shikenan uwar karuwai ta siyar dani wajan ‘yan ‘yankan kai?”yadda bobo ya kafeta da idone yasa ta ‘kara shiga taitayinta gabaki d’aya a tunaninta bobo shine shugaban yan shan Jinin shiyasa yake kallanta yana Tuna’nın yadda zai tsotse mata Jini.(😂😂😂wonder shall never end 😂😂 bobo ya zama shugaban yan shan Jini ).
Kallan Direction d’in doctorn bobo yayi kafun ya furta “ let’s talk” yana kai ‘karshen maganarsa bai jira jin amsar saba ya bar d’akin shida Robert , shima doctor cikin sauri ya bawa nurse d’in umarnin su kula da ita kafun ya bar cikin d’akin , koda ya fito be tarar da bobo ba shiyasa yayi Saurin
Bud’e office dinsa da ke facing d’akin da Abla take ciki, a zaune ya tarar dashi kan kujera yayın da Robert yake tsaye gefensa cikin shigar ‘ba’ka’ken kayansa, tun kafin ya zauna bobo ya kallesa alamar ‘karin bayani, wani files doctor ya mi’ka masa yana zama kan kujerarsa “ wannan details din tane, alamu sun nuna tana cikin matsananciyar damuwa da ta saka wa zuciyar ta , hakan kuma babban illa ne da zai iya sawa ta kamu da ciwan zuciya , secondly she have stomach ulser , hakan ya samone daga rashin abinci me lapiya da bata samu , ayyuka masu wuya da kuma rashin cin abinci akan lokaci hakan ne yasa ta kamu da stomach ulser me mugun hatsarin gaske da idan ba’a kula da abincinta ba zaiyi affecting kayan cikinta.” Sai kuma yayi shiru yana tantamar karasa masa zancansa, “ And?” Cewar bobo yana zuba masa idanuwansa , ajiyar zuciya doctor ya sauke “ alamu sun nuna cocaine d’in da aka sha’ka mata shine yake ‘ko’karin ta’ba mata kwakwalwarta , sannan akwai allura da akai mata da ta wuce ‘ka’ida ta maye , sai kuma wata allura last da akai mata me mugun illa da idan ta ‘kara 2 hours tana bacci bazata ta’ba tashi ba”ya ‘karasa a hankali yana kallan bobo, cike da mamaki bobo ya furta “Cocaine ? Wannan yarinyar?” Cikin tabbatar da bincikensu doctor ya furta “ yes sir”, bobo be kuma cewa komai ba ya tashi tsaye hannunsa d’auke da file d’in Abla , agogon hannunsa ya duba kafun ya mikawa doctor hannu sukai shaking , kai tsaye d’akin da aka kwantar da Abla bobo ya ‘kara komawa a wannan lokacin an tufke mata gashin kanta , amma yadda ta takure waje d’aya tana kuka ne zai bawa duk Wanda ya ganta tausayi , duk Wanda yaji sautin kukanta yasan daga ‘kasan zuciyar ta yake fitowa, yadda take kuka sosai bobo yaji ba dad’i cikin zuciyarsa da yayi sanadiyar ta’bo masa tabansu da bayasan tunawa a rayuwa , kujerar da take side d’in gadon ya zauna , yadda take ‘boye fuskarta cikin rigar big boss da ta kudun dune ne Yaso bashi dariya , musamman dramer da yake ‘ko’karin shiryawa da kaso 90 aciki yasan me wuyane sosai. Gabaki d’aya nuni Robert yayi wa nurses din akan su fita, suna fita shima be ‘kara one minutes ba ya bar d’akın yayi saura bobo da Abla kawai gashi ta sunkuyar da kanta ‘kasa taki yadda ta d’ago da fuskarta ya lura a tsorace take gabaki d’aya , mamakin abunda doctor ya fad’a game da lapiyar tane ya tsaya masa a rai haka kawai yaji yana san jin ko wacece ita, da inda iyayenta suke , yafi tsawan 5 minutes zaune a wajan be tankamata ba , shima Abla bata d’ago kanta va sai ma ‘kara tura kanta da tayi cikin rigar jikinta. Knocking d’in da akai ne ya bada izinin shigowa , LG laura ce sanye da wasu ‘kananan kaya a jikinta , gashin kanta ta d’aureshi ta baya sai faman lilo yake , kallan Abla dake kan bed tayi duk da bataga fuskarta ba taji ranta ya mugun ‘baci lokaci d’aya taji wani irin tsanar Abla ya shiga cikin zuciyarta , ji take kamar ta kasheta lokaci d’aya ta mutu musamman yadda taga tana ‘kara rirri’ke rigar big boss a jikinta “ in kin gama kallanta zaki iya bani abunda ya kawo ki?” Cewar bobo ya furta wa LG da French, da Sauri ta furta “ sorry sir” ta mi’ka masa ‘karamun book d’in da ta shigo dashi , har yanxu zuciyarta ta kasa ha’kura so take taga wata me zarrarce take ‘ko’karin wasa da ranta , ganin bobo ne yasaka bata d’au wani mataki akanta ba da tasan har da yarinyar awajan da babu abunda zai saka ta zuwa , mi’kewar bobo ne yasa ta sara masa duk da ba uniform a jikinta na sojoji, Daidai bakin gadon Abla ya nufa kafun ya d’an juyo Daidai saitin LG ya furta “ We’re going in not less than few minutes” sara masa tayi tare da furta “ yes sir” tana juyawa, koda zata bar d’akin sai da ta ‘kara jiyowa ta kalli gadon da Abla take Kai.
“ Hey !” Cewar bobo yana kalan Abla , da Sauri Abla ta zabura har tana bige hannunta , yadda fuskarta ta ‘bacı da hawayene yaso bashi dariya , gashi ta wani zaro masa ash eyes d’inta da ya cika da kwalla , kana ganin yanayin fuskarta zaka fuskanci ‘kiris take jira ta ‘kara saka wani kukan , “ quel est ton nom ? ( ya sunanki ?)”, cewar bobo , bin bakinsa da kallo Abla tayi a tsorace ko kwakkwaran motsi batayi , shi kuma bobo atunaninsa tana Jin French shiyasa yayi mata da yaran dan Abla gabaki d’aya bata kama da yan Africa,ganin tayi masa shiru tana binsa da manyan idanuwanta yasa a wannan karan yayi mata turanci “ what’s your name ?”, yanxu ma shiru tayi masa idanuwanta gabaki d’aya ya cika da kwalla, lokaci zuwa lokaci tana kallan gefenta, kamar ace mata takkk ta arta a guje , shigowar doctor ne yasa ya mayar da kallansa bakin door din har ya ‘karaso hannunsa d’auke da wata farar paper yana mi’kawa bobo, d’an kallan paper bobo yayi yana ‘kara kallan doctor d’in “ ta samu matsalar maganane?” Girgiza masa kai doctor yayi “ A tsorace take shiyasa , idan akai mata dole kuma zai sa mata ciwan kai”, kansa bobo ya jinjina masa , wayarsa da ta d’anyi Haske ne ya sa ya kalla kafun ya nufi kofar fita , doctor ma ya bi bayansa, yayi saura sai Abla kawai da ta ‘kara du’kun’kune kanta cikin doguwar rigar jikin ta da har yanxu ta’ki bari a ta’bata. 5 minutes later Bobo ya dawo cikin d’akin bayansa LG ce sai kuma doctor da Robert da suka shigo, yadda LG Laura take kallan rigar big boss kamar taje ta hankad’a wacce take sanye cikin rigar sa da ko ita da ta sansa sama da shekara 10 ko gashin kansa bata ta’ba ta’bawa ba sai yau wata yar iska ta nanuke rigarsa kamar zata had’iye , kana kallan fuskar LG yadda tayi jaa zakasan ranta a’bace yake tana ‘ko’karin dannewa ne kawai.
‘Dan gajeran murmushi bobo ya saki tare da zama akan kujerar kusa da gadan Abla da ta ‘kara ta kure jikinta , har zai mata turanci sai kuma ya fasa tuno yadda tayi Hausa d’azu , hausan da shi kansa yayi mamakin yadda akai ta ‘iya yinsa amma bashi da lokacin tanbayar yadda tayi shiyasa cikin cool voice ya furta “ ya sunanki?” Itama Abla da mamaki ta d’ago fuskarta ta zubawa bobo , bata san lokacin da bakinta ya furta “ shima farin meshan jinin nan ya iya Hausa ?” Da mamaki bobo ya kalleta sabida maganarta wato d’an shan jini ta d’auketa , “ lalle kina da aiki babba” cewar bobo cikin zuciyarsa . Be kuma ce mata komai ba ya mike tsaye tare da kallan LG cikin French ya furta “ ku taho tare da ita and ku rufe mata kanta bansan ganin gashi a waje , yana kai ‘karshen zancan ya bar d’akin, a zuciye LG ta matso gadon da Abla take, wani farin yadi da ta gani a ‘kasa ta jefa mata tare batare da la’akari da yaran da ta iya ba cikin French tace mata ta kulle kanta, dukda Abla bata gane me take nufi ba itama da Sauri ta d’auki farin mayafin ta yafa akanta tana ‘kara rike coat d’in jiginta gagam( Ni kam zan so Big boss yaga yadda ake cakud’a masa Riga ko tsarabar mari ne ta samu😹🥹). LG ta zo zata cire mata rigar Abla ta ‘kara ri’ke wa gagam musamman yadda batasan aga jikinta, a karo na biyu LG ta ‘kara saka hannunta azuciye zata cire rigar Abla ta gantsara mata cizo , zafin da tajine yasa ta tsinkawa Abla mari , itama bata sauke hannunta ba Abla ta daddage ta tsinka mata mari dama da hannu ( kowa yasan zafin hannun bahaushe ba irin na bature bane rainan madara da Milo) a gigice ta saka ‘kara sabida zafin marin da taji batayi aune ba Abla ta ‘kara bata wani tsaraban cizon da ya saka LG ware murya ta kwala ‘kara , sai kuma ta fara dukan Abla , itama Abla bata ‘kyaleta ba , duk da yadda LG ta fita girma da ta doketa zata saka hannu ta rama dan tayi al’kawari kafun su shanye mata jini sai ta Gana musu azaba. Da Sauri a ka tura ‘kofar shigowa , yadda yaga suna dukan junane yasa bobo ‘karasawa wajan ya ‘ban’bare Abla , be tsaya wani tunani ba ya d’auke fuskar LG da mari , itama Abla ya d’aga hannu zai Mareta yaga shatin marin LG a fuskarta shiyasa ransa ya ‘kara ‘baci , hannunta kawai ya kama zatayi masa musu itama ya daka mata tsawar da yasa ta kame bakinta , ko kallan inda LG take beyi ba suka fito daga d’akin, kai tsaye fitowa sukai daga cikin asibitin d’in gabaki d’aya ,yadda Abla taga zagara zagaran maza ko wannansu sanye da ba’ka’ken kaya da bindugu a hannunsu yasaka ta soma share hawayenta , jikinta har karkarwa yake sabida tsoron ganin ko wannansu da binduga datayi , sosai kirjinta ya soma sama da ‘kasa hatta tafiyar ‘ko’karin canzawa ya fara tana lumshe ido, yadda ta soma kakkare wa a bayan bobo tana kulle idanuwanta ne yasa ya d’an juyo ya kalleta , zai mata magana ta ‘kara firgita zata saka gudu Sabida bindugar da ta gani a hannun Robert , wani irin juwane taji yana ‘ko’karin kamata , ganin yadda take ‘boyewa abayansa ne yasa ka ya d’an jiyo ya kalleta , sosai ta runtse idanuwanta ko bud’e bata sanyi har suka ‘karaso wajan motar da Robert ya bud’e masa , nuni yayi mata akan ta zauna , ba musu kuwa ta zauna dan sosai tsoran mutanan da ta gani da bindugu ya kamata , ko d’ago da kanta batasan yi musamman yadda ta rintse idanuwanta dukda sanyin Acn da yake cikin motar Alba zufar tsoroce ta fara fito mata , babu abunda take nanatawa cikin zuciyar ta sai Innalillahi wa inna ilaihi raji’un , gabaki d’aya ta sada’kar shikenan ‘karshenta ya zo , lokacin shanye Jininta yayi , shima bobo ko sau d’aya be kalli side d’in da take ba da alama abu yake me muhimmanci a cikin wayar sa , direct Airport suka nufa , a wannan karan ma koda bobo yasata ta fito batayi musu ba amma ta ki kallan kowa sai faman kare fuskarta take hatta bobo ta’ki yadda ta kallesa , ana zuwa wajan shiga jirgi Abla ta d’ago da idanuwanta , karo na farko arayuwarta data fara ganin jirgi shiyasa tana kallansa ta fashe da kuka me tsuma zuciya , tana girgiza musu kai , muryarta har rawa yake wajan furta “ Dan Allah kuyi hakuri”, yadda tayi maganar sai ta baka tausayi , hatta bobo sai da yaji ba dadi cikin cool voice ya furta “ babu abunda za’ai miki kinji? Taho mu tafi” kanta Abla ta jinjina masa kafarta har rawa take wajan taka step din jirgi, LG tana bayansu gabaki d’aya ba’kin cikine ya kamata kamar zuciyarta zata buga sabida tsanar Abla da tayi Alwashin tunda bobo ya mareta sabida ita sai ta Gana mata azabar da sai ta kwammace bata duniya ( To faaa 🥱), suna shiga cikin jirgin yawanci sojojin bobone ko tsaye sanye da blank din kaya da Sauri ta matso inda yake dan harga Allah tsoran su Robert take , duk inda ya taka Abla tana binsa a baya , Adai dai wani waje me shegen kyau Bobo ya tsaya , kujerune sosai A wajan kamar ba a cikin jirgi ba , yadda tsarun kujerun suke sai sun burge mutum , yan mata biyu da su bobo suka taho dasu ko waccensu tana zaune kan kujera ta saka belt d’inta , itama Abla waje bobo ya nuna mata sai bin ko ina take da kallo tana zama ya saka mata belt d’in da Hausa ya furta “ kar ki motsa daga inda kike idan ba haka ba jirgin sai ya had’iyeki ya cinye ki” ya fahimci tsoran jirgin ta keji shiyasa ya fad’a mata haka , yadda Abla ta ri’ke kujerar jirgi sai ta baka dariya hatta bobo saida yayi murmushi kafin ya bar wajan , LG ma da wasu mata suma duk a wajan suka zauna , yadda Abla taji wani irin girgiza na tashin jirgi sosai hakan ya girgixa ta ware murya tare da kwala kara cikin Sauri kuma ta toshe bakinta hawaye na gangaro mata cikin zuciyarta har ta fara adduar shahada ganin shikenan ta tabbata kashesu za’ayi , tun tana tsorata yadda LG take binta da mugun kallo itama Abla taka take binta , ga tsoro ga masifa , yadda sanyin Ac take kad’a ko ina ne yasa Abla ba shiri bacci ya d’auketa .
2 hours 45 minutes ne ya shigo dasu ‘kasar U.S cikin Garin New York , da karfi LG ta d’akawa Abla duka da yasata zabura cikin sauri, a zuciye ta cire mata belt d’in jikinta tana bin fuskarta da wani irin kallan tsada , agadarance ta furta “ let’s go” kamar Abla bazata bisu ba ganin yadda sauran yan matan suka tashi yasa itama ta tashi ta soma binsu har suka sakko cikin jirgin, Bobo na tsaye sai su Robert da wata farar baturiya sai faman sakin murmushi take ita kadai , wad’an da Abla ta gani ne ya saka lokaci d’aya jikinta ya soma raba da Sauri ta koma bayan bobo tana karanta adduar da zata zo bakinta duk da a Wannan lokacin babu bindugu a hannansu , kallan farar matar bobo yayi bansan akan me suka tattauna ba illa “ dis is the girl” da bobo yace mata , yanxu ma murmushi ta ‘kara saki tana nufo inda Abla take ta kamo hannu, da Sauri Abla ta bud’e baki zatayi ihu bobo ya furta “ idan kika Kuskura kika mun ‘kara sai na tarwatsa kanki” ba shiri kuwa Abla tayi shiru tana zazzare idanuwa saida ya bata minute d’aya kafun ya furta “ babu abunda zata yi miki, tafiya kawai zatayi dake kika kuskura kika bud’an baki kuma..” ya ‘karasa yana d’auko wata ‘karamar bindiga, saura kad’an fitsari ya kwacewa Abla lokacin da ta ga bindigar jikinta har rawa yake lokacin da farar matar nan ta kama hannunta suka wata bakar mota , ko kwakkwaran motsi Abla ta kasa har driver ya tashi motar suka bar wajan .shima Bobo motar da Robert ya bud’e masa ya shiga , ragowar sojojinsu suma suka shiga cikin motocin su guda shida suka bi bayan motar bobo , ita kuma LG da wasu sojoji suka bita tare da ‘yan matan nan . Tunda motocin su bobo ta soma tafiya a kan babban titin da zai kaisu 5th Avenue lokaci d’aya motocin bayan bobo guda biyar suka fara ‘balle bottom d’in rigar su suna cireta sai bakar singlet da suke bari hatta ta kalman ‘kafarsu ko wannansu ya cire ya nannad’e ’kafar Wandunansu zuwa gwiwa ,tun kafun ayi horn aka wangale wa bobo babban gate d’in cikin gidan, Victor tsaye a wajan cikin girmamawa ya sarawa bobo , cikin Sauri Robert ya sara masa shima yana fitowa daga cikin motar , Victor ya shiga ya tada motar tare da barin wajan , lokaci d’aya gabaki d’aya sauran sojojin sukai parking d’in motocin su suka fito , tun kafun a basu umarni ko wannansu ya kwanta a kasa a jere cikin layi , lokaci d’aya suka soma birgima a kasa duk da Nisan da ke tsakanin first gate da second gate haka suka dunga birgima kamar wasu kifaye suna tunkarar gate 2, anan ma still gate aka bud’e musu suka cigaba da birgima zuwa babban gate din cikin gidan dukda daga second gate zuwa main gate ya fi nisa haka suka dunga birgima suna furta “ sorry sir “ har suka ‘karaso main gate kafun kamar wad’an da aka saka tsere suka soma zaga compoud din cikin gidan cikin gudu gudu .
Bobo kuwa direct main part d’insu Victor yayi parking motar sa yana fita Victor ya ja motar ya bar wajan cike da girmamawa , yana shiga cikin falourn ya tarar da ko ina shiru kamar babu mutane a cikin falourn, Adaidai lokacin da little da prince suka fito daga cikin wani ‘kofa hannun d’auke da coffee, little yana ganin sa yayi saurin zuwa Wajan da yake tare da hugging d’insa , shima prince hugging d’insa yayi kallan su yayi tare da kallan coffee d’insa hannunsu , fahimtar hakan little yayi ‘kasa ‘kasa da murya kafun ya furta “ big yaya bobo help us wannan shine coffee na 8 Kenan kuma yaya big boss ya hanamu hawa lifter ta step muke bi, please”, murmushi kawai bobo yayi yau big boss a sama yake kowanene tsautsayi ya fad’a bazai ji da dad’i ba . Coffee d’in hannu ya kar’ba kafun ya furta “ dare yayi kuje ku kwanta” cikin had’a baki suka d’an zaro ido take da furta “ yaya !” Shima nasan I don ya d’an