“ Yaya Little kalla” inda ta nuna masa ya kalla d’in , be aune ba yaji ta fad’i amsar da yake shirin fad’a , hararar ta yayi kafun ya furta “ Lil wannan cheating ne ai , kinsan zan fad’i masa shine kika sa na kalli wani waje , ban yadda ba’a sake” kamar had’in baki prince da Abla suka furta “ No “ yaya Lil babu wani cheating, kawai bakasan amsan bane “ pillow d’in gefen sa ya jefo mata “ Ni zaki yi ma wayo ? Don’t mind ,you will definitely fail “ da haka suka ci gaba da quiz d’in kowa yana so yaji, prince shine judge d’insu, har aka gama da equal mark suka tashi kowa ya ‘ki barin kowa yayi winning , Lokacin sallah nayi ,su little suka nufi masallaci ita kuma Abla ta koma d’aki.
5pm Abla ta ro’ki su Little su nuna mata yadda ake using kayan kitchen bayan ta fad’a musu abinda ta ke bu’kata , kamar da gaske suma suka ce zasuyi girkin dan tare zasuyi suna so suga ko Abla za tayi me dad’i da kanta ko kuma sai ta kalli vidoe , da wannan gasar kowa ya saka apron a jikinsa dan tace musu kunnan su sai yayi girgid’i, idan ka kalli Prince da Little yadda suka saka Apron d’in kansa sai mutum yayi dariya dan yau ne karan su na farko , Duk abunda take bu’kata ta lissafo musu sai da James ya zo ya d’auko musu dan su kansu basusan inda kayan suke ba , Apple pie Abla tace musu za’a fara , Little yace a bashi shine zai kwa’ba da kansa , tunda Abla ta zuba masa flour gabaki d’aya kusan rabinta a jikinsa ya kwashe ta , idan ka kalli fuskar Little futu futu da flower kamar Wanda yayi dan be , hatta kansa gabaki d’aya flour ne ,” Ya’ya Little ka ganka kuwa , kamar d’an Aljani “ dariya prince ya kwashe da ita shima ga knife a hannunsa yana yanka albasa , ko ‘bareta bayayi yake dadda tsata gida uku, shi kadai sai matsar kwalla yake , Abla na gefe tana ‘bare tafarnuwa sai dariya take musu, ganin dariyar da take musu yayi yawa shima Little ya d’auki flour ya kwatsa mata , a ta kaice sai da suka ‘bata cikin kitchen d’in da flour , ko wannansu kuma kamar sunyi dan be musamman Prince da Little . 6:10pm suka gama abincin da suke , Abla ta fara gyara kitchen d’in su kuma suka fito da Abincin zasuje Dinning dashi, kamar daga sama suka ji sallar Bobo, ga spoon d’in da yake ba’kin Little shi a dole ba zai yi’ke a hannu ba , be san lokacin da ya saki spoon ya fad’i ’kasa ba ganin Big Boss a bayan Bobo, sakin baki Bobo yayi yana kallansu ganin duk gabaki d’aya sun ‘bata jikinsu da flour , shi dariya ma suka bashi, banda Big Boss da yayi mugun had’e masu rai , cikin tsokana Bobo ya furta “ mun samu sababbin chefs a gidan kenan?” Fiki fiki sukayi da idanuwansu “ yaya abinci Kawai mukayi fa kad’an !” Cikin tsare gida Big Boss ya furta “ yau she aka fara haka ?” Shiru sukayi suna sunkuyar da kansu, taku d’aya yayi Prince yayi saurin furta “ No yaya bari nayi maka ba yani, we just made it for fun..!” Kallan da ya jefa wa prince ne yayi saurin sun kuyar da kansa ‘kasa “ For fun right?Good !” A na tsaka da haka itama Abla ta fito jikinta futu futu da flour ,” even you Sister ?” Cewar Bobo yana d’an ware eyes d’insa sabida mamaki, har bawa zuciyarta tayi “ shikenan na kad’e har ganye na “ cewar Abla cikin zuciyarta, sau d’aya Big Boss ya je fa musu wani mugun kallo, kafin ya juyar da kallansa zuwa Bobo, d’an girgiza kansa Bobo yayi kad’an kafun yayi danne danne a wayar sa , cikin mintunan da basu fi biyu ba James ya shigo falourn cikin girmamawa , a fuske Big Boss ya furta “ The menu” James ya gane me yake nufi shiyasa cikin girmamawa ya furta “ yes sir” yana nufar hanyar kitchen , be jima ba ya dawo d’auke da wani Book , fiki fiki Little yayi da idanu, ko kallan sa Big Boss be yi ba sai ma umarnin sa da ya daki kun nuwansu “ from now henceforth, kune chefs d’in gidan,all the details of food , one mistake hmm “ ya na kai karshen maganar sa yayi hanyar part d’insa , da sauri Little ya furta “ Yaya Sister tana zuwa makaranta “ da katawa yayi da tafiyar kafun ya d’an jiyo da kallansa side d’in Little “ And ?” Da sauri Little ya girgiza masa kai “ Zamu yi as you wished “ , yana barin wajan suka kalli Bobo gabaki d’ayan su , murmushi ya sakar musu “ Ni babu ruwa na , ku dena kallo na , ai you guys kun iya girki tun daga shigar jikinsu” yaya cewar little “ babu wani yaya , yanzu za’ayi sallar magrib kuje ku canza kayan jikin ku , Lil sister aikin yayi kyau daman ya kamata su iya , Dan ko ruwan zafi basu iya dafawa “ yana kaiwa nan shima ya wuce part d’insa , kallan juna sukai su uku ganin punishment d’in da suka janyo wa kansu, ga kuma yadda ko wannan su yayi futu futu kamar ‘yan bori yasa ba shiri suka ‘kyal’kyale da dariya , sai da sukayi dariya mai isar su sannan kowa ya wuce part d’insa ganin an kusa tayar da Sallah.
****Abla tana koma wa d’aki wanka tayi ta tsaftace jikin ta tunda bata da tsarki, a maimakon ta fito falo sai ta ‘kara d’auko notes d’in ta na makaranta tana ‘kara duddu basu, abunda bata fahimta ba sai ta d’anyi d’igo a wajan , sai da ta gama gabaki d’aya sannan ta fara searching abubuwan da bata gane ba , tun bata gane wa har ta fahimta gabaki d’aya .
9:00pm suka fito cin abinci ban da Big Boss , cikin tsokana Uncle yane lumshe idanuwan sa , wannan ‘kamshin abinci daga ina yake fitowa , shima Bobo murmushi yayi wa Uncle “ Uncle yaran ka sunyi hankali ai tunda gashi sun iya abinci kaga James ya huta na kwana biyu” kamar zai kuka Little ya furta “ Haba Yaya kai da zaka bawa Yaya Big Boss hakuri ? Amma shi kenan nasan Uncle d’ina zai bashi “ tun kafin ya ‘karasa Uncle yace “ Wana Uncle d’in ? Ai ko ni bazan bashi hakuri ba , yadda nake jin ‘kamshin girkin nan har kwakwalwata nasan ba ‘karamun dad’i zai yi ba , yanzu Kawai ku tashi kuyi serving d’in mu “, kallan sa Prince yayi “ But Uncle Yaya be fito ba “ da hannu Uncle ya nuna masa hanya “ maza je ka fad’a masa ya sakko ya d’an d’ana abincin ku , nasan har rewards zai basu” yadda Prince ya zazzaro idone ya saka Bobo girgiza kansa ,” Shima ya san sauran ne yayi gigin zuwa , mu da muke bayin Allah talakawa azu ba mana abincin nan kafun ‘ya’yan cikin mu su fito saurin toshe bakinta Abla tayi Sabida dariyar da taji tana ‘ko’karin kwace mata , da haka suka wuce Dinning gabaki d’ayansu, Abla ce tayi serving d’in su. Tun kafun su fara d’an d’ana abincin suka fara santi, Little aka fara sawa yayi testing d’in abinci , shima da farko kamar bazai ci ba har yana ya mutsa fuskarsa, tun da yaci 1 spoon yaji yadda abinci yayi mugun yi masa dad’i ko uffan be ce musu ba ya cigaba da cin abincin sa . Ganin hakan yasa suma suka soma cin abincin , babu Wanda beyi mamaki yadda d’an d’ana girki ya fito ba kamar wacce tayi rayuwa wajan masu girkin, shi kansa Bobo be san lokacin da ya furta “ Amma Sister daman tun tuni kin iya abincin nan shine ba kya mana ?” Murmushi Abla ta saki dan har ya d’an bata kunya “ Yaya ba fa ita kad’ai tayi ba , muma har da namu contribution d’in “ , hararar su Bobo yayi “ contribu ba contribution ba “ shima Uncle sosai ya yaba da girkin har yana tsokanar su zai saka Big Boss ya bar musu punishment d’in girki har na tsawan shekara suna yi musu” bud’ar bakin Bobo ya furta “ Don’t mind Uncle ai daga yanzu sun zama Chief bawai na tsawan shekara ba , prince da ya fi kowa tsanar aiki ya furta “ Haba Yaya Bobo fisabilillahi, I swear lokacin da nake yanka onion lokacin da naji idanuwana suna hajijiya ‘karar harbi kawai nake ji cikin kunne na “ gabaki d’aya dariya suka kwashe da shi “ ko jira ga kake ji sai ka yanka onion , Sister idan akwai pepper ma duk ki basa yayi, idan bakuyi wasa ba Restaurant za’a bud’e muku ku soma girki” ‘bim Prince ya rufe bakin sa yana cuno baki , Abla da Little sai faman dariya suke masa ‘kasa ‘kasa . Ana kammala cin abincin falour aka koma , ko hirar minti 30 basu yi kowa ya nufi d’akin sa musamman Little da Prince da suke rakin bayan su zai cire Abla ta yau dare su , sun d’auka girkin ba wahala amma ta sasu suna ciwan baya, rakı kala kala kamar ba maza ba , suna shiga d’aki tunda sukayi wanka suka shirya ko wannan su ya d’ane Bed d’insa .
WASHE GARI
Gabaki d’ayan su da wuri suka tashi tun bayan sallar asuba da sukayi suka fad’a kitchen tun da Big Boss ya mayar dasu chiefs d’in gidan, prince sai kunbura baki yake shi a dole ya gaji , da yasan tsautsayin da zai hau kansu da bayi gigin zuwa Kitchen d’inta , a fakaice Little yayi mata rad’a a kunne kafun su had’a baki lokaci d’aya su furta “ Chief Yaya Prince “ hararar su yayi , ya’ki kula su kuma , wani idea ne ya fad’o wa Abla ta saka suka suka soya plantain, sai Chips da musu kamar sugar Nigeria, Ga scrambled eggs da tayi musu da yaji Kayan ‘kamshi da albasa , farfesu Little yace yana so , duk da babu kayan had’in da zatayi na Nigeria amma tayi amsa irin yadda taga ni a vidoe , tun kafun a gama abinci suma soma nishi dan hatta Clam Chowder sai da sukayi da Bagel and Lox . Suna gama suka jera abincin su a dinning daman ko gigin fad’a wa Big Boss babu Wanda yayi , a wannan karan ma haka su Uncle suka dunga santin abincin su , abu kad’an suce shikenan sun samu chefs tunda gabaki d’aya sunsan efforts d’in Abla ne tunda Bobo yace ko ruwan zafi su Little basu iya tafasawa ba.
Da rana ma the same abunda ya faru kenan su sukayi lunch , dad’in su d’aya ma Big boss da Bobo basa cikin gidan shiyasa sai da suka gama game d’insu san ransu kafun suyi lunch d’insu.
8:30pm nayi Little yace yau fruit za’a sha, daman Yaya Big Boss yace su dunga motsa jiki bayana uban chocolate da snacks da ya kai d’akin sa , shiru kawai Bobo yayi musu Sabida lokacin Big Boss be dawo cikin gidan ba . 9:10 nayi Little ya gudu d’aki sabida karma su had’u da yaya, yace musu bacci yake ji, shima prince da Abla guduwa d’aki sukai kai hukuncin ya dawo kansu.
MONDAY
Da wuri Abla tayi shirin makaranta , bata dad’e basu Little sukai dropping d’inta a makaranta, tana shiga class ta tarar da Eshaal tana duba Books d’inta “ Hey” cewar Eshaal , itama Abla “ Hey “d’in tace mata tana zama , juyo mata da Book d’in Eshaal tayi “ Thanks God kinzo , kinga sai kiyi mun bayanin wannan topic d’in dan naga wannan karan da gaske so kike ki ‘kwace mun position “ murmushi kawai Abla tayi mata wai zata kwace mata position , bayanin topic d’in tayi mata dallah dallah yadda zata fahimta, suna cikin yi fanan itama ta shigo class d’in ganin suna karatu itama tayi saurin ‘kara sowa wajan su “ yanzu tsakani da Allah haka zamuyi daku ? Aushe kuna nan kuna karatu salan in anzo exam ku barni da zare ido” d’an girgiza kanta Abla tayi tana murmushi da kuma suka cigaba da d’akko topic d’in da basu gane ba , Wanda ya fi iyawa a cikin su yana yi musu ba yani. Teacher na shigowa kowa ya nufi seat d’insa , Mss Atem ce ta fara shigowa class d’in, lokacin ta nayi ta fita sauran teacher suka shigo har zuwa lokacin break. Tsakanin ta da Baby sai harara da ba’ka’ken magana amma ko sau d’ay bata ta’ba tanka mata ba sai dai tayi murmushi. Suna shiga capteria order abunda suke so sukai su uku dan yanzu Baby gaba ta farayi da Fanan tunda taga tana yiwa su Abla magana . Suna cikin cin abincin su Bad Boys suka shigo student d’in Wajan suka fara kururuwan kiran su nan su , dan ko ba komai idan a ka gansu dole ne a saka wani yin abu su kuma abunda suka fi enjoying Kenan shiyasa suke ‘kaunar Bad Boys su shigo ko dan dramer da zasu gani.
Table d’in su Abla MAI DALA ya nufa , d’an hararar sa Fanan tayi “ Me kuma kazo yi mana anan , kaman ta warning d’in da Nani tayi maka ko?” Tsaki Mai Dala yayi bayan ya ja kujerar da tayi ragowa a wajan su “ koma Menene ni ba Wajan ki nazo ba , so better stay out of me , idan ba haka ba wallahi yanzu na saka ai miki wula’kanci “ hannu ya mi’kawa Abla yana furta “ Hey” ko inuwar da ta kwa sosa Abla bata kalla ba , balan tana ya saka ran zasu gaisa d’in, shiru Fanan tayi masa dan ta kula itama Abla ba kanwar lasa bace “ ina miki magana kina share ni , ba lalla’ba ki nazo yi ba , nazo miki da umarnin kar’bar soyayyata , ko ina so ko ba kyaso , yanzu ma Number wayan ki na zo ki bani dan bani da lokaci”, hauka Abla ta watsa masa shi yasa hakan ya tun zurashi ya daka mata tsawa yana ‘ko’karin ri’ke mata hannu, cikin had’e rai ta d’auki juice din gabanta orange ta watsa masa a farar white uniform d’insa , gabaki d’aya wajan shiri ya d’auka sabida kowa yana so yana reaction d’in Mai Dala , kallan banza Abla ta je fa masa “ Duk haukan ka , Duk rashin mutum cinka kasan a inda zaka dunga yinsu , idan kanaji da rashin mutumci akwai Wanda suka fika , idan wukanci kake ji dashi akwai Wanda suka danne ka iya rashin wula’kanci, wannan ne last warning d’ina akan ka , duk lokacin da ‘kaza min hannun ka yayi gigin ta’ bani “ tana kai karshen maganar ta tayi wucewar ta , a bokansa zasu bita yayi saurin dakatar dasu “ wannan wasan ba naku bane , sai na wula’kanta ta , irin wula’kancin da bata ta’ba zato ba , sai ta san tayi kuskuran shigowa gonar Mai Dala “ da haka ya nufi hanyar fita a fusace suma friends dinsa suka mara masa baya . Hankalin su Fanan ba ‘karamin tashi yayi ba dan sun san tunda Mai Dala ya fad’a hakan sai yayin da gaske. Har aka tashi suna zuba ido suga ne zaiyi amma shiru. Lokacin da Little ya zo d’aukan tane suka had’u da su Fanan , cikin fara’a ya furta “ Lil wad’an nan ne sababbin friends d’inki?” Kanta Abla ta jinjina masa tana murmushi “ that’s good , What’s your name ?” Ya ‘karasa yana nuna su , Fanan ce ta fara furta “ sunana Fanan” kafun Eshaal ma ta fad’a masa sunan sa “ sunayen ku masu dad’i hope babu Wanda yake takurawa Lil a makaranta, if they is any kawai ku fad’a mun “ kallan suna sukai kafin su d’an girgiza masa kai alamar ba kowa , da haka sukayi sallama su Fanan suka wuce suma su Little suka kama hanyar gida .
*******Tun daga wannan lokacin wani irin sha’kuwa yashiga tsakanin Eshaal , Fanan da kuma Abla , kusan duk inda kaga d’aya to zakaga sauran suna wajan, itama Fanan yanzu ta watsar da Baby sabida wula’kancin da take mata . Ga wani irin amin ta da ya shiga tsakaninsu musamman da gabaki d’ayan su masu san karatu ne . Duk lokacin da Little ya zo d’aukar ya sai sun gaisa dashi har suka zama kamar yan uwa suma duk lokacin da zasu tafi sai ya tsokane su.
Yau ya kamata 3 weeks da zuwan Abla makaranta , kusan satı d’aya da ‘yan kwanaki kenan bata saka Big Boss a cikin idanuwan taba , duk lokacin da yake gida tayi gigin yin kuskure daman tasan sai ta d’auki haukan ta a hannu.
Gabaki d’aya su ukun suna zaune a class bayan teacher ta fita suna jiran last period d’in da zasuyi suka ji an shigo cikin class d’in, ba kowa bane face Mr Jabcon, kusan satı 2 Kenan yana kiran Abla office d’insa amma bata zuwa , last kiran da yayi mata ne lokacin da taje yake ‘ko’karin jire belt d’in jikinsa Abla ta hanka d’asa ta gudu hakan ne ya haifar masa da gocewar ‘kashi a ‘kafa shiyasa yayi Alwashin duk hanyar da zai bi sai ya wula’kanta Abla. Kamar da gaske ya fara yi musu teaching d’in da ya kawo sa , ana saura 5 minutes a tashi ya fito da wasu ‘yan envelope masu d’auke da wasu ‘kananan hotuna , ganin suna da yawa ne yasa ya watsa su tare da umartan kowa ya d’auka , d’aukan kuwa sukai suna duba abunda yake cikin hotan, duk Wanda ya kalla sai ya jiyo ya kalli