magabatansa don sukawo sadaki akuma sa rana, to ni dai nace yaturosu duk sanda yakeso, yanzu dole zanje yola insanya fili dakuma gonan nan namu na gado a kasuwa idan aka siya intarkata kuɗin nan nasamu nasaiwa yarinyarnan kayan ɗaki dakuma kayan aikace aikace kamar de yanda kowani iyaye kemawa ƴarsu dan baiyiwuwa ace mu miƙata haka"
Ajiyar zuciya Inna tasauƙe haɗe da gyara zama " Duk naji batunka Malam, amma kuma mezai hana kabar shi mijin nata yayi mata komai, ae naga yana da halin da zai iyayi mata fiye da wannan ma"
Murmushi kawai Baffa yayi shi kam tun ba yau ba yasan cewa bakoda yaushe ne Inna take gane karatun da'ake biya mata ba, don haka baiƙara cewa da'ita komai ba yawuce ɗakinsa, domin yasan kozai shekara a wajen yanason ganar da'ita tofa bazata fahimcesa ba,,, Inna kuwa baƙin ciki ne yakamata ina ma laifin yace zaiƙara jari da kuɗin, sai yace wani wai zai siyawa Zahrah kayan ɗaki,, haka taita ƙananun maganganunta babu maijinta ma balle yatanka mata......
Da yamma Dr.Sadeeq yaƙira Baffa yasanar masa cewa Baffansa zaizo da dare donsu tsaida magana, duk da cewa Baffa yayi mamakin sauri irin na Dr.Sadeeq ɗin amma saiya share yace Allah yakawosu lafiya,,
Hargida Baffa yaje yasanarwa Alhaji Umar abun da Dr.Sadeeq yace, kuma dama Alhaji Umar ɗin tuni yasan da maganar saboda duk abun da yafaru Baffa yanazuwa ya sanarmasa har kawo lefen da akayi ma Baffa yasanar masa,, sosai Alhaji Umar yayi murna yakumace zaizo gidan Baffa'n da dare a ƙarɓi baƙin dashi......
Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakane yakasance domin ana idar da sallan Isha Baffa Amadu da wani shaƙiƙin amininsa suka zo gidansu Zahrah,, sosai Baffa da Alhaji Umar suka musu tarba na mutunci,, zama sukayi haɗe dayin magana ta fahimtar juna, nan Baffa Amadu ya miƙa sadakin Zahrah ga Baffa naira dubu ɗari (100,000) bawani ɓata lokaci Baffa yasanya lokacin aure wata ɗaya, aikuwa take kowannensu yacika da farinciki haka sukayi sallama cike da girmama juna.......
(Team Dr. Saiku fitarmana da ankon biki, nasan duk Baba Zaid ze saya mana auren Zahrah'nsa ne ae 🤣🤣😜)
*4/Junuary/2020*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
~Fatymasardauna~
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
Zahrah na zaune a ɗakinta Inna takutso kanta cikin ɗakin.
"Idan kin gama rubuce rubucen banzan naki kije Baffan ki nanemanki!" Inna tafaɗi haka aƙufule, ko jiran amsan da Zahrah zata bata batayi ba tayi ficewarta acikin ɗakin,,, da kallon mamaki Zahrah tabi bayan Inna wai meke faruwane tun dawowarta amakaranta tafuskanci cewa ran Inna a matuƙar ɓace yake da'ita, domin kuwa ko abincin rana Inna batayi mata tayi ba, kamar yanda ta sabayi mata kullum, to koma dai menene Allah yasa bawani abu bane me zafi... Tattara books ɗin dake gabanta tayi haɗe da miƙewa ta sanya hijab a jikinta kana tafice daga cikin ɗakin.....
Da sallama ɗauke a bakinta takutsa kanta cikin ɗakin Baffan nata,, zama tayi akan tabarman dake shimfuɗe a tsakiyan ɗaki, haɗe dayi mawa Baffa barka da gida,, fuska ɗauke da fari'a Baffa ya amsa mata..
Gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa "Bakomai yasa nayi ƙirankiba sai dan na sanar dake abun dayake faruwa sannan kuma na danƙamiki haƙƙin ki a hanunki, yau da safe yaron nan likita yazo yasameni akan cewa zaituro magabatansa don sukawo sadakin ki, nakuma bashi dama, to yanzu dai sun riga da sun danƙamin sadakin ki a hanuna saboda haka ga abunki naira dubu ɗari ne cus nakine halak malak" Baffa yaƙare maganar yana me miƙa ma Zahrah maƙudan kuɗin dake hanunsa....
Gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi laƙwas gaba ɗaya duk wani kuzarinta ya gudu, hakanan taji wani iri a cikin zuciyarta.
"Ki karɓa mana Zahrah" Baffa yafaɗi haka ganin da yayi ko ɗago kanta takasa yi.
Girgiza kanta ta shigayi a hankali cikin muryarta me sanyi tace "Duk abun da ka yanke a gareni Baffa dai dai ne, amma maganar sadaki ka riƙe a wajenka, saboda ko kabani babu abun da zanyi dasu!" taƙare maganar cikin ladabi.
"A'a Zahrah ki karɓi abunki haƙƙin kine, saboda haka nima babu abunda zanyi dashi ki karɓi abunki saiki adana a wajenki, idan kuma wani abu zaki saya saiki saya, amma kada kiyi almubazzaranci dasu, zaifi kyau kisaya abu me mahimmanci wanda zai amfaneki yanzu ko gaba" maganar da tafito daga bakin Baffa kenan.
Shiru Zahrah tayi ita tama rasa yanda zatayi gaba ɗaya yanayinta yasauya, cikin sanyin jiki Zahrah tasanya hanu ta karɓi sadakin nata a hanun Baffa bawai dan ranta yasoba sai dan Baffa ya matsa akan cewa saita karɓa..
"Yauwa kinga idan kika riƙe abunki a hanunki ae yafi ko, sai kuma maganar sa rana, nasa nanda wata ɗaya, ai inaganin hakan yayi domin kafun lokacin insha Allah mungama iya ƙoƙarin da zamuyi wajen sayan ƴan kayayyakin ɗaki"
Wannan magana ta sa rana yafi komai rugaza mata zuciya, fiye da maganan sadaki, haka nan taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta,, amma haka tayi mawa Baffa sallama cikin sanyin jiki tanufi ɗakinta...
Zama tayi akan katifarta haɗe da rumtse idanunta, take hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta suna gudu akan fuskarta,, shikenan yanzu saura mata wata ɗaya tazamo matar aure? tambayar da tayiwa kanta kenan, bazata iya faɗan wani irin yanayi ta tsinci kanta aciki ba, fargaba ne ko kuma tsoro ne shine abun da bata sani ba,, idanunta ta buɗe haɗe da maida kallonta ga kuɗaɗen dake riƙe a hanunta,, tsurawa kuɗin idanu tayi tamkar mai son gano wani abu ajikin kuɗin,, hawayene suka kuma ɓalle mata, batasan dawani idanu zata kalli Dr.Sadeeq ba, shi wani irin mutum ne? yasani ƙwarai cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace da ita da bazawara duk ɗaya suke, amma kuma shine ya cire maƙudan kuɗaɗensa yabada amatsayin sadakinta alhali kuma farashinta baikai haka ba, ita ba irin matan nan bane dasuka dace a sayesu da tsada har haka ba, domin kuwa acikin abubuwa goma da zasu ƙara farashinta babu kaso tara, saboda haka bata cancanci wannan sadaki ba,, hanu tasanya ta share hawayenta, haƙiƙa bazatace batason Dr.Sadeeq ba amma kuma batajin son nasa acikin jini da jikinta, amma hakan bawai wani abu ne da zaisanya taƙi aurensa ba, domin shi ne ma mutum na farko aduniya daya cancanci ta aura, kodan halaccin daya gwada mata a rayuwa.... Cikin wata jakarta tasanya kuɗin sadakin nata, haɗe da dawowa ta kwanta akan katifarta, bazama ta iya ƙarisa assigment ɗin nata ba domin kuwa gaba ɗaya yanayinta yasauya damuwa ta bayyana a tattare da'ita,, da ƙyar ta iya jawo wayarta taƙira Husnah ta sanar mata da duk wani abun daya faru,, daɗine ya kama Husnah sosai take ta hau farinciki haɗe da cewa gobe zatazo yakamata su fara shirye shiryen biki tunda wuri, domin wata ɗaya bawani lokaci ne me tsawo ba idan har darai da kuma lafiya...
*****
"Kiyi kuka da kyau Saleema amma kuma kozaki mutu bazaki auri Sadeeq ba matuƙar bai fasa auren da zaiyi da waccar ƴar ƙasƙantattun mutanen ba, ni bazan iya haɗa iri da jinsin matsiyata ba!" Abunda Hajiya Habiba take faɗa kenan cikin ɓacin rai.
Ɗago kai Saleema tayi takalli mahaifiyarta ta fuska caɓa caɓa da hawaye, cikin muryar kuka Saleema tasoma cewa " Wlhy inasonsa Mom kuma bazan taɓa iya auren wani bayan shiba, nidai na amince zan aureshi a haka, idan yaso bayan auren sai nasan yanda zanyi naƙori ita yarinyar"
Kallon ke shashasha ce Hajiya Habiba tashiga yi mawa Saleema, cike da baƙin ciki taja tsuka haɗe da watsawa Saleema'n harara "Nibansan yaushe zuciyarki ta mutuba wlhy Saleema, ashe ke baki da hankali? to nifa kisani nagama maganata aure da Sadeeq ne anfasa, kuma suzo su kwashe lefensu bama buƙata, domin kuwa kamarni Hajiya Habiba bazan lamunci cinfuskaba, saboda abunda suke shirin yi yanzu cin fuskane a gareni" fuuuu haka tayi wucewarta sama, tabar Saleema tana ta ruskar kuka, saikace wanda akace ubanta ya mutu....
****
Baffa na zaune a wajen sana'arsa wasu maka makan motoci guda biyu suka faka adaf dashi.. Sosai yayi mamakin ganin Alhaji Ma'aruf yakuma dawowa garesa a karo na biyu, wanda ko kusa baiyi tunanin haka ba..
Bayan sun gaisane Alhaji Ma'aruf ya nisa haɗe da cewa "Nasan zakayi mamakin dawowata gareka Malam Hayatu, sai de kuma me nema baikamata ya gajiya ba"
Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe haɗe da tattaro duka nutsuwarsa yadubi Alhaji Ma'aruf...
"Bazan taɓa ɓoyemaka ba Alhaji, kamardai yanda nafaɗa maka afarko yanzu ma hakane, domin maganan da nakeyi maka yanzu ma jiya aka kawo sadakin yarinyar, saboda haka sedai nace kawai kuyi haƙuri"
Kai Alhaji Ma'aruf yashiga jinjinawa, zuwa yanzu dolensa zaibawa Zaid haƙuri akan cewa yayi haƙuri yacire yarinyar aransa, domin kuwa idan ba wani ikon Allah ba to babu alamun cewa Zaid zaisamu auren yarinyarnan Zahrah..
Haka Baffa da Alhaji Ma'aruf suka rabu, bayan Alhajin yayi mawa Baffa alkhairi maiyawa, amma sam wannan karon Baffa yaƙi karɓa yace bai buƙata, duk yanda Alhaji Ma'aruf yaso Baffa ya amshi kuɗin hakan bai samu ba,, haka Alhaji Ma'aruf yayimawa Baffa sallama shida tawagar body guard ɗinsa suka bar wajen, sam Alhaji Ma'aruf baiji daɗin hakan ba, yaso ace ɗansa yasamu abunda yakeso.....
Cike da tsananin damuwa Alhaji Ma'aruf ke kallon Zaid dake zaune a ƙasa yayi shiru, gaba ɗaya ya sanja, komai nasa yazama sanyi sanyi, ga alamomin damuwa da suka bayyana kansu a jikinsa, baisan wani irin masifaffen soyayya ɗannasa ya kamu dashi ba, baimasan taya ya Zaid zai ɗauki maganar da zai faɗa masa ba, amma dai yazama dole yafaɗa masa gaskiya amatsayinsa na mahaifinsa.
"Zaid!"
Alhaji Ma'aruf yaƙira sunan Zaid murya a tausashe.
"Na'am Dad" Zaid ya amsa murya ƙasa ƙasa.
"Inaso kabani hankali da nutsuwarka, dan Allah Zaid ka kwantar da hankalinka, nasani kuma kaima kasani nema cikin nema haramunne, kacire wannan yarinya acikin zuciyarka domin kuwa yau naje nasamu shi Baffan nata, yakuma shaidamin cewa a halin yanzu har ya karɓi sadakinta, saboda haka zaifi kyau kacireta a zuciyarka, kanemi wata nasan babu wata mace da zata ƙika"
Tamkar wanda Dad ɗin ya watsa masa ruwan zafi haka yaji sauƙar maganganun mahaifinsa acikin kunnuwansa, da sauri yaɗago jajayen idanunsa ya watsawa mahaifin nasa su,, bakinsa na rawa yace "Ankarɓi sadakinta kuma Dad?"
"ƙwarai kuwa Zaid abunda Baffan nata yafaɗamin kenan, shiyasa nace ka cireta a ranka"
Kai Zaid yashiga girgizawa,,,,, "Bazai taɓa yiwuwaba Dad, wlhy wani bazai taɓa auran Zahrah ba matuƙar ina numfashi acikin duniyar nan, inasonta fa Dad meyasa bazaku gane hakan ba? bazan iya cigaba da rayuwaba idan har babu Zahrah a gareni, nasan laifinane Dad, amma duk da haka bai dace a hanani Zahrah ba, saboda inasonta inamata wani irin so me tsanani please Dad niko yanzu dan Allah a ɗaura mana aure idan yaso daga baya ni na amince zan shawo kanta, nasanma tana sona har yanzu, kuma nasan daga baya zata yafemin abunda nayi mata!"
Cike da tsananin mamaki Dad ke kallon Zaid wanda gaba ɗaya ya ruɗe alokaci ɗaya, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikinsa ba ? Dad yatambayi kansa cike da tsananin mamaki, domin kuwa sam Zaid ba haka yake ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu amma kuma wani babban abun mamaki shine yauga Zaid nan yana faɗin wai bazai iya rayuwa ba idan babu wata,,
"Zaid!" Dad yakuma ƙiran sunansa cike da tausayawa domin shikam baitaɓa ganin soyayya irin wannan ba...
Zaid bai iya amsawa mahaifinnasa ba, saide idanunsa daya ɗago ya kalli Dad ɗinnasa dasu.
"Zaid ka kwantar da hankalinka, ba ita kaɗai bace mace a duniyar nan akwai mata da yawa, kana da ƴancin da zaka zaɓi duk irin macen da kake so" Dad yafaɗi haka ga Zaid cikin lallami...
"Idan ni inada ƴanci ita kuma dana cuta fa? nacutar da ita Dad cuta mafi muni, na zalunceta, banda wata hanya dazanbi na goge laifina a wajenta, sai ta hanayar aurenta, dan Allah Dad kayi wani abu, bazan iya jure rashin Zahrah ba!" yanzu kam har ƙwalla suncika idanun Zaid batare daya sani ba. (hmm so mugun wasa)
Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sa kai yafice daga cikin falon Dad ɗin nasa, da kallo kawai Dad yabisa dashi harya fice, baisan me yake shirin faruwa da ɗan nasa ba amma ae so ba hauka bane.....
Zaid yana fita daga ɓangaren Mahaifinsa direct part ɗinsa yanufa, idanunsa gaba ɗaya sun rufe yayinda kansa ke matuƙar sara masa, sam bazai iyaba, bazaitaɓa iya jure rashin Zahrah ba, lallai yazama dole yakuma yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa,, tabbas yazama dole ya kusanto Zahrah zuwa garesa koda kuwa hakan zai jawo faruwar abubuwa masu tarin yawa...key ɗin motarsa ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe babu wani abun dayayi saura aciki banda tsananin soyayyar Zahrah.....
Da wani irin mahaukacin gudu Zaid yafigi motarsa yafice daga cikin gidan saura kaɗan yabitakan me gadi daya wangale masa gate, Allah ne ya ta ƙaita Me gadin yayi saurin matsawa gefe, domin kuwa ko gama buɗe gate ɗin baiyi ba Zaid yayi yo kansa....
Tuƙi yakeyi amma kuma kwalbar giya ne riƙe a ɗayan hanunsa yana sha, jinkansa yake gaba ɗaya yana juyawa, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi, idanuwansa Zahrah kawai suke hango masa, batare da Zaid yakulaba motarsa tayi karo da wata babbar mota, take motar tasa ta ɗagu sama haɗe da faɗowa ƙasa sannan kuma tashiga gungurawa kan titi, batare da Zaid dake cikin motar ya tsira ba.....
*(Dan Allah ku daina min kutse acikin labarin nan, kudaina saurin yanke hukunci, haryau ban ce ga wanda zai auri Zahrah a tsakanin Zaid ko Dr.Sadeeq ba, kubarni ni kaina nasan abunda ya dace, zaifi kyau ku sanyamin idanu kukuma ci gaba da bina harzuwa ƙarshen labarin nan, amma abun da wasunku sukemin banajin daɗinsa, suna nunawa kamar ina shirin yin abun da bai dace ba, suna nunawa kamar bansan me nakeyiba, dan Allah kuyi haƙuri zancigaba da rubuta labarin nanne kamar yanda yazomin acikin kai dakuma zuciyata, idan kukayi haƙuri komai zaizo cikin sauƙi kuma ina da tabbacin cewa ƙarshen labarin zai muku daɗi, nasan dama dole zan fuskanci ƙalubale a wajen wasunku, amma banyi tunanin abun zaiyi tsanani har haka ba,, amma bakomai namuku uzuri my lovely fans nasan ƙaunace tajawo hakan😅... kuyi haƙuri nayau baida yawa wlhy gaba ɗaya banganewa kaina bane shiasa inafatan zakumin uzuri)*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*(Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareki Masoyiyar asali MY SHALELE (marubuciyar RAGGON MIJI) kiji daɗinki Shalelena iya wuya munatare inakuma yi miki son so)*
*CHAPTER 84 to 85*
Kyakkyawan murmushinsa ne ɗauke akan fuskarsa still hannayensa a ware suke, alamar ta taho zuwa garesa.
Ahankali tashiga takawa tana nufar inda yake, ganin haka yasanya Zaid sakin ajiyar zuciya me ƙarfi, haɗe da sake sakin murmushi alokaci na ba adadi,, koda tazo gareshi yana shirin yaji ta rungumesa amma kuma sai yaji saɓanin haka, domin kuwa tana zuwa kusa dashi, sai gani yayi ta raɓa ta gefensa ta wuce batare dako kallonsa tayi ba. Cikin hanzari yasha gabanta haɗe da kamo hanunta. Cak ta tsaya daga tafiyan da takeyi haɗi da rumtse idanunta,, a hankali ya zame guiwowinsa ƙasa, ya durƙusa mata, duka hannayenta ya kama ya riƙe acikin nasa hanun....
Cikin murya me ɗauke da matuƙar rauni yace da'ita...... "Koda kalamaina baza suyi tasiri acikin zuciyarki ba, dan Allah inaso ki tsaya ki saurareni, ki dubi halin danake ciki Zahrah, banda wani sauran farinciki a duniyar nan idan har babuke a tare dani, haƙiƙa nayi nadama nakumayi dana sanin abun dana aikata a gareki, amma dan Allah Zahrah kiyi haƙuri kiji tausayina ki yarda muyi aure, wallahi namiki alƙawari zandaina duk wani abu danakeyi, zan baki farinciki me ɗorewa, zan mantar dake duk wani damuwa, me yasa bazaki cigaba da sona ba Zahrah? meyasa bazakiji tausayina ki yarda da tuban danayi ba, inasonki Zahrah so irin wanda bantaɓa yiwa kowa irinsa ba acikin wannan duniyar, zan iya fansar da komai nawa idan har zaki amince ki aureni, zan iya rayuwa babu komai babu kuma kowa, amma bazan iya rayuwa babu keba, zan iya sadaukar da duka dukiyata, dakuma duk wani abu nawa dana mallaka, matuƙar zansameki amatsayin matata, dan Allah Zahrah ki yarda dani mana, ninefa Zaid, nine mutumin da kika fara so acikin rayuwarki, shin mai yasa bazaki tausayamin ba, kikalli cikin idanuwa na Zahrah hakan kaɗai ya'isa bayyana miki irin tsananin ƙaunar danakeyi miki, inasonki, wallahi inasonki Zahrah!!.." gaba ɗaya zuciyarsa ta karye, sosai rauninsa ya bayyana... A kan fuskar Zahrah kuwa hawayene ke zuba tamkar anbuɗe famfo sannan kuma haryanzu idanunta akulle suke, yayinda harkawo yanzu hannayenta ke cikin nasa hanun. Bazatace yaushene ko kuma tayayane itama ta tsinci kanta da zamewa ƙasa ba, ta dai tsinci kanta da kafa guiwowinta a ƙasa. kukane yaci ƙarfinta bazata kuma iya cewa ga abu ɗaya dake damunta ba... Hanunta tashiga ƙoƙarin cirewa daga cikin