x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 24 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 69001 words
  • 72000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 229

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
bacci" Zahrah itama tatambayeshi.


"So da ƙauna dakuma tunaninki susuka hanani bacci! kefa mai yahanaki bacci?" yatambaya cike da son jin amsar da zata fito daga bakinta, "Allah yasa itama tunani na ne ya hanata bacci" yafaɗi hakan a zuciyarsa.


Kunyane yaɗan kamata amma sai ta basar haɗe da sauƙe ajiyar zuciya "A'a nikam karatu nake, shiyasanya banyi bacci ba, amma yanzuma zanyi baccin." tafaɗi hakan a taƙaice.


Ko kaɗan baiji daɗin amsar da ta basa ba, amma yasan cewa wataran dole zatayi tunaninsa kamar yanda shima yake nata tunanin.


"Naji daɗi sosai da kika amince dani Zahrah na! hakan yasa na ƙara jin sonki sosai da sosai a cikin zuciyata!!" cikin shauƙin so yafaɗi maganar.


"Umm banji mai ka faɗa ba!" Zahrah tafaɗi hakan cikin wani irin salo wanda batasan ma tayi shi ba, duk da kuwa cewa taji mai yace, iskancine kawai irin nata.


Lumshe idanunsa yayi da suka soma sauya kala, sosai yanayin yanda tayi maganar ya sauƙar masa da kasala.


"Bacci kika farane Zahrah na?" yatambayeta cike da kulawa, domin kuwa shi anasa zaton dagaske batajisa ba.


"Um!" Zahrah ta basa amsa a taƙaice cikin ƙasa ƙasa da murya, domin kuwa tanaso yayarda cewa baccin takeji, saboda har yanzu, bata gama amanna dacewa sonsa take ba, kuma koda za'a kasheta tasan cewa ba sonsa take ba, kawai dai ta tsinci kantane da amince masa, amma batun soyayya kam babu shi.


"To kiyi bacci mai daɗi kinji My princess, inasonki sosai, ki kulamin da kanki, banson koda ɗigon wani a bune ya raɓe ki!" Dr ya faɗi haka cikin shauƙin SO (Sisters kujisafa su likita ashe an iya kalaman love, lol.)


"Uhumm sai da safe." Zahrah tafaɗa a taƙaice bayan ta zare wayar daga kunnenta.
"Gaskiya abune mai matuƙar wahala koyawa zuciya So'n abun da bata so, ya Allah kataimakeni, haƙiƙa banajin tsanarsa haka kuma banajin soyayyarsa a zuciyata, sannan kuma inaji ajikina cewa zan'iya rayuwa dashi, to me hakan ke nufi, ba so bane kuma ba ƙi bane to menene?" tatambayi kanta a bayya ne, saidai kuma bata da amsar da zata bawa kanta.


Komawa tayi ta kwanta bayan ta kashe wayarta ta gaba ɗaya.


Cike da saƙe saƙe bacci yayi awungaba da ita.


Ɓangaren Dr Sadeeq ma, sai da yajima yana saƙawa da kuncewa, ba abun da yake ɗaure masa kai, kamar yanda ya kasa fahimtar cewa Zahrah, na son sane ko bata sonsa. da ƙyar dai shima bacci ya'iya ɗaukarsa.


Washe Gari.

Yau tun saven thirty suke da lecture, dan haka da wuri tasoma shirya kanta, sosai tayi kyau cikin shigar jar abaya haɗe da jan hijab ɗin dake jikinta, hand bag ɗinta ta rayata a bisa kafaɗanta. Kana tafice zuwa tsakar gida. Zama tayi akan taburma haɗe da jawo farantin ƙosai da kuma kofin kunun da Inna ta aje mata tasoma sha. Baffa ne yafito daga cikin ɗakin sa yanaganin Zahrah yace
"Yauwa kinfito ko, tun ɗazu kuwa likita yake jiranki a waje"


"Eh Baffa nafito" tabashi amsa cike da mamakin jin cewa wai Dr yajima da zuwa, yanama jiranta a waje, amma kuma bai ƙira ta a waya yasanar mata ba.


Aƙagauce taci abincin kasancewar har bakwai tayi.


Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushi, itama murmushin ta sakarmasa bayan tagama ƙaremawa kwalliyarsa ta yau kallo.


"Kinyi kyau my princess!" yafaɗa cike da nishaɗi, domin kuwa sosai tayi masa kyau, jan kayan da tasa ya karɓi kalan fatarta.


"Kaima haka" tabashi amsa a taƙaice.


Murmushi yakumayi haɗe da buɗe mata murfin motar nuni yayi mata da hanunsa alamar tashiga, wani murmushi mai tsayawa a zuciya tayi masa haɗe da shigewa cikin motar tayi mawa kanta mazauni.


Tafe suke suna hira cike da nishaɗi, wanda gaba ɗaya yawan hiran Dr ne maiyi mata shi.
A haka har suka iso cikin makarantar, ƙoƙarin buɗe murfin motar ta soma yi.


"Ya haka? baki sallameni ba fa, kike ƙoƙarin tafiya" Dr Sadeeq yafaɗi hakan cikin sigar zolaya.


Murmushi Zahrah tayi masa haɗe da yin fari da'idanunta "Bangane ba" tafaɗi haka cikin salo.


Lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanu yashafi sajensa, "Inanufin bakice kina sona ba"


Dariya haɗe da kunyane suka kama Zahrah sai kawai ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, domin kuwa bazata iya masa abun da yakeso ba.


Saida yaga shigewarta cikin hall kafun yaɗauke idanunsa daga kanta, yanason mace mai kunya gashi Zahrah takasance me kunya. Cike da tarin tunaninta yabar cikin makarantar.


Ita da Husnah suna fitowa a lecture sukayi mawa kansu ma zauni a inda suka saba zama ko da yaushe.


Cike da tsananin farinciki Husnah tace "Naji daɗi ƙwarai Zahrah da kika amincewa Dr, wallahi gayen ya haɗu da yawa ƙawata, tabbas idan kika auresa kin more don nasan za kisha madaran soyayya!"


Hararan wasa Zahrah ta wurgamawa Husnah, cike da son basar da zancen tashiga shafa cikin ta " Nifa yunwa nakeji" tafaɗa tana mai turo baki gaba.


"Kada dai kice zakimin sakalci, domin niba Doctor bane" Husnah tafaɗa cikin tsokana. dukan wasa Zahrah takai mawa Husnah, da sauri Husnah ta kauce.
Cafeteria suka nufa acan suka cika cikinsu, daganan suka sake shiga cikin wani lecture'n.


Jikin wata bishiya dake kusa da ƙofar fita daga makarantar yayi parking motar sa, gyara zama yayi haɗe da duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. Kallonsa ya mayar zuwa bakin tangamemen gate ɗin makarantar tasu, hakanan yakejin ba zai iya fuskantar ta gaba da gaba ba.


Amatuƙar gajiye su Zahrah suka fito a lecture. Tare suke tafe ita da Husnah, domin yau zataimawa Husnah rakiya ne zuwa super market. kai tsaye suka nufi ƙofar fita daga makarantar kasancewa driver'n gidansu Husnah najiransu a waje.


Wani irin faɗuwar gaba taji, ya risketa adai dai lokacin da ta fito daga cikin makarantar.


Daga ɓanagaren Zaid kuwa zuciyarsa ne tashiga dukan uku uku, alokacin da'idanunsa suka sauƙa akan Zahrah, hanu yasa ya murje idanunsa domin tabbatarwa da kansa cewa ita ɗince kokuwa gizo idanunsa suke masa.
Tabbas itaɗince Zahrah'n sane, har yanzu tananan da kyawunta, dakuma surarta mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen ɗa Namiji.


"ZAHRAH!" yaƙira sunanta a bayyane, duk da kuwa yasan cewa bazata ji sa ba. dai dai lokacin daya soma yunƙurin buɗe murfin motarsa don yaƙarasa gareta, dai dai lokacin itakuma ta shige cikin mota tare da Husnah.


*13/December/2019*



*Voted, Comment, and Share please.... Follow me on Wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
*Phatymasardauna*


*Dedicated to My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna
___________________


*Editing is not allowed📵*


*CHAPTER 57 to 58*


Cikin Hanzari ya buɗe murfin motar tasa ya fito, sai dai baikai ga ƙarasawa garesu ba, motar su ta gangara kan titi haɗe da ɗaukar hanya.


Hannayensa duka biyu yasanya ya kama ƙugunsa, haɗe da furzar da iskan numfashi ta bakinsa, sam baiso haka ba, amma babu yanda ya'iya dole binsu zaiyi.


Kallonsa yamaida ga sauran cincirindon ɗaliban da suke tsaye a bakin gate ɗin makarantar.


Gani yayi gaba ɗaya sun saki baki da hanci suna kallonsa, sai kace wanda suka ga baƙon halitta, bama kamar ƴan matan dake tsaye a wajen.
Tsuka mai sauti yayi haɗe da komawa cikin motarsa, da gudun gaske ya cilla motar tasa kan titi, haɗe da rufa mawa motar su Zahrah baya.


"Yadai, naga lokaci ɗaya duk kinyi wata iri dake?" Husnah tatambayi Zahrah wacce tazama silently lokaci ɗaya.


A jiyar zuciya ta sauƙe haɗe da maida kallonta ga Husnah " Faɗuwar gaba nakeji Husnah, ban kuma san dalilin hakan ba" Zahrah ta faɗi haka cikin damuwa.


"To fa, Allah dai ya tsare, amma ki yawanta addu'a, domin hakanne zaisa koma mene ne yazo da sauƙi" inji cewar Husnah.


"Insha Allah!" Zahrah tafaɗi hakan tana mai kwantar da kanta a jikin kujeran motar, tanajin Husnah tace da Driver'n ya karkata akalar motar, ta sanja shawara shoprite kawai zasuje, bamusu kuwa ya sanja hanya zuwa Shoprite ɗin. Itadai Zahrah batace dasu komai ba.


Basu wani jima suna tafiya ba, suka iso tangamemen Shoprite ɗin. "Muje ko" Husnah tace da Zahrah tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar.


Cikin sanyin jiki Zahrah, tafito daga cikin motar suka nufi cikin shoprite ɗin.


Basket biyu Husnah ta ɗauka nata ɗaya na Zahrah ma ɗaya, acewarta Zahrah ta zaɓi duk wani abun da take so, sam bahaka Zahrah tasoba amma babu yanda ta'iya, domin kuwa Husnah kafiya gareta, idan tace kayi abu tofa wai dole sai kayi.


Kayan shafa suka soma ɗauka, kafun suka garzaya zuwa kan su jaka da takalma ƴan yayi, basu tsaya anan ba hadda kayan ciye ciye sai da suka ɗauka.


Cike da gajiyawa Zahrah ke tura Basket ɗin da kayanta ke ciki, ita mamaki ma take yanda Husnah tasa suka jidi kaya mai yawa har haka, amma idan tayi la'akari da irin gata da kuma kuɗin da mahaifin Husnah ke dashi, to sai tagama ba wani abun mamaki bane, kuma kuɗin kayan bazai mawa Husnah wahalar biya ba, domin kuwa anshagwaɓata sosai agida.


Daki daki aka lissafa kayan nasu, inda Zahrah ta ɗauki kayan dubu ishirin Husnah kuwa na dubu ishirin da biyar ta eba, ƙoƙarin miƙa wa Cashier ATM card ɗin dake hanunta Husnah ta soma yi. Amma sai Cashier'n yayi murmushi haɗe da cewa
"Ai Hajiya ba'a buƙatar kuɗin ku, domin kuwa an riga da an biya muku, tunkafun ku kammala sayayyan, sannan wanda yabiya muku yace idan ma kuna da buƙatar ƙari, to kukoma ku ƙara, duk shi zai biya kuɗin"


Cike da mamaki Zahrah da Husnah suka shiga kallon juna.


"Anbiyamana fa kace Cashier? shin ka kosan me kake cewa?" Husnah tatambayeshi cike da mamaki.


"Ƙwarai kuwa nasan me nake cewa, kudai ku ɗau kayanku kawai kuje, sannan ku gode mawa Allah, don shi yaje fo muku tsuntsu daga sama gasashshe " Cashier'n nan yafaɗi haka yana mai washe baki, kasan cewar shima anbarmasa kyautan ragowan canjin su.


Mamakine ya lulluɓe su Zahrah domin su a iyaka sanin su basu da wani wanda zai biya musu kuɗin siyayyan da sukayi, domin kuwa basu zo da kowa ba banda driver, inakuwa driver zaisamu maƙudan kuɗaɗe irin haka har ya biya musu kuɗin siyayya alhali shima yana fama da kansa.


"Kozaka iya faɗamana wanda ya biya mana kuɗin ?" Husnah ta tambaya.


"A gaskia bansan saba, sai dai da duk kan alamu irin larabawan nan ne da suke zuwa Nigeria lokaci zuwa lokaci" Cashier ɗin nan yafaɗa musu haka, domin shi a yanda yafahimta, da dukkan alamu wanda.yabiya musu kuɗin baiyi zubi da ƴan nan gida Nigeria ba, duk da kuwa cewa muma muna da kyawawan maza amma kuma kyawun wani ya ɗare na wani.


Idanu Zahrah da Husnah suka zaro atare, sakamakon jin abun da Cashier yace.


"Balarabe fa kace?" Husnah ta sake tambaya cike da mamaki.


"Eh Balarabe, kece Zahrah ko?" Cashier'n nan ya tambaya yana mai nuna Zahrah da hanunsa.


"Ya'akayi kasan sunana ?" Zahrah ta tambayesa cike da mamaki.


Murmushi kawai yayi haɗe da miƙa mata wata farar takarda.
"Ungo yace inbaki"


Cikin tsoro Zahrah ta karɓi takardan da Cashier ke miƙo mata, haɗe da buɗewa.


_"Kiɗauki duk wani abun da kikeso MY ZAHRAH! ban damuba koda duka Shoprite ɗin zaki ce kinaso, zan iya mallaka miki kome kikeso a duniyar nan, ko da kuwa dukiyata zata ƙare"_ abun da aka rubuta a jikin takardan kenan.
Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, "To waye?" tatambayi kanta a fili.


"Yadai me aka rubuta acikin takarda'n?" Husnah ta tambayi Zahrah cike da zaƙuwa.


Bata takarda'n Zahrah tayi domin batasan me zatace da'ita ba.


Husnah tana gama karanta takarda'n tasaki murmushi haɗe da kallon Cashier'n nan daya zura musu idanu... "Mungode sosai, idan ka haɗu da wanda yabiyamana kuɗin, ka isar mana da saƙon godiya" daga haka ta kama hanun Zahrah suka fice daga cikin Shoprite ɗin, bayan sun ɗau ledodin siyayyarsu.


"Saida sukazo bakin mota kafun Husnah ta saki hanun Zahrah, still fuskarta ɗauke da murmushi tace "Mekika fahimta game da wannan takardan, da kuma biya mana kuɗin sayayya da akayi?"


Cikin ɗaurewar kai Zahrah tace "Ni ban fahimci komai ba, sai ma tsananin mamaki da nake, taya haka zata kasance, anya kuwa ba wata maƙarƙashiyan ake shirin ƙulla mana ba Husnah?"


Dariya sosai Husnah ta kwashe dashi, domin kuwa maganar Zahrah takai a dara.


"Maƙarƙashiyan soyayya ba, babu wani aljanu, kawai dai inaga wani ne yaganki kuma ya yaba, shine kawai" Husnah tafaɗa tana mai danne dariyanta.


"Bangane ba me kike nufi?" Zahrah ta tambaya cike da ruɗu, domin ita kwata kwata ma bata fahimci inda kalaman Husnah suka dosa ba.


"Kada ki damu zaki gane mushiga mota"
Jiki a sanyaye Zahrah tabuɗe murfin motar tashiga, a gidan baya sukai mawa kansu masauƙi ita da Husnah..
Suna shiga driver yayi mawa motar key suka ɗauki hanyar Suleja unguwar su Zahrah.
(yauwa kuyi haƙuri jiya nayi mistake sunan unguwar su Zahrah ba Maraba bane, sunan unguwarsu Zahrah Suleja ne, kainane ya ɗau charge shiyasa)


Yanaganin tafiyarsu yasaki ƙawataccen murmushinsa, "Haryanzu tananan da halinta na tsoro, yayi imani Zahrah bazata taɓa sanjawa ba"
" komai naki yana burgeni Zahrah, inason komai naki!" Zaid dake cikin motarsa yafaɗi haka cike da shauƙi.


"Nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kimin bayani mana Husnah, me takardan nan take nufi ne?" Zahrah tafaɗi haka cikin zaƙuwa.


"Ki kwantar da hankalinki ƙawata, kawai dai bazai wuce irin mutanen nan masu alkhairi bane suka aikata hakan, wayasani ma ko Dr Sadeeq ne" Husnah tafaɗi hakan tana mai kallon Zahrah.


"Mene? kinanufin wai Doctor ne zaiyi haka? gaskiya banjin cewa shi ne, domin idan da shi ne, dole zai bayyana kansa na gansa, kodai ke akeso amawa wannan hidiman akayi mistake aka ambaceni" Zahrah tafaɗi haka cikin kokonto.


Dariya Husnah takuma sawa, haɗe da dafa kafaɗan Zahrah..


"Wai lafiyanki kuwa Zahrah? kinga yanda kika firgice lokaci ɗaya sai kace wacce ta aikata aikin rashin gaskiya, to ni miye ma abun damuwa ne don wani yabiyamana kuɗin sayayya? kinga bafa mu muka sa sa ba, ko ma waye shi yasanya kansa, kishare kawai ƙawata" Husnah taƙare maganar ta ta bayan ta ɓare sweet ta jefa acikin bakinta.


"Hmmm" kawai Zahrah ta'iya cewa, haɗe da mai da kanta jikin kujera, itakam gaba ɗaya kanta ya kulle, taya za'ace bakasan mutum ba, amma kuma ya biyamaka kuɗin siyayyan da kayi, irin haka ne mutum sai yaje ya jefa kansa a matsala.


Tafiya suke amma Zahrah ta kasa cewa komai, sai ma Husnah ce keta ƙoƙarin janta da hira, amma jefi jefi take amsa mata, domin kuwa wannan faɗuwar gaban da takeji har yanzu baidaina ba.


A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah'n... Har cikin gida Husnah tayimawa Zahrah rakiya, kana ta fito tashiga mota suka tafi.


Zama tayi akan katifarta haɗe da zubawa kayan siyayya da sukayi ido, sam zuciyarta bata kwanta da wanda yabiya musu kuɗin kayan ba, zuwa yanzu ya kamata ace tayi hankali, domin sarai yanzu tasan salon yaudaran maza baida ƙarshe, suna iya yimaka komai don su samu biyan buƙatarsu, wannan yana ɗaya daga cikin babban dalilin da yasanya ta amince da auren Dr Sadeeq, ko ba komai idan ya aureta ta tsallake wani babban siraɗi na daga yaudaran da Maza sukeyi mawa ƴan mata a wannan zamanin.


Ƙaran wayartane yakatseta daga tunanin da takeyi, cikin sanyin jiki ta ɗaga ƙiran nasa, haɗe da kara wayar akan kunnen ta.


"Barkanki da hutawa My Princess!"


Dr Sadeeq yafaɗa cike da tsantsar kulawa.


Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa "Kaima barkanka dai ya aiki?"


Ɓata fuska yayi tamkar dai tana ganinsa haɗe da cewa "Aiki ba daɗi kokaɗan, ya kundawo a super market ɗin kenan?"


"Eh" tabashi amsa a taƙaice. Domin tsabar gajiyan da ta kwaso har wani bacci bacci takeji.


"Naga kamar kingaji da yawa, ki samu ki ɗan huta, zuwa anjima zanzo gida, inaso na samu Baffa, idan yabani dama zanturo magabata na ayi maganar auren mu, domin banso akai nanda wata ɗaya ban mallakeki ba!" yaƙare maganar cikin yanayin shauƙi.


Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, sakamakon jin abun da Dr Sadeeq yace. Wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki, wanda baza'a ƙirasa da farinciki ba, ba kuma za'a ƙirasa da yanayin baƙin ciki ba.


"Zahrah na!" yaƙira sunanta jin cewa tayi shiru batace dashi komai ba.


"Umm" ta'amsa masa a kasalance.


"Naji kinyi shiru, ko dai bakiyi farinciki da hakan bane?"
Yajefo mata tambayar da batayi zaton zai mata shi a yanzu ba..


"A'a nayi farinciki mana, kawai dai kainane ke ɗan min ciwo" tafaɗi haka don ta kare kanta, gudun kada yafuskanci wani abu.


"Ayya kiyi haƙuri, anjima idan zanzo zan tahomiki da magani ko, yanzu ki kwanta ki huta, nasan ma stress ne, insha Allah zuwa anjima zaki ji ki normal" yafaɗi hakan cike da kulawa.


"To" kawai ta'iya cewa dashi, haɗi da zare wayar akan kunnen ta.


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da share ruwan hawayen da suka fito daga cikin idanunta. "Yazama dole nakoyi soyayyarka Dr Sadeeq, domin bayan kai babu wani wanda zai bani kulawa kamar haka, ya Allah kamin maganin matsalolina!" tafaɗi hakan a bayyane, bayan ta ɗaga idanunta zuwa sama.


Da ƙƴar ma ta'iya cusa abincin da Inna ta bata, domin kuwa hakanan taji zuciyarta ta cunkushe.


Kwanciya tayi akan katifarta tana ƴan tunani, take bacci ɓarawo ya siɗaɗo ya ɗauketa, batare da tashiryawa hakan ba....


Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar kujera, wanda take ita kaɗaice kuma na mussaman acikin bedroom ɗinsa, dake cikin guest hause nashi. ɗan ƙaramin table ne aje a gabansa, wanda samansa ke ɗauke da zungureriyar kwalbar wine da kuma glass cup.


Wayar sace riƙe a hanunsa, gaba ɗaya hankalinsa akan wayartasa yake, murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda yake playback ɗin vedi'on daya mata ɗazu fitowarta daga cikin shoprite, batare da ta sani ba.


Harzuwa yanzu bai tantance mai yakeji a jiki da zuciyarsa ba a game da Zahrah, abu ɗaya yasani shine, yasan cewa "yana matuƙar
End Ads