’kofar kad’an , a hankali ta shiga cikin d’akin bakin ta d’auke da sallama , da Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa ganin sa sanye da Singlet sai dogon ba’kin wandon jikin sa , sau d’aya ya kalleta ya d’auke eyes d’in sa , tun kafin tayi magana ya d’an nuna d’akin da hannun sa , kamar Wanda aka saka dole ya furta “ Ki gyara mun”, be jira jin amsar taba ya shige cikin dressing room d’insa , bin bayan sa da kallo Abla tayi tana hararar sa ‘kasa ‘kasa ,ganin bata da wani za’bin yasa ta ajje coffee d’in hannun ta ta soma gyara masa d’akin , mistakenly bata san ganin ya akai ba , sai ganin light d’in d’akin ya d’auke gabaki d’aya , a mugun rikice Abla ta kwalla ihu, lokaci d’aya mafarkin da tayi d’azu yana ‘kara dawo mata cikin kai , ga gudun d’akin da gabaki d’aya ya ‘kara hautsina ta , almost 2 minutes sai faman ihu Abla take gabaki d’aya ta birkita kanta , ita kanta batasan me taneyi ba , ji tayi an finciko ta , lokaci d’aya Big Boss ya kunna light d’in da kashe , wani ihun Abla ta saki tare da sulalewa ‘kasa a sume , Sabida yadda tayi arba da ‘ka’k’kar far damtsen hannun sa ga shi ko riga babu a cikin sa . ‘Karamin tsaki Big Boss ya ja ganin yadda ta sume, a hankali ya soma bin d’akin da kallo gabaki d’aya Abla ta ‘kara binkita shi , hatta saman bed d’insa gabaki d’aya ta cukur kud’asa. Lips d’insa ya taune kad’an tare da komawa cikin dressing room d’in sa , almost 10 minute yayi a ciki kafun ya fito har lokacin Abla tana kwance a ‘kasa , ruwa ya d’akko mana sanyi ya soma zuba mata a fuska , a firgice Abla ta farka sabida ruwan da taji a kanta , har lokacin be dena zuba mata ruwan ba sai da ya juye mata shi gabaki d’aya a jikinta .
“ Just 10 minutes na baki ki gyara abunda kika ‘bata , sannan ki d’auki dirty legs d’inki and leave this place immediately “ ko kallansa Abla batayi ba Sabida abunda yayi mata , da tayi niyar barin d’akin saidai in kashe ta ne yayi sai kuma ta fasa , ganin ya d’auki system d’insa ya bar cikin d’akin. Cikin hanzari ta soma gyara masa d’akin, hawayen da bata san na mene ne ba suna sakko mata cikin idanu, tana gamawa ta fito daga cikin d’akin sabi sanyin da takeji bakinta har rawa yake . A falour ta tarar dashi yana operating system d’insa , batare da ta kallesa ba ta furta “ na gama “ har ta wuce ya dakatar da ita , cikin wani black wallet me shegen kyau ya d’auko wani paper note na kud’i guda d’aya ya jefa mata, ko arzi’kin kar’ba da hannun ta bata samu ba , cikin ta’be baki ya furta “ For your work”, kallansa tayi tare da kallan kud’in da yake fad’i a ‘kasa , ji tayi hawaye na shirin zubo mata tayi saurin had’iye su , hannu ta saka ta d’auki kudin lokaci d’aya wani murmushin ta kaici ya fito mata , ko uffan bata kuma ce masa ba ta fice daga falourn, kusan saura kad’an suci karo da Bobo da yake ‘ko’karin shigo cikin d’akin, sau d’aya ya kalleta ya girgiza kai , cikin tausasa murya ya furta “ ki je ki canza kayan jikin ki , kar mura ya kama ki , nan da 2 hours ki same ni a garden “ a sanyaye Abla ta furta masa “Tom “ , shi kuma ya wuce falourn Big Boss .
“ Na d’auka kayi accepting nata ? Why please Dude? “ cewar Bobo Lokacin da yake shigowa cikin falourn , ko sau d’aya Big Boss be d’ago ya kalle saba ya cigaba da abunda yake , sama Bobo yayi yana ‘kara fuskantar Big Boss “ magana nake maka fa , why are you treating her like this ? Yaushe zakayi accepting d’in ta as a family of this house ?”da kawa tawa Big Boss yayi cikin ido ya kalli Bobo ,” She will never be !” , d’an murmushi Bobo yayi kafin ya furta “ Really ? Nasani Kai ma kasani , da aiko ta akai dan ta cutar da mu da a tun ran farko zamu gane , da bazata ta’ba yin kwana d’aya a cikin gidan nan ba , please ka sassautawa yarinyar nan , duk da bansan labarin taba nasan itama ta sha wahala a rayuwar ta” d’an ta’be bakinsa Big Boss yayi batare da ya sake cewa komai ba , shima Bobo mi’kewa yayi tsaye yana kallan Big Boss , “ Bana so kayi abunda zai zamo maka matsala nan gaba , i know you very well , bansan menene ka ke shiryawa ba , but please don’t hurt her “, yana kai ‘karshen maganar sa ya bar falourn , shima Big Boss ba tare da damuwa da abunda Bobo ya fad’a ba ya cigaba da aikinsa.
Kamar yadda Bobo ya umarce ta , wajan ‘karfe 12:10pm ta nufi garden d’in, a zaune ta tarar dashi cikin wata runfa me kyau , ga kujerun zaman sha’katawa suma a wajan , gaban sa wasu drinks d’in da alama sha yake sabida yadda ya nuna a cikin d’aya daga cikin cup d’in wajan , yana ganin Abla ya sakar mata murmushi tare da nuna mata wajan zama . Jiki a sanyaye Abla ta zauna gabaki d’aya ta tsargu sabida batasan akan me yake nemanta ba , shima ya fahimci hakan daga reaction d’in ta , wani murmushi ya ‘kara sakar mata “ karki damu baki mun laifin komai ba , “ itama Abla murmushi ta saki ganin ya gano ta , book d’in hannun sa ya ajje yana fuskantar ta da kyau “ Nasan kin yi mamakin dalilin kiran ki da nayi ko ?” Kanta Abla ta jinjina masa , “ karki ‘kullace sa akan abunda yake miki, and karki tunanin tsanar ki yayi , its not like that”, d’an kallan sa Abla tayi dan bata fahimci maganar sa , wani murmushi Bobo ya saki kafun ya furta “ Big Boss ! Yeah Big Boss nake magana , ba mugu bane kamar yadda kike tunani zan iya cewa he’s the best soul ever, yana yin rayuwane ya mayar dashi hakan ba wai ke kad’ai ba , kowa ma hakan ne , idan baka san halinsa ba , bazaka ta’ba sanin ya yake ba ,” yana kai ‘karshen maganar da yayi shiru , Abla kuwa tunda ya fara yaban Big Boss ta d’an ta’be baki cikin zuciyar ta “ Wannan mugun ne zaka ce yana da kirki mutumin da be san komai ba a rayuwar sa sai mugun ta “ katse mata tunanin ya yi tahanyar ci gaba da magana ,” Nasan zaki yi mamaki maganganu na “ ya ‘karasa yana kallanta “ lokaci kawai zaki basa , he will trust you too! Yana da dalilin da yasa baya yadda da kowa , bawai sabida yana tsoran za’a cutar da shi ba , No ! Yana yin komai ne for his family, Little kamar d’an sa haka yake ,no matter abunda zai masa , ya fishi jin zafin” d’an ‘karamun dariya Bobo yayi , “ He’s a bit arrogant sometimes i think, but he’s the best brother i have ever in my life , farin cikin family d’in sa shine na farko a wajan sa “ shiru Bobo yayi lokaci d’aya mood d’in sa ya canza , lokaci ya kalla kafun ya sakar mata murmushi kad’an “ idan lokaci yayi zaki san komai amma kakki ‘kulla ce sa please “shiru Abla tayi masa sai kallan sa da take , mi’kewa tsaye yayi yana d’aukan wani ‘karamar waya dake kan table d’in wajan “ zamu cigaba wata ran yanzu ya kamata ki koma cikin gida okay ?” Itama mi’kewar Abla tayi tana furta “ Na gode sosai Yaya Bobo “ , kansa ya jinjina mata “ its okay “ , bata kuma cewa komai ba ta juya , sai da yaga ta ‘bacewa ganin sa tukunna ya saki wani shegen murmushi, cikin dariya dariya ya furta “ Dude”, dai dai lokacin da ake kiran sallah , shiyasa ya bar duk abunda yake ya nufi masallacin gidan.
Abla taba komawa cikin d’aki Alwala tayi , tayi sallar azhr d’inta , kud’in da Big Boss ya jefa mata ta d’auka tana ‘kara bin ta da kallo , lokaci d’aya taji ranta ya soma ‘baci, “ ‘kazama ! Villager “ shine ya ‘kara fad’o mata cikin rai, murmushin ya’ke Abla ta saki tana girgiza kanta kad’an. Ganin tana ‘ko’karin sawa kanta dawu ta ajje tunanin komai a gefe ta fara duba books d’inta na makaranta.
Da daddare ma hakan ne ya faru , suna zaune su hud’u a falourn daga ita sai Little , prince sai kuma Uncle , tare sukai dinner d’in su , su hud’u gwanin burgewa , suna gamawa suka dawo falourn suna hiran su , Abla sai data daidai ci Big Boss ya kusa shigowa gidan ta gud’u d’aki abun ta .
**** MONDAY
Yau ya kasan ce Monday , da wuri Abla ta shirya cikin uniform d’inta, tana fitowa gabaki d’aya su Little sun tanadar mata breakfast d’inta , ita kad’ai taci banda su sannan suka had’a mata wani box shine na kayan za’ki, yau basu bita makarantar ba , tana fitowa madam sarah ta kar’bi school bag d’inta , Abla zata hanata Madam sarah tayi saurin bud’e mata ‘kofa , tazo zata karfi chocolate box d’in hannunta Abla tayi saurin dakatar da ita , a haka motocin su suka bar cikin gidan , cikin sa’a kuwa bata had’u da Big Boss ba , hakan ba karamun dad’i yayi mata ba kuwa.
Tana shiga school ta tarar dasu Fanan a class duk da yawanci kad’an ne wanda suke ciki. Hugging d’in juna sukai gabaki d’aya su ukun, kafun Abla ta samu seat ta zauna , “ kin kusa fara cin dukan makara fa “ murmushi Abla ta sakar wa fanan da tayi maganar “ amma kece zaki yi dukan ko ?” Ido d’aya Fanan ta kashe mata kawai , “ Ni kuma gaskiya sai dai naciki tara babu wani duka “ , hannu Abla ta mi’ka mata “ oya give me five “ itama Eshaal ta d’ago hannun ta da niyar su tafa sai taga Abla tayi saurin janye hannun ta tana dariya , d’an hararar ta Eshaal tayi “ wallahi Allah dai ya hana mugunta “ wani gwalan Abla tayi mata tana furta “ Oho dai “ . Baby ce ta shigo cikin class d’in yadda take so calm yau sai ta bawa kowa mamaki , ga face d’in ta da mutum ya kalla yasan tana cikin damuwa, a seat d’in su ta zauna tare da kifa kanta , kallan Eshaal , Fanan tayi “ Me aka yiwa Baby ? Tun ran friday naga sauyi a face d’in ta gabaki d’aya batasan yiwa kowa magana, bata cewa a fita yawo yanzu ko music bana gani tana sawa , idan nace ta shirya mu fita yawo sai tace No”, ‘karamun murmushin Eshaal tayi mata “ Fanan nima bansan meke damun taba , tun ran Thursday take a haka , ko abinci bata ci sai taji yunwa ta isheta , duk lokacin da zan farka sai injita tana kuka , i try to asked her but tace mun bakomai “, shiru sukai gabaki d’ayan su , fanan zata kuma magana teacher ya shigo class d’in, fasa fad’an abunda take so ta fad’a tayi tare da komawa seat d’inta . Har teachers suka shigo suka fita Baby bata cewa kowa komai ba , itama Eshaal time to time tana kallan Baby, haka kawai taji bata san ganin ta cikin wannan mood d’in, ta fi san ganin ta a ‘yar rigimarta.
A na fita break yawan ci class suka fice kamar had’in baki yayi saura su hud’u , Abla , Fanan, Eshaal, sai Baby da ta sunkuyar da kanta . Kamar zasu wuce sai Eshaal ta nufi inda take , cikin taushin murya ta furta “Baby ?” Shiru Baby tayi mata batare da ta amsa ba , a karo na biyu Eshaal ta ‘kara furta “ Baby?” Uhm kawai Baby tace mata “ Me zaki ce na taho miki dashi ?” Cewar Eshaal , a hankali Baby ta furta “ Nothing Just go “ kallan juna Fanan da Eshaal sukai , sabida basu ta’ba ganin Baby cikin wannan condition d’in ba , alama Fanan tayi wa Abla ko zata yi mata magana , kanta ta jinjina mata gabaki d’aya suka dawo seat d’in , a hankali Abla ta furta “ Baby ?” ‘Karamun tsaki Baby tayi zata tashi tabar wajan Abla ta dawo da ita , ta bud’e baki zata yi magana itama Abla cikin fad’a fad’a ta furta “ shout up , me ke damun kine ?Tun d’azu ana so ayi miki magana kina yi wa mutane wula…” bata ‘karasa ba Baby ta fashe da kuka tana rufe face d’in ta , gabaki d’aya jikin sune yayi sanyi ganin yadda take kuka, cikin sanyin murya Abla ta furta “ kiyi hakuri banayi haka dan kiji haushi naba “, kukan face d’in ta Baby ta shara tana kallan su da itanuwanta da sukayi jajawur har sun fara kunbura sabida kukan da tayi , a hankali ta furta “ Ni ba kuyi mun komai ba , just go and leave me alone “, hannunta Abla ta kama cikin tausasa murya “ kinsan me ? “ cewar Abla, girgiza mata kai Baby tayi tana ‘kara share hawayenta , ya’ke kad’an Abla tayi sabida abunda zata fad’a “ Nima ina da Sister kamar ki , Sunan ta Arwa “ sai kuma tayi shiru , gabaki d’aya idanuwa suka zuba mata , a hankali ta furta “ itama batajin magana kamar , ko me yake damun ta bazata bud’e baki tayi magana ba sai dai tayi ta kuka , tun ina lallashin ta, har na soma yi mata fad’a , amma kin san ita tana da sau’kin kai bakamar keba , idan na tanbayeta abu tana fad’a mun, kema ko bazaki fad’awa kowa damuwar ki ba , ki dunga ro’kan Allah ya sassauta miki abunda ke ranki zaki ji dad’i kinji?” A maimakon Baby ta amsa mata sai jefo mata mata tanbayar “ Tana ina ?” Kwalla ce ta so tarar wa Abla cikin sauri ta goge tana ‘kara ‘ka’karo murmudhi akan face d’inta “ Ta mutu, Arwa ta mutu , ta tafi ta barni” gabaki d’aya sai suka zuba mata idanuwa cikin su kuwa har da Baby da take goge eyes d’in ta , kamar zatayi kuka ta soma magana “ Kusan kwana hud’u kenan ina yin wasu mafarkai, wasu mutane mace da namiji suna ta ambatan sunana , ko wannan su yana mi’ko mun hannu akan na cece sa , gefe d’aya kuma kamar suna mun fad’a , musamman muryar na mijin da yake cewa ni ba yarinyar kirki bace , na canza halina ko kuna babu shi babu ni,bansan ko su wanene ba , amma kusan kullum sai nayi mafarkinsu , duk lokacin da suka mi’komun hannun dan na cece su sai naga wasu irin gizo gizo ba ‘ka’ke , jikin su duk jini suna tunkaro inda nake , kullum nayi mafarkin nan sai nayi kuka musamman yadda gizo gizon suke tsoratar dani sai naji kamar suna inda nake, duk lokacin da na kulle idanuwana muryar mutanan nan nake ji, duk da bansan ko su wanene ba amma sai nake jina jima da zan dauwama a inda suke , ina san ganin su ko sau d’aya ne , zuciya ta tana mun ciwo”, ta ‘karasa tana fashewa wani saban kukan . Wani iri Abla taji cikin zuciyarta ‘kafarta kamar ana mata tafiyar tsutsa , lokaci d’aya mafarkin da tayi itama ya fad’o mata , bata san dalili ba , haka kawai taji zuciyar ta na bugawa , kukan Baby ne yasa ta kawar da nata tunanin, suma face d’in su Eshaal duk ya canza kamar zasuyi kukan , murmushi Abla ta sakar mata , “ ki dunga yawai ta addua , mafarki ba gaskiya bane kinji? Duk lokacin da zaki kwanta bacci ki tabbata kinyi Alwala sannan ki saka addua insha Allah zaki dena mafarkin “ hawayenta Baby ta share tana jinjina mata kai “ Na gode “, zaro ido Eshaal da Fanan sukai ganin yau Baby tana yin godiya , ganin yadda suke kallanta ne yasa ta banka musu harara, gabaki d’aya kuma sai suka saka dariya , seat d’inta Abla ta koma ta d’auko chocolate box d’in ta , “ Nasan yanzu za’a dawo class , lets just have this chocolates” Kallan Eshaal, Baby tayi a hankali ta furta “ kiyi hakuri!”, a tare gabaki d’aya suka had’a baki Wajan furta “ Awwwn..” cike da tsokana Fanan tazo dai dai kan Baby ,” ya Allah idan aljanune suka saka Baby ta shiryu Allah yasa su ‘kara saka ta , ta shiryu idan taki shiryuwa kuma su lakad’a mata duka ,” yanxu ma gabaki d’ayanzu sukai a hankali Baby ta furta “ Am sorry Eshaal , duk abubuwan da nayi miki a baya , idan banyi miki ba bana jin dad’i a raina sai inji kamar zan zauce shiyasa bana jin dad’in idan ban miki ba “ Murmushi Eshaal tayi mata kafun ta furta “ zan yafe miki with just one condition “ shiru sukai gabaki d’aya su suna jiran abunda Eshaal zata fad’a “ har sai kin nemi yafiyar AMMA”, kanta Baby ta jinjina mata “ yes I have that intention”. Ko mintu 3 basu ‘kara ba