x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 223

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ki manta da komai, kuma daga yau ɗinnan nagama maganata, next week zaki koma school insha Allah, tun yanzu saiki fara shiri !" Dr yafaɗa fuskarsa babu alamar wasa.


Aikuwa yanayin yanda taga fuskar tasa a ɗaure tamau yasa takasa ce dashi komai, hakanan yake mata kwarjini a cikin idanunta.


Miƙewa yayi tsaye, haɗe da cewa "Kibiyoni waje inason muyi wata magana"


Saurin kallonsa tayi, domin ita rabonta da fita waje tun randa mummunar ƙaddaranta ya rusketa, wanda kuma da bazata taɓa mantawa ba.


Jiki a saluɓe haka ta rufa masa baya, suna zuwa bakin motarsa taja ta tsaya, haɗe da sake tamke fuska.


Murfin ƙofar mai zaman banza ya buɗe haɗe da fiddo wata ƙatuwar leda,


" Idan har kika kumamin musu to tabbas zamu ɓata dake, sannan kuma wlh allurai shida zan danneki na miki da ƙarfin tsiya bandamu ba koda ma sun karye a cikin jikinki, ke kikaso!" Dr Sadeeq yafaɗa cikin tsare gida, yayinda yake miƙo mata zungureriyar ledan dake hanunsa.


"Dan Allah kayi haƙuri kada kamin allura, amma a gaskia ni baxan iya karɓan komai daga gareka ba, ni bazan sake karɓan abun kowa ba, domin kuwa da haka Zaid yasamu ya cuci rayuwata yasamin babban tabo mai wahalar gogewa!" Zahrah tayi maganar cike da tsoro da kuma ƙunan zuciya.




"Alluran dai kikeso kenan, shikenan bana ɗaukosu dama nazo dasu kusan guda goma" Dr Sadeeq yafaɗa yana mai niyar sake buɗe murfin motar.


A tamanin Zahrah ta ruga zuwa gida,


Dariya sosai Dr Sadeeq yashigayi, sosai yarintar Zahrah yake burgesa, haƙiƙa Zahrah yarinyace, domin kuwa kallo ɗaya zakai mata ka fuskanci cewa tsananin yarinta na damun ta sosai, akan allura gaba ɗaya ta ruɗa kanta.


Baiyi yunƙurin komawa cikin gidan ba, sai neman wani yaro yayi yabasa ledan yace ya kai cikin gidan, shikuwa key yayi mawa motarsa yayi tafiyarsa.


Zahrah kuwa tana shiga cikin gidan kaitsaye ɗakinta tawuce haɗe da banko ƙofar ta rufeta gam, faɗawa tayi kan katifarta tana mai sauƙe a jiyar zuciya, ko da taji ƙaran tashin motar Dr Sadeeq ɗin, wani sanyi taji a cikin zuciyarta, haka kawai yazo ya zurkuɗa mata wannnan maka makan alluran nasa, ai wlh bata saɓuwa.....


*New York City*


Kwance yake akan makeken gadon sa, daga shi sai ɗan wani 3 guater jeans, yayin da ya ware ƙafafunsa, duk da cewa akan gado yake, amma saboda tsabar iskanci irin na Zayd sanye yake da takalma (toms) aƙafarsa, yayinda hanunsa ke riƙe da wata zungureriyar kwalbar giya, gefensa kuwa wata kyakkyawar baturiya ce kwance tsirara bako ɗigon abun rufa tsiraici a jikinta, daganinta kasan irin cikakkun ƴan iskan nanne, gaba ɗaya ta tsare Zaid da idanunta, sai wani lasan baki takeyi tamkar tsohuwar mayya, bakomai yasa hakan ba, face yanda gaba ɗaya ta gama kwaɗaituwa da Zaid ɗin, amma kuma yaƙi amincewa ya kusanceta, gaba ɗaya wani irin muguwar sha'awarsa takeji, duk kuwa yanda ta nu namasa zallan karuwancinta a fili, yaƙi kusantar ta, saima sake je fata cikin kogin sha'awa da yayi,


Zaid kuwa da gangan yaƙi kusantarta, domin yanzu tsagwaran iskanci yake ji dashi, sai ya ɗauko mace yagama ƙwaƙuleta, yabarta batare da yayi sex da'ita ba, wayarsace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, har ƙiran ya katse Zayd bai ko kalli inda wayar take ba balle yasan wake ƙiransa,,


Cike da salo irin na ƴan bariki wanda ta yarda cewa idan hartayi masa zai kusanceta, ta sake matsowa daf dashi, a hankali ta zura hanunta acikin 3 guater jeans ɗinsa, haɗe da soma shafa kan mararsa a hankali, yayinda ɗaƴan hanunta ke kan faffaɗan ƙirjinsa tana shafawa slowly, ta yadda zaiji abun har tsakiyar kansa, cike da ƙwarewa tashiga murza ....


A hankali yaɗago idanunsa da suka soma sauya launi ya sauƙesu akan baturiyar, ai kuwa yayi kyakkyawan gani, domin kuwa fuskar Zahrah yagani ta bayyana akan ta baturiyar, bakomai yasa hakan ba face giyar da yasha da tasoma yi masa aiki, da ƙarfin gaske yajawo baturiyar jikinsa, haɗe da matseta ƙam a ƙirjinsa, take jikinsa yasoma ɓari,lokaci ɗaya yashiga bata kyakkyawan romance wanda yasanyata tafara nishin daɗi.


Gaba ɗaya baturiyar nan tadawo masa Zahrah acikin idanuwansa, baisan sai yaushene matsanancin sha'awar da yakemawa Zahrah zata sake saba, a kullum a ko wani daƙiƙa sha'awar Zahrah sake ninkuwa masa takeyi acikin zuciyarsa,


Hmmm duk jaraba irin ta wannan baturiya yau fa sai dai ta haƙura, domin kuwa Zaid tun kan abunnasa yagama shiga jikinta, yayi saurin tureta gefe, wani irin masifaffen ɓacin raine yazo masa, ƙarya ne yasani ba Zahrahn sa bace wannan, sharrin giyane kawai, idan har giya zata iya sanyawa yaga fuskar wata a matsayin Zahrah, to bata isa sawa ɗanɗanon wata yakasance tamkar na Zahrah'nsa ba, Zahrah da ban take komai nata na dabanne, cikinta a cike yake, bakamar sauran matan dayake mu'amala dasu ba, wanda su gaba ɗayansu a wage suke daga ciki har waje, ita kuwa Zahrah daga ciki har waje a haɗe take, bakomai yasanyashi ture baturiyar nan gefe ba face jinsa da yayi ya faɗa zuruf tamkar anzura ƙwallo a raga, bathroom ya wuce kaitsaye yasakarmawa kansa shower.


Itakuwa mayyar baturiyar dolenta ta maida ɗan fingilan rigarta ta fice daga cikin ɗakin, cikin matsanancin sha'awa, Zayd ya jangwalo mata bala'i.


Zayd kuwa a daddafe yayi wanka, domin kuwa wani irin ciwo marar sa ke yi, koda yafito a wankan a daddafe yasha tea da lamon tsami, kwanciya yayi lamo yana mai sauƙe numfashi akai akai, lallai yazame masa dole yakoma Nigeria kodan Zahrah ma, yazame masa dole yakomawa Zahrah domin kuwa bazai zauna sha'awarta ta kashe shi ba, amma ya ɗau alƙawarin cewa wannan karon bazai mata da ƙarfi ba, lallaɓata zaiyi tabasa kanta cikin sauƙi, da wannan tunanin bacci yayi awungaba dashi,
(Hmmm ayi bacci lafiya Zaidun Munubiya,lol).


Nigeria.


Yaune ranar da Dr ya shaidawa Zahrah cewa zata koma makaranta.


Don haka tun tashinta, tatashi tanajinta wani iri, gaba ɗaya ji take gabanta na faɗuwa, hakanan take tsarge, gani take tamkar kowa yasan maiyafaru da'ita, a daddafe tayi wanka, wata simple gown tasanya ajikinta, wanda bata da ado ko kaɗan, wata ƙatuwar lufaya ta zura wanda tsawonsa ya wuce guiwarta. Jin maganarsa a tsakar gidan, yasa taji ƙirjinta ya ɗan buga kaɗan, cikin rashin kuzari tafito daga cikin ɗakin.


Kamar yanda yayi mata kyau, haka shima yaga tayi masa kyau, duk da cewa babu ɗigon kwalliya akan fuskarta.


"Muje ko!" Yafaɗa a taƙaice, saurin ja da baya tayi haɗe da girgiza kanta, domin kuwa ko karen hauka ne ya cijeta, bazata yarda ta shiga motarsa ita kaɗai ba.


"Muje Baffa na jiranmu a waje" Dr Sadeeq yafaɗa domin yaga alamar a tsorace take,


Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe haɗe da bin bayansa, domin kuwa tuni yariga da yayi gaba.


(Please two days zakuna haƙuri dani domin typing ɗin ba ya yawa, ina busy ne sosai, dan Allah kada kuyi ƙorafi, insha Allah next page zanmuku da yawa)


*27/November/2019*


*Voted, Comment, and Share please...follow me on wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*


*🌈Kainuwa Writers Association*


*{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}*


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*Chapter 42 to 43*


Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi ɗare ɗare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haƙora yake kai kace anmasa kyautar ƴan kuɗaɗe ne.


Dakansa ya buɗe mata murfin motar ɓangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige ɓangaren driver haɗe da mawa motar key...


Tunda suka ɗau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba ɗaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya, akai akai yake satan kallonta tacikin madubi..
A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu, dai dai bakin ƙofar hall ɗin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall ɗin zasu gudanar da lecture.


A hankali ta buɗe murfin motar ta fito kafaɗarta ɗauke da jakar makarantar ta, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta nufi cikin hall ɗin kai tsaye, ko wai gensu batayi ba, tanashiga hall ɗin kallo yadawo kanta, take taji wani irin muguwar faɗuwar gaba haɗe da karyewar zuciya, gani take tamkar kowa yana ganin abun da yafaru da ita rubuce akan goshinta.


Karab idanunta suka sauƙa akan Husnah wacce take faman aikin haɗa wasu takardu dake gabanta. wani irin sanyi taji zuciyarta tayi sakamakon ganin husnah, domin kaf makarantar bata mu'amala da kowa bayan husnah, da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah, domin koda wasa batayi tunanin ganinta ba.


"Kamar mafarki nakeyi gaskia naji daɗi sosai ƙawata!" Husnah tafaɗa cike da tarin farinciki.


Zama sukayi a tare dai dai lokacin Sir Bature yashigo cikin hall ɗin, tsit haka ajin ya ɗauka ana ta sauraran lecture ɗin dayake yi musu, a zahirin gaskia tanajin abun da yake cewa, amma kwata kwata bata fahimtarsa, awa biyu suka ɗauka chur suna lecture, kafun daga bisani yafita daga ajin, gyara zama Husnah tayi haɗe da mai da kallonta ga Zahrah cike da kulawa tace " Yanzu ina likitan yake ?"


Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa " Ba maganar Doctor bace damuwata Husnah, babban damuwata shine gani nake tamkar abun da Zaid yamin yana rubuce a gaban goshina, Husnah gani nake tamkar kowa yasan abun dake damuna !" Zahrah taƙare maganar cikin raunin zuciya.


" Kada kice haka Zahrah, babu wanda yasan abun da yafaru dake, kada ki ɗaga hankalinki ƙawata kinfasan kowa da irin tasa ƙaddaran, kuma zuwa yanzu na tabbatar kin mai da al'amuranki ga Allah, shima Zaid nasan kinbarsa da Allah "


Murmushi mai ciwo Zahrah tayi haɗe da kallon ƙawarta ta, cike da ƙuna tace " Banda wata hanya wanda tawuce barinsa ga Allah, nasan nan bada jimawa ba Allah zai bimikin haƙƙina " taƙare maganar cikin raunin zuciya,


Hannayenta Husnah ta kama suka fice daga cikin ajin, kai tsaye cafeteria suka nufa don cin abinci. Balaifi sosai tasamu nutsuwa a yau ɗin domin kuwa Husnah bata barta tayi kaɗaici ba. Ƙarfe 5 dai dai suka fito daga cikin lecture ɗin ƙarshe na ranan yau ɗin, kasan cewar ta kwana biyu bata zo makarantar ba, sai take jinta gaba ɗaya duk ta gaji, cikin nutsuwa take takunta yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, ba abun da zuciyarta keyi banda bugawa, gaba ɗaya tsoron fita daga cikin school ɗin takeyi, gani take tamkar tana fita za'a kamata, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafunta, dagani kasan bason tafiyar take ba. a hankali ta matsa gefe, haɗe da waigowa don ganin waye wannan ya matsa mata da horn ɗin motarsa, karab idanunta suka sauƙa akan sa, kasancewar gilasan motar tasa gaba ɗaya a sauƙe suke, sam batayi tsammanin ganinshi ba, murmushi yasakar mata haɗe da cewa " Da baki matsaba ai dana take ki !" yafaɗi maganar cikin yanayin tsokana, ɗan guntun murmushi itama tayi haɗe da taɓe baki, "ai idan haka ta kasance zanfikowa jin daɗi " Zahrah tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.


"Shigo mutafi!" yafaɗa cikin tsare gida.


Saurin kallonsa tayi bakinta ɗauke da tarin tambayoyi, amma kuma takasa koda motsa bakinta ne balle ta furta wata kalman.


"Kintsaya kina kallona, ba dole idan bazaki bini ba, saina yi tafiyata!" yaƙare maganar yana mai niyar tada motar tasa.


Da sauri ta zagaya haɗe da buɗe murfin motar, gefen mai zaman banza ta shiga haɗe da tamke fuskarta tamau tamkar wanda yagayamata magana marar daɗi.


Da ƙyar ya iya ɓoye dariyan dake cinsa, domin kuwa tsoro ya hango ƙarara akan fuskar Zahrah, "Naɗauka ai zakijamin ajine, da sai na tafi na barki ba ruwana!" yafaɗi hakan cike da shauƙi.


Harara ta watsa masa haɗe da sake turo baki gaba, cike da shagwaɓa wacce batasan tayi ba tace "Nifa idan surutu zakamin ka sauƙeni nayi tafiyata"


Yanzu kam kasa ɓoye dariyarsa yayi saida ya dara kafun ya ce " Bazan sauƙe kiba ai bani na ɗauko ki na saki ba, zaki iya fita da kanki ma, ai nasan ke jaruma ce zaki iya kare kanki ako da yaushe, har ma zaki iya shiga cikin ko wani abun hawa da ƙwarin guiwarki !"


Saurin kallonsa tayi domin kuwa sarai ta fahinci inda maganganunsa suka dosa, wato dai shima ya hango zallan tsoron dake kwance akan fuskarta.


"Shikenan tunda haka kace" tafaɗi maganar tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar ta fita.


"Haba ƴar ƙanwata, nifa wasa nake miki, kiyi haƙuri ki bari na kaiki gida kinji ko!" Doctor yafaɗi maganar cikin lallashi, domin yafahimci cewa saurin fushi ne da'ita.


A cikin zuciyarta tayi hamdala, sakamakon hanata fita daga motar da yayi, domin dama burga ce kawai tsoron dake cikin zuciyarta bazai barta ta iya tafiya ba, duk runtsi tafiso shiɗin ya kaita domin tafi yarda dashi fiye da kowa a yanzun..


Kwantar da bayanta tayi akan kujeran motar haɗe da lumshe idanuwanta, gaba ɗaya jinta take a gajiye, ga wani irin ciwon kai dake damunta, a hankali take buɗe idanunta, a zabure tatashi zaune sakamakon ganin da tayi Doctor ya nufi wata hanyar da ita saɓanin hanyar gida.


"Inazaka kaini !" Tafaɗa a razane, kuma cikin yanayin tsoro,


"Saidake zanyi!" Yayi maganar babu alamar wasa akan fuskarsa.


"Dan Allah kayi haƙuri ka sauƙeni, ka barni naji da duhun dake cikin rayuwata, kada ka ƙaramin wani bala'in dan Allah!!" tuni hawaye sungama wanke fuskarta.


Wani irin kallo Doctor yayi mata haɗe da sakin murmushi bai kuma sake ce da ita komai ba, saima maida hankalinsa da yayi ga tuƙin da yake,


Yanzukam kuka mai sauti ta sanya haɗe da soma cewa " Dan Allah kada ka sake cutar da rayuwata, zan iya amincema ka kasheni amma bazan iya jure wa ba, idan kaci mutumcina, wlh na yarda ka wurgani kan titinnan mota ta taka ni, amma dan Allah kada kamin komai!!" taƙare maganar cikin matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Daidai lokacin suka iso gaban wani makeken mall wanda yagaji da ƙawatuwa,
yana parking motar baiko kalletaba yayi saurin ficewa daga cikin motar haɗe da dannawa gabaki ɗaya ƙofofin fita a motar luck, domin yasan dole zatayi ƙoƙarin fita daga cikin motar,


Kuka sosai Zahrah keyi haɗe da sanya ƙarfinta tashiga dukan glass ɗin motar, tana mai ihun neman taimako amma babu kowa a wajen balle tasaran za a temaketa, domin kuwa wajen parking space ne.


"Ashe duniya cike take da azzaluman maza, ashe itakam rayuwarta a haka zata ƙare? wayyo Allah itakam ƙaddaranta kenan" abun da take faɗa kenan acikin zuciyarta tana kuka mai tsuma zuciya,domin a zaton ta hotel ya kawota zai kuma lalata mata rayuwa.


Daidai lokacin Doctor Sadeeq ya dawo hanunsa ɗauke da manyan manyan ledodi guda biyu, yana shiga cikin motar yakuma danna mata luck haɗe da mawa motar key da gudun gaske ya hau titi.


Zahrah kam muryanta har ya dashe kukanma harya daina fita domin gaba ɗaya ta gama sadaukar da cewa yau ce ranar mutuwarta, kukantane yasoma tsagaitawa ganin sun nufi hanyar unguwarsu, a hankali hawayenta suka daina zuba, yayinda tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, bakomai yasa hakanba face ganinsu da tayi sun shigo cikin unguwarsu tsulum, a bakin ƙofar gidan nasu yayi parking cike da kulawa yajuyo da kallonsa ga Zahrah wacce take ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, alamar taci kuka ta ƙoshi.


"Banga laifin kiba Zahrah, domin dole zakiji matuƙar tsoro, a iya tsawon rayuwata bantaɓa cutar da wata mace ba, kuma bazan fara akan ki ba, bazan taɓa iya cutar dake ba Zahrah, inaso ki yarda dani, ban kuma yi haka don na cutar dake ba, nabiya dake ta mall ɗinne don inaso muje kiyi sayayyan abubuwan dakikeso da kanki, amma sai naga gaba ɗaya kinfirgita, kiyi haƙuri na tsorataki ko ƙanwata !!" Doctor Sadeeq yafaɗi maganar cikin tsananin tausayawa da kuma lallashi ga Zahrah'n..


Kuka kawai Zahrah takuma fashewa dashi haɗe da cusa kanta cikin cinyoyinta, a hankali ya kama hanunta haɗe da matsewa a cikin nasa hanun, "Banason kuka Zahrah, bana ce kiyi haƙuri ba!" Dr yafaɗa cikin damuwa.


"Bakaine zaka bani haƙuri ba likita, nice zanbaka haƙuri, nayi maka mummunar fahimta, dan Allah kayi haƙuri, wlh tsoro nakeji banso wani abu yasake faruwa dani...!" taƙare maganar tana kuka sosai.


"Idan kinaso nayi haƙuri to kidaina kuka kinji ƙanwata!" yafaɗi maganar yana mai ƙare matse hanunta a cikin nasa hanun.


A hankali tashiga share hawayen dake ambaliya akan fuskarta, ji takeyi zuciyarta tayi mata sanyi.


"Bakya kyau idan kina kuka, kinfi kyau idan kina dariya, kije gida kiyi wanka ki huta, banso kisake zubar da hawayenki kinji Zahrah, ungo wannan ledan kishiga gida, akwai waya a ciki na samiki sim da komai, akwai games dayawa a ciki,nasan zai ɗebe miki kewa, banson ganinki cikin damuwa Zahrah, kije gobe zanzo na kaiki school dakaina, Allah yasa bazakimin gardamaba " yaƙare maganar yana ƴar dariya.


Murmushi itama Zahrah tayi haɗe da ƙarɓan ƙatuwar ledan dayake miƙo mata, batare da tayi masa gardama ba, cikin rashin kuzari ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, harsai da yaga shigewarta cikin gida kafun ya ta da motar tasa ya bar unguwar tasu..


Zahrah tanashiga cikin gida kai tsaye ɗakinta tawuce, jakarta da ledan da Dr Sadeeq ya bata ta ajiye. Kayan jikinta tashiga cirewa, zani ta ɗaura a kirjinta haɗe da sanya hijabi tafice daga cikin ɗakin, zaune ta taradda Inna a tsakar gida, sannu da gida kawai Zahrah tayi mata, haɗe da shigewa cikin bayan gida, tana fitowa a wanka ta bi lafiyar katifarta domin dama dai bata wani jin yunwa, ledan da Doctor yabata ta jawo haɗe da buɗewa, kyawawan dogin riguna ne suka bayyana acikin ledar saikuma dangin su snacks dasu choculate, kyakkyawar kwalin wayar da tagani acikin ledar taciro SAMSUNG GALAXY S10 shine sunan da ke rubuce ajikin kwalin wayar, wani irin faɗuwa gabanta yayi take nunfashinta yashiga gudu
End Ads