x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 56 - IBTISSAM BOOK 1

  • 165001 words
  • 168000 words
  • Out of 200864 words

Category: Romance Story +18

Views 303

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
Abla sannan su fara ‘kus’kus a tsakaninsu, lokaci d’aya hayaniya ya fara tashi a cikin ajin , haka Kawai Abla taji zuciyar ta tabuga da ‘karfi, ganin surutun yayi yawa yasa itama Fanan d’aukar hotan , tana ganin jikinta ya soma rawa tayi saurin yaddar da hotan tana kallan Abla , “ Menene ?” Cewar Eshaal dan gabaki d’aya Abla ta kasa motsawa ma Sabida yadda taji ‘kirjin ta yana bugawa , inda suke Mr jabcon ya ‘karaso kafun ya d’aga murya yana nuna musu Abla “ kunga wannan hotan ? Lokacin da take iskancin da wani ne aka d’auka, da Sauri kirjin Abla ya fara har bawa cikin sauri ta d’auki hotan guda d’aya kafin ta saki wani ihu tana jefar da hotan “ ‘karya ne , ‘karya ne wannan , bani bace ba wallahi “ lokaci d’aya Abla ta fashe da wani matsanan cikin kukan ganin hotan ta ‘karara a tsirara jikin wani na miji ga hannunsa d’aya da ya d’ora kan breast d’inta , ita kuma Abla tana masa murmushi, ‘kin d’aukar hotan Eshaal tayi ganin itama jikinta ya soma rawa lokaci guda.

Allah sarki Abla sai girgiza musu kai take ta kasa magana ma sabida yadda kirjinta yayi mata nauyi , ga jabcon da yake ta maimaita kalmar prostitute ce Abla , da sauri ta kama hanyar fita a guje ko school bag d’in ta bata d’auka ba , zata fita aka turo ‘kofar a jikin, LG ce a tsaye cikin kakin sojoji, tana ganin Abla ta tsinka mata mari “ prostitute , na dad’e da fahimtar cewa ke karuwa ce daman tun tuni , kinzo kin fake sabida my man? You as a prostitute ? Matar da tayi karuwanci a Garinsu, “ sai kuma cikin d’aga murya ta nuna musu Abla “ wannan da kuke gani prostitution take yi , har aka siyar da ita tazo ‘kasar nan , duk Wanda ya ra’be tama zai ta koya masa ne “ cikin kuka Abla ta bangaje ta ta gudu, suma Eshaal da fanan bags dinta suka d’aukar mata sukayi saurin bin bayanta suma ko wanne da kwalla a idanunsu dan sun san sharri ake mata musamman jabcon da Eshaal ta lura dashi yana yawan kallan kirjin Abla.

Abla kuwa da iya ‘karfin ta take gudu gabaki d’aya bata san Inda zata take saka ‘kafar taba , kuka Kawai take ido arufe , saura kad’an su Little su kad’eta. Ganin gadda take kuka hankali a tashe ne ya d’aga masa hankali gashi ta ‘kiyi wa kowa magana , mota kawai ta shiga ta sunkuyar da kanta tana ‘kara fashewa da kuka , shima Little kamar zai yi kuka ya tanbayesu abunda ya faru , babu abunda suka ‘boye masa , gabaki d’aya sai da suka zayyane masa komai , wani irin kwallan ‘bakin cikine suka tarar wa Little a ido da ‘karfi ya furta “My sister ?” Har yana tsoratar dasu fanan, Rai a ‘bace bai kuma cewa su Eshaal komai ya kar’bi jakarta, shi kad’ai sai faman girgiza kansa yake , a mota babu yadda beyi da Abla tayi shiru ba amma kamar ‘kara tun zura ta yake dan jikinta har ya d’au ki wani irin zafi Sabida kukan da tasha, hankali a tashe Little yake kallan ta ganin yanayin da be ta’ba ganin Abla a ciki ba , tun kafun ya ‘karasa gida ya kira Yaya Bobo ya fashe masa da kuka , tun kafin Bobo ya tanbayesa kuma ya kashe kiransa , lokacin fita Bobo zai yi har ya shiga mota ya fita ya koma cikin gida hankali a tashe .

Big Boss na tsaye shima yana shirin fita motocin su Abla suka shigo cikin gidan , babu Wanda ta kalla ta ruga cikin gida a guje tana kuka shima Little cikin Tashin hankali ya bi bayanta.

Abla ta shiga cikin gida babu Wanda ta kalla , tunda ta saka gudu sai saurin kukan ta da suke ji, tana shiga cikin d’aki toilet ta kulle ‘kofar tare da sakar wa Kant ruwa me sanyi, ita kadai sai kuka take kamar ‘kirjinta zai fito , idanuwanta har sun kunbura , ga mugun ja da face d’inta tayi.

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y


IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee ✨


🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅


AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__


✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

NOT EDITED

S____34💞

“Me ya faru ? “Cewar Bobo ganin yadda hankalin Little ya tashi lokacin da ya shigo cikin falourn , ga Abla da itama ta wuce ta na kuka , kasa magana Little yayi sai kansa da yake girgiza musu , cikin Sauri ya bi bayan Abla , shima prince da uncle bin bayan sa sukai dan ga baki d’aya little ya tayar musu da hankali, fahimtar kamar da matsala yasa Bobo bin bayansu banda Big Boss da tun bayan kallo d’aya da yayiwa Little be ‘kara kallansa ba, har yanzu yana tsaye a inda yake sai ma folding hannunsa da yayi waje d’aya , face d’insa kamar kullum babu fara’a kwata kwata a kanta.
Little be zame ko ina ba sai d’akin Abla , cikin Sauri ya shiga Bedroom d’inta ganin ‘kofar d’akin abud’e amma gabaki d’aya bata cikin d’akin , ‘karar ruwa da yaji a toilet da kukan ta ne yasa yayi saurin nufar ‘kofar kamar zaiyi kuka yasan har yanzu kuka take, knocking d’in ’kofar ya somayi da d’an ’karfi “ Lil ! Lil ! Please open the door let’s talk , please ki kwantar da hankalin ki , komai zai dai dai ta“, shurun da yaji babu amsa ne yasa hankalinsa ‘kara tashi Daidai lokacin da su Bobo suka shigo cikin d’akin suma “ Please sister na ro’ke ki , ki bud’e ’kofa zaki iya raunata kanki “ ya kasa maganar sa shima yana hawaye dan har cikin zuciyarsa yake jin wani irin d’aci da ba’kin cikin abunda akai wa Lil d’insa , kallan sa Bobo yayi cikin d’an d’aga murya ya furta “ I’m asking you kamun bayani , me ya faru ? Wani ne ya ‘bata mata rai ?” Kansa little ya girgiza masa hawayen face d’insa basu dena sakkowa ba , hankali a tashe prince ya furta “ Dan Allah little ka fad’a mana ka ta yar mana da hankali , and kaga may be tana using bathroom ne ma ba wani abun bane “ kuka little ya fashe musu dashi yana nunawa Bobo ‘kofar toilet d’in” No yaya zan muku bayani daga baya , just please yaya ku bud’e ’kofar nan , zata iya jiwa kanta rauni , d’an Allah yaya “ ya ‘karasa yana ‘kara sakin wani kukan dai dai lokacin da suka ji kamar fad’uwar abu a cikin toilet d’in, lokaci d’aya suka soma bugun toilet din suna kiran sunan ta “ Sister ? Sister ? Sister ?” amma babu amsa, Shirun da suka jine ya Matu’kar tayar musu da hankali , da iya ‘karfinsa Bobo ya saka ya daki ‘kofar da kafad’unsa , amma kamar Wanda ya daki kataho ko motsi batayi ba, a karo na biyu ya ‘kara da kar ‘kofar da ta d’an motsa kad’an , kafad’unsa ya ta’ba tare da kallan Little da face d’insa tayi ja sosai , cikin ‘yar damuwa Bobo ya furta “ called your brother “ da sauri Little ya nufi down stairs har lokacin Big Boss na tsaye Inda suka barsa , Little yana ganinsa yaji wani saban kukan na zuwar masa da Sauri yayi hugging d’in Big Boss yana yin kukan sa ‘kasa ‘kasa , lumshe eyes d’insa Big Boss yayi Sabida yadda yaji zuciyar Little ya bugu da Sauri kamar ba zai yi magana ba sai kuma cikin ya mutsa face ya furta “ what happen?”
A hankali Little ya sauke ajiyar zuciya , yasani ko be fad’a wa kowa ba dole zai fada wa Big Boss , shiyasa cikin sanyin jiki ya labartawa Big Boss abunda ya faru , tun lokacin da ya ganta tana kuka da bayanin da su Eshaal sukai masa , shiru Big Boss yayi batare da ya tanka ba sai ma d’an ta’be bakinsa da yayi kad’an , kamar wanda aka saka dole ya furta “ wannan ya saka kuka ?” Kansa Little ya jinjina masa wasu hawayen na ‘kara taruwa cikin eyes dinsa , Ya bud’e baki zai yi magana sai ya tuno da abunda ya sakko dashi ‘kasa , cikin kwantar da murya Little ya furta “ yaya please ‘kofar toilet d’inta aruf…e ta..ke” kallan da Big Boss yayi masa ne ya sa ragowar maganar sa ta rarrabe , cikin rashin damuwa Big Boss ya furta “ And ?” Hawayen sa Little ya share ,” Yaya Dan Allah ba danni ba , ka bud’e ’kofar toilet d’inta , zata iya jiwa kanta rauni” kallan diamond watched dinsa Big Boss yayi kafun ya d’an ya mutsa face d’insa kad’an “ am going out “, shine kad’ai abunda Big Boss ya iya furtawa , cikin Sauri Little ya haura sama yana goge kwalla har ya wuce d’akin Abla, yana shiga yatarar da har lokacin Bobo na du’kar ’kofar amma ta ki bud’uwa , almost 2 minutes gabaki d’ayansu suka juyo saitin bakin ‘kofa sabida ‘kamshin turaran Wanda basu ta’ba Saran zai shigo d’in ba, Little har da murnarsa ganin Big Boss a bakin ‘kofar Abla amma duk Wanda yaga face d’insa zai ganta a had’e sama da sauran lokuta, babu Wanda ya kalla a cikin su har ya ‘karaso cikin d’akin, gabaki d’aya matsa masa hanya sukai har ya ‘karaso wajan ‘kofar, da iya ‘karfin da Allah yayi musu shida Bobo suka daki ‘kofar da ‘karfin gaske , amma Sabida ‘koface bata wasa ba yasa ta motsa Batare da ta bud’u ba , a karo na biyu suka kara dakar ‘kofar wannan karan sai data d’anyi ’Kara , a karo na uku da Big Boss yayi mata wani irin Wawan bugu ‘kofar ta jijjige gabaki d’ayan ta , rai a ‘bace Big Boss ya hankad’a ‘kofar ciki da har saida Bobo yayi saurin dafe ta , daga inda yake yana iya hango ta cikin jacuzzi, da alama ruwa ta sakar wa kanta , gabaki d’aya bata motsi gashi Jacuzzin ya cika taf da ruwa har yana zuba ga abun side d’in jacuzzin da ya faffashe a ‘kasa , ransa ba ‘karamun ‘baci yayi ba Sabida ‘bata lokacin sa da yayi, d’an ’karamun tsaki ya saki kad’an lokacin da yake ‘karasowa cikin toilet d’in , da hannu d’aya ya d’ago da ita cikin ruwan , Sabida yadda jikin ta ya saki gabaki d’aya baya tayi zata fad’i yayi saurin taro ta da d’ayan hannun nasa , d’aya daga cikin ‘bathrobe d’in cikin toilet d’in ya na d’a mata tare da d’aukar ta gabaki d’aya kamar wata Baby, babu Wanda ya kalla a cikin har ya kwantar da ita kan gadon d’akin, cikin Sauri Little ya ‘karaso wajan gadon ganin Lil d’insa bata motsi, kamar me rad’a ya furta sunan wata allura , Bobo dake bayansu jinjina masa kai kawai yayi ya juya , shima prince da uncle juyawa sukai suka bar d’akin, yayi saura Big Boss da ke tsaye lumshe da idanuwansa sai kuma Little da ya ‘kurawa Abla idanuwa shima kamar zaiyi kuka Sabida yadda eyes d’insa suka fara red . Cikin ‘kan’kanin lokaci Bobo ya dawo d’auke da wani ‘karamun kit ya mi’kawa Big Boss tare da allura da ya fad’a , shima little yana ganin allurar ya fara kulle eyes dinsa dan harga Allah baya san abunda zai ‘kara ta’bata , ganin yadda yake faman kawar da kaine yasaka Bobo kama hannunsa suka bar d’akın. Kusan 2 minutes yana tsaye a wajan be motsa daga inda yake ba , a hankali ya d’auko allurar tare da had’a ta yadda yake so , hannu d’aya ya kai Daidai saitin hancinta, yadda yaji nunfashinta baya fitowa ne yasa ya d’an matsa cikin ta kad’an batare da ya kalle taba , lokaci d’aya Abla ta fara fito da ruwa daga bakin ta tana tari , tun tanayi da ‘karfi ‘karfi har ta fara ajiyar zuciya kafun ta ‘kara fashewa da kuka tuno abunda ya faru, ko uffan be ce mata ba ya d’auko allurar zai mata , sai alokacin Abla ta farga, yadda ta gansa ne ya ‘kara firgita ta ga hawaye sun ‘bata mata face d’inta sosai , cikin muryar kuka ta furta “ Ni banaso Dan Allah kar kayi mun allura “ ta ‘karasa fad’a tana yarfa hannayen ta , be bi ta kanta ba ya ‘kara d’aga allurar zai yi mata ta ‘kara fashe masa da kuka , a wannan karan sosai ransa ya ‘baci, yadda take kukan ne ya ‘kara harzu’kashi, cikin tsananin ‘bacin rai ya daka mata tsawa , ita kanta bata san lokacin da ta had’iye kukan da take ba , sai idanuwa da take zazzaro wa , har ya gama allurar bata sani ba sai da ya zuba mata rikitattun idanuwansa masu ladaftar da mutane , cikin kausash shiyar murya ya furta “ Just 10 minutes na baki ki sakko , idan kin isa ki ‘kara even a minutes “. Yana Kai ‘karshen zancan sa ya bar d’akın. Da kallo Abla ta bishi har ya fice daga cikin d’akin ga hawayen ta har lokacin ya ‘ki tsayuwa , ganin time d’in da ya bata ya fara yasa cikin sanyin jiki ta koma ta watsa ruwa tare da saka wata doguwar riga me kauri Sabida sanyin da take ji a cikinta .

A hankali Abla take sakkowa daga kan stairs din cikin sauri tun kafun ta ‘karaso little ya nufi inda take ,” Lil are you okay ?” Ko magana ta kasa sai kanta da ta jijjiga masa alamar eh , hannunta ya kama suka ‘karaso cikin falourn, suma gabaki d’aya su Bobo ita suke kallo banda Big Boss da gabaki d’aya baya cikin falourn , cikin d’an fad’a fad’a Bobo ya furta “Karka bari na ‘kara tanbayar ka , Little me akai mata ? “Kallan Abla Little yayi ganin lokaci d’aya ta soma hawaye ga kanta data sun kuyar ‘kasa , a hankali little ya bud’e bakinsa tare da labarta musu gabaki d’aya abunda ya faru, wani irin shegen murmushi Bobo ya saki kafun ya furta “ Woow!, wannan ne dalilin da yasa kika tayar da hankalin ki ?” Cewar Bobo yana kallan Abla , shima face d’insa d’auke da tsantsan ‘bacin rai , sai kuma cikin cool voice ya furta “it’s okay , kukan ya isa haka ! Wannan ba babban dalilin da zaisa ki kulle kanki a toilet ba , kinsan da kin ‘kara wasu minutes din shikenan sai dai wani labarin ake ?” Ya fad’a mata cikin d’an ’bacin rai , da Sauri Abla ta girgiza masa kai , a hankali ta furta “ Kuyi hakuri “, shiru kawai Bobo yayi mata, shi kansa uncle mamakin Wanda yayi wannan aikan, banda prince da wata shegiyar dariyar mugunta da ta so kamasa dan yadda yaga mood d’in Yaya Bobo yasan ba ‘karamun cin ‘kaniyar ko wana d’an iska zai yi ba .
A hankali yake takowa zuwa cikin falourn , gabaki d’aya ya canza shigar d’azu da alama wani saban wankan ya sake , daddad’an ‘kamshin turaransa da suka ji ne ya ankarar dasu fitowar sa , face d’insa gabaki d’aya a had’e take har ya ‘karaso cikin falourn, Daidai kan one sitter ya zauna tare da crossing leg d’insa , ‘kara sunkuyar da kanta ‘kasa Abla tayi , kamar bazai yi magana ba sai kuma ya furta “what happen? “ Little ya bud’e baki zai bashi amsa shima ya samu kasan nashi kallan, kamar zata yi kuka ta labarta musu gabaki d’aya abunda ya faru, d’an ta’be bakinsa Big Boss yayi kad’an kafun ya furta “ wannan abun ne yasa kika sa muka ‘balla ‘kofa ?”ya mutsa fuska Abla tayi zata sake wani kukan ya d’an daka mata tsawa , a hankali Abla ta furta “ kayi hakuri”, wani ‘karamun locker Big Boss ya bud’e tare da ciro wasu gun a ciki guda uku yana sakawa kan center “ idan kina san ki mutu basai kin saka wa kanki ruwa ba , ga gun nan ko wanne akwai bullet a ciki, idan basuyi miki ba , zaki iya hawa last floor sai ki fad’o , it’s most be easier ki mutu”, da Sauri uncle da Bobo suka furta “ Please Big Boss ….” Yanzu ma lips dinsa ya d’an motsa kad’an batare da ya kallesu ba ya
End Ads