ya fito duk waje. Kamar zatayi kuka ta furta “ Mugu kawai me kamar da Elizabeth , mutum kullum cikin d’aure fuska dole ka dunga kula da zaki ai, Allah sarki jama’a bayın Allah , nasan banı kad’ai yake cin zaliba, kai sai kace Bishiyar giginya ”, yadda Abla ta dafe tana masifa wani sai ya d’auka Big Boss d’in ne a gabanta take surfa masa bala’I, babu abunda ya fad’o mata sai kararan da ta sakawa su Zinariyya, ji take da zata samu kararan nan da babu abunda zai hana ta fesa masa shima.
*****Gabaki d’aya wunin ranar a d’aki Abla tayi zamanta sabida haushin Big Boss da take ji , sai da ta tabbatar baya cikin gidan tukunna ta fito falour, har lokacin hancin da d’an jansa. Tana fitowa kuwa suka saka game abunsu, tun suna yi har suka gaji , prince yaja wayar sa , Little ma yaja tasa wayar banda Lil da ta koma kallo, d’an d’agowa Little yayi ganin Abla na kallo kafun ya mayar da kallansa kan Tv da take kalla , ganin ba wani abun ake ba sai labarai, tashi yayi ya bar falourn gabaki d’aya basu kula da mi’kewar saba , kai tsaye d’akın su ya nufa , cikin mintuna da basu fi 5 ba ya dawo d’auke da wani kwali a hannun sa , yana zuwa be ce mata komai ba sai ya d’ora mata kwalin akan cinyar , kallan kwalin tayi kafun ta kallesa alamar ‘karin bayani, ido d’aya Little ya kashe mata “ For you” da Sauri Abla ta zaro ido dukda bata gama tantance abunda yake cikin kwalin ban, tana shirin fara masa Godiya yayi saurin toshe kunnuwanta “ A beg karma ki fara , ni banaso “, murmushi Abla tayi masa fuskarta cike da annashuwa “ thank you so much Yaya Little “ d’an hararar ta little yayi kafin ya furta “ ban kar’ba ba , just open it my friend “ murmushi Abla ta ‘karayi tare da furta “ thank you “, ‘karamun box d’in ta kalla duk da bata gama Tantance abunda ta gani ba , a hankali ta bud’e kwalin cikin sauri ta zaro idanuwanta waje ganin iPhone 12 babba a ciki, har wani kwalla ne suke ‘ko’karin tarar mata cikin ido “ Yaya Little… “ cikin Sauri Little ya furta “ it’s okay bari na nuna miki yadda zakiyi anfani da ita, everything yana ciki nuna miki kawai zanyi akwai sim akwai card and data every is intact “, ita dai Abla sai faman murmushi take gabaki d’aya tarasa abunda cewa gashi ya d’aure mata face a dole baya bu’katar Godiyar ta . Cikin ‘kan’kanin lokaci Little ya nuna mata yadda zatayi anfani da wayar , komai sai da ya nuna mata , Abla babu abunda take sai murmushi hatta phone number d’insa sai da ya saka mata da ta su Prince , gabaki d’aya Numbers d’insu sai ya saka har da ta Big Boss da iya familyn ne zasu sameshi duk lokacin da suka kira sa , har wajan la’asar tana suna zaune a falourn tunda babu Wanda zatayi hira dasu a wayar , ana kiran sallar la’asar ta koma d’aki , sai da tayi sallah tayi komai tukunna ta d’auki wayar da little ya bata , Duk abunda ya koya mata sai data ‘kara shiga ta gani gabaki d’aya , last wajan numbers tashiga , lokaci d’aya taga numbers d’insu gabaki d’aya , hararar ta Big Boss tayi kamar idanuwanta zasu fad’o , har zata goge number sai ta fasa ganin Little yayi mata saving da Yaya Big Boss , sai tayi sauri ta goge sunan ta saka masa HORROR tare da hotan d’an Aljani agefe. Camera Abla ta shiga ganin yadda face d’inta ta fito sosai , guda d’aya tayi snapping tana gwalo , tana ganin yadda hotan yayi ta ‘kyalkyale da dariya har tana kulle face d’inta , ita kad’ai sai dariya take abunta har da fad’awa kan gado.
************
********
GREENWICH VILLAGE
( Honeymoon lover’s😹🤣)
Wasu irin tsofaffin gida je ne aje aje cikin ‘kauyen Greenwich, amma ko wana layi zaka ga tsaf tsaf babu wani hayani ko surutun mutane a Wajan . A bakin wani gini motocin su Robert suka tsaya, tundaga subun ginin mutum zai san ba ‘karamun dad’ewa gidan yayi ba , tun kafun a ce su fito Alice ta soma zazzaro idanuwanta , tun shigowar su Garin take tottoshe hancin, tundaga sama har ‘kasa take bin ginin da kallo da ko gate babu a jikinsa sai ‘kofa , LG kuwa kukan takaici kawai take ganin irin Wajan da aka kawo su , ko ina ka wai ga zaka tarar da tsofaffin gida je gabaki d’ayansu kusan yanayin su d’aya gashi ko wana idan ka duba babu gate a ciki, daga can d’an nesa dasu wasu tsofaffun turawa ne suke kallan , musamman lokacin da sukaga su Alice na kuka sai suma su bud’e bakinsu da ko hakwara babu suna kwaikwayon su Alice , da su Alice sun kallesu zasu yi Sauri su koma , suna juyawa tsofaffun nan zasu ‘kara fitowa gabaki d’aya gashin kansu fari ga fuskarsu d’aya gama ya mutsewa alamar tsufa .
Fito da su jabcon da suka gama jigatuwa akai dan kafun su fito ma sai da Robert ya ‘kara musu shegen duka . Wata mata ce ta fito daga cikin gidan hannun ta d’auke da sanda tana dogarawa, itama gabaki d’aya tsufa ya gama bayyana a jikinta ga gashin ta da yake fari tas dashi, kallan ta su Alice sukai ganin yadda take dogara sannan, itama matar kallan su tayi d’aya bayan d’aya kafun ta kalli Robert “ wad’annan ne ‘yan iskan yara ?” Ta fad’a cikin turanci , cikin girmamawa Robert ya furta “ Yes Mah” kanta ta jinjina masa tana ‘kara bun su Alice da kallo da lokaci d’aya gabaki d’aya sukaji shakkar matar ya shigesu, a tsawa ce ta furta “ ku biyo ni, ‘yan iskan yara “ cikin Sauri gabaki d’aya suka biyo bayanta har da su Ossy da duk lokacin da LG ta waiwayo yake ‘boye kansa sabida be manta da irin dukan da tayi masa ba . Suna shiga suka soma bin falourn da kallo gabaki d’a wasu tsofaffun kayane a ciki, ga uban abubuwan da aka zubar da ya ‘bata gabaki d’aya falourn , hatta jikin bango sai da aka ‘ba’b’bata , lokaci d’aya Alice ta soma amai Sabida yadda ta ga gidan, sandar ta matar nan ta d’aga ta kwala mata tare da jefo mata wani ‘kyalle ta goge , kuka Alice ta saka tun da take bata ta’ba d’aukan ko jaka ba sai dai a mi’ko mata , yau gashi zata goge aman da tayi Wanda bata ta’ba , zata yi complain matar ta ‘kara buga mata sanda tare da zazzare mata mitsi mitsin idanuwanta , cike da tsoro Alice ta d’auki ‘kyanlan shima tana yatsuna face , jinjina kai kawai matar tayi ganin abunda Alice take , kallan su Robert tayi kafun ta furta “ Babu matsala zaku iya tafiya “ okay mah “ cewar Robert kafun su bar cikin gidan , tsayawa kallan yadda gidan yayi kaca kaca sukai cikin daka tsawa MADAM GLO ta sa su kalleta , suna kallanta ta soma tattakawa tana kallansu d’aya bayan d’aya kafun ta dam’ki kan Alice da ta soma ihu kamar wata mahaukaciya haka MADAM GLO ta dunga jijjiga mata kai , a tsorace LG ta soma ja baya ganin yadda Itama GLO ta soma kallanta , ware ‘kafafuwanta madam glo tayi ta biyo LG a guje , itama LG tana ganin haka ta saka ihu ta arta a guje, yadda GLO take gudu kamar wata a gwagwa shine ya ‘kara tsorata LG suna su Alice Suka soma ihu, a hankali kuma ta juyo da kallanta zuwa su Jabcon da suma suka fara ra’bewa a jikin bango, gadan gadan ta biyo su da sanda suma suka dunga ihu , gabaki d’aya sai MADAM GLO ta hauka tasu suka fara guje guje da ihu su had’ai , sai da ta tabbatar tsoran ta ya shiga zukatansu tukunna ta dakata , a bun mamaki Aushe lokacin da Madam Glo take rikitasu Ozzy d’anewa hannun LG yayi, idan ka kallesu sai ka d’auka Wanda ya d’auki yaro tana Ankara da abunda tayi ta nakasa a ‘kasa kuwa , itama Alice ganin ta d’ane a cinyar Jabcon ta wanke face d’insa da mari. Cikin had’e rai MADAM GLO ta tuna musu kayan gyaran gidan , “ hour d’aya na baku ku gama gabaki d’aya aikin da zan saku idan ba ranku ya ‘baci “ cikin Sauri Suka d’auki kayan suka soma gyara falourn , sai haki suke gwanda jabcon da ossy da suke aikin amma Alice da LG babu abunda sukayi gabaki d’aya sun jigata , suna gamawa madam glo ta sakasu gyara wasu d’akuna guda uku, kowanne da tsohon gado a jikinsa , ga kuma ban d’akin guda biyu d’aya a cikin d’akı sai d’ayan a tsakan kanin d’a kuna guda biyu, suna gamawa madam glo ta basu flowers akan su watsa akan gadon , hakan kuwa sukai d’aki d’aya ne kawai basu sawa flower ba , wasu mattun kaya takawo musu akan su canza kaya , cikin su babu Wanda yayi Tuna’nın shiga toilet musamman LG da Alice da suke ‘kan’kamunsu, suna gamawa ta kawo musu wani irin taliya me shegen ruwa gabaki d’aya kasa ci sukai sai kallanta da suke, banza Madam Glo tayi musu tayi wucewarta.
********9:30pm gabaki d’aya ta kora su d’aya , Alice da Jabcon, itama LG da Ozzy , gabaki d’aya ta saka su hawa kan gadon da suka watsa wa flower , saida zata fita tace musu kusha soyayya lapiya, tana fita LG ta kalli Ozzy cikin Sauri Ozzy ya sauka daga kan gadon ya koma gefe a ‘kasa , a d’akin su Alice ma , cikin Sauri Jabcon ya saukar mata daga kan gadon sabida irin kallan da ta jefa masa , gabaki d’ayan su kallo kallo suke jefa wa juna musamman su Alice da suke ji kamar suje su sha’kesu su mutu, suna zaune ko wannensu yana jefa wa d’an uwan sa mugun kallo suka ji gabaki d’aya wutar gidan ta d’auke , cikin sauri Alice da Jabcon suka rungume juna dama duk matsorata ne , basu san ya akai ba sai ganin ‘karamun haske kawai sukai da ya ‘kara har gitsasu suka kuma kurma ihu, a hankali ta d’ago da fuskarta da gabaki d’aya wasu abubuwane a fuskar ga farin gashin ta a hargitse, gabaki d’aya sai tazama hoto musamman yadda take wangale hakwaranta , su Alice babu abunda suke sai ihu, bakinta ta turo musu alamar kiss , cikin wani irin murya ta furta “ Kiss! kiss “ a hargitse su Alice suke kallanta ga wani irin gumi da suke yi cike da tsoro, ihu ta saka suma su Alice suka saka ihu, gashin Alice ta janyo ta tsinka mata mari kafin ta janyo kan Jabcon shima , hakan be ishetaba dan dole ta dunga had’e musu fuska a dole sai sunyi kiss , gabaki d’aya ta haukata su Alice ,ita kad’ai sai faman firgitasu take.
A d’akin su LG ba lokacin da aka d’auke huta cikin Sauri ta nufi ‘kofa da niyar guduwa suka ga an bankad’o musu ‘kofa , tsofaffin d’azu ne suka shigo cikin d’akin gabaki d’aya sun canza kamannin su sai suka koma kamar wasu ‘kananan aljanu, da sun kalli su LG zasu ‘kyal’kyalle musu da dariya , suma kamar abunda Madam Glo tayi suna haka sukai musu , su da suka fi kowa har kan gado suka sasu kwanta suna watsa musu flower , Sabida tsabar firgita LG bata san lokacin da fitsari ya ‘kwace mata ba , gabaki d’aya cikin daran nan madam glo da tsofaffin nan suna hana su Alice sakat sai da suka tabbatar sun wajigasu, a dole sai da suka su rungume juna , idan kunga yadda Alice take toshe hancin ta sai ta Baku dariya musamman yadda Jabcon yake nunfashi gabaki d’aya hudodin hancinsa a fuskarta.
https://chat.whatsapp.com/EgRmBePVeNnLUQh1Rrzm1F
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨
🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅
AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__
✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨
💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus
🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.
NOT EDITED
S____38💞
***NYC****
Gudu take sosai cikin kurmun daji da babu ko d’igon haske banda ba’ki’kin da wajan yayi, daga gefe wasu irin kukane yake tashi ta ko ina a cikin dajin me tsoratar wa , yadda take jin kuka na nufo ne yasa ta ‘kara ‘karfin gudun nata , tana gudu tana jin sunanta da ake ta faman kira , data wai ga sai taga rami kamar za’a ja wota, daidai zata wuce ta wata ‘kofa taji wasu murya na kiran sunanta suna mi’ko mata hannu wansu, lokaci d’aya Abla ta tsaya tare da waiwayo wa , gabaki d’aya bata ganin fuskokin mutanan sai da muryarsu da take ji, cikin sauri ta nufi inda take jin muryoyin su , “ ki temaka mana , ki temaka mana “ shine abunda mutanan suke cewa , saurin ta Abla ta ‘kara daniyar zuwa wajan su, ko step uku batayi ba taga kamar muryar mutanan da take ji yayi ‘kasa alamar sun fad’a rami amma duk da hakan bakin su be dena ambatan “ ki temaka mana ba “****
A firgice Abla ta farka daga bacci da ya d’auketa , gabaki d’aya gumi ya ji’kata kamar babu sanyin Ac a d’akin , runtse idanuwanta Abla tayi tana karanto duk adduar da ta zo bakinta , jikinta har yanzu be dena rawa ba , shiyasa tayi saurin janyo wayarta ta kunna ‘kirar sudais tana ‘kara lumshe idanuwanta,ta jima tana sauraran karatun Al-qur’anin kafun ta soma a jiyar zuciya sabida sau’kin da ta samu cikin zuciyarta . A hankali ta ‘kara matso da wayar daidai saitin ta, tana ‘kara karanta addua cikin zuciyarta , kafun ta samu kwanta har lokacin karatun da take ji bata kashe ba.
THE NEXT DAY
ko da safe haka Abla ta tashi a sukuku, gabaki d’aya mafarkin da tayi jiya ya tsaya mata arai , da ta kulle idanuwanta sai taji kamar suna ambatan sunanta . Kawar da tunanin tayi a gefe lokacin da Little yake sakkowa , “ Lil yau kin tashi da wuri fa “ d’an ‘karamun murmushi tayi sabida gabaki d’aya yadda take jin kanta not in the mood “ Yaya Little ina kwana?”, sosai ya kalleta ganin tayi magana in a cool way , “ Lil lapiyan ki ‘kalau kuwa ? Ko baki da lapiya ?” ‘Dan zaro masa ido tayi da mamaki “ No! Lapiya ta ‘kalau fa “ har yanzu be d’auke idanuwan sa a kanta ba ya furta “ Are you sure?”! da sauri Abla ta furta “ yes”, knodding kansa yayi alamar gamsuwa kafun ya furta “ in a few minutes su Yaya zasu fito , sai muci breakfast d’in mu all a tare , ko ?” A wannan karan itama Abla knodding kanta tayi batare da tace komai ba , haka kawai take jinta wani irin kamar ba ita ba .
9:30am gabaki d’aya suka fito banda Big Boss , a maimakon su jira sai suka nufi dinning abun su , tunda sun san ba yanxune zai fito ba , har aka gama breakfast d’in Abla bata ci wani abinci dayawa ba , ganin idanuwansu ne yasaka take tuttura abincin gudun kar suyi mata magana. A na gamawa ta mi’ke zata tafi Bobo ya dakatar da ita “ Lil can you make a cup of coffee ?” A hankali Abla ta furta “ yes !” Tana nufar inda coffee maker yake , komai cikin sanyi take yin sa yau, tana gama had’a coffee d’in ta d’akko masa , girgiza mata kai yayi tare da nuna Mata upstairs da hannunsa guda d’aya “ Not for me ! Ki Kai masa sama “ ta gane abunda yake nufi, “ Toh Abla Kawai tace masa ta nufi hanyar part d’insa . Tana hawa kai tsaye falournsa na biyu ta shiga tunda tasan bazata tarar dashi a cikin falourn farko ba , ana biyun ma sai taci rashin sa’a baya falourn , kamar zata ajje masa coffee d’in ta wuce sai taga rashin dacewar hakan , ‘kofar bedroom d’in sa tayi knocking sau d’aya, shurun da taji anyi mata yasa ta ‘kara knocking a karo na biyu , still ba’a amsa mata ba , zata juya taji kamar an bud’e