansa da yake a ji’ke alamar wankesa yayi shima , ga face d’insa da har yau babu fara’a kanta itama da alamar ruwa , d’ayan door d’in d’akin ya shiga , ko 30 minutes be yi ba kamshi turaransa me shegen kamshi da tafiya da zuciyar mutum
ya bada isowarsa, dan tun kafin ya fito daga cikin d’akin ko ina ya karad’e da kamshi. cikin wani Dogon farin wando me laushi ya fito daga cikin d’akin, kana kallan wandan zakaga da kad’an ya wuce gwiwar’kafarsa. Sai fararar kafafuwansa da suka fito farare tass dasu musamman yanda suke cikin wani white din takalmi. lokaci d’aya murd’ad’d’iyar surar jikinsa ta bayyana cikin farar singlet d’in jikinsa, yadda singlet d’in ta kama masa jiki sosai hakan ya fito da six pack d’in jikinsa, wani remote ya dakka lokacin da ya kwanta akan king size bed d’insa, take a Wajan sanyin d’akin ya ‘karu sosai ga wani irin black dummm da d’akin yayi kamar babu kowa a cikinsa.

****** karfe 12:10pm su little suka dawo cikin gidan , dan bobo ko zama beyi ba ya ‘kara ficewa bayan little ya shiga cikin gida . A kwance ya tarar da Abla kan 2 sitter ganin bata ji shigowar sa ba yasa ya lalla’ba bayanta Daidai saitin kunnuwanta ya fara kukan mage “ meow ! meow !”da Sauri Abla ta bud’e idanuwanta ganin little a gefen ta yasa ta tashi zaune “ Allah yaya little ka bani tsoro fa” d’an murmushi yasaki kafun ya bata amsa “ naga baki ji shigowa taba kuma ba bacci kike ba shiyasa na miki haka “Tom
Shikenan , yanzu dai sannu da zuwa , bari na kawo maka ruwa ko ?” Cewar Abla tana mi’kewa tsaye , mayar da ita yayi kan kujerar yana girgixa mata kai “ No bana bu’kata keda ya kamata ki fara tanbayata ina naje ?”, itama kanta Abla ta girgiza masa “ But atleast ya kamata kasha ko ruwane kaji?”, zaman shi ya gyara kan kujerar kafin yace mata “ okay”, cikin ‘kan’kanin lokaci ta dawo d’auke da ‘karamin tray me cup da lemo da ruwa , ruwan kawai ya d’auka yasha tun kafin ta zuba masa , wani envelope ya mi’ka mata , tun kafin tayi magana ya rigata “karki bud’e ki bari sai kin koma d’aki”, bata kawo komai aranta ba ta amsa masa da Tom Daidai lokacin da yake mi’kewa “ bari naje wajan yaya kinji ?” Bata san lokacin da bakinta ya su’buce ba ta furta “ lapiyansa ‘kalau?” Murmushi little yayi mata kafun yayi knodding kansa “ yeah ! Yaya yana lapiya nasan yanxu yana d’akinsa , bari naje wajan sa and don’t forget sai kinje d’aki zaki bud’e envelope d’in kinji ?” Da toh Abla ta amsa masa bayan ta tafi, itama d’akinta ta koma da Sauri dan ta matsu taga menene a cikin envelope d’in, tana shiga ta bud’e su wata farar ta karda ta gani guda biyu aciki paper d’in farko ta ‘kurawa ido tanbarin sunan “ HORACE MANN SCHOOL” ‘kurawa paper d’in ido tayi sosai kamar tana san fuskartar abunda yake jiki, a hankali ta soma karanta application d’in jiki, kamar wacce akai wa abu kuka ya ‘kwace mata , wani irin kuka take kamar Ance mata zata mutu dan dagasken gasken kuka take sosai, ta jima tana kuka har ‘kirjinta ya soma yi mata zafi sannan ta soma ajiyar zuciya , hawayen ta basu tsaya ba , ga murmushi da dariya da ya kwace mata lokaci d’aya “ ni ? nice zan fara zuwa makaranta ? Dagaske ne ko wasa ? Da gaske daman zan koma makaranta , Arwa ta kina ina kizo ki ga zan koma makaranta” ita kad’ai sai magana take wa kanta sabida application d’in shiga Horace mann school da ta samu, cikin Sauri ta ajje paper , ta shiga toilet tayo alwala , sai da ta yi na fila raka’a hudu sannan ta zauna ta dinga addua Sabida tsananin farincikin da ta shiga , ga hawaye da murmushi kwance akan face d’inta . Tana idarwa paper ta d’auka da gudunta ta fito daga cikin d’akin tana niyar sauka , suka ci karo da little , cikin Sauri tayi hugging d’insa , murmushi ya sakar mata kafin a hankali ya furta “ suprised” itama murmushi da hawayene akan face d’inta yadda ta kwa’be face kamar me shirin yin kuka “No katkı yi kuka mana ! Let’s go for the other surprised” yana kai ‘Karshen zancansa ya kamo hannunta suka sakko ‘kasa , a tsats tsaye ta tarar da yaya bobo , yaya Prince sai uncle , Big boss ne kawai baya falan, suna ganin ta suma suka had’a baki Wajan furta “ surprised”, zatayi kuka prince yayi Sauri cewa “ No LiL d’in Little , haka kikeso ki fara zuwa school kana kuka ? Ko so kike mu kıra miki simba ?” Yanxu ma ‘kara ta’be face tayi zatayi kuka bobo ya harari prince “ rabu dasu Sister , zan rama miki , let’s enjoyed the cake together kar yayi melting”, daga nan suka zauna bayan sun yanka medium cake din da aka yi tanbarin school a jiki. Murmushi da hawaye suna sakko mata ta kalli uncle da yaya bobo nata sun kuyar da kanta “ Nagode sosai Allah ya saka muku da mafificin alkairi, Allah ya biya muku bu’katun ku na aikairi , Allah yasa ku gama da duniya lapiya, nagode sosai”.ta karasa tana kallan little shima dan bakinta bazai iya misalta godiyar da take so tayi musu ba , Allah ne kad’ai zai iya biyansu, ahankali ta furta “ yaya little nagode sosai”murmushin da baya ‘boyuwa har yanxu ya sakar mata “ you don’t have to thank me , ai bani na saki a school , makarantar da aka sakaki marabaci zan zama” ya ‘karasa a zolaye Sabida tayi dariya , sosai kuwa tayi murmushi tana sunkuyar da kanta ‘kasa . Wani Brown a kwati dake gefensu little ya matso mata dashi “ ga uniform d’in makarantar ki , kinga yau Friday, Monday kuma zaki fara zuwa school amma bazaki tafi da wannan kan naki me kama da na bishiya ba “, rankwashi bobo ya kai masa aka da harsaida yace oushhh, “ kai me yasa tsokananka ya fiya yawa ?” Cewar bobo kafun ya kalli Abla “ sister je ki shirya su kaiki saloon yanxu “ da Sauri prince ya ce masa yaya bobo ai bamu bata namu gift d’in ba , mi’kewa tsaye yayi tare da wani black box d’an ‘karami ya mi’ka mata “ wishes you all the best sister , nasan zaki karad’e kowa a class d’in ku , this is my gift,” da murmushi akan face d’inta ta furta “ thank you yaya prince “, shima little wani box ya mi’ko mata siriri “ Nima ga nawa gift d’in” shima fuskarta cike da murmushi ta furta “ thank you so much yaya little”, bobo kuma wani ATM d’insa ya mı’ka mata “ duk lokacin da kike bu’katar kudi zaki iya d’auka , it’s your gift , little yace duk kyautar da batayi ba sai ansake “ dariya ce ta kwace mata , da hawaye. Face d’inta ta furta “ ‘nagode yaya bobo “ dan gabaki d’aya ta rasa me zata ce musu, “ ah’ah ni kuma sai ku tsaya na bawa my only daughter gift d’inta okay “ box d’insa shima ya mi’kawa little “ oya karkayan suyi mata yawa help her , it’s also my gift”, gabaki d’aya she’s speechless, bata ta’ba kawowa akwia wad’an da zasu sota arayuwa ba makamanciyar ydda su little suke mata , murmushi da kuncin face d’inta ya kasa ‘boyuwa , kar’ban kayanta prince yayi ,little kuma ya ri’ke box d’aya da akwatin school d’inta “ let’s go sister , kafun ayi sallah sai mu kaiki inyaso sai mu dawo mu d’auke ki , okay ?” Kanta kawai tayi masa knodding da harshenta yayi mata nauyi, ko da zasu wuce sai data kalli elevator ganin har lokacin bataga big boss .
Har cikin d’akin sai da suka kai mata kayan , gashi sai faman tashin kamshi yake ko ina tsaf tsaf da shi , kasa hakuri little yayi saida ya tanbayeta “ sister waya gyara d’akin nan ?” Bata damu da tanbayar tasava shiyasa kai tsaye ta furta “ Ni na gyara mana “, shima prince yayi mamaki da tace ita ta gyara dan ko ina a
End Ads