Almost 30 minutes Abla tana baccinta a bakin ‘kofar Wajan , a hankali ya bud’e kofar d’akin , sanye yake cikin ba’ka’ken kayan Valentino , tundaga kan rigar jikinsa da shape d’in wuyanta ya fito sosai kamar V har zuwa wandan jikinsa duk ba’ka’kene, hakan ya bawa faffad’zan farin ‘kirjinsa fitowa sosai tare da sarkar diamond din wuyansa , gabaki d’aya fuskar Big Boss babu annuri akanta hakan ya bawa ba’kin sumar gashin kansa fitowa sosai musamman da ta sake shan wani gyara na musamman har wani Santsi take yi. Yadda yake sanye da black d’in kaya Haka takalmin ‘kafarsa yake black colour ‘kirar Leather loafer , hakan ya bawa farar fatar ‘kafar sa fitowa kad’an, gabaki d’aya hannayensa ya saka cikin aljihu , kallo d’aya yayi wa Abla ya d’auke kansa , mamakin aljanun yarinyar yake , tayi laifi sannan ta soma bacci ?” Red lips d’insa ya d’an tauna kad’an cikin nutsuwar sa da izzar da take yawo cikin jikinsa ya nufi medium size fridge dake gefe kad’an daga inda yake , kaloli hud’u ne a jikin fridge d’in , blue d’in ciki ya danna lokaci d’aya wani side na fridge d’in ya bude sai ga wasu manyan ruwa masu shegen sanyi da suka fara ‘kan’Kara fitowa , Daidai saitin inda take kwance ya nufa tare da bud’e bottle d’in bai tsaya bata lokaci a ya tuttula mata ruwan sanyin a fuska .
A firgice Abla ta bud’e idanuwanta sabida ruwan sanyin da ta ji a jikinta lokaci d’aya kuma ga sanyin Acn da yake ratsa mata jiki, ita kanta bata san lokacin da mayafin kanta ya zame ba , uban tulin gashinta ya fito sosai . Yadda ta gansa tsaye akanta yayi folding hannunsa yasa ta ‘kara shiga taitayinta , zuciyar sai bugawa take da Sauri sauri gashi tutaran da ta fasa gabaki d’aya ya ‘bata mata jiki shiyasa ta ko ina take jin ‘kamshinsa cikin hancinta. Gabaki d’aya takasa d’ago da fuskarta Sabida gudun had’uwa da tasa dan tasan mugun kallan tsanar da ya saba yi mata zata gani , tsoran ta d’aya ma karya ce sai ta biya shi kud’in turaransa, cikin kausashshiyar murya cike da natsuwarsa ya furta “ Are you mad ?yadda yayi maganar mutum sai yayi tunanin bashi yayi taba , kanta Abla ta soma girgiza masa dan bakinta yayi nauyin da bazata iya magana ba , ji take kamar wacce aka kulle wa bakin da gangan dan sosai yayi mata nauyi ita ka d’auki sai faman zaro eyes d’inta take sabida tasan bata da gaskiya . Hakan da tayi ba ‘karamun ‘kara tinzurashi tayi ba, shiyasa cikin ‘bacin rai ya d’aga hannunsa ya wanke face d’inta da mari da har saida taji d’igon fitsari akan pant d’inta still sai da ta d’auki wucin gadi kafun jinta ya dawo mata Daidai sabida bala’in da take ji ta shiga , neman kukan tayi ta rasa gabaki d’aya , cikin zafin rai ya dam’ko gashin kanta da batasan lokacin da ta ri’ke masa hannu ba Sabida azabar zafin da ya jiyarci ganta , muryarta kamar zata shid’e ta furta “ Dan Allah kayi hakuri, Dan Allah , Dan Annabi, yaya little ne yasa na gyara maka d’akin bansan kana ciki ba.” Tsaki ya saki tare da hankad’ata a maimakon ta fad’i Daidai sai ‘kugunta ya bugu, da ‘karfi ta saki ‘kara sai kuma tayi saurin toshe bakinta dan ba’karamin buguwa ‘kugunta yayi ba , sosai ta yi ‘ko’karin had’iye kukanta dan ba ‘karamun buguwa tayi ba awajan, wani ‘karamin cutter ya je fo mata , batare da damuwa da condition d’in da take ciki ba ya nuna gashin kanta cikin yatsına fuska “ yanke gashin kanki” cikin azama Abla tayi saurin waye masa idanuwanta , har ta manta da zafin da ‘kugunta yake mata , gashin da su Little suka kashe masa kud’i sosai d’azu wajan gyara wa , tun da take ba’a ta’ba gyara mata kai haka ba , shiyasa tun da suka dawo daga saloon d’in taji tana ‘Kaunar ganin kayanta amma yanxu lokaci d’aya yace ta yanke , kamar zatayi kuka ta bud’e baki zata ‘kara bashi a hakuri a karo na biyu kallan da yayi mata yanxu ne yasaka ba shiri Abla ta d’auki cutter d’in hawaye sam sun’ki tsaya wa haka ta soma yanke uban tulin gashin kanta da hannunta . Sai da ya tabbatar da ta yanke rabi da kwatan gashin sannan ya bar wajan yana Jan wani ‘karamin tsaki.
“ For my perfume just 1 week na baki duk inda turarena yake ki dawo mun dashi , if you dare to this obey , next time ba gashin kanki zance ki yanke ba , d’an ya tsan hannunki zansa ki yanke , get lost stupid” ya ‘karasa a d’an tsawace . Cikin sauri ta mi’ke tsaye hannunta ri’ke da dogon gashin kanta da ta yanke ,ita kanta batasan ya akai ‘kofar ta bud’e ba , tana ganin ta fita daga cikin bedroom d’insa ta bar part d’insa a guje .
Allah ya temaketa babu kowa a cikin falourn ,shiyasa bata tsaya ba ta wuce bedroom d’inta , tana shiga ta jefar da mayafin hannunta , gashin hannunta da ta ri’ke ta jefar shima tare da ‘karasawa gaban mutubi, gefen face d’inta da big boss ya mata sosai wajan ya d’an tashi yayi ja , ga gün ta gashin kanta da ko tufkeshi tace zatayi bazai tsayuwa ba , kamar wata ‘kamar ya rinya ta zube ‘kasa ta soma birgima ita kad’ai ga kuka da take yi duk a lokaci d’aya .
Ya jima a ‘kasa tana kuka har saida taga sallar la’asar na ‘ko’karin wuce ta, ta tashi tana turo unique cute lips d’inta, a haka tayo alwala tayi salla ranta duk ba dad’i , babu abunda ya fi tsaya mata kamar yanke gashin da yasa tayi, tana ‘idar da sallan ta kwanta a kan gado kamar wata me zazzabi yau ko addua bata tsaya tayi kwakkwara ba.
**** 8:10pm yau takai wa simba abincinsa, tunda ta je ‘kofar wajan take hararar ‘kofar kamar Itace ta sa a aske mata gashin kan nata , cikin masifa masifa Abla ta jefa wa simba abincinsa tana binsa da wani irin harara duk da balefi ta rage tsoransa yanxu sosai , ta jima tana harararsa kamar idanuwanta zasu fad’o ’kasa , sai da ta gama harararsa sannan ta ja wani ‘karamin tsaki tana barin wajan. “ yadda yake mugu daman ai dole ya raini muguwar halitta, ga fuskarsa kamar anna kiyar da aka buga a kwata , Allah dai zai saka mun, kuma kayi wa turaranka dan yadda ka guntulen gashi wallahi babu wani kud’in turare da zan biya , sai shegen kyau kamar aljani “ita kad’ai take surutunta har ta wuce cikin gida .
✨✨✨✨✨
8:35pm su Big Boss suka fito daga cikin masallacin , shi kad’ai sai faman lumshe idanuwa yake , “ yaya bari na tafi Wajan little sister kaji?” Kansa Big Boss ya jinjina masa kawai batare da ya bud’e bakinsa ba , gabaki d’aya sai little da prince da kuma uncle suka koma cikin gidan banda Big Boss da Bobo . Cikin Sauri bobo ya ‘karaso Inda yake a tsaye cike da tsokana ya furta “ UGA da kansa , our humble Big Boss “, sau d’aya Big Boss ya kalleta ya d’auke kansa “
Haba mana my G wannan d’aure face da kayi mun kamar jira kake nayi magana ka kawo mun naushi ? Nifa na manta when last kayi ma murmushi , just d’anyi mun ko da ya ‘Kene mana “ ko kallansa Big boss beyi ba ya furta “ leave this place “, cikin Sauri bobo ya d’aga masa hannu “ maida wu’kar, we need to talk please , ina Alice?”Banza Big Boss yayi masa kamar be ji shi ba”please mana answer me ko sau d’aya ne , I know definitely His excellency ya kira ka time , and bazasu samu peace of mind ba , idan basu ga yar suba “ , dakatar Dashi Big boss yayi cikin I don’t care ya furta “ And so ?” Gashin kansa bobo ya ta’ba yasan halin Big boss da kafiya me tankwarashi kam sai Allah “ nasan you’re aware of hukuncin da nasa su LG su yi mata , nasan kasani sarai but why again kasa a d’akko maka ita ? And to a place da babu Wanda ya sani har yanxu ? Family d’inta sun shiga damuwa “ rai a ‘bace kamar a zuce Big Boss ya makawa Bobo wani irin kallo “su family d’in nata basu san da ta’bin haukan kanta ba ? If you dare ka ‘karamin maganar wata so called aljana a wajan you will see how I will maltreat her sai naga Wanda ya isa ya kwace ta ,not even her father “, har ya juya kuma ya ‘kara kallan Bobo cikin ido “ if not baka gida , ko prince what do you think will happen to him? Zaka d’auki blame d’in abinda zai samu little ? Hey not even so called that people ( his parent)”, yana kai wa ‘Karshen maganar sa ya bar wajan yasan idan ya tsaya ransa ne zai ‘baci and every thing can happen”, Murmushi kawai bobo ya saki Daidai lokacin da wayar hannunsa tayi flash alamar kiran waya, “CHIEF “shine sunan da ya fito kan wayar sa , cike da girmamawa Bobo ya d’an ’kame dukda mutumin baya kallansa , kusan mintuna biyu kafin shima ya bar wajan har lokacin kuma be kashe wayarsa ba .
****** Abla kuwa tun lokacin da su Little suka koma cikin gidan suke janta da hira , dukda yadda take tsoran had’uwa da ita dan yanxu kam ta bashi shugaban malintar mugaye tunda ya yanke mata gashin kan ta, duk yadda taso gudu little ya ‘ki bata wannan chance d’in dan dole ta zauna sukai hira tun bata sakewa har ta warware gabaki d’aya, basu wani jima sosai ba suka wuce dinning dan yau fruits kawai unclee yasa akai masa d’akinsa , shiyasa susu uku kawai sukai dinner d’insu, suna kammalawa little yaje Zaije d’akı ya dawo, Abla tana ganin haka ta gudu d’aki itama , tana Tuna’nın yadda zata Kai masa coffee batare da ta ganshi ba . Ita kad’a a cikin d’akin sai faman masifa take kamar yana kallanta , lokaci zuwa lokaci kuma bud’e drawer da ta ajje gashin nata sai kuma ta kalli Wanda yayi saura akanta , ji take da za’a bata dama itama da sai ta aske masa gashin kansa tass , batasan lokacin da maganar da take so tayi ya fito fili ba “ kuma wallahi kwalkwal zanyi maka kamar kod’ad’d’an farantin Zinariyya “, ita kanta maganar da ta fad’a ta bata dariya .
Ba ita ta sakko daga cikin d’akin ba sai wajan around 11 , lokacin gabaki d’aya babu kowa a falourn da alama ko wannansu ya koma part d’insa , Tuna’nı Abla ta soma akan ta tsaya ta kai masa coffee d’inne ko kuma itama tayi wucewarta dan a gajiye take yau , haka ta cigaba da Tuna’nın mafita , daga ‘karshe sai tayi deciding ta fara bashi coffee d’insa kar ya zuba mata kwando kwandon bala’in sa, Tun tana jiran dawowar sa har bacci ya d’auketa a cikin falourn.
Sai wajan ‘karfe 2am Big Boss ya shigo cikin gidan , yadda yaganta kwance akan kujera ne yasashi ya d’an ta’be lips d’insa kafun ya danna button d’in falourn , gabaki d’aya fitilun suka d’auke ya sama sai dum light mara haske , ko takan inda take be biba ya nufi part d’insa . karfe 3:20am fitsari ya farkar da Abla , lokaci d’aya ‘kirjinta ya buga sabida duhun da ta gani, da ita ‘karfinta ta kwalla ihu , tana faman dube duben hanyar guduwa , yadda take fusge fusge kamar wacce take ‘ko’karin ficewa daga cikin haryacinta, cikin kuka ta soma maganganun da ita kanta bata san me take cewa ba “ Duhu , Wayyo dubu banaso, banasan duhu, Wayyo Allah na , please wani ya temaka mun dan Allah,” bata fi mintuna biyu tana maganganu ba Abla ta fice daga cikin hayyacinta gabaki d’aya ga kanta da ya soma sara mata sosai , amma dukda hakan ‘ko’karin neman hanyar barin falourn take , cikin Sauri take ta zagaye d’akin tana ‘ko’karin guduwa amma Sabida yadda ta kasa kwantar da hankalinta waje d’aya yasa bata lura da haske kad’an d’in da yake wajan stairs ba , burinta taga ta fita daga Wajan shiyasa ko kula da inda take ta kawa bata yi , har ‘kafarta ta daki wani waje tayi baya baya zata fad’i, da hannu d’aya ya ri’ke mata hannun duk da kasancewar cikin duhune , Abla kuwa tunda taji an ri’keta ta ‘kara fashewa da kuka tana fad’in “ please ku kunna fitula , banasan duhu dan Allah “, be furta ko uffan ba ya kunna light d’in falourn , gabaki d’aya ta had’a gumi ga face d’inta da ya ‘baci da hawaye sosai , tana ganin haske tana soma a jiyar zuciya , ko uffan be ce mata ba ya juya ya bar wajan , itama cikin Sauri ta nufi d’akin tana sakin wani ajiyar zuciyar.
WASHE GARI
Tunda akai sallar asuba Abla bata koma bacci ba sai data gyara d’akinta sosai ta wanke toilet shima sannan tayi wanka cikin doguwar ‘bakar riga har ‘kasa , kamar tayi kuka duk lokacin da ta kalli gashin kanta ta gansa a aske , bata tsaya ‘bata lokaci ba yau ta kaiwa simba abinci har cikin d’akinsa , ganin be motsaba yasa ta ‘kara tura masa abincin, nan ma still yana zaune ba kamar da ba da duk lokacin da aka kai masa abinci zai mi’ke ba , kamar wata mara gaskiya ta sand’a zuwa inda yake , a hankali kuma kamar me rad’a ta fury “Simba ? Simba ? Baka jina ? Ka tashi ga abincin ka nan karkasa a sakani wani punishment d’in dan Allah kaji?”ganin har lokacin be motsaba yasa Abla ta ‘kara matsowa inda yake dan yanxu bata tsoranshi sosai “ Simba ?” Nan ma still shiru simba be kula taba sai idanuwansa da yake motsawa , finger d’inta d’aya ta saka ta dankwali kansa sai ta daka tsalle tayi gefen ‘kofa, a karo na biyu still ganin be motsa ba ya ‘kara matsowa inda yake ta kara dan gwalar kansa , sosai ta matso inda yake tana furta “ simba ? Dan Allah ko zabura ne kayi, tsakanin da Allah kar me gidan ka yace guba na baka kaga jiya yasa na yanke gashi yau kuma ina tunanin hanci ko baci zai sa na guntule ,”’ita kad’ai kamar wata me iskokai ta furta “ Toh ko dai bashi da lapiya ne ? Oho Nidai nasan ban baka guba ba dan haka wallahi bazan tsaya a hukun tani ba “ ko da zata fito daga d’akin sai data le’ka wai sabida kar wani ya ganta tukunna ta wuce ta bar wajan, ita kad’ai sai mita take a cikin zuciyar ta wai simba ya mayar da ita yar iska , Sabida tana masa magana (🙄🙄Abla dole Big Boss yace kina da almatsu tsai akanki, daman zaki yana magana ? Ko kema kinsha abunda yasha ne ?🙄🙄 Team Abla wallahi kuyi mata fad’a dan mu ba ruwanmu duka zata sha 🤭).
Tana koma cikin gida ta tarar da uncle shi kad’ai zaune a kan kujera, cike da girmamawa ta ‘karasa har inda yake ta gaishe dashi, “ uncle ina kwana ?” Da murmushi akan face d’insa ya furta “ Lapiya Lou daughter kin tashi lapiya ?” Itama Ablan face d’inta d’auke da murmushin ta furta “ Lapiya Lou Alhmdllh “, suna cikin zamansu Bobo shima ya fito , cike da girmamawa ta gaishesa shima , a Daidai lokacin da su little suka fito “ Sister yau har kin tashi ? Kwanda ma ki more baccinki na yau da gobe kafun ki koma school Allah , karkizo kina school kina lumshe musu idanuwa” cewar little , gabaki d’aya dariya suka saki Sabida abunda little ya nufa , kallan yaya bobo little yayi “ yaya ina yaya Big Boss yake ?” Harararsa bobo yayi kafin ya furta “ na siyar dashi , ina kasan kara ganin sa kaje kasuwa “, cikin d’an zaro ido prince ya furta “ kai….. yaya bobo, yaya big boss din zaka siyar ? Su kuma Victor da Anthony suna ina ?” Direct bobo ya bashi amsa da “ suma na siyar dasu” yanxu gabaki d’aya kuma dariya suka saki jin abinda bobo yace , cikin dariya dariya little ya furta “ ni fa yanxu ku dena sakani dariya sosai , sister zaki yadda na dunga rakaki school ?” Da murmushi akan face d’inta ta furta “ eh “ satar kallan inda bobo yayi yana d’an langwa’be masa “ yaya ai zaku dunga bari na ina raka sister makaranta ko?” Da bud’ar bakin prince shima sai ya furta “ Nima yaya please zan rakashi , tunda ba court zan dunga zuwa ba yanxu for a while “ cike da tsokana shima uncle ya furta “ Nima zan dunga rakasu “yanxu ma kusan tare sukai dariyar Sabida yadda sukamayar da abun joke , daga nan dinning suka nufa gabaki d’ayan sukai breakfast, sai da suka kammala su uncle suka dawo falour shi kuma bobo ya fita. Haka suka cigaba da hirarsu gwanin burgewa har Suka d’auko game sunayi.
12 nayi Abla ta koma d’aki ta d’auko system d’inta tana anfani dashi har lokacin sallah yayi , tana idar wa kuma tabi
Lapiyar gado ta kwanta .