gaske, gaskia komai na Zaid me kyau ne, domin kuwa kowani kaya yasanya saiya yi kyau, bakuma kayanne yake masa kyauba, shi ɗin kansa ne yake mawa kayan kyau,lol.
Haɗaɗɗen takalminsa sau ciki ƙiran kamfanin Gucci yasanya, aƙafansa, bayan ya ɗaura tsadadden agogon nan na Rolex a hanunsa mai kyau da burgewa. Daddaɗan ƙamshi ne kawai ke fita daga jikin shi, ƙamshine mai wahalar mantawa.
Black facing cap, yasanya akansa, domin kuwa yanayin garin ana ɗan busa sanyi, duk dakuwa cewa daga cikin sanyin yafito.
Wayarsa yaɗauka haɗe da car key ɗinsa, kai tsaye yafice daga cikin ɗakinnasa. Ɓangaren Mom ɗinsa yanufa. Hajiya Safara'u ne tsaye a gaban ƙatoton teburin cin abinci, yayinda Alhaji Ma'aruf ke zaune tana serving ɗinsa, batasan da shigowarsa ba saiji tayi ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗarta, cike da soyayyar mahaifiyarta sa yace "Barka da gida Momy!"
Cike da tsananin farinciki itama ta rungumesa haɗe da basa sumba a kan kumatunsa, "Barkanka da dawowa my son, ya gajiyar hanyar?"
"Alhmdlh!" Zaid yafaɗa a taƙaice, bayan ya janye jikinsa daga na mahaifiyartasa. Ƙoƙarin juyawa yakeyi, Mom tace "Inakuma zaka my son ba abinci kazo ciba?" cike da kulawa ta tambayesa.
Ɗan ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa "Banajin yunwa Mom, idan nadawo zanci!" baijira jin maizasu ceba yasakai yafice daga cikin falon.
Da kallo kawai Mom tabisa har yafice, fuskarta ɗauke da damuwa, itakam ta rasa wani irin haline da Zaid, sam ba'a iya gane gabansa da bayansa.
"Miye abun shiga damuwa Hajiya Safara'u? zuwa yanzu yakamata ace duk wani hali na yaronnan Zaid kin gama saninsa!" Alhaji Ma'aruf yafaɗi hakan cike da nuna kulawa ga matar tasa.
"Nasan halinsa Alhaji, amma kuma ace mutum shi baya taɓa sanjawa, ko da yaushe fa Zaid bayason zama a cikin mu, sannan kuma sam baya sakewa damu!" Mom tafaɗi hakan cike da damuwa.
"Zauna muci abincin mu, aishi ba ƙaramin yaro bane, yasan me yakeyi!" Alhaji Ma'aruf yafaɗi hakan yana mai kama hanun Mom yazaunar da'ita a kusa dashi.
Zaid kuwa yana fita daga ɓangaren mahaifiyartasa, kai tsaye wajen motarsa yanufa, koda driver yanemi da yabarsa ya tuƙasa, ɗaga masa hanu yayi alamar baya buƙata, shida kansa yayimawa motar key, ya harbata zuwa kan titi.
Tafiya yake cikin nutsuwa yayinda airpiece ke saƙale a kunnuwansa, wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ganin cewa babban manager'n company'nsa dake nan gida Nigeria ne ke ƙiransa yasanya shi ɗaga ƙiran. Banji mai Manager'n nasa yace masa ba, sai gani nayi ya'aje wayan, haɗe da buga dogon tsaki, lokaci ɗaya yakarkata akalar motar tasa zuwa wata hanya daban saɓanin hanayar daya nufa, wanda zai sadasa da unguwar su Zahrah.
Dr Sadeeq kuwa yana barin unguwar su Zahrah kaitsaye gidansu yanufa, acewarsa gwamma yayi maganin matsalarsa tunkafun tayi nisa.
Usaina mai aikin ɓangaren Hajiyarsa yasanya tane ma masa iso awajen Hajiyar tasa, domin kuwa bai isketa a falo ba.
Da sallama yashiga cikin ɗakin Hajiyar tasa, fuskarta ɗauke da fari'a ta amsa masa sallaman da yakeyi. Zaune take akan gado, yayinda take duba wasu kayayyaki dake zube a gabanta.
"Barka da huwatawa Hajiya!" yafaɗa cike da ladabi.
"Yauwa barkanka, kamar kuwa kasan ina nemanka, wai me kake nufi da auren nan ne Sadeeq? har yanzufa banga kana wani cuku cuku ba, kayan lefe ma saini kabarmawa ɗawainiyar haɗasu, gashi kuma Salima tacemin tunda kaje sau ɗaya baka sake zuwa ba, mai ke damunka ne wai?" Hajiya tatambayesa cike da kulawa.
Kansa yashiga sosawa haɗe da sake yin ƙasa da kansa, "Am...dama Am...." "Dakata banson wani kwana kwana, kafaɗi abunda zaka faɗa kai tsaye kawai" Hajiya ta katsesa daga kame kamen maganan dayake ƙoƙarin yi mata.
"Hajiya kamar dai yanda na faɗamiki ne, wallahi Hajiya dagaske nake, yanzu nasamu wacce nakeso kuma idan harkin yarda aurenmu bazai wuce nan da Sati uku ba, kamar yanda kikeso!" yafaɗi hakan cike da ladabi.
Sororo haka Hajiya ta tsaya tana kallonsa, "anya kuwa Sadeeq yana lafiya? " tatambayi kanta.
"Inagadai bakasan mekake cewa ba Sadeeq, wato nikakeson watsamawa ƙasa a cikin idanu ko, ya yi maka kyau, to inaso kabuɗe kunnuwanka da kyau ka saurareni, wallahi ko da wasa kakuma zuwamin da irin wannan zancen saina ɓata maka rai, nagama baka duk wata dama dazan baka, bakuma zan sake baka wata daman ba, tashi kabani waje, tunda nalura kai baka da tunani!" Hajiya ta ƙare maganan cikin faɗa.
Cikin rashin kuzari haɗe da sanyayewar guiwa Dr Sadeeq yamiƙe daga gaban mahaifiyartasa, haɗe da nufar ƙofar fita daga cikin ɗakin,
Saida yakai ɓaƙin ƙofar fita ckafun yatsaya cak, haɗe da juyo da kallonsa ga Hajiyar tasa cikin murya mai rauni yace "Hajiya dan Allah.."
"Fita kabani waje nace!!" Hajiya takuma faɗa cikin ɓacin rai tanamai yi masa nuni da ƙofar fita daga ɗakin...
*(Readers nifa Hajiyannan tasoma ban haushi yasin🙄🤣)*
*Kuyi manage da wannan ba lallai gobe nayi typing ba shiasa, namuku yau*
*11/December/2019*
*Voted, Comment, and Share please..... Follow me on Wattpad @fatymasardauna*
*6:17 pm*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
'''{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
(Kuyi haƙuri shekaran jiya nayi mistake ɗin number 52 to 53 zansa, sainasaka 53 to 54🙏)
*CHAPTER 55 to 56*
Cikin sanyin jiki Dr Sadeeq yafita daga cikin ɗakin mahaifiyarta sa. Gaba ɗaya jiyayi zuciyarsa ta cika da ƙunci. Yana isa ɓangarensa ya zube akan ɗaya daga cikin kujerun falonnasa, "yanzu wazai je yasamu da wannan matsalar? tabbas yasan Hajiyarsa mutum ce mai kafiya, idan tace eh zai yi wuya ta dawo tace a'a"
hanunsa yasanya cikin sumar dake kwance akansa haɗe da yamutsa ta, sunan Aunty Raliya ce yafaɗo masa arai, tabbas ita kaɗaice ƴar uwarsa da zai kai mata matsalansa har ma ta tayasa magancewa, sai dai kuma yanatunanin itama ra'ayinta ɗayane da Hajiya, amma yasan idan yayi mata kyakkyawan bayani zata fahimcesa, zumbur yamiƙe daga zaunen dayake.
Ko bedroom baishiga ba yakuma ficewa daga cikin falon, mota ya koma, haɗe da kunnata, mai gadi ne ya wangale masa gate ɗin gidan yafice.
Hajiya najin ƙarar ficewar motarsa daga cikin gidan ta sauƙe ajiyar zuciya.
"Gaba ɗaya tunaninta ya kulle, batasan wani irin abu Sadeeq keshirin shigo mata dashi cikin gida ba, kusan sau uku kenan tana bashi dama, akan yafito da matar aure, amma dazaran lokacin da ta ibar masa yacika, sai ya farayi mata kame kame, yanzu da tagaji da sakarcinsa ta zaɓa masa mata, sai yake nema yawatsa mata ƙasa a idanu, bakuma zata lamunci hakanba.
Direct Dr Sadeeq gidan Aunty Raliya yanufa, domin baida wata ƴar uwa da ta wuce ta a duniyar nan.
Yanashiga gidan tunbai gama fitowa daga cikin motarsa ba, su Meenal da Affan ƴaƴan Aunty Raliya, suka rugo da gudu zuwa garesa, dama wasan ball suke a farfajiyan gidan nasu, hakan yasa duk wanda yashigo da kuma wanda zaifita zasu gansa.
Rungumesu yayi a jikinsa, haɗe da shafa kawunansu, "Oyoyo babies ɗina, ashe girma yazo muku, har wasan ball kukeyi!" yafaɗi hakan cike da nishaɗi.
"Eh Uncle ai harma nafita iyawa!" Affan yafaɗi haka cike da zumuɗi.
"Ƙaryayake Uncle baifini iyawa ba" Meenal tafaɗi hakan tana mai kama ƙugu, alaman ƙarya Affan ɗin yakeyi.
Murmushi kawai Dr yayi haɗe da sake shafa kansu, "kuyi wasa da kyau, idan nafito zan baku alewa!" yafaɗa yana mai nufar kofar da zata sadashi da babban falon gidan. Yayinda yabar su meenal sunata tsallen murna saboda yace zai basu alawa.
Da sallama ɗauke a bakinsa yashiga cikin falon.
Aunty Raliya dake zaune tana kallon tv, ta amsa amsa masa sallamar tasa, fuskarta ɗauke da fari'a, haɗe da yi masa iso.
Ƙarasowa yayi yazauna akan kujera, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, gaba ɗaya a gajiye yakejinsa, domin tun safe yau baisamu nutsuwa ya huta ba.
Aunty Raliya da kanta, ta jere masa kayan fruit da juice agabansa, cikin tsokana tace dashi
"Ango kasha ƙamshi, duk gajiyar shirye shiryen bikinne haka?"
Ɗan ɓata fuska yayi haɗe da ɗaukan apple ƙwaya ɗaya ya kai bakinsa.
"Ango labari ya sauya salo" yafaɗi hakan bayan ya cinye gutsuren apple ɗin dake bakinsa.
Cikin mamaki Aunty Raliya tace "bangane ba mekake nufi?"
Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da gyara zamansa.
"Akwai matsala Aunty!" yafaɗi hakan lokacin da gaba ɗaya yanayin fuskarsa ya sauya.
"Akwai wacce nakeso na aura, yarinyar tana matuƙar buƙatar taimakona, nayi ƙoƙarin na fahimtar da Hajiya hakan, amma taƙi saurarata, yanzu haka daga gida nake, nasoma yi mata bayani, tace natashi na bata waje, gaba ɗaya kaina yakulle bansan yazanyiba Aunty Raliya!"
Ya faɗi haka cikin damuwa.
Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Aunty Raliya ta sauƙe "Turƙashi, lallai kuwa kazo da babbar magana, amma maiyasa tunda baka bayyana wacce kake so ɗinba, sai yanzu da komai yariga da yayi nisa? kafasan Hajiya da kafiya balallai ne ta fahimce ka ba, shawarata a gareka shine, kamabar wannan zancen, domin balallai kasamu abun da kakeso ba!" Aunty Raliya tafaɗi hakan da'iyaka gaskiyarta.
Cike da rauni Dr Sadeeq ya kalli Yayartasa. "Dan Allah taimakona zakiyi Aunty, kije kisameta kibata baki, wallahi inamatuƙar son Zahrah, sannan kuma yarinyar tana buƙatar kulawata, nikaɗai nasan matsalarta, please Aunty!!" yafaɗi haka yana me marairaice fuska, hadda haɗa hannuwansa biyu ga Aunty Raliya'n alamar roƙo.
"Abune me matuƙar wuya amincewar Hajiya, amma zan jarraba, saidai kafun naje gareta, dole sainasan wacece yarinyar kuma su waye iyayenta, saboda kada aje Hajiya ta amince, akuma zo asamu wani mummunan labari akan ta"
Wani irin bugawa ƙirjin Dr Sadeeq yayi, domin kuwa anzo wajen, lallai baizama dole kowa yafahimcesa ba domin sanin sirrin Zahrah, zai iya sanyawa kowama yaƙi amincewa da aurensa da'ita, wanda shi a wajensa baiga ta'inda aurensu zai zamanto rashin dacewa ba, amma ba'a ƴar ɓoye a harkan aure, domin koda anɓoye tofa sai ya bayyana.
"Sunanta Zahrah, a unguwar Maraba take, sannan kuma marainiyace bata da uwa bata da uba, baffanta ne yake riƙonta, yarinyar tana da hankali sosai Aunty, sannan kuma tana da tarbiya, bata da wani aibu ko abun kushewa a tattare da'ita, saidai kuma..." kasa ƙarasa maganar yayi, domin kuwa baisan yanda yayartasa zata ɗauki maganar ba.
"Ƙaddarace kuma tana kan kowa, haka kuma babu wanda ya'isa ya tsallake mata idan har tafaɗo kansa, akwai wani tsohon saurayinta da ya yaudareta yayi mata fyaɗe, watannin baya da suka wuce, wanda hakanne ma sanadin haɗuwata da'ita, amma ni banɗauki hakan amatsayin wani abu ba dazai hanani aurenta, kasancewar kowa da'irin tasa ƙaddaran a rayuwa!"
Sororo haka Aunty Raliya ta hangame ido da baki tana kallon Dr Sadeeq har ya idar da zancensa mai kama da tatsuniya.
Salati Aunty Raliya tasanya cike da tsantsar mamaki haɗi da al'ajabi, lallai Sadeeq baisan meyake faɗa ba.
"Fyaɗe! fyaɗe fa kace Sadeeq, anya kuwa kansan mekake faɗa? yanzu kai saboda rashin hankali irin naka, karasa wacce zaka gani kace kanaso, sai yarinyar da taraba budurcinta wa ƙattin maza, yarinyar da wani yagama sanin sirrinta!" Aunty Raliya ta faɗi haka cike da ɓacin rai.
Saurin rumtse idanunsa yayi domin jin magananganun Aunty Raliya'n yake tamkar sauƙan aradu, a kunnuwansa.
Cigaba tayi da cewa " Lallai yanzu na tabbatar dacewa ba lafiyanka lau ba, taya kana cikekken namiji mai hankali da kuma kamala, karasa wacce zaka aminta da ta zamo uwar ƴaƴanka sai wacce wani ƙato ya haiƙemawa, yazama dole kasanja tunani Sadeeq, wannan ma ai zancen banzane, to gwarama kasani wannan yarinyar ba zaka taɓa aurenta ba matuƙar mu jininka ne!" Aunty Raliya ta ƙare maganar cikin hargowa.
"Haba Aunty maikikeson cewa ne? dan Allah kada kimin haka, nafaɗamiki matsalatane don bani da wacce tafiyemin ke, dama nasan za'a samu rashin fahimta, domin zakuga kamar Zahrah ba kamemmiyar mace bace, alhalin kuma bahaka take ba, tsautsayine yafaɗa mata, amma ni nayarda na amince zan aureta a haka, kada fa kimanta duk wanda yarufa asirin wani to Allah zai rufa masa nasa asirin, kitaimaka mu inganta rayuwar Zahrah, kitaimaka mucireta daga ƙunci, musanyata cikin farinciki!" yafaɗi haka cike da rauni.
Murmushi mai ciwo Aunty Raliya tayi haɗe da cize laɓɓanta cikin takaici ta ce dashi.
"Kuskurenka na farko a rayuwa shine yarda dakayi cewa da gaske fyaɗe aka mata, shin ka ko san ƴan matan yanzu kuwa Sadeeq? to bari kaji wani abu, a shegen son kuɗi irin na ƴan matan yanzu, su da kansu suke saida budurcinsu ga wani daban, idan suka samu makahon da'idanunsa ya rufe ruf har yazo musu da zancen aure, sai su taƙarƙare su zabgamasa ƙarya kan cewa fyaɗe akamusu, bayan suda kansu suka kasa budurcin nasu a faifayi suka kai tallanshi kasuwa, ni ƴar uwarka ce ta jini bazan taɓa son wani abun da zai cutar da kai ba, saboda haka tun muna mubiyu nidakai, mubunne maganarnan anan, tun kafun ma yaje ga kunnen Hajiya, domin kasan idan taji cewa wacce kake shirin kawo mata ita amatsayin suruka, ba mutumiyar ƙwarai bace to zatayi mugun saɓa maka!!"
Take idanun Dr Sadeeq suka kaɗa sukayi ja, bakomaine ya sanya hakan ba face irin munanan kalaman da Aunty Raliya ta dinga jifan Zahrah dashi, tabbas yasan cewa mafi ƴawancin ƴan matan yanzu suna sayarda budurcinsu saboda abun duniya, amma banda Zahrah'nsa aciki, yasan Zahrah macece mai kamun kai, kuma duk wanda yayarda da ƙaddara dole ne ya tausayawa mata masu tsintar kansu a irin halin da Zahrah ta tsinci kanta a ciki.
"Ita bakamar yanda kike tunani bane Aunty Raliya, ki saurareni saina baki gaba ɗaya labarinta, marainiyace ta cancanci a tausaya mata, nima Namiji na tausaya mata balle ke mace, kuma dama ance ciwon ƴa mace na ƴa mace ne!" Dr yafaɗi hakan cike da son ganar da Yayarta sa, cewa ba bu wani aibu agame da aurensa da Zahrah.
Gaba ɗaya duk iya abun da yasani agame da Zahrah, bai ɓoye mata ba, sai da yasanar mata, atunaninsa hakan zai sanya Aunty Raliya ta ƙaunaci Zahrah, amma me sai gani yayi tana taɓe baki haɗe da kawar da kanta gefe alamar ma ta'inda maganar tasa take shiga tanan take fita.
Yana idar da zancen ta dubeshi haɗe da ɓata fuska tace "Kagama? kai a tunaninka zaka bani wata hujja dazata sanya naga dacewar aurenka da'ita ne, hmm niba yarinya bace Sadeeq, yakuma zama dole kasanja tunani, kakuma manta da maganar wata wai ita Zahrah, idan kuma kafison kafuskanci ɓacin rai daga wajen Hajiya, to kaci gaba da zama akan bakan ka harmaganan takai ga kunnen Hajiya!!" tanakaiwa nan a zancenta ta miƙe fuuu tawuce cikin ɗakinta tabarshi zaune.
Hannayensa yasanya duka biyu ya tallafi kansa, lallai akwai babban ƙalubale a gareshi, agun Aunty Raliya ma kaɗai ga'irin ɓacin ran daya fuskanta, inaga Hajiyarsa kuma.?
Miƙewa yayi daga zaunen da yake tamkar wanda ƙwai ya fashewa a jiki haka yake tafiya, gaba ɗaya ƙwaƙwalwarsa tasake dagulewa, yazone don yasamu mafita amma sai gashi abubuwa sun sake dagulewa.
Da ƙyar yake iya tuƙa motar tasa. Haka yanufi gida cikin rashin kuzari, sai dai fa haryanzu bai saduda da maganar Auren Zahrah ba, yanaji ajikinsa cewa Zahrah zata zamo matarsa Insha Allah.
Gagarumin meeting su ZAID suka gudanar mai zafi, a babban hotel ɗin nan wato SHERATON, sosai aka samu riba dakuma ƙarin buɗi a ɗaya daga cikin company'n nasa da suke Nigeria, hakan yasa yaƙarawa gaba ɗaƴa ma'akatansa albashi.
Sunjima suna meeting ɗin dan haka amatuƙar gajiye suka fito dukansu, lokacin har dare yasoma rufawa. Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, yayi yaga karfe 6 daidai na yammaci, ɗan ƙaramin tsuka yayi haɗe da soma yunƙurin cire rigan suit ɗin jikinsa wada yaɗaura akan kayan dake jikinsa,
saboda gajiyan da yayi bai iya tuƙi da kansa ba, sai driver'nsa yaƙira yayi driving ɗinsa.
Gyara kwanciyansa yayi ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sarawa kansa keyi masa, daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa sosai meeting ɗinnan ya ɓata masa rai, domin kuwa ya hanasa ƙarasawa ga ZAHRAH'nsa, wacce saboda itane ma gaba ki ɗaya yadawo ƙasar, yayi missing din Zahrah sosai, yayi missing kyakkyawan murmushinta haɗi da kyawawan idanunta, yayi missing kallon kyawawan laɓɓanta masu daɗin tsotso. Gaskiya dole ya killace Zahrah tayanda zata zama nasa shi kaɗai.
Suna isa gida kai tsaye ɓangarensa ya wuce, a gajiye yashiga bathroom yayi wanka, koda yafito a wankan, direct masallaci ya wuce donyin sallan magriba. Sai da yajira aka yi sallan isha tare dashi a masallaci, kafun ya siɗaɗo yadawo ɗaki ya kwanta, yau ko abar ƙaunar tasa wato wine baisha ba bacci ɓarawo yayi gaba dashi.
Zahrah ce kwance akan katifarta sai juyi take ta kasa bacci, gaba ɗaya kanta ya kulle zuciyarta cike take da tarin tunanuka kala kala. "Anya banyi sauri kokuma gangancin yarda da kuma amincewa da soyayyar Dr da nayi ba?" zuciyarta ta tambayeta.
Zumbur haka ta miƙe zaune, haɗe da soma girgiza kanta
" A'a banyi kuskure ba, tabbas bayan shi babu wani maiso da nuna tausayi gareni!" tabawa kanta amsa a bayyane.
Wayartace takawo haske alamar shigowar ƙira, kasancewar ta sanya wayar a silent hakan yasanya wayar batayi ƙaraba.
"Doctor" shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar.
"Shima baiyi bacci ba kenan" tafaɗi hakan a bayyane.
Saida wayar ta kusa katsewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran haɗe da kara wayan akan kunnenta.
"My princess bakiyi bacci ba kenan?" Dr Sadeeq yatambayeta cikin muryarsa mai ɗauke da damuwa.