x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 39 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 114001 words
  • 117000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 239

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ta cikin mayafin..


Tana fitowa tsakar gida ta kalli Husnah wacce yanzu ake zana mata nata lallen, murmushi tayi mata haɗe da kashe mata ido ɗaya, dariya suka sanya su duka domin sukaɗai suka san ma'anar hakan.... Murmushi yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya alokacin dayaga fitowarta daga cikin gida,,, buɗe murfin motar tasa tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama,, cikin murya me ɗauke da kasala ya amsa mata sallaman haɗe da maida kallonsa gareta. Murmushinta dake ƙara mata kyau akoda yaushe tayi masa haɗe da ɗan tsaida idanunta akansa,,,, shiɗinma kallonta yake batare dayace komai ba, azuciyarsa kuwa mamakinta yake ta yanda ta'iya tsaida idanunta akan sa a yau ɗin, bayan kuma yasani sarai batayi masa dogon kallo.
"Namiki kyau ne ƴan mata?" yatambayeta yana me duban kansa,, dariya ne ya kwace mata amma kuma saitayi saurin sanya hanu ta toshe bakinta,
"Wow! gaskiya wannan zanen lallen yayi kyau sosai!" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin kamo hanunta, sam shi bai lura da zanen bama sai yanzu,, saurin maida hannayenta cikin mayafin dake jikinta tayi haɗi da cewa "Sai an biya kuɗi me yawa sannan ake kallon wannan zanen" murmushi yayi me sauti, ba ɓata lokaci ya sanya hanu acikin aljihunsa, kuɗi yaciro wanda baisan ko nawa bane, ya ɗaura mata akan cinyarta.
"Karki hanani gani please" yafaɗi maganar yana me marairaice fuska,
"Naƙi wayon kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan" tafaɗi haka cikin sigar wasa.


"Laluma aljihunsa yayi dama da hagu amma kuma yaji babu ko sisi, kawai saiya marairaice idanunsa yana kallonta, dariya yanzu kam tashigayi, sai da tayi dariyarta ta ƙoshi sannan tace "Kasan baka da kuɗi kuma kakeson ganin zanen lallena?"
Jin shiru bai bata amasa ba yasanyata saurin ɗago kanta ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata idanu kamar wani wanda bai taɓa ganinta ba, murmushi kawai tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sosai takejin wani iri ajikinta idan yana kallonta.


"Zahrah na!" yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi. Zahrah bata iya amsa masa ba, sai dai ta dawo da kallonta gareshi..


Yabuɗe baki zaikumayin magana kenan wayarsa tasoma ƙara,,


"Hajiya"


shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, dakatawa da maganar yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa.. Hajiya dake zaune akan kujera cikin yanayi na ɓacin rai tace


"Kana'ina ne?"


"Ina wajen Zahrah Hajiya" yabata amsa cike da girmamawa.


"Kabar duk abun da kake kazo gida inason ganinka" tana kaiwa nan azancenta ta kashe wayar.


A hankali ya zame wayar daga kan kunnensa haɗe da sauƙe ajiyar zuciya kallon Zahrah yakumayi haɗe da ɗan sakin murmushi.


"Hajiya nason ganina yanzu, ki riƙe wannan saboda hidimar walimanki na gobe, maybe bazaki sake ganina ba sai bayan na angonce!" yafaɗi haka yana me miƙa mata wasu kuɗaɗe masu yawa daya ciro daga cikin wata ƴar loka dake cikin motar.


"A'a ae bana buƙatar komai don mungama duk wani abun da zamuyi, kuma komai na walima yazama ready, sannan kuma inada kuɗi a wajena ka...."


"Shiiii kinsan banason yawan musu please ki karɓa kinji baby na, ki ajiye kobazakiyi komai dasu ba nasan zasu miki amfani wani lokaci" yafaɗi haka ta hanyar katseta daga maganar da takeyi batare daya bari ta ƙarisa ba,, badon ranta yasoba ta amshi kuɗin haɗe dayi masa godiya kana ta buɗe murfin motar ta fice, shima tada motar nasa yayi yabar ƙofar gidan, zuciyarsa cike da mamakin ƙiran da Hajiya tayi masa, Allah dai yasa ba wata matsalan ne takuma kunnu kai ba, idan dai har akan aurensa da Zahrah ne tofa shikam gaskiya sai dai kowama yayi haƙuri saboda ayanzu baijin zai iya sanja muradin sa...


Fuska ɗauke da mamaki Dr.Sadeeq ke cewa "tafasa aurena kuma Hajiya?"


"Badole tafasa aurenka ba, wace uwa ce zata yarda da irin abun da katsiro dashi? tun ma ba'aje ko inaba kana nuna banbanci ƙarara, gashi abanza ka jawo zubewar mutumcin dake tsakanina da Hajiya Furaira, yanzu da wani ido kakeso nasake kallonta!" Hajiya tafaɗi haka cikin ɓacin rai.


Sunkuyar dakai ƙasa Dr.Sadeeq yayi yana me hamdala acikin zuciyarsa da aka soke batun aurensa da Saleema, dama shi Allah yasani ko ya auri Saleema ba lallaine yakamanta mata adalci ba, saboda abun a bayyane yake yafi ƙaunar Zahrah fiye da kowacce mace a yanzu idan aka cire mahaifiyarsa dakuma ƴar uwarsa ta jini.


"Dama haka kakeso ai shikenan burinka yacika, gakuma kayan lefe dakuma kuɗin auren da kakai can sun dawo maka dashi, sai kaje kayi ta fama da wacce zuciyarka ta zaɓa ma ni tashi kabani waje !"


Sumi sumi haka Dr.Sadeeq yatashi daga gaban mahaifiyartasa cikin sanyin jiki yafice daga cikin falon...


Yana shiga ɗakinsa yasaki wani irin ajiyar zuciya, wayyo Allah shikam daɗi kasheshi, dama yafi kowa tunanin yanda zaman nasu zai kasance saboda shi a tsarin rayuwarsa bai da niyar auren mace sama da ɗaya bare yanzu daya samu Zahrah yasan cewa ita kaɗaima ta'ishesa rayuwa, yaji daɗin fasa wannan auren ƙwarai...


*Zaid*


Gaba ɗaya jikinsa yaƙi daɗi duk yanda yaso koda a daddafene yaje yaga Zahrah hakan yagagara, saboda wunin yau ma gaba ɗaya baiyishi cikin daɗi ba, kasancewar ciwon zuciyarsa yatashi yasanya Dr.Bilal ya dinga basa magani masu sanyasa bacci gudun kada ya matsantawa kansa da tunani, haka dai yanaji yana gani tashi zaune ma yagagaresa, haka ya kwana yana begen ganin Zahrah....


*Friday*


Kowa dake gidansu Zahrah shirin zuwa wajen walima kawai yakeyi, yayinda amarya Zahrah tasha kyau cikin wani haɗaɗɗen sari da aka ɓata lokaci wajen naɗa mata shi ajikinta, yauma dai meckup aka tsantsara mata akan fuskarta nagani na faɗa, take fuskar amarya Zahrah yaci gaba da walwali,, motoci Dr.Sadeeq yaturo suka kwashesu har zuwa inda za'a gudanar da walima,,, walima fa ya ƙayatar saboda Malami aka ɗauko na musamman yagudanar da wa'azi akan yanda ake zamantakewar aure, sanan kuma yaƙara da wa'azi me ratsa jiki harsaida amarya tayi kuka,, bayan anƙare walima ne kuma aka soma rabon abinci haɗe da kyaututtuka kamar su memo da kuma jaka wanda Dr.Sadeeq ne duk yayi su, sai dai babu hoton amarya da ango ajiki sai dai sunansu kawai. Walima fa yaƙayatar kowa sai dai yace Alhmdlh haka aka tashi a taron walima kowa yanacikin farinciki,, yayinda gobe asabar kuma take ɗaurin aure💃.


*(Maza kuzo fa, mata kuma ku faɗawa Mazajenku su je ɗaurin auren😂 🙊Nidai baruwana Team Zaid kada kuga laifina Dr.Sadeeq ne yace ingayyaci kowa da kowa 😂💃😜)*


*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*



*WATTPAD*
@fatymasardauna


*(Wannan fejin baki ɗayansa nakine My KHAIR74 kinasani nishaɗi sosai, kiyi farinciki marar iyaka kiji daɗinki akullum inayinki sosai KHAIR74)*


*Editing is not allowed📵*


*NOTE: Masoyana masu cece kuce inagaisuwa agareku, sannan ina mai baku haƙuri, idan akwai wacce wannan hukuncin baiyi mata daɗi ba tayi haƙuri dama shi Aure nufine na Allah, kuma ance matar mutum ƙabarinsa, abun danakeso ku fahimta shine, balallai ne koda yaushe mutum yasamu abun da rai dakuma zuciyarsa keso ba, SO baƙarya bane haƙiƙa so gaskiya ne, amma kuma bako da yaushe bane burin so ɗin ke cika ba, ita rayuwa dama haka take tana iya sauyawa ako da yaushe akuma kowani lokaci.....*


*CHAPTER 88 to 89*


Yauma dai kamar jiya agajiye take matuƙa, suna komawa gida ta yi wanka da ruwa me zafi sai alokacin ta ɗanji ta samu nutsuwa a jikinta. Kwanciya tayi luf akan katifarta haɗe da jawo wayarta tasoma buga game, tayi hakanne gudun kada tunani ya samu daman bijiro mta acikin zuciya...


"Kinada baƙo a waje fa Zahrah" maganar da tafito daga bakin Husnah wacce shigowarta ɗakin kenan..


"Baƙo kuma Husnah?" Zahrah tatambaya cike da mamaki.


"Ƙwarai kuwa amma sai dai gaskiya inaga ba ya ɗaya daga cikin abokan Doctor, yakamata kije ki gansa dan naga kamar yamatsu dason ganinki" Husnah tafaɗi haka bayan tayi mawa kanta masauƙi akan katifar da Zahrah take kwance...


Cike da mamaki Zahrah tamiƙe tsaye haɗe da ɗaukar mayafi ta rufa ajikinta, hakanan taji tamatsu da taga waye ne ke neman nata.....


Tana fita waje tasoma raba idanu ko zata hango wanda akace yana ƙiranta, sai dai kuma bata ga kowa ba...


"Zahrah" taji anƙira sunanta daga bayanta,, da sauri ta juya don ganin kowaye.


Wani kyakkyawan saurayi handsome guy tagani tsaye a bayanta yana ta zuba murmushi, kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikekken ɗan gaye ne, kuma ɗan hutu, domin kuwa fatar jikinsa da kuma kayan dake sanye ajikinsa kaɗai sun isa tabbatar maka da hakan..


Takowa yashigayi gareta, har saida yazo kusa da'ita kafun ya ja ya tsaya, kallon kallo suka shiga yiwa juna, Zahrah kallon mamaki da kuma al'ajabin me ya kawosa wajenta take yayinda shikuma yakeyi mata kallon ƙurilla,, wani yawu ya haɗiya a maƙoshinsa bayan yagama ƙare mata kallo daga samanta har ƙasanta... "Zahrah ko?" yafaɗi haka yana me nuna ta da yatsarsa...


Kai kawai Zahrah ta'iya jinjina masa alamar "Eh" still amma kuma idanunta nakansa..


Murmushi yakuma yi mata haɗe da gyara tsayuwarsa "Naji daɗin ganinki ƴan mata, sunana Abid, nasan baki sanni ba amma kuma idan babu damuwa me zai hana muje mota sai muyi maganan, saboda nazomiki da wata magana ce me mahimmanci" yafaɗi haka yana me sake dubanta da kyau...


Kallon sa itama ta sakeyi sosai kafun ta ce. "Kafaɗi duk abun da zaka faɗa anan inaji, amma bana buƙatar shiga cikin motarka" ta ƙare maganar tana me ɗage kanta sama.


Murmushi Abid yakumayi akaro na barkatai "lallai ba'a banza ba Zaid yakasa magance matsalarsa yarinyar akwai taurin kai" yafaɗi haka acikin zuciyarsa...


"I'm sorry bacutar dake zanyi ba, kada kiji tsorona, nazo miki da magana ne me matuƙar mahimmanci, nasan abune me wahala amma kuma keda kanki zakiso ace kinzamo silar ceto rayuwar da take shirin gushewa, nasan bazakiso ace ta sanadiyarki Zaid ya rasa rayuwarsa ba, kina da tausayi Zahrah, me yasa bazaki yarda ki aure sa ba?" abunda ya fito daga bakin Abid kenan..


Kallon baka da hankali Zahrah tashiga bin Abid dashi, da ƙyar ta'iya cewa "Bansan maganar Zaid bace takawoka wajena ba, da bantsaya ɓata lokacina wajen saurararka ba, don bazan ɓata lokacina abanza ba, dan Allah kufita a rayuwata, kacewa Zaid ya ƙyaleni na huta, domin kuwa ko maza sun ƙare a duniya bazan taɓa auren Zaid ba!" Zahrah tafaɗi haka cikin dakiya dakuma ɓacin rai...


"Ba gaskiya bane Zahrah, wannan maganar da kika faɗa ba daga cikin zuciyarki tafito ba daga bakinki tafito, kobaki furta ba raunin kalamanki sunnuna cewa kinason Zaid har yanzu, me yasa bazaki yafe masa ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, dan Allah Zahrah ki taimaka ki auri Zaid, haƙiƙa nida Zaid muna biyewa zuciyarmu muna aikata abunda baidace ba, amma kuma ina me tabbatar miki da Zaid ɗin dakika sani a yanzu bashine wanda kika sani ada ba, soyayyarki ta sanjawa Zaid tunani, soyayyarki ta juyamasa ƙwaƙwalwa, wallahi ke kaɗaice muradinsa acikin duniyar nan, Zaid baisan damuwa ba sai akanki Zahrah, yayi nadama me tsanani akan abun daya aikata miki, akan ki Zaid yafara sanin menene ƙunci, akanki yafara sanin menene ɗacin soyayya dakuma zaƙinta, haka akanki Zaid ya kasa fuskantar gabansa dakuma bayansa, akan kine kuma dalilinkine Zaid yakamu da ciwon zuciya me tsanani, ahalin yanzu Zaid yana acikin wani hali, Zahrah ke kaɗaice zaki iya sanjasa ki kuma ceto rayuwarsa please koba don nida Zaid ba kodan ceton rayuwarsa ki taimaka ki auresa!" Abid yaƙare maganar cike da raunin murya sosai yake matuƙar tausayin Zaid musamman ma dayaje yagansa yau, gaba ɗaya yafita hayyacinsa...


Murmushi me tsananin ciwo Zahrah tayi haɗe da sanya haƙoranta tacije lips ɗinta, kallon Abid tayi kana ta girgiza kanta


"Meyasa ku kazamanto mutane masu tsananin son kansu? Zaid rayuwarsa kawai zai rasa, amma ni gani da raina ta sanadiyarsa ne kuma narasa farinciki na, rayuwata tazamo marar amfani a gareni, ya katsemin farinciki dajin daɗi na, yakawo kansa gareni alokacin dayaga dama, yakuma sanyamin soyayyarsa alokacin dayaga dama, sannan yakuma ketamin haddina alokacin da yaga dama, yayimini duk wani abu da ransa keso alokacin dayaga dama, nima kuma yanzu nadawo mutum zankumayi duk wani abun daya dace alokacin dana ga dama, idan shi ne ya aikoka da waƴannan yaudararrun kalaman to kaje kasanar masa cewa kalaman naku basuyi aiki akai na ba, zaifi kyau kubarni nayi rayuwar aurena cikin farinciki da salama, domin kuwa gobe iwarhaka najima da zama matar wani insha Allah, inaso kuma kasani cewa najima da barin Zaid da Allah, haƙiƙa ya cutar dani, amma kuma dama hakan yakasance rubutaccen ƙaddarata ne wanda Allah ya rubuta, kaje kawai Abid bana tunanin sake burin haɗa rayuwata da ta Zaid!" hanu tasanya ta sharce hawayen da suka silalo daga cikin idanunta haɗe da juyawa tasoma tafiya...


"Komai yana hanunki Zahrah idan har kikace afasa aurenki da wanda zaki aura aɗaura da Zaid nasan iyayenki zasu amince, shin maiyasa bazaki cika muku burinku ba? kinasonsa shima kuma yana sonki, ki amince ki aure sa, wallahi namiki alƙawari ko nawa kikeso aduniyar nan zan mallakamiki shi koda kuwa duka dukiyata kika buƙata nabaki zan baki, amma bazan tilastaki ba sai dai inaso kisani idan Zaid ya rasa rayuwarsa a yanzu kece SANADI" Abid yana kaiwa nan azancensa yabuɗe murfin motarsa, wata ƴar madaidai ciyar jaka ya ɗauko, takawa yashigayi harsai da yazo kusa da'ita kafun ya tsaya... "Ki amshi wannan jakan idan kika buɗe laptop ɗin dake ciki zakiga yanda Zaid ya koma A SANADI'N SONKI" Abid yafaɗi haka yana me miƙa mata jakar.. Tsintar kanta tayi da kasa ƙin karɓan jakar, yana bata jakar ya juya yayi tafiyarsa,,, har motar Abid ta ɓule Zahrah na tsaye sororo hanunta riƙe da jaka,,, saurin share hawayenta tayi, haɗe da nufar cikin gidan su,,, sumi sumi haka ta shige cikin ɗakinta, abun yayi mata daɗi sosai data iske Husnah hartayi bacci,, mayafinta ta cire haɗe da neman waje ta zauna, kanta ta kifa akan guiwowinta, damuwane cike azuciyarta, takasa sanin wani hali take ciki, kanta ta ɗago takalli jakar da tashigo dashi, da sauri tajawo jakar haɗe da buɗeta, a hankali ta zaro laptop ɗin dake cikin jakar, saida ta ƙarewa laptop ɗin kallo kafun ta buɗeta, tana danna wani madanni laptop ɗin takawo haske take kyakkyawan hoton fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin, mamakine yakamata ganin hotonta wanda batasan ma dashi aduniya ba, balle tasan yaushe ko wace ranace aka ɗauketa hoton ba, ƙurawa hoton nata idanu tayi tamakasa yin komai, bata ɗauke idanunta akan hoton ba har saida hasken screen ɗin laptop ɗin ya gaji dan kansa ya ɗauke.. Ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe haɗe da sake kunna laptop ɗin, batasan inazata shiga ba, bata kuma san mezata fara dubawa ba, hakanan ta ji zuciyarta ta ingizata da tashiga ɓangaren hotuna,, tana kutsawa ɓangaren hotuna, hotunantane suka farayi mata wellcome, mamakine yasake kasheta ganin hotunanta kaca kaca babu adadi acikin laptop ɗin, wanda ita a iya tsawon tarihin rayuwarta ma bata kasance mace meyawan sonyin hoto ba, yanzu haka ko hotonta ƙwaya ɗaya bata dashi acikin wayarta,,,, bata da me amsamata tarin tambayoyin dake ranta dan haka kawai saita shiga wuce hotunan nata, hotunan Zaid takuma cin karo dasu wanda saida gabanta yayi wani irin faɗuwa yayinda ƙirjinta yashiga dokawa da sauri.. da ƙyar ta'iya view ɗaya daga cikin tarin hotunan nasa, sanye yake da wandon jeans baƙi dakuma wata farar riga saikuma hular sanyi daya sanya akanshi yayinda kunnensa ke sanye da farin earpiece, yayi kyau matuƙa a hoton domin kuwa fuskarsa ɗauke take da wannan ƙawataccen murmushin nasa wanda yake ƙara masa kyau ako da yaushe... Ƙura mawa hoton nasa idanu tayi, saitaga tamkar shiɗinne da kansa agabanta, batasan sanda wasu hawaye suka silalo daga cikin idanunta zuwa kan ƙuncinta ba,, tajima tana kallon hoton nasa, haka kuma hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta, ɓangaren vedios takuma kutsawa, sai dai vedion farko da ta gani shine wanda yakusa tarwatsa mata zuciya, yakuma ɗaga mata hankali,, Zaid tagani kwance akan gadon asibiti ansanya masa oxygen, yayinda aka dasa masa wasu ƙarafan na'urori akan ƙirjinsa dai dai saitin zuciyarsa, da badon ɗan abu kamar computer'n dake gefensa wanda shike nuna alama yana da rai ba, to tabbas da saidai ace dashi gawa,,, wani irin sarawa taji kanta yayi, yayinda wani irin kuka yazo mata alokaci guda, saurin sanya hanu tayi ta toshe bakinta haɗe da rumtse idanunta, a hankali ta jingina bayanta da bango,,, hawayene suka shiga gudu wani na koran wani akan fuskarta,, duk yanda taso daurewa kasawa tayi saikawai tafashe da wani irin kuka me sauti, kuka take sosai yayinda ta rungume wannan laptop ɗin akan ƙirjinta,,,, kamar amafarki Husnah kejin gunjin kuka natashi acikin ɗakin, dayake ita ba me nauyin bacci bace yasanyata buɗe idanunta ahankali, aikuwa dagaske ba amafarki bane, kukan Zahrah taji raɗau acikin kunnenta, da sauri ta tashi zaune haɗe da dawo da kallonta inda sautin kukan ke fitowa,, sake waro idanunta tayi ganin da tayiwa Zahrah na kuka tsakaninta da Allah. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Zahrah meyafaru kike irin wannan kukan?" Husnah ta tambaya cikin ruɗewa... Jin muryar Husnah acikin kunnenta yasanya, tataso daga inda take da sauri ta faɗa jikin Husnah ae kuma saita ƙara volume ɗin kukan nata,, kai Husnah ta dafe cike da tashin hankali, "Allah yasa dai bawani gagarumin abubane yafaru" Husnah tafaɗi haka
End Ads