x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 60 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 177001 words
  • 180000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 248

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tawace ni kaɗai, bakuma wai don bana kishinki bane yasa hakan tafaru ba a'a, ni kalan nawa kishin ba irin na wasu bane, inakishinki sosai, sai dai kuma kome acikin nutsuwa nakeyinsa, ke kinsan inasonki ina kuma kishinki " yaƙare maganar yana me lakace mata dogon hancinta.


Kukane yakuma ƙwace mata sai kawai tafaɗa jikinsa, ta rungumesa ƙam, shima rungumeta yayi yana shafa bayanta ahankali, haɗe da hura mata iskan bakinsa, acikin kunnenta.
Saida tayi kukanta sosai, kafun ta soma sauƙe ajiyar zuciya, cikin murya me sanyi tace.
"Kai na da banne Mijina, irinka basu da yawa acikin duniya, haƙiƙa nafi kowacce mace sa'a dana sameka, dakai kaɗai zan rayu har izuwa mutuwa ta, kaima ka rayu dani ni kaɗai kaji, bazan iya jure ganinka da wata mace ba bayanni, Ina maka son da bansan iyakarsa ba!"


Murmushinsa dake ƙara masa kyau yayi, haɗe da sanya iskan bakinsa ya hura mata fuska.


"Dake kaɗai Zan rayu Zahrah na, ni nakine ke kaɗai, amma idan kina kukan nan fa, dole zan ɗan yi ƙasa da idanuna, na hango wata, saina kawota ko wanke wanke ne tanayi mana ko, idan dare yayi kuma sai ina raba muku kwana ko..."


Bata bari yakai ƙarshen zancen nasa ba, ta muntsine sa aciki, saida yasaki wata ƴar ƙaramar ƙara, cike da shagwaɓa tace "Wallahi nidai babu ruwana dakai, idan dai har kace zakamin kishiya!"


Dariya yayi sosai haɗe da cusa kansa acikin ƙirjinta. "Ni na isa ma nayiwa ƴar sakalalliyar matata kishiya, amma bandai saniba wataƙila idan naga kin tsofe na miki!" yanzuma cikin zolaya yayi maganar.


Hannayenta tasanya acikin gashin kansa, tashiga ya mutsawa, hadda kai masa cizo a wuyansa. Sai da tayi masa buji buji da kayan jikinsa kafun ta ƙyalesa, gashin kansa ma gaba ɗaya ta hargitsa masa shi. Koda ta kawo masa abinci tare sukaci, yana kwance ajikinta itakuma tana bashi abincin abaki, ahaka har ya ƙoshi.


Kallonta yayi da idanunsa, dake tsumata kana yace "Namatsu abani ke Baby na, wallahi ina kewar ɗumin ki sosai, amma Hajiya gaba ɗaya ta kanenaye min ke, waidole saikinyi arba'in, Babyna kice tabarmu mu koma gidanmu kinji!" cikin yanayi na shagawaɓa ya faɗi haka.


Murmushi Zahrah tayi, haɗe da sanya hanu ta shafi kumatun sa, cike da ƙaunarsa tace "Kayi haƙuri Hubby, nima ina kewar sucking ɗinka, kuma ai bawai bazan dawo bane zan dawo fa" tafaɗi hakane don kawai ta kwantar masa da hankali.


Ya buɗe baki zaiyi magana kenan muryar Hajiya ta karaɗe kunnuwansu, inda take cewa.
"To iyayen rashin kunya, saika tashi katafi dare na ƙarayi, ke kuma miji daɗi, ga yaronki nan, abincinsa yakeso ki basa." kunyar Hajiya ne yakama Zahrah, haka ta amshi yaron kanta a ƙasa.
Doctor kuwa turawa Hajiya baki yayi, haɗe da cewa "Hajiya zantafi, amma kiɗanyi haƙuri ba yanzu ba mana"


Baki Hajiya ta sake tana kallonsa. "Sannu marar ta ido, wallahi saika tafi yanzu kuwa" Hajiya tafaɗi haka tana me kama hanunsa, haka yanaji yana gani ta fitar dashi daga ɗakin, Zahrah kam dariya taketa yi masa. Bayan ta shayar da yaron natane, tashiga toilet tayi wanka, doguwar rigan bacci tasanya, kana ta ɗauko diary'nta, rubutu tayi aciki, ta mayar dashi ma'ajinsa. Kwanciya tayi luf akan gado, cike da tunani kala kala bacci ya ɗauketa....


*** *** ***


Yau kwanansu 50 cif cif agidan Hajiya, sunƙara kwanaki 10 akan kwanakin gama wankansu, idan kaga Zahrah bazakace ita bace, sosai taƙara cika da kyau, fatarta ta ƙara haske, komai nata yasake cika, gwanin sha'awa, yau ne zata koma gidanta, tuni Dr.Sadeeq ya sanja mata kayan furnitures ɗinta, komai yasanya mata sabo, Hajiya kuwa tun tuni taketa ɗirka mata magunguna, haka Aunty Raliya ma ta dage sai bata wasu magunguna masu ƙarfi take, ita kuwa sha take abunta, wanda taji yanada bauri ne kawai take ajiyewa bata sha.


Wanka ta tsantsara cikin wata jar atamfa Super Exclusive, wacce taji ɗinkin riga da sket, sosai kayan ya amshi jikinta, zama tayi da kanta, ta tsantsarawa fuskarta kwalliya, sai gashi kuwa kyawunta ya ƙara bayyana, dogon gashinta dayasha gyara ta tubke da ribbon haɗe da kafa ɗaurin ɗan kwalinta me kyau, wani red ɗin takalmi tasanya aƙafanta me tsinin gaske, ɗan ƙaramin mayafi ja ta ɗauka ta rufe jikinta dashi, babu abun dake fita ajikinta, sai daddaɗan ƙamshi.


Yana tsaye ajikin motarsa dake fake a compound ɗin gidan, yaga fitowarta, kusan suman tsaye yayi. "Tabbas Zahrah me kyauce, tahaɗu tako ina, kullum ƙara kyau da cika take, lallai kuwa da yayi saken barin Zahrah, tabbas da yazama soko, marar rabo, samun mace kamar Zahrah, babban sa'ane daya samu a rayuwarsa" yafaɗi haka acikin zuciyarsa, yana hangame da baki wajen kallonta, baisan ma taƙaraso garesa ba, saida yaji ni'imtaccen ƙamshinta na ratsa cikin hancinsa.


Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da kashe masa idanunta ɗaya. "Ya dai kwalliyar tayi maka ne" tafaɗi haka tana me juya masa bayanta. Alaman yaganta da kyau.


Yawu ya haɗiye, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan hips ɗinta, baigama dawowa hayyacinsa ba, yakuma jefa idanunsa akan ƙirjinta, jikinsa na rawa ya jawota ya rungumeta.


Wani irin ajiyar zuciya suka sauƙe atare.
"I really Miss you Babyy!!" yafaɗi haka akasalance.


"Miss you too dear!" itama ta mayar masa da amsa cikin muryar raɗa.


Hajiya dake kallonsu ta window tasaki murmushi haɗe da komawa cikin falonta ta zauna, aranta tanayi musu fatan shiriya.


Saida suka biya ta JABI lAKE sukayi sayayya tukun kafun daga nan suka wuce gida.


Wanka ta sakeyi ta shirya kanta cikin wata irin fitinanniyar sleeping gown, wacce ta bayyana komai na surarta bata ɓoye komai ba, rigar doguwace har kusan ƙafa, amma kuma duk da haka itaɗin kamar babu take, kasancewarta shara shara. dogon gashinta ta sake a bayanta, haɗe da shafe jikinta da shu'umar Humra, wani sweet Lip Gloss tashafa akan leɓenta.


Yana zaune a falo yana danna laptop ɗinsa, ƙamshinta ne yafara kawo masa ziyara, lokacin daya sauƙe idanunsa, akanta sai da yaji wani irin shock ajikinsa, da sauri ya miƙe ya ƙarasa gareta. buɗe hannayensa yayi daniyar rungumeta, da sauri ta matsa gefe, tanayi masa dariya, haɗe da yin wata irin tsayuwa, wacce takusa zautar dashi.


Lumshe idanunsa yayi tare da sanya hanunsa ya jawota jikinsa. Ƙam ya rungumeta, sai gashi yana sauƙe ajiyar zuciya akai akai. Kallon juna suka shiga yi idanun ko wannensu ɗauke da tsananin sha'awar ɗan uwansa. Jikinsa na rawa ya kama lip ɗinta na ƙasa, yana tsotsa ahankali, jiyake kamar yanashan honey. da kanta ta zame rigar dake jikinta, ta faɗi ƙasa, take surarta ya bayyana, hmmm ba yau yafara ganinta ba, amma kuma ya zautu ƙwarai daganin surar jikinta, jiyake kamar ma baitaɓa kusantarta ba, sosai yayi missing ɗinta. Jikinsa na rawa ya ɗauketa suka wuce bedroom, tuni dama Asad yayi bacci, dama shi haka yake sam baida ƙiriniya, daya ƙoshi sai bacci, bakuma zai tashiba sai dai idan yanajin yunwa.


A yau ɗin ne suka sake tabbatar da cewa sunyi kewar juna, musamman ma Doctor Sadeeq da kusan cinyeta ne kawai baiyi ba, gaba ɗaya ya zauce, ya susuce, wasu maganganu yake wanda ita kanta batasan me yake cewa ba, saboda sun lula wata duniya ta musamman, wacce sukayi nisa acikinta basaji basa gani, kansu kawai suka sani. Aranan nan wata zuma suka shayar da junansu, wanda bazasu taɓa mantawa ba. Wannan ranan takasance rana ta biyu masu muhimmanci a garesu.


*** *** ***


Bayan wata 6........


America


Zufa ne keta ketowa ta goshinsa, gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa, kai komo yaketayi agaban labour room ɗin sama da 1 hour kenan yana abu ɗaya, jiyake kamar yasanya hanu akansa yaita ƙwala ihu. Ɗaya daga cikin Nurse ɗin dake kanta na fitowa ya nufi wajenta, da sauri idanunsa sunkaɗa sunyi jajur dasu. Murmushi Nurse ɗin tayi masa haɗe da cewa "Ina tayaka murna, matarka ta haihu, kasamu baby girl" wani irin sanyin daɗi yaji acikin ƙirjinsa, baisan lokacin dayayi sujja don nuna godiyarsa ga Allah ba.


Ana kaita ɗakin hutu, wata nurse tace yashigo ya karɓi babynsa, lokacin daya sanya hannayensa ya amshi babyn, wani irin kukane ya ƙwace masa, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskarta kuwa, bugun zuciyarsa ne ya ƙaru, saboda kokaɗan yarinyar bata kama da mahaifiyarta, durƙushewa yayi aƙasa, riƙe da yarinyar tasa yana kuka, hakan kuwa sosai yabawa likitotin mamaki.


Bakomaine yasa sa yake kuka haka ba, face tsananin danasani na rayuwar da yayi abaya da yake. yakasance mazinaci, mashayin giya. "Yanzu idan ƴarsa mafi soyuwa agaresa, tataso taji labarin abun da ya aikata a baya, wani irin kunya zaiji? mezaice da'ita idan ta tambayesa, meyasa yazamo haka?" tambayar da yayiwa kansa kenan, amma kuma baida amsa, baida kuma me amsa masa.


Rungumeta ya sakeyi tsam, acikin ƙirjinsa, ahankali yace.


"Kindawo gareni Zahrah, Allah yadawomin dake, Inasonki Inasonki, inamiki so na musamman Allah ya albarkaceki ƴata!!!" kiss ya manna mata akan goshinta, kana yazuba mata idanu, bazaiyi mamakin kamannin daya gani akan fuskar ƴartasa ba, saboda yasan ba aja da ikon Allah, kuma hakan ma wata rahamace da Allah yayi masa, Allah ya hanasa Zahrah alokacin dayaso, yanzu yakuma basa Zahrah alokacin dayaso, hancinta bakinta duka kalan nasa ne, amma kuma idanunta tamkar idanun Zahrah aka ciro aka sanya mata, kallon farko da yarinyar tayi masa, saida yaji tsikar jikinsa ya tashi, saboda gani yayi tamkar Zahrah ce dakanta agabansa. yana rungume da yarinyar ya ƙarasa gaban Afrah dake kwance akan gado tana kallonsu, ranƙwafowa yayi ya manna mata kiss akan goshinta, hanu yasa yashafi kumatunta, haɗe da cewa "Nagode ƙwarai Afrah, Allah ya miki albarka, bazan manta da wannan ƙoƙarin da kikamin ba, Inasonki"


Karo na farko kenan arayuwarta da taji kalmar nan tafito daga bakinsa akanta, "Inasonki" ta maimaita kalmar abakinta cike da mamakinsa.
Kansa yajinjina mata haɗe da sakin murmushi.


"Ki kwanta ki huta, nasan kinsha wahala sosai" yafaɗi haka yana shafa kanta.
Lumshe idanunta kawai tayi saiga hawaye nabin kan fuskarta. Hanu ta miƙa masa ya bata yarinyar, ba iya mamaki ba hadda tsoro saida ya bayyana akan fuskar Afrah, sakamakon ganin fuskar yarinyar ɗago kanta tayi ta kalleshi da sauri.


Kamar yasan me take tunani, murmushi yayi mata haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗanta. "Kada kidamu, Allah ne yayi ikonsa, Allah ne yadubeni yayimini rahama, sannan kuma ko da ace kowa zaiyi mamakin kamannin yarinyar ni bazanyi ba, saboda wacce take kama da ita, jinin jikinane, sannan kuma Allah yana da ikon yin komai"


Ajiyar zuciya kawai Afrah ta sauƙe haɗe da kafe yarinyar nata da ido, tabbas da badan taji ƙauna irinta uwa da ƴa akan yarinyarba, to tabbas da tace ba itace ta haifi yarinyar ba, Zahrah ce, shine aka sanja mata, aka ɗauki nata aka kaita wani gun, itakuma aka kawo mata wannar, a matsayin ƴarta. Rungume ƴar tata tayi, tanajin ƙaunarta aranta.
***


Suna komawa gida Zaid yayiwa Afrah kyautar zuƙeƙiyar mota, tare da kuɗi Naira Million 3 duk na murnan ta haifa masa baby ne, washe gari kuwa suka tarkato suka dawo Nigeria, abisa takurawan Mom ɗinsa. amma da anyi suna yace zasu koma. Aranan da aka haifa masa Zahrah aranan ya mallaka mata babban kamfaninsa na ƙera takalma, dake Italy, aranan kuma akasanjawa kamfanin suna zuwa sunan yarinyar, saɓanin da dayake sunan Zaid.


Tunda aka haifi Zahrah Zaid baibari kowa ya ɗauketa ba, inbanda uwarta, nan ma nono kaɗai take bata, idan yaɗauketa yashiga ɗakinsa da ita, kulle ƙofar yake da key gudun kada wani ya damesa, komai na duniya shiyake mata, wani irin so da ƙaunar yarinyar yake ji, wanda baitaɓa jin irin saba, akullum kallon Zahrah kawai yakeyiwa yarinyar. Irin soyayyar dayake yiwa yarinyar shike tsorita kowa.


Ranan suna kamar yanda ya alƙawartawa kansa cewa idan ya haifi ƴa mace sunan Zahrah zaisawa yarinyar, hakance takasance domin kuwa sunan nata yasaka, wato FATIMA ZAHRAH, koda Afrah taji sunan da ƴartata taci sai kawai tayi murmushi, ko kaɗan batayi fushi da faruwar hakan ba, saboda tasan albarkacin Zahrah itama zata samu soyayya ta musamman daga wajen Zaid ɗin, haka kuma albarkacin Zahrah ƴarta itama zata samu gagarumar soyayya daga wajen ubanta.


Nairori sunyi kuka a wannan rana, sosai Zaid yayi ɓarin kuɗi tundaga randa aka haifeta kawo yau dayake suna, dukiya kawai yake ɓararwa, tun abun nabawa Mom ɗinsa da Afrah mamaki, har suka daina mamaki, saboda zuwa yanzu sunsan soyayyar da Zaid keyiwa ƴarsa Zahrah ta wuce gaban kwatance, harta bacci akan ƙirjinsa takeyi.


(Sai haƙuri idan kunga typing error, Yau banyi editing ba, wai ina kukene masoyan Zaid, kwata kwata naga alama bakwa farinciki, ace matar Zaid ɗinku nada ciki, amma ku kasa nuna farincikinku, ashe soyayyar takuma, batakai zuci ba, haka team Doctor ma, kuma ashe soyayyar taku ta bogece, tunda anmasa haihuwa ko barka bakuje ba.....)






*✅OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*



*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To Brother KHABIER*



*🌈Kainuwa Writers Association*



*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Godiya ta Musamman Agareku HASSAN ATK and HUSSAINI 80k haƙiƙa kuɗin kun cancanci babban yabo, ako da yaushe akullum kuma ina yaba ƙoƙarinku, Allah Yabiya muku baƙatunku na alkhairi. Dani da sauran marubuta muna godiya sosai agareku*





*NOTE* *Nasan daga fara book ɗinnan kawo yanzu na ɓata ran wasunku da yawa, amma inaso kusan cewa sam bahaka naso ba, wannan labarin me suna SHU'UMIN NAMIJI ƙirƙiransa nayi da kaina, ba wani ko wata bane suka bani labari ko shawaran nayi, sannan kuma inaso yawancinmu musan cewa yarda da ƙaddara yana daga cikin imani, balallaine kasamu abunda kakeso alokacin da kake soba, haka kuma balallaine akullum kazamo me nasara ba, haƙiƙa Nasara wani babban jigone da kowa keson samu acikin rayuwarsa, haka kuma rashin nasara ma wani jigo ne da ke sawa mutum ke gane kuskurensa awasu lokutan, idan da'ace komai muka nema zamu samu, to tabbas da ayanzu dayawanmu munshagala da bautar ALLAH Hakan kuma sam ba dai dai bane, arayuwa akwai abu biyu NASARA da kuma FAƊUWA, balallaine kazamo me sa'a ba ako da yaushe, dayawanku suna jin haushin abun da nayi, na hanawa Zaid auren Zahrah, inaso ku fahimceni, banhana Zaid auren Zahrah da gangan ba, ko wai don son zuciyata ba, a'a, inaso kufahimci cewa rashin Zahrah acikin rayuwarsa shine mafarin shiriyarsa, koda a gaskene ba wai a novels ba, idan kanemi abu baka samuba, kada kazargi wani abu, kada kuma kaga kamar ALLAH Baya sonka ne, ko kaɗan bahaka abun yake ba, bai zama lallai abun da kakeso yazamanto alkhairi agareka ba, haka kuma wani lokaci Allah Yakan jinkirta baka abun da kakeso koda kuwa abun alkhairi ne a gareka, kada kayi fushi domin hakan ma wata JARABAWA ce agareka, ALLAH'n daya haliccemu yafi kowa sonmu, shi ke bamu, shi kuma ke hanamu, kada ki/ka sa damuwa acikin zuciyarka, wai don waninka yasamu kai baka samu ba, kaima watarana zaka samu Insha Allah, sannan kowa aduniya baya wuce rabonsa, haka Idan ALLAH Maɗaukakin Sarki ya tsara abu, to babu wanda ya isa ya sauya, natsinci kainane kawai da fara typing ɗin wannan labarin batare da nayi tunanin komai ba, hakanan nafara rubutashi, cikin ikon Allah kuma yabani sa'a, kuka karɓeshi hanu bibbiyu, haƙiƙa labarin nan nice nake rubutasa, amma kuma bani ke da ikon abun da zai faru acikinsa ba ALLAH Ne, komai da ɗan Adam zaiyi acikin duniyarnan bashi keda ikon yinsaba ALLAH Ne kawai ke bashi dama, to haka ALLAH Yatsara cewa Zahrah ba matar Zaid bace, babu kuma wanda ya isa ya bawa Zaid ita sai ALLAH..... Kuyi haƙuri masoyana ina rubuta muku labarinne aduk yanda yazo kaina, nasan dayawa kunji ba daɗi, saboda bakwason Doctor, sai dai kuma babu yanda nidaku zamuyi dole sai haƙuri, wasu har yanzu suna ran cewa, Zahrah zata koma ga Zaid, sai dai ina mai baku haƙuri domin awannan labarin Zaid ba zai taɓa auren Zahrah ba, haka ƙaddaransa take, kuma duk musulmi yanada kyau ya yarda da ƙaddaransa walau mai kyau ko marar kyau.*


*CHAPTER 117*


Two years Later!


Acikin shekaru biyunnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda haihuwan Husnah, da kuma ƙarin girman da akayiwa Doctor Sadeeq a wajen aiki, Zahrah kuwa tazama lecturer acikin jami'ar da tayi karatu. Abubuwa dayawa sun faru acikin waƴannan shekarun.


Tsaye take agaban wani babban table tana haɗa wasu takardu dake gabanta, ajikinta sanye take da Abaya gown, maroon colour, wanda jikinsa yaji adon duwatsu da kuma flowers masu kyau, yayinda Abaya Vail ɗin dake yafe saman kanta, ya sauƙo har zuwa ƙirjinta, babu wani kwalliya akan fuskarta, lipstick ne kawai sai kuma kwallin data sanya acikin ɗara ɗaran idanunta, sosai taƙara kyau, cika da kuma wayewa, duk da cewa a ƴan shekaru biyun da suka wuce itaɗin ba baya bace wajen kyau, amma ayanzu komai nata yaƙara ninkuwa akan nada, yanzu tana amsa sunanta na cikakkiyar mace. Kallonta ta maida kan agogon dake ɗaure akan tsintsiyar hanunta. "4:30 pm" ta faɗa tana ɗan waro idanunta, da sauri tacigaba da tattare takardun, wasu tasa acikin jakarta, wasu kuwa ta sanyasu acikin wata drawer dake cikin office ɗin. Wayarta da jakarta ta
End Ads