naso na daure amma kamar bazan iya ba, duk da haka amma bazan karaya ba, zanta jarrabawa, watarana sai labari"
Hawayen da suka cika cikin idanunta ne suka tsiyayo waje, "Inama ace wannan ƙaunar itace tasamu daga wajen Zaid" tafaɗi haka acikin zuciyarta.
Ganin tana hawaye yasanya hanunsa ya share mata, jawota yayi ya rungumeta acikin ƙirjinsa, acikin zuciyarsa yace "Zanyi ƙoƙari nasoki Afrah, zan yi ƙoƙari nasama miki gurbi acikin zuciyata, nagode da kulawarki agareni" abunda Zaid bai saniba shine, maganar da yayi, ba iyaka zuciyarsa ta tsayaba, harta fito fili.
Murmushi Afrah tayi haɗe da sake shigewa cikin jikinsa, hanu yasa ya ɗago haɓarta, suka jefa idanunsu acikin na juna, bakinsa ya ɗaura akan nata bakin, yashiga tsotson lips ɗinta a hankali, wani irin sanyin daɗi taji acikin ruhinta, kamo laɓɓansa itama tayi, ta shiga tsotsa, har mamaki takeyi idan tana tsotsan laɓɓansa, saboda laɓɓansa taushine dasu, kamar laɓɓan mace wacce tasan kanta.
Kissing ɗin juna sukeyi sosai, yayinda yasanya hanunsa a bayanta, ya zame mata zip ɗin rigar dake jikinta, bata da wani manyan breast amma tana rage masa zafi, yanda yake murza breast ɗinta cikin nutsuwa yana kuma tsotson lips ɗinta, shi yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi laƙwas, haƙiƙa Zaid yasan kan mace, yasan yanda zaiyi ya zautar da ita, a iya romance kaɗai, yana bata gamsuwa hundred percent, tuni ta cire masa rigan jikinsa, tashiga goga masa breast ɗinta akan chest ɗinsa, take yashiga fidda wani irin numfashi, daman tasan hakan shine logonsa, takaranceshi sosai, (Ko miji baya sonki, idan kika karanci halayyarsa, zakiji daɗin zama dashi, musamman idan kika fuskanci, abun da idan kikayi masa zaki ruɗasa, ko acikin sex ko romance, please ƴar uwa kada kiyi wasa da wannan daman) sosai suke kashe juna da salo, ɗaukarta yayi caɗak, yanufi bedroom da ita, akan gado ya shumfuɗeta, yashiga tsotseta.. Hmmm Zaid jarababbe Afrah jarababbiya, haka suka mannewa juna, duk da cewa Afrah ko farcen Zahrah bata kamo ba, amma balaifi itama tana da nata ni'iman, don dama ko wace mace da irin ni'imarta, sannan kuma baya ga haka, sosai yake samun gamsuwa a wajenta, domin itama ta iya romancing namiji, kuma sosai take gyara kanta, don Zaid yaji zam zam, lol. Amma kuma Zaid kam yasan daga kan Zahrah yagama jin wani zam zam, wanda zai gamsar dashi. (Kunsan muɗin na musammanne😉 idan kina da kishia me suna fatima, to kiji tausayin kanki🤣😜 saura kuma su o'o dan sunansu ba fatima bane, suce nayi ƙarya, namesake kuzo kufaɗamusu cewa maganata gaskia ce.🤗)
***
Tsaye yake acikin kitchine gaba ɗaya ya haɗa gumi, banda ƙonewan da yayi a hanunsa yafi sau biyar, yanzuma ƙonewa yayi a babbar yatsarsa, na hanun dama, ya tsaya yana hura wajen, kwanon soya ƙwaine ɗaure akan gas, yayinda hanunsa ke riƙe da cokali, gaba ɗaya gaban gas ɗin ya ɓaci da manja, gashi har gaban rigar sa manjan ya taɓa, waishinan wainar fulawa yakeyi (Hana baba tashi, mudai muke cemai anan, amma sauran garuruwa bansan me suke ƙiranshi ba, kunsan hana baba tashi akwai daɗi, musamman idan yaji yaji😋😂)
Ƙoƙarin juya wainar fulawan yake, amma yaƙi juyuwa, gaba ɗaya ya ƙona hannayensa, har wainarma tasoma ƙonewa, da ƙyar ya samu ya kwashe, kuma dama wanda ke cikin kaskon shine na ƙarshe, kashe gas ɗin yayi haɗe da ɗaukan tissue ya goge gumin dake tsastsafowa a goshinsa, plate ɗin wainar da kuma roban yaji yaɗauka ya nufi falo.
Tana zaune akan sofa, tayi piecess da ƙafafunta, sanye take da wata ƴar riga marar nauyi, itanan zaman jiransa take, yakawo mata wainar fulawanta taci. Yana shigowa cikin falon tasaki dariya, domin kuwa har kumatunsa manja ne.
Ganin haka yasanya sa ɓata fuska, haɗe da tsayawa yana jifanta da hararan wasa.
Shagwaɓe fuska yayi kamar wani ƙaramin yaro, plate ɗin wainar yakawomata gabanta ya aje mata, haɗe da aje mata roban yaji, muƙut haka ta haɗiyi wani yawu tsabar kwaɗayi, tuni ya wunta ya tsinke, jawo plate ɗin gabanta tayi, haɗe da gutsuran wainar fulawan takai bakinta. Da sauri ta tofar da wainar fulawan sai kuma tashiga kelaya amai, babu ƙaƙƙautawa, amatuƙar ruɗe yayo kanta, shiya riƙeta harta gama yin aman, dakansa ya gyara wajen, zama yayi haɗe da jawota jikinsa cike da tausayinta, yashiga yi mata sannu.
Kwanciya tayi luf acikin ƙirjinsa tana me sauƙe ajiyar zuciya, sosai tagalabaita, amai ba wasa ba.
Bayanta yake shafawa a hankali, yana ɗan jijjigata, kamar wata jaririya.
"Abincinne ba daɗi, yasa kikayi amai?" yatambayeta.
Ya mutsa fuska tayi haɗe da ɗaga masa kai ashagwaɓe tace "Ƙauri haɗe da warin hayaƙi wainar fulawan keyi"
Narke fuska yayi haɗe da karya wuyansa gefe, "yanzu duk ƙoƙarin nan da yayi, yatashi a banza?" yatambayi kansa.
Ajiyar zuciya yayi haɗe da cewa "Kiyi haƙuri, bansan ya akayi yayi warin hayaƙi ba, yanzu to mezakici?" cike dakulawa ya kuma tambayanta.
Zahrah ƴar rigima da shagwaɓa, sake narke masa tayi, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, haɗe da cewa "Ni yanzu, Banana PineApple Smoothie kawai zan sha"
"Banana pineapple smoothie ba abincine wanda zai riƙeki ba, kifaɗamin yanzu me kike so bayan smoothie ɗin?"
"Gasashshen nama, wanda aka sa masa, sweet pepper dakuma onion" ta faɗi haka tana tanɗe baki.
Hanu yasanya yashafi gefen kumatunta, inda dogon suman kanta ya kwanta, "Wannan ba abun damuwa bane, kinaso muje mu sayone kokuma naje ni kaɗai?"
Tsulum tatashi zaune haɗe da cewa "muje tare"
Ɗaki suka koma shida kansa ya shiryata cikin, wani doguwar riga na lace, yanaɗe mata jikinta da wani vail marar nauyi, shima kayan jikinsa ya sauya, suka fita hanunsu sarƙe acikin na juna.
Wani haɗaɗɗen hotel suka nufa, hotel ɗin namusammanne, domin kuwa sai waƴanda suka amsa sunansu ne suke zuwa cin abinci wajen.
Yana riƙe da hanunta suka kutsa cikin hotel ɗin, awani ɓangare wanda babu yawan jama'a sosai suka zauna, suna zama wata waiter da jikinta ke sanye da uniform taƙaraso wajensu, cike da girmamawa ta basu menu, dan zaɓan abun da suke so, Zahrah ce takarɓi menu'n tazaɓi abun da takeso akawo mata, Dr.Sadeeq kam bai buƙaci komaiba, saboda a ƙoshe yake.
Mintuna kaɗan aka kawowa Zahrah abun da takeso, gyara zamanta tayi, haɗe da ɗaukan gasashshen namanta tasoma ci, harwani lumshe idanunta takeyi tsabar daɗi, ji take kamar bata taɓa cin wani nama me daɗin wannan ba, sosai taci naman, kana ta ɗaura banana pineapple smothie akai, shidai kallonta kawai yake, kome tayi burgesa take, kallonshi tayi da fararen idanunta, haɗe da ɗaukan tsokan nama guda ɗaya, takai bakinsa, babu musu yabuɗe bakinsa tasamai, ɗage masa giranta guda ɗaya tayi sama, haɗe da cewa "Yakaji naman, daɗi ko? hmm ai daga yau kullum anan zanna cin nama!" taƙare maganar tana jijjiga kanta, shidai murmushi kawai yaketa aika mata.
Harta gota, zata wuce, sai kuma tayi saurin dawowa da baya, sake ware idanunta tayi akan yarinyar, tabbas itace bazata manta fuskarta ba, kallon yarinyar tashigayi sosai, itakuma yarinyar sai dariya take tana kaɗa kanta, da'alama tana cikin farinciki. "Zahrah!" taƙira sunan yarinyar ahankali, yanda ita kaɗai da tayi maganar ne zataji me tace, "Itace wacce hotunanta suka cika jikin bangon ɗakin Zaid, kenan itace Zahrah'n Zaid? itace mafarki dakuma burinsa?" abun da Afrah ke faɗa kenan acikin zuciyarta, tsintar kanta tayi da tsayawa tana kallon ta, bawata babba bace bazata wuce 20 to 21 year ba, aƙalla tasan zata fita da 3 year, ita kanta yarinyar tayi mata kyau, domin kuwa tana da burgewa, kyawunta abayyane yake, "Hmmm idan dai har Zaid zaina mafarkin samun irin wannan tauraruwar, me zaiyi da irina?" Afrah ta tambayi kanta a bayyane.
"Mekikeyi a tsaye anan kuma?"
Muryar Zaid yakaraɗe cikin kunnuwanta, da sauri tajuyo tana kallonsa, sam ita tama manta da cewa tare suke.
Kallonta yayi naɗan sakanni, kafun ya raɓa ta gefenta ya wuce.
Ƙirjin Dr.Sadeeq ne ya buga, alokacin dayaga gilmawan Zaid ta bayan Zahrah, amma kuma da dukkan alamu shi Zaid ɗin bai lura dasu ba.
"Ya kamata mutafi ko princess, idan yaso saimu yi take away ɗin naman mutafi dashi gida, sai ki ƙarasa ci acan" Dr.Sadeeq yafaɗa a ƙagauce.
"Um um nidai Hubby kabarni please, nakusa nacinye fa" Zahrah tafaɗa a shagwaɓe.
Babu yanda ya iya, dole haka ya barta, taƙarasa cin namanta.
Tana kammalawa kuwa, yakama hanunta suka bar cikin hotel ɗin, ba gida suka nufa direct ba, saida suka biya wajen saida ice cream yasaimata, kana suka ɗauƙo hanyar gida.
Gaba ɗaya jin zuciyarsa yake a jagule, "Meyakawo Zaid wannan hotel ɗin? Kodai bibiyan matarsa yake?" tambayar da Dr.Sadeeq ke tayiwa kansa acikin zuciyarsa kenan, amma bayida wanda zai basa amsoshin tambayoyinsa. (😂 Doctor fa yana tsoron Baba Zaid yasin)
Suna isowa bakin gate ɗin gidannasu, me gadi ya wangale gate ɗin Doctor yatura hancin motarsa ciki.
Tana ganin shigarsu cikin gidan, tasaki wani irin murmushi, tun fitowarsu a hotel ɗin take biye dasu, acikin motarta, batare da tabari sun gane hakan ba.
"Zanyi muku zuwa na musamman" tafaɗi haka a bayyane. Haɗe dayin reverse ta juya akalar motarta zuwa gida...
(Zanfara yi muku 1 read more, saboda banason editing, wallahi wuya yake ban😥)
*20/february/2020*
*✔️OTE me on Wattpad*
@fatymasardauna
#Love
#Romance.......
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers }_
Yana zaune acikin falon, taturo ƙofa tashigo bakinta ɗauke da sallama, cike da mamaki yake kallonta. "Bakije gidan Ƙawartaki bane?" ya tambayeta yana me tsareta da kyawawan idanunsa.
Murmushi tayi haɗe da ƙarasowa cikin falon, zama tayi gaf dashi, haɗe da ɗaukan hanunsa ta ɗaura akan cinyarta. "Naje nasamu batanan, kuma dama banaso nabarka kai kaɗai agida, shiyasa na dawo" tafaɗi haka tana me ƙara faɗaɗa murmushinta.
Kansa yajinjina haɗe da ɗaukan goran ruwan dake aje a gabansa, yakai bakinsa, kallonsa take tanaso tafaɗa masa abun dake cikin ranta, amma kuma tsoro takeji saboda batasan taya zai ɗauki maganar ba.
Matsewa kawai tayi haɗe da sanya hanunta ta saƙalo hanunsa, fuskarsa takafe da ido kana tace "Yau nahaɗu da Zahrah"
Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, cike da tsananin mamaki yace "Wace Zahrah?"
"Zahrah wacce kasani, wacce kuma tunaninta ke maƙale acikin zuciyarka, babu dare babu rana" ta bashi amsa.
"A ina kikasanta, har kikasan cewa itace Zahrah'n danake tunani akowani lokaci?" yajefomata tambaya yana me kafeta da idanunsa.
"Duk wanda yasanka dole zaisan Zahrah, mussamman ma ace wanda yake kusanci dakai, ko kamanta cewa har yanzu akwai hotonta acikin ɗakinka?"
Miƙewa yayi daga zaunen dayake haɗe da cusa hannayensa cikin aljihun wandonsa.
"Zahrah ɗaya na sani a rayuwata, kuma tajima da mutuwa, saboda haka ni bansan wata Zahrah ba" yanakaiwa nan azancensa yasakai yawuce cikin bedroom ɗinsa, ko waiwayenta baiyi ba.
Mamakine ya bayyana ƙarara akan fuskar Afrah, sakamakon jin kalaman Zaid da tayi, "Dare safe rana, bashida wani aiki sai tunaninta, tasha jinsa yana kuka a toilet, dukkuma akan Zahrah ɗinne, amma wai kuma yau da bakinsa yake cewa Zahrah ta mutu, anya kuwa Zaid yana lafiya?" Afrah ke magana da zuciyarta.
Murmushi tayi asakamakon tunawa da wani abu da tayi, tashi tayi tanufi ɗakin da Zaid yashiga.
Yana zaune agefen gadonsa hanunsa, riƙe da wani littafi da kuma biro, da'alama nazartan littafin yake, amma kuma idanunsa cike suke da ƙwalla, yanajin motsin shigowar Afrah, yayi sauri ya rufe littafin, ransa a ɓace, ya juyo gareta.
"Mekikazo ɗauka? Bana faɗa miki cewa bakoda yaushe ne, nake da buƙatarki ba, please get out!" yaƙare maganar yana meyi mata nuni da ƙofar fita daga cikin ɗakin.
Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da takowa zuwa garesa, tana zuwa gabansa ta durƙusa haɗe da zube guiwowinta a ƙasa.
"Kagafarceni idan abun dana faɗa maka akan Zahrah ya ɓata maka rai, banyi haka donna ɓata maka ba, saidai kuma zanfaɗa maka koda zaka tsaneni ne, wallahi bazaka taɓa yin rayuwar farinciki ba, harsai kasamu Zahrah ka ƙara neman yafiyarta, nasan cewa kana da buƙatar Zahrah akusa dakai, fiye da yanda kake da buƙatar ko wace mace a duniya, amma kuma ƙaddara babu yanda bata juyawa bawa, dan Allah kayarda dani, akwai abunda zanyi wanda zaisa kusamu jituwa a tsakaninka da Zahrah, harma da mijinta"
Kallonta yayi da jajayen idanunsa haɗe da tashi, kawai yawuce cikin bathroom.
"Afrah bazata taɓa ganewa bane, shi kaɗai yasan irin zogi da kuma ciwon da zuciyarsa keyi masa, aduk sanda aka ambato masa sunan Zahrah, a yanzu so yake yasa aransa cewa, babu wata Zahrah, domin wacce yasani tajima da mutuwa, wanda yake gani a yanzu, wata Zahrah'nce daban kuma ta wani ce" tsaida zancen zucin nasa yayi, haɗe da cire rigar dake jikinsa, direct gaban shower ya nufa, tsayawa yayi haɗe da sanya hanunsa ɗaya, ya dafa jikin bango, ruwane keta dukan kansa dakuma bayansa, sauda dama idan yana acikin ƙunci, tsayawa yake gaban shower ruwa yaita dukansa, dahaka yake ɗan samun relief.
*** ***
Kwance take akan kujera, sanye take da wani dogon sket, wanda yake a tsuke daga sama har ƙasansa, sket ɗin irin roba ɗinnnan ne, rigarta kuwa wata ƴar vest ce marar nauyi, fara ƙal da ita, tunda ta samu cikin nan, bata rabo dajin zafi, hakan yasanya bata cika zama da kaya masu nauyi ba, wayartace rike a hanunta, kunnenta kuwa sanye suke duka da airpiece, waƙar film ɗin Sanam Teri Kasam takeji, harwani lumshe ido take, saboda tanason waƙoƙin film ɗin sosai, sweet ne abakinta tana ɗan tsotsa, gudun tara yawu, dayake bata ƙure volume ɗin waƙarba, hakan yasanya tajiyo bugun ƙofar da akeyi mata, da mamaki take kallon ƙofar falon, ita dai tasan batayi da kowa cewa yau zaizo wajenta ba, kuma yanzu ba lokacin dawowan Doctor bane, batajin zata iya tashi dan haka saita bawa me knocking door ɗin damar shigowa kai tsaye.
Da sallama ɗauke a bakinta, tashigo cikin falon. Kallon kallo suka shigayiwa juna ita da Zahrah, ita tana kallon Zahrah ne fuska ɗauke da murmushi, yayinda Zahrah kuwa ke ƙare mata kallo, saboda batasanta ba ma ita kwata kwata.
"Da dai anbani izinin shigowa, aida sai na shigo" takatse Zahrah daga kallon da take mata, ta hanyar faɗan haka.
Murmushi Zahrah tayi haɗe da tashi zaune tace "Bismillah, shigo"
Ƙarasowa tayi tsakiyar falon, haɗe da zama akan kujera.
"Sannu da gida" tace tana murmushi.
"Yauwa sannunki da zuwa" Zahrah tafaɗi haka itama tana murmushi. Miƙewa tayi da niyar takawo mata ruwa da lemo, da sauri tace. "A'a barshima basai kinkawomin komai ba, daga gida nake banajin ƙishi"
Kallonta kawai Zahrah tayi kana ta koma kan kujera ta zauna, cike da ƙosawa Zahrah tace. "Baiwar Allah Bangane wace ke ba fa"
Murmushi takumayi akaro na barkatai. "Sunana Afrah, dama nasan baki sanniba, amma ni nasanki, kiyi haƙuri bansaniba ko hakan danayi yaɓata miki rai, jiya naganki a hotel kinacin abinci keda wani, wanda nake kyautata zaton cewa mijinki ne, tunda naganki, naji kin kwantamin arai, kuma wallahi da zuciya ɗaya nake sonki, please idan bazan takuraki ba, inaso muzama ƙawayen juna"
Murmushi Zahrah tayi me sauti, haɗe da cewa "Nagode ƙwarai da ƙauna, amma kuma inaganin kamar akwai matsala, idan har muka fara ƙawance yanzu, dududu fa yau nafara ganinki, kinga dole kafun abota musan halin juna" inji cewar Zahrah.
"Da alamu bakida wata matsala nima kuma haka, kuma insha Allah bazakiyi danasanin ƙawancen mu ba" taƙara da cewa "Akan hanya nake, watarana zanyi miki zuwa na musamman amma kafun nan,please samin number'n wayarki" miƙawa Zahrah wayarta da ta cirota cikin jaka tayi.
Babu musu Zahrah ta amshi wayar tasanya mata number'nta aciki, kana ta miƙa mata abarta.
Murmushi tayi haɗe da miƙewa tsaye, "nagode sosai" tace kana ta nufi hanyar fita daga cikin falon, Zahrah na ganin ficewarta ta sauƙe ajiyar zuciya, haɗe da komawa ta kwanta, aranta tana addu'an neman tsari daga sharrin mugayen mutane, da kuma aljanu....
*** *** ***
Gaba ɗaya yau tatashi jikinta arikice, ganin haka yasa Dr.Sadeeq hana kansa zuwa office, yazauna tare da ita, yanata amsar shagwaɓanta, zuwa yanzu sosai shagwaɓanta yafi na da, tun da tasamu cikin wani sakalci da taɓara ya tsiro mata, shikuwa doctor biye mata yake, hakan yasa gaba ɗaya yanzu tazama wata, shagwaɓaɓɓiya da ita sai kace ƴar shekara 4.
Kwance take akan sofa yayinda kanta ke ɗaure bisa cinyarsa, minti irin me tsinkenan ne abakinta, tana tsotsa a hankali, yayinda shikuwa ke shafa sumar kanta a hankali.
_______
Mamakine ya matuƙar kashesa, ganin unguwa da kuma inda Afrah ta kawosa, ɗago idanunsa yayi ya watsamata su, "Inane nan?" yatambayeta still idanunsa na kanta.
Murmushi tayi masa haɗe da cewa "Unguwar su ƙawartawa da nake gaya maka ne, kuma ganan ma gidan nata" taƙare maganar tanayi masa nuni da gidan dake gefensu, bugawar zuciyarsa ne ya ƙara tsananta, take yaji kansa nayi masa wani irin sarawa.
"Kimaidani gida Afrah, tunkafun ranki ya ɓaci!" cikin yanayi na ɓacin rai yake maganar.
Dama tasan za ayi haka, hanunta ta ɗaura akan nasa cikin son ta rarrasheshi tace "Kayi haƙuri Dear, bazamu wuce 30 minute ba, nasan kasan gidan, kakuma san wacece acikin gidan, banyi haka donna ɓata maka ba, nayi hakane don kawai kasamu salama, ƙwarai nasan idan harta yafema kuma ayau idan kuka ga juna, tabbas komai zai wuce, duk da nasan sai ahankali, amma kuma dukanku zaku samu sassauci...."
"Kimaidani gida nace kona ɓaɓɓala ƙashinki gida biyu anan wajen!!" amatuƙar hasale yaƙare maganar.
Saida ta tsorita domin bata tsammaci wannan tsawan daga gareshi ba.