sai na mugun sa’bamiki , stupid !”a hankali cikin shashshekar kuka Abla ta soma bashi hakuri , rai a ‘bace ya daka mata tsawa “ Get lost”, cikin kuka sosai Abla ta ruga stairs inda d’akinta yake , tana gudu tana share hawa yan da suke zubo mata .
***** Tana shiga d’aki kan bed ta fad’a tare da fashewa da saban kuka , kuka kawai takeyi abunta ,duk da irin abunda yayi mata yanzu kwata kwata bata ji zafinsa ko d’aya a cikin zuciyarta ba, sai ‘kara tuno face d’insa da tayi da yadda dogon murd’ad’d’en gashinsa yake motsawa , a hankali face d’insa ta soma yi mata gizo kamar yanxu ne yake mata fad’an shiyasa ta ‘kara fashewa da wani saban kukan, tun tanayi da ‘karfi har ta somayi a hankali sabida muryarta data d’an dishashe, lokaci d’aya kuma ta soma sakin a jiyar zuciya alamar bacci ne ya d’auketa, ga d’an mitsitsin bakinta da ta turo lokacin da take baccin.
****Big Boss
Tana wucewa sama ya ja siririn tsaki , cikin ‘kasa ‘kasan ma’koshi ya furta “ stubborn rat”, doguwar maganar da yayi yanxu har kansa ya soma yi masa ciwo, ga face d’insa da ya ‘kara had’ewa kamar har yanzu tana gabansa, diamond watches d’insa ya kalla da fararan idanuwansa a karo na biyu ya ‘Karajan wani siririn tsaki tare da nufar part d’insa .
************
10:00am Little , Bobo , prince da uncle suka shigo cikin falourn , babu kowa a ciki shiyasa ko wannansu ya nufi part d’insa sabida su canza kaya, Prince sai mita yake wa little lokacin da yace zai je part d’in yaya , da kyar ya samu little ya hakura sabida shi yunwa yake ji, da Zaije d’akin Abla ma saida prince ya ro’ke shi akan ya dawo da wuri, cikin rashin sa’a yana shiga ya tarar da Abla tana bacci shiyasa ya dawo falourn , lokacin gabaki d’aya suna kan dinning suka jiran fitowar su , ganin babu Abla a bayansa yasa bobo tanbayar sa “ ina little sis d’in taka ?”, d’an kalar tausayi little yayi “ yaya tayi bacci sai dai kafun ta farka ayi mata wani breakfast d’in ita da yaya “ kansa bobo ya jinjina masa “ it’s okay ! Let’s eat”, daga haka gabaki d’aya Suka zauna James yayi serving d’insu tunda Abla bata wajan . Suna gama cin abinci little be jira kowa ba ya nufi part d’in Big boss , kusan kullum light d’in part d’insa a dum yake shiyasa basa damuwa da hakan , direct bedroom d’insa ya nufa bayan yayi knocking sau uku ganin big boss be amsa masa bane yasa ya shiga cikin d’akin, nan ma still dum light ne a wajan , a hankali little ya furta “ yaya ?!” Shiru yaya be amsa masa ba , a karo na biyu ya ‘kara ambatan sunansa amma still be amsa masa ba duk da yana jin lokacin da little ya shigo cikin d’akin amma ya sharesa , cikin turo baki little ya hau kan gadon tare da fara yaye masa white blanket d’insa , be bud’e eyes dinsa ba sai cikin cool voice d’insa ya furta “ little what do you want?”, muryar little d’auke da murmushi ya furta “ yaya ni fa maganar sister nazo nayi maka ya kamata ta fara zuwa school please and naga kana bacci fa” shiru big boss yayi masa ba tare da ya amsa masa ba , a shagwa’be little ya furta “ please yaya kaji?am your little ka manta , ina so sister ta fara zuwa makaranta please”, shiru big boss ya ‘kara masa har saida yace masa “ please” , yanxu ma cikin cool voice kamar bashi ba ya furta “ bani da kudi” wani irin dariya little ya saka da har saida big boss ya bud’e lumshash shun eyes d’insa “ haba yaya taya zaka cemun baka da kudi? Please just for my sake kaji?” ‘Dan ta’be baki big boss yayi lokacin da ya zubawa little idanuwansa “ kana da kudi sai ka sata mana , ni na hana ka ?” Girgixa masa kai little yayi “ but yaya kace fa ko me nakeso na fara tanbayar ka !” Dakatar Dashi big boss yayi ta hanyar furta “ jiya da kuka kashemun kud’i shima kun tanbayeni?” No yaya , cewar little “ okay fine ! Allowed me to sleep”, yana kai ‘Karshen zancansa yaja duvet dinsa , d’an turo baki little yayi tare da kwanciya a side d’insa ba tare da ya ‘kara furta komai ba shi a dole yayi fushi.
✨✨✨✨✨✨✨
NIGERIA
KANO STATE
Tun lokacin da dady ya furta komawarsu Eshaal U.s baby take fushi dashi sabida batasan komawa da Eshaal ta fisan ta yi tafiyarta makaranta ita kad’ai shiyasa tace wa dady ya samo mata wani school a cikin Garin Kano. Sosai ta tada bala’i cikin gidan daga momy har dady babu Wanda ta ragawa dan sai da tayi kwana uku bata kula kowannansu, kullum cikin rarrashinta suke yi dady har kyautar mota yayi mata dan ta wuce shiyasa ta d’an sassauta fushinta, amma duk lokacin da taga Eshaal ko AMMA ta fara ci musu mutumci kenan musamman Amma da take gani Itace ta Shirya ko wani makirci na komawar Eshaal U.S. Duk da ta ha’kura ta d’au Al’kawarin sai ta musgunawa Eshaal har sai taji tafisan zamanta a Nigeria , kullum cikin kawowa dady da momy ‘karar Eshaal take , musamman momy da tafi kowa tsanar Eshaal haka zata kamata tayi ta dukanta kamar wata jaka , sau biyu momy tana tsinkawa AMMA mari lokaci na farko da Baby taji babu dad’i cikin zuciyar ta Sabida Momy bata ta’ba Marin ta agabanta ba , bata kawo komai aranta ba ta share tunanin duk da lokaci zuwa lokaci hakan na fad’o mata arai .
Yau ya kama saturday, ranar da yayi Daidai da saura kwana biyu su Baby su koma U.s karatu, tun safe Baby ta fita ita da momy da dady sabida siyayyar da suka fita da baby ta za’bi duk abunda take san siya amma ko kusa dady be bawa Eshaal 5k ba ta siyayya kuma ba kowa ne ya hana hakan ba face momy, a cewarta idan baby ta dawo zata bata tsofaffin kayanta sai tayi anfani dasu . Eshaal ko ajikinta inda sabo ta saba da irin halin momy da take nuna mata tsana a fili , shiyasa tana gama abincin rana kayan sawarta ta zauna ta goge duk da yadda Amma ta so ta bata amma Eshaal ta’ki bata sai ma zuwa da tayi ta kwantar da Amma akan ta huta . Tun tana yar ‘karamarta bata da uwa kamar Amma Sabida dukda yadda AMMA take aiki a karkashinsu ta fisan ta fiye da kowa na gidan har Dadyn ta. Sabida yadda ada ya nuna mata soyayya amma tun bayan mutuwar mahaifiyarta soyayyarsa ta koma kiyayya baya san ganinta , bayasan ta ra’beshi bayasan komai da ya dangan ce ta shiyasa itama take jan jikinta, yanxu a rayuwa bayan Amma bata sakewa da kowa Sabida ita kad’ai ce sırrın ta .
**** Ana idar da sallar la’asar Eshaal ta shiga cikin kitchen Sabida sha’awar d’an malelen da take , cikin d’an ’karamin tukunya ta d’ora musu ruwan d’an malelensu , gabaki d’aya saida ta yanka tomato, cucumber ,albasa da zasuci d’an malelensu , ruwan da ta d’ora yana tafasa ta saka tsakinta da ta wanke tare da barbad’a masa gishiri kad’an, tun kafun ya dafu ta soya musu manja . Tana gamawa har wani murmushi take saki , cikin wani medium tray ta juye musu d’an malelen , ta saka manja , tumatur , cucumber , da albasa , sai tabi kansu da wani irin yaji me shegen dad’i da AMMA ta daka , tun kafun ta faraci har ta fara had’i yar miyau ita kadai.
Direct d’akin Amma ta wuce lokacin tana zaune daga kan carfet , da sallama ta shigo cikin d’akin , itama Amma fuskar ta d’auke da fara’a ta amsa mata , d’an malelen Eshaal ta ajje mata a gabanta , “ Amma ina zuwa yanxu zan dawo “,
Cewar Eshaal, bata jira cewar AMMA ba ta fita cikin d’akin da Sauri . Cikin ‘kan’kanin lokaci kuma ta dawo d’auke da wani tray din da ban , cikinsa lemo ne da ruwa da ta d’akko musu “ AMMA yau d’an malele nake sha’awar sha , shiyasa na yi mana shi yanxu , and plx AMMA karkice mun azumi kike dan yau ba Monday bace kuma ba Thursday bane , Dan Allah kisha kinji” murmushi Amma tayi mata ta saka hannu suka soma shan d’an malelen, lokaci zuwa lokaci Eshaal tana bata labari masu dad’i dan tayi dariya , ganin tana ‘ko’kwarin kwarewa ne yasa AMMA dakatar da ita “ ya isa haka Eshaal ya kamata ki dena magana idan kina cin abinci kinga yanxu ma kin kusa kwarewa.” Insha Allah AMMA “ cewar Eshaal.
Adaidai lokacin da suke tsaka da Shan d’an malelensu a Daidai lokacin su kuma su Baby suka dawo gidan, tacı black abaya da wani ba’kin glass da ta saka akan fuskarta , sai faman ya tsine fuskar take musamman yadda take tauna cin güm d’in bakinta . Bata tsaya d’aukan siyayyar taba tayi wucewarta . Tana shigo cikin falourn ta tarar da bakowa , har wajan kitchen baby ta le’ka amma bata ga Eshaal ko AMMA ba , bakinta ta ta’be zata wuce sai kuma ta dakata tare da nufar d’akin Eshaal , nan ba still bata ciki , cikin Sauri baby ta nufi d’akin AMMA tare da banka ‘kofa , da Sauri Eshaal ta juyo saitin ‘kofar , itama AMMA kofar ta kalla tana cire hannunta daga kan abincin .Wani irin sallallami BABY ta saka da ‘karfi kamar wacce taga wani mugun abu “ Mommy , Mommy kina ina ?”, muryar momy sukaji tana cewa menene ya faru baby na ko sun ‘kara yi miki wani saban rashin kunyar ne…” itama dakatawa tayi tana bin su Eshaal da kallo “ munafukan Allah abunda kuke yi kenan? Wato idan mun fita zuwa kuke ku satar mana abinci batare da sanin mu ba ? Uban wa ya baku damar ta’ba mana kaya wato har da d’aukar lemo da ruwa tunda ga gidan ubanku ko? Halin matsiyata a jikin ku yake kenan ko ?” Da Sauri Eshaal ta girgiza mata kai “ momy babu ruwan AMMA a ciki , hasalima ni ce na dafa na kawo mata babu laifinta a ciki.” A zuciya momy ta shigo cikin d’akin “ dan ubanki zaki rufe mun baki ko sai na gurza miki shi da bango? Duk salan iskanci da bari ta koya miki shine har kike da zarar fad’amun babu ruwan ta a ciki?” Sun kuyar da Kai ‘kasa AMMA tayi amma kwata kwata yanayin face d’inta be canza ba , a hankali ta furta “kiyi hakuri “ dogon tsaki Momy taja “ muna fuka daman kullum abunda kika iya kenan ayi hakuri ayi hakuri , banzaye kawai dangin matsiyata ,“ tana kai ‘karshen zancanta ta juya , itama baby cikin ta’be baki ta kalli Eshaal “ ki tashi kizo ki jera mun kaya na a cikin kwaba , idan kinga dama kuma ki zauna karkiyi , dan gin matsiyata” tana kai ‘karshen maganarta itama ta juya tana banko musu ‘kofa. Fashewa da kuka Eshaal tayi , wannan cin mutunci har ina dan kawai ta sha d’an malele shine suka cancanci wannan wula’kanci? Lallashinta AMMA ta soma “ kar kisaka wannan abun cikin ranki , komai me wucewa ne , kinji ? Ki goge hawayenki ko so kuke su ‘kare kirasa na kuka ranar Auranki?” ‘Boye fuskarta Eshaal tayi tana goge face d’inta , time to time kuma tana murmushi Sabida maganar AMMA ita da bata da ko da saurayi ina taga mijin aure ? Murya a sanyaye itama ta furta “ AMMA dan Allah kiyi hakuri akan abunda su Baby suke miki?” Girgiza mata kai AMMA tayi “ karki da mu ni babu abunda sukai mun, ya kamata ki tashi ki bita , kar ta sake miki wani abun, ni ki bari zan kwashe kwanukan” da Sauri Eshaal ta girgiza mata kai “ No AMMA be kamata ina wajan kice zaki kai ba , kawai kiyi zamanki ki huta Sabida kar ciwan ‘kafarki ya tashi kinji ?” Murmushi AMMA ta sakar mata “ Allah ya albarkaci rayuwar ki , ya banı ikon sakaki farinciki kamar yadda kika sani “, da Ameen Eshaal ta amsa lokacin da take kwashe kayan da har taji d’an malelen ya fita a ranta.
Tana kaiwa kitchen d’akin Baby ta wuce gabaki d’aya ta har gitsa d’akin shigowarta dan kafun su dawo saida Amma ta gyara mata , tana kan gado hannu d’auke da wayar ta , ga lemo da take sipping, kunnanta kuma pod ne da alama wa’ka take ji sabida yadda take gyad’a kanta , Eshaal bata ce mata komai ba ta fara kimtsa mata d’akin Sabida kwana biyun nan neman abun fad’a Baby takeyi, tana gama gyara d’akin kayan siyayyar da su baby sukai ta fara jera mata bayan uban tulin kayan Baby da ta ‘kara gyara wa , kana kallansu kasan da gangan kuma baby ta ‘bata su, tun da ta soma gyaran baby take neman hanyar janta da fad’a amma ko kusa Eshaal bata kula taba , tana gamawa tayi wuce wat ta itama batare da ta kula taba.
✨✨✨✨✨✨✨
*NEW YORK*
11:45am Abla ta farka daga baccin da ya d’auke ta , bakinta d’auke da adduar bacci ta soma bud’e idanuwanta da Suka d’an kunbura, lokaci d’aya kuma ta lumshe su ta sake bud’ewa tana mikewa zaune “ Yah Allah Yaushe barci ya d’auke ni haka ?” Cewar Abla lokacin da Mike tsaye , Daidai gaban mudubin d’akin ta tsaya tana bin fuskarta da kallo , sai a lokacin ta tuno da zafin da d’an yatsan ta yake mata , cikin Sauri ta tsugunna ta shafa wajan , a hankali kamar me rad’a da wani ta ta’bile bakinta “ mugu kawai , Allah sai ya sakamun tsabar mugunta harda takan d’an yatsa Sai ya wani dunga d’aure fuska kamar bread, ai ko shi bread yana fara’a tunda yana da dad’i , me fuskar tuwo kawai” ya ‘karasa tana turo bakinta kamar da wani take . Face d’inta ta wanke lokacin da ta kalla Agogo , bata zauna a cikin d’akin ba ta sakko down stairs . Bobo ne zaune kan kujera sai uncle da prince , har ‘kasa Abla ta tsugunna ta gaishe da uncle kafun ta kalli yaya bobo shima cikin fara’a ta gaishesa “ har kin tashi daga baccin Kenan ?” Kanta Abla ta jinjina masa tana murmushi kafin ta juya Side d’in prince shima ta gaishesa , da murmushi akan fuskarta ya furta “ fine lil sis , kinga tun da wuri little ya saka a miki abinci ya kamata kici yanzu” d’ayan side d’insa ta duba taga little d’in baya wajan fahimtar hakan yasa ya furta “ karki damu little yana d’akin yaya big boss yana bacci but nasan any moment from now zaki gansa”, tunda ya ambaci Big boss taji zuciyarta ta buga da ‘karfi daurewa kawai take shiyasa a hankali ta furta “ okay “, har zata mi’ke sai kuma ta fasa ta fuskanci su bobo da suka zuba mata ido, kamar zatayi kuka ta furta “ Nagode sosai, Allah yasaka da Alkairi, Allah ya saka muku da mafificin Alkairi, Allah ya dauwamar daku cikin farin ciki, Nagode sosai.., “ zata cigaba da adduar bobo ya katseta “ ki dena wannan godiyar , we’re all family now ! Banaso kinji ? Ko so kike little ya sakko ya saka mana kuka yace mun ta ‘ba masa lil d’insa ?” Ya ‘karasa yana d’an zaro mata ido , murmushi ne ya kwace mata lokaci d’aya ta furta “ Ah’ah “ shima fuskarsa cike da murmushi ya furta “ Good ! Now yaya prince a bawa lil d’in mu abinci “ mi’kewa tsaye prince yayi kafun ya furta “ Now” tray din abincinta ya dakko mata ya kawo mata har inda take , da kanshi yayi serving d’inta , cikin d’an tsokana ya furta “ yaya naga alama lil d’in nan ta fara sabawa da abincin mu”, murmushi kawai Abla ta sakar masa tana kare face d’insa , “ don’t mind him daughter , ci abincin ki karyayi sanyi “ cewar uncle .
Balaifi ta soma cin abincin su duk da ba sosai ta iya ci ba amma ba kamar dama tunda yanxu bata Amansa , tana cikin ci taji muryar little yana furta “ my lil”, at the same time ‘kamshin turaransa ya daki hancinta , jikinta har ya soma rawa kad’an lokacin da ta d’ago face d’inta ta kalli saitin sa , da Sauri kuma ta sun kuyar da kanta ‘kasa tana wasa da spoon d’in hannunta , duk taku d’aya da yake kamar da bugun nunfashinta yake , addua kawai take karanto wa cikin zuciyarta , ganin suna ‘kara kusan to Inda suke “ lil sai yanzu kika tashi?”, cewar little yana katse mata rud’anin da ta jefa kanta , da Sauri ta jinjina masa kanta murya na rawa ta furta “ ehe..eh mn”, shima kansa little ya jinjina mata “ thank god kin fara cin abinci da d’ure zamuyi miki”, kasa magana tayi sai kifkifta idanuwanta da take kamar zatayi kuka , ta kasa d’ago eyes d’inta ko sau d’aya ta kalli direction d’insa gashi ya hana ta zo inda yake.
Tunda big boss ya shigo cikin falourn babu Wanda yayi wa magana har ya zauna akan kujerar da yake yawan zama , fuskarsa gabaki d’aya ba annuri a tattare dashi , cikin nutsuwa yake danna wayar hannunsa , “ yaya sannu da zuwa”cewar prince , amaimakon ya amsa masa sai ya lumshe masa eyes d’insa kamar yadda ya saba , bobo da uncle kuwa face d’insa suke bi da kallo shiyasa ya ‘kara d’aure face d’insa .