x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - IBTISSAM BOOK 1

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 200864 words

Category: Romance Story +18

Views 270

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
matane sanye da ba’ka’ken kaya , wasu suna mata tausa cike da taka tsantsan , wata kuma tana d’aukan slice d’in fruit tana saka mata a baki, jikinta sanye yake cikin bom short, rigar jikinta ma kamar singlet haka take yar figil ko cibiyarta be rufe mata ba , ga gashin kanta da ya sha gyara dukda a gida take hakan be hana fuskarta daukan makeup ba, ta d’an muskuta zamanta lokacin da d’aya daga cikin masu aikin ta kai mata slice banana bakinta , sai ya d’an goci gefen bakinta, cikin ‘bacin rai Alice ta mi’ke tsaye , yar aikin baturiyarda zatayi 50 years ta d’aga hannu ta wanka wa mari , da yaransu na turanci ta soma magana “ dan ubanki haka akace miki akeyi, me yasa ku talakawa baku da hankali ne ? You’re very stupid , kije an koreki “, hakuri dattijuwar matar ta soma bata hakan ya ‘kara tunzura Alice ta ‘kara wanka mata mari, gabaki d’aya ragowar yan aikin saida suka shiga taitayinsu , sunsan Alice ba kirkine da ita ba yanxu zata sa akoreka sannan a ci maka mutunci musamman yadda her excellency take mugun ji da ita , ita da mijinta Sabida itace kwallin kwal din yarsu dasuke da ita. Cike da wulakanci ta bada uwarnin afitar da yar aikin , haka suka d’auketa kuwa duk da shekarunta sukai waje da ita , zata koma kan ragowar yar aikin wayarta tasoma ringing, murmushi ta saki da Sauri ta d’aga wayar tana furta “ ki shirya bayan mun dawo daga Club zan yi siyayya sabida my man, I need anything unique , All my clothes basuyi mun , “ bansan me aka ce mata ba sai murmushi da tayi kit ta kashe wayar, yan aikin da suke binta a baya ta mika wa wayar cike da yanga kafun su bud’e mata d’akin clothes dinta da yake shake da kayan sawa , cikin tatta’be fuska ta soma bin kayan da kallo, duk wacce ta ciro intaga batayi mata ba sai ta yar dar a kasa yan aikin kuma suna kwashewa , haka ta dunga zazzaro kaya tana Wulli dasu hatta pant da bra haka ta dunga zazza’kulosu tana yar darwa , shoes da bag gabaki d’aya sai data rikito dasu , tana zuwa gaban mudubinta dake shake da kaya haka ta dunga wurgi dasu batare da tayi anfani da abu d’aya dake cikin kayan d’akin ba , gabaki d’aya saidata burki ta ko ina yayi kaca kaca sabida ta wahalar dasu sannan tayi ficewarta , kuma dole su gyara mata shi tsaf kamar yadda yake idan ba Haka ba gabaki d’aya sun gama aiki kenan.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
KANO
NASARAWA G.R.A
kid’an da yake tashi da sanyin safiyane ya farkar da Eshaal daga baccin data koma tun bayan sallar asuba da tayi ,dogon tsaki taja sabida tasan babu d’an iskan da zaiyi wannan abun sai baby , d’ayan pillow dinta ta d’auka ta toshe kunnuwanta ko zata denaji kid’an amma duk a bazan , wani tsakin ta kuma saki cike da haushin baby data hanata bacci , a hankali ta zuro da santala santalan fararan kafafuwanta da suke sanye cikin kayan baccinta pink colour , dogon gashinta ya soma sukurkucewa Sabida baccin da tayi, half slipper dinta ta saka ta Fito daga cikin bedroom dinta , ita kadai sai faman sakin tsaki take, tana shiga d’akin baby taga fitilar d’akin a kashe sea light masu kaloli data bari a kunne , ita kanta Eshaal bata san Baby na d’akin ba taje ta Kashe kid’an . Tun shigowarta Baby ta ganta tayi mata shiru ne Sabida tana so ta d’anyi wani mistake d’in da zata saka dad momy hukunta ta. Plan d’inta kuwa yayi aiki sabida kashe mata kid’a da Eshaal tayi a harzu’ke baby ta furta “ uban wa yace ki shigomun d’aki da har zaki kashe mun kid’a ko kina ba’kincikin ke baki dashi”, kallan sama da kasa Eshaal ta bita dashi “ sai akace miki sabida kina da wad’annan banzayan abubuwan zai dameni? Ke kika damu dasu da har kike tunanin kunnasu, dama karatun alkuran kika sa da an fafata a ga me ilimi.baby taji haushin kalaman Eshaal Sabida tasan magana Eshaal ta fad’a mata , “Mtsww bani da lokacinki, ki koma ki kunna mun kid’ana tunda ba uwarkice ta siya mun ba” cewar baby, a tsawa ce Eshaal ta kalleta” na fad’a miki duk lokacin da kika kwaso shararki ki dena sako mun mahaifiyata, ko me zakiyi ya tsaya a iya kaina , amma bakyaji ke kullum abun tashin hankali kika iya ?” A gadarance baby ta furta “ An fad’a, idan kinyi zuciya ki tattara ki barmun gida , ko kuma yan uwan matacciyar uwarki su d’aukeki, ko da yake ina ma Suka damu dake ? Daka ke har uwar taki data she’ka”, da karfi Eshaal ta buge mata baki, zafin da tajine yasa ta sha’ko wuyan Eshaal, itama da maganganun Baby suka ‘bata mata rai ta sha’ko Baby take a Wajan Suka soma danbe daman ba wani karfi ne da baby ba sai cika kurin bala’i, da iya karfinta Eshaal ta zage ta dunga luftar Baby, ita kuwa Baby sai faman ihu take wai Eshaal zata kashe ta , a guje momy da Amma suka shigo d’akin, cikin fusata momy ta cafko gashin Eshaal da karfi ta bugata da bango, wata bakar waya da ta gani me kyau ta d’auka ta soma jubgar Eshaal dashi da iya karfin, Eshaal sai ihu take tana bata hakuri amma kamar ‘kara ingiza momy take , Amma sai faman bata hakuri take amma itama tsawan da Momy ta daka mata ne yasa ba yadda ta iya taja bakinta tayi shiru, momy kuwa sai da tayi wa Eshaal shegen duka , kafun ta kalli AMMA “ munafuka daman kece kike kitsa mata duk wani abu da zatayi, shine dan muna furta zaki biyo bayanta kiga meke faruwa , da izinin wa ma kika shigo cikin d’akin”, kiyi hakuri hajiya” sai alokacin Baby ta kalleta tare da jan wata ashariya “ kutumar uba! Da izinin wa kika shigo mun d’aki da wannan warin jikin naki har ki taka mun carfet? Baki da hankaline ? Ko cuta kikeso kisakamun?”, da Sauri AMMA taja baya tana furta “ kiyi hakuri” ta’be baki Baby Tayi” daman ku talakawan nan haka kuka iya , ayi hakuri a yi hakuri, kunsamu an d’auke ku aiki ma sai kunyiwa mutum shish shigi, tukunna ma wai kinyi wanka ? Naji d’akinta ya fara wari gaskiya “, Eshaal bataji dad’in maganganun Baby ba akan AMMA ko ba komai a haihuwa zata haifi kamarta ko wacce ta fita , yanxu tana bud’e bakinta kuma momy zata ‘kara dasa mata wani saban dukan ta Lura baby da gangan take yi Sabida tayi magana yadda momy zata kara dukanta , cike da dattako AMMA ta furta “ Eh nayi “, da Sauri baby ta dakatar da ita “ a hakan ne kikai wanka sai faman tsami kike ? Plx maza maza ki tattara kinfitar Munda ga d’aki dan harna fara jin amai na taso mun , ga wani bashi bashi da d’akina ya d’auka, yanxu ma “ kiyi hakuri “ Kawai Amma tace , momy kuwa tana tsaye tana kallan yadda Baby ke wula’kanta AMMA amma ko a jikinta sai dad’in Hakan da take ji ma , kallanta momy tayi up to down kafun ta nuna mata Eshaal da ke nishin wahala “ ki kwashe wannan kayan wankin ki fitar da ita daga nan d’akin ,da kalar kazamai tayi kama , sunnan plx ko me zaki taba kisaka leda haka sabida kamar yadda baby ta fad’a Nima na fara jin wari warin nan gaskiya “, gabaki d’aya AMMAHta tsargu shiyasa ta saukar da kanta ‘kasa ta kasa kallansu, “ ba magana ake miki ba , kutattara kubarmun d’aki”, rai a ‘bace Eshaal ta mike , har kunyar kallan AMMAH take sabida wulakanci da su momy sukai mata , bata damu da yadda Suka zuba mata idanuwa ba , ta kama hannun AMMAH suka bar d’akin, har cikin d’akinta ta kai AMMA, abun mamaki tsugunnawa Eshaal tayi tana bawa AMMAH hakuri Sabida irin wulakancin da Suka yi mata bakowane xai iya jurewa ba sai me ‘kololuwar hakuri , murmushi akan fuskar AMMAH kamar babu abunda ya faru ta dakatar da ita “ Haba mana Menene haka kike ‘ko’karinyi ni wallahi babu Wanda na rike cikin raina , karki damu kinji “, banji dadin abunda sukayi miki bane AMMA , nasan kawai kina ‘boyewa ne amma nasan baki ji dad’in Hakan ba “,yanxu ma wani murmushin Amma ta sakar mata tare da d’akko mata manzafi” ki shafa wannan kada kiyi ciwan jiki, ina da ayyuka “ ,toh Kawai Eshaal Tace mata , sai da tayi wanka da ruwan dumi sannan ta shafa man zafin, komai cikin Sauri take yinsa sabida bata san wani wulakanci baby zatayi wa AMMAH ba musamman taga tana had’a musu breakfast, shiyasa gabaki d’aya ta d’auki ragamar yin abincin gidan . Tana fita kitchen ta nufa ta soma kokarin d’aura breakfast, fish pepper soup ta had’a sai chips and plantain da ta had’a musu, ga hot tea da ya sha kayan kamshi, batasan almabuzzuranci shiyasa komai Daidai tayi , and Tasan bata isa taci komai data girka ba Indai ba baby ce tace ta koshi ba .

A wajan cin abinci ma babu irin tujara da Baby batayi ba , iya shegenta kawai take yi momy na biye mata , duk abunda sukai kuma daidai ne dan awajan breakfast dinnan sai da dad ya turawa baby 200k cikin account dinta amma ko gaisuwar Eshaal be amsa ba sai ma hade rai da yayi, baby kuwa dagangan ta’ki Tashi daga wajan dinning sai data tabbatar komaj yayi sanyi lokaci yaja sosai kafun ta tashi tabar Wajan, sai alokacin su Eshaal suka karya wajan around 12. Da rana ma haka tayi musu wannan iskancin bata bari sunci abinci ba sai wajan la’asar , already momy da dad kowa yafita sabgarsa.

9:00pm lokacin da Eshaal take ‘ko’karin kwanciya Baby ta tsuro da zancen wainar fulawa take sha’awa, haka eshaal ta hakura da kwanciyar da zatayi ta je kitchen ta fara kwaba kwainar fulawa , saida ta soya su duka ga bacci da take ji, tana kawo wa baby tace mata ta manta bata fad’a mata ba wainar ta fita ranta bata sha’awa . Eshaal jitayi kamar ta sha’ko wuyan baby ta tsuntsun ka mata mari Amma babu yadda ta iya musamman yadda taga momy na jifanta da kallan tsana . Gabaki d’aya wainar masu gadi ta bawa dan alokacin tasan AMMA tayi bacci, still bataje ta kwanta ba saida baby ta gama yin duk abunda zatayi kafin ta mike ta nufi d’akinta tana cewa Eshaal “ ki kashe TVn”. Kashewar kuwa tayi sabida babu yadda zatayi itama gashi baccin take ji, tana shiga d’aki Kayan bacci Kawai ta saka tayi alwala itama tabi lapiyar gado . (Asuba ta gari🚶🏻‍♀️).

🍃🍃🍃🍃🍃
GERMANY
FRANKFURT

1pm Fanan da mameey suna zaune a falo suna hira, rabi da kwata hankalin fanan yana kan game d’in da take yi cikin game d’in hannunta, kamshin turaran Emperial magesty da a wajan yayanta kawai take ji ta soma juyowa, yadda kamshin ke ‘karuwane yasa ta mayar da hankalinta kan hanyar shigowa. Shid’inne kuwa sanye da ‘kananan kayan kanfanin fendi red colour , sosai sukayi masa kyau musamman yadda suka haska chocolate colour skin d’insa , dogo ne sosai Amma ba irin over dinnan ba, kyakkyawane shi da ko wace mace idanta kansa zata ‘kyasa , duk da ba fari bane amma Allah yayi masa baiwar kyau , yana da medium size eyes farare tas dasu , sai dogon hancinsa da yayi wa fuskarsa kyau , siririn lips d’insa med’an duhu duhu sosai yayi wa cute face d’inshi kyau , sumar kansa da ta sha gyara sai faman kyalli take musamman yadda take a cike ba’ka’kirin da ita. Cike da zolaya fanan ta furta “ oh my god , yaya BiiBii kayi kyau wallahi yanda kasan American guy d’in nan , Anya bamu had’a Jini dasu ba kuwa ?”yana karasowa inda take ya dungure mata kai “ Allah Dagaske yayi Bibi gabaki d’aya kamannin sune dakai musamman gashin kanka , and bama kama da mameey gabaki d’aya ,and ni kuma ban ta’ba ganin Dad d’ina a zahiri sai a hoto, balantana na tantance “, ta karasa maganar tata a sanyaye tana cigaba da yin game d’inta “ hey chill up ! I’m around , bansan kalar face d’innan okay ?” Cewar BIBI, itama nodding kanta tayi “ don’t worry yaya bibi, I have you ai , Yaushe zaka bani labarin friends d’inka? “ Na fasa “ cewar BiiBii “ common plx yaya bibi inaso naji kana bani labarin nan naku, and har yanxu baka fad’a mun inda suke ba , the reason why kuka rabu dukan ku , baka fad’a mun ba “, yadda taga lokaci d’aya mood d’in sa ya canzane yasa tayi shiru , cikin sanyin murya ta furta “ am sorry yaya bibi , I don’t mean to hurt you “, bece mata komai ba ya mike tsaye “ mameey zanje wani waje ba dad’ewa zanyi ba , fanan see you later “, be jira amsarsu ba ya kama hanyar barin kallon, kunnanta mameey ta kama “ sau nawa zan fad’a miki ki dena yi masa magana akan friends dinsa haka ? Duk yadda naso ya manta abunda ya faru na Lura kece kike dawo da komai baya ko? Me yasa bakyaji”, kiyi hakuri Mameey , but ai yana farinciki everytime yana bani labari akansu “, ke dai kika sani cewar mamy, ki tashi ki barmun falo tunda baki isa a yi miki magana ba “, Haba mamey nace fa sorry , ringing din wayar ta kiran I phone 12 ta d’auka ganin besty ‘baro ‘baro a jiki “ Mamey besty ce take kirana , na tafi d’aki”, bata jira amsar mameey ba ta rufa a guje tana picking d’in call d’in. Girgiza kai Kawai mameey tayi , a fili ta furta “ Allah ya shiryeki fanan”.

🍂🍂🍂🍂
VENEZUELA 🇻🇪
ANGEL FALLS , VENEZUELA_!

Angel falls ,Wani babban dajine dake ‘kasar Venezuela da bakowa ne yake iya shigarsaba musamman yadda yake da mugun tsoratarwa, da yawa wad’anda suka shiga basa iya fito wa daga cike , sai manyar criminals da suka san hanyar su ta shiga . Venezuela tana d’aya daga cikin manyan kasar da tafi ko wace kasa a duniya criminals shiyasa da yawa wasu daga cikin mugaye suke zamansu a can kasar.
Angel falls babban dajine me shegen girma da mutum bazai ta’ba iya hasashen ‘karshen saba , musamman babban dutsen da ke cikin dajin me shegen girma , babu abunda yake tashi a cikin dajin sai kukan suntsu ko na wani dabbar, yawanci mugayen jamun daji a cikin dajin suke rayuwa , sannan duk mahalu’kin da yashigo baya fitowa da rai saidai ane mesa a rasa , ga shegen duhu da dajin yake dashi. Daga cancikin dajin Angel falls wani irin kunane ke tashi wajan ‘Karan dutsen da a ‘kalla girmansa zai iya had’a manyan manyan gidan antajiran billionaires sau goba , ga tsaho da yake dashi.
Wasu ‘katun ‘katun mutanene manya manyan gaske ga su jinga jinga, suka fara nufo babban dutsen ko wannansu jikinsa sanye da ba’kin kaya hatta fuskokinsu ba’a iya gani Sabida wani abun shan iska da sukasaka abakunansu, cylinder da suke zu’kar nunfashin na bayansu , duk inda zasu wuce wajan masu tsaran wajan tasu nuna musu wani tanbari dake hannunsu sannan su yanki hannun su Jini ya fita kafun su wuce , sun fi su su ashirin haka suka dunga wuce wasu zaratan mutane dukda girmansu amma mutanan sun fisu girma , kuskure kad’an suke jira su kasheka Sabida gabaki d’ayansu babu Imani a tattare da su, haka zaratan mazan nan suka dunga wuce abubu kala kala har suka zo ‘kofar shiga cikin dutsen , Anan ma wani abu ne me kamar na’ura jikinsa irin na gizo gizo , ko wannansu yazo wucewa wannan abun zai cake su a hannu, haka suka soma wuce wa d’aya bayan d’aya kuma haryanzu akwai abun shakar nunfashin nan akan fuskarsu, idan suka shiga wasu irin abubuwan had’a chemicals ne masu had’arin gaske , tundaga kan Acids, Thallium da sauran chemicals masu had’arin gaske , mutanene burjik a Wajan kowa ka ganin fuskarsa a had’e kowa da kalar abunda yake yi a Wajan , ga wasu poisons da suke had’a wa me bala’in had’arin gaske cikin su har da Hydrogen sulfide Wanda duk Wanda ya sha’kesa yake fad’awa coma ko kuma ya mutu take a Wajan. Ga ‘bangaran Arsine shima da duk Wanda ya sha’ki gas d’insa take a Wajan yake shigewa cikin jinin mutum.babban cikinsu kuwa petroleum distillates ne meshegen had’ari bayan coma da yake saka mutum har Lung cancer yake sawa mutum ko mutum yayi ta suma . Gabaki d’aya wajan chemicals ne ake had’awa masu had’arin gaske , zataran mazan nan wata kofa suka shiga , suna shiga suka ajje kayan da suka d’auko suka koma wasu suka d’auka suka ‘kara shiga , ko wannansu idan zai wuce sai ya nuna tanbarin spider d’insa.
Daga ciki akwai wani waje da yafi ko ina mugun tsaro ,kasan tuwar da mugun tsafi suke anfani, mutane burjin a ciki kan wasu kujeru masu shegen tsad’a , suna da yawan gaske amma kowannansu fuskokinsu a rufe yake , babu Wanda yasan junansu Sabida ‘ka’idar ‘kungiyar Black magic spider babu yadda ko sanin juna , amma ko me kakeso za’a samar maka shi, ko da kuwa manyan ‘kazaman kud’i kake ko d’aukaka zasu baka , hatta idan mutum kace a kashe mata take a Wajan za’a kashe sa, sabida yadda suke mugun anfani da black magic. Duk
End Ads