x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 204

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Malam Adamu baiyi ƙasa a guiwa ba wajen kaimawa Alhaji Umar kuɗinsa, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗi sosai, nan yaɗauki maƙudan kuɗaɗe yabamawa Malam Adamu, amma Malam Adamu haka yaƙi karɓa acewarsa, shi don Allah yayi bawai don abiya saba, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗin hakan, haka dai Alhaji Umar da Malam Adamu suka soma zumunci, watarana Malam Adamu na zaune, Alhaji Umar yaƙirasa yace mai yasayamasa gida anan suleja, bakaɗan ba Malam Adamu yayi farinciki, har ƙwallan murna saida yayi, gidane daidai da zaman talaka Alhaji Umar yasai mawa Malam Adamu, ɗakuna huɗu ne acikin gidan sai ɗan madaidaicin filin tsakar gida, da kitchine da kuma makewayi, Koda Zainab tazo taga gidan itama taji daɗi sosai, bawani ɓata lokaci suka tattaro suka dawo gidan,, a kwana a tashi Asaran mai rai, wata rana aka wayi gari Baban Malam Adamu ya rasu, sosai mutuwar tajigata ƴaƴansa, amma babu yanda suka iya duk wani mai rai mamacine sunriga da sunyi imani da hakan,, bawani ɓatalokaci Malam Adamu ya ɗauko mamansa suka dawo garin Abuja da zama,, baifi wata uku da dawowar Goggo (Maman Malam Adamu) Abuja ba, tace ga garinku nan, Allah sarki su Malam Adamu sunkuma jin zafin rashin mahaifiyarsu,, bayan wani lokaci Hayatu yayi aure, Malam Adamu ne yace masa yadawo nan Abuja su zauna, tunda akwai ɗaki a gidansa, Hayatu bai ƙi ba, yaɗauko matarsa suka dawo,, tundaga kan Zahrah Malam Adamu da Zainab basu sake haihuwa ba, Zahrah tanada shekara huɗu Malam Adamu yasanyata amakarantar furamari (Primary) Zahrah yarinya ce mai hazaƙa sannan kanta yana ja sosai, kwanci tashi Zahrah ta kammala makarantar furamari (primary) ɗinta, bawani ɓata lokaci Malam Adamu yasama mata gurbin cigaba da karatu (Admission) a wata junior school dai dai da ƙarfinsa,, Zahrah na aji ɗaya a junior school, Mama (Zainab) takwanta rashin lafiya, abu kamar wasa hardai takaisu ga asibiti, kwanan mama ɗaya a asibiti Allah yayi mata rasuwa, kuka kam Zahrah da Malam Adamu sunsha shi, domin kuwa sunyi rashin jigon rayuwarsu, haƙiƙa Zahrah tayi rashin uwa ta gari, shiko Malam Adamu yayi rashin mace ta gari,, sati ɗaya da rasuwar Mama Malam Adamu yakwanta jinya, abu kamar wasa saigashi ko tashi baya iyawa, Wata rana ne aka wayi gari Malam Adamu baya numfashi, Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un !! Zahrah tayi kuka bana wasaba lokaci guda tayi rashin farincikin rayuwarta,,,,, koda Alhaji Umar yazo ta aziya, baiyi ƙasa a guiwaba, cewa yayi ya ɗauki nauyin karatun Zahrah harta ƙare jami'a, yayinda riƙon Zahrah yadawo wajen Hayatu da matarsa (Baffa, Inna) sam Zahrah batajin daɗin riƙon da Baffa da Inna keyi mata domin tsananin tsangwama suke nuna mata, gahi Baffa yahau kan ɗan gadon da Babanta ya bar mata yacinye,,, Ayanzu Zahrah tana da shekara 20 aduniya, kuma harzuwa yanzu Alhaji Umar ne ke ɗaukan nauyin karatunta.....


Cigaban Labari


Adai dai bakin titin yayi parking motarsa, domin sam shikam baijin cewa zai iya shiga, wannan unguwar talakawan da tsadaddiyar motarsa, shi sam baisan ma uban me yasa Bash yayi guest house ɗinsa a wannan unguwar ba,, zama yayi a cikin motarsa haɗe da ɗaukar wayarsa yadanna mawa lambar (Number) Bash ƙira, ringing biyu kawai wayar tayi Bash da ke kwance jikin wata ƴar iskan sa ya ɗaga,, "Ina bakin titi " yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar tasa,, baiwani ɗau lokaci ba saiga Bash ya ƙaraso,


"kaga *SHU'UMIN NAMIJI* maifirgita ƴan mata, Shu'umi mai sace zuciyar duk wacce yaso, ko shaiɗan yana tsoron shu'umancin ka !!" Bash yafaɗa dai dai lokacin dayakema kansa masauƙi acikin motar, ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa " Kai ni duk ba wannan ba waishin meyasa ka tsalleki ko wani unguwa kazo nan kayi guest house ɗinka ?, ka duba fa gidajen area'nnan gaba ɗaya na talaka wane " Zaid yaƙare maganar yana maibin gidajen da kallon ƙyama,, murmushi Bash yayi haɗe da cewa
" Bazaka gane bane my man, amma wallahi ƴan mata nake samu a arean nan bana wasaba, kai bana ta ƙaice maka, yarinya sai ta kawomaka budurci (virginity) ɗinta a ɓagas, badon komai ba sai don tsananin talauci daya adda beta, yanzu haka akwai ƴan mata a ƙasa idan kana buƙata.." Bash yaƙare maganar yana murmushi mai ɗauke da nuna shi tantirin ɗan iska ne,,


taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa "Bazan iya iskanci da low class ba gaskia, kudai kuyita fama harku ɗaukomawa kanku wata cutar, yaƙare maganar yana ƴar dariyan mugunta,,


gyara zama Zaid yayi haɗe da cewa " Nazo maka da wani babban harka ne idan zakayi " shima Bash gyara zama yayi da kyau haɗe da cewa "Inajinka abokina "


Zaid ya buɗe baki zaiyi magana kenan idanunsa suka sauƙa akan wata kyakkyawar budurwa, wacce ke sanye da hijab iyaka guiwarta, hijab ɗin irin mai roba ɗinnan ne, hakan yasa ya bayyana duk wata sura na jikinta, wani irin abu Zaid yaji daga ƙasan ƙafarsa harzuwa cikin kansa, yayinda tsikar jikinsa yashuga zubawa, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa, da alokaci guda suka kaɗa sukai ja, koda yabuɗe su don sake kallon wannan halittar da'idanunsa sukai masa to zali da'ita, sai yaga saɓanin haka, domin ko a alamar gilma wanta baigani ba, saurin fita daga motar yayi haɗe da soma waige waige ko Allah zaisa yaganta, amma ko alamar ta bai gani ba........








(Tofa readers waishin wace budurwa ce Zaid ya gani ?)




*14/October/2019*



*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*




*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*




*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna




*Editing is not allowed 📵*


*Chapter 7*


" Lafiya kuwa Zaid wakake nema ne ?" Bash yatambayeshi,, ɗan taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa " bakomai kawai ina duba yanayin unguwar ne " yaƙare maganar yana mai komawa cikin motarsa yazauna,,, sama sama Bash da Zaid sukayi magana, domin kwata kwata hankalin Zaid baya jikinsa, burinsa kawai shine idanunsa su sake yi masa to zali da wannar kyakkyawar fuska da jikin, daya gani.....




Tunda Zahrah tafito daga gidan su Husnah tafuskanci cewa da akwai mai binta a baya, hakan yasanya taji wani irin tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, don haka ta ƙara ɗaga ƙafufunta, "Assalamu Alaikum !!" muryan Namiji mai cike da kamala ya doki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya da tafiyan da takeyi batare da ta juyo ba,, cikin takunsa na burgewa ya ƙaraso gareta, kyakkyawan saurayi ne, mai ɗauke da launin fata choculate colour, dogo ne amma ba har canba, yanada faffaɗan jiki mai burgewa, sannan yana da kwarjini ba laifi,, murmushi yayi mata haɗe da cewa "Ƴan Mata bazaki amsa sallaman nawa bane ?" saurin sunkuyar da kanta ƙasa Zahrah tayi haɗe da cewa "Wa'alaikassalam"


Lumshe idanunsa yayi domin kuwa bakaɗan ba zazzaƙar muryarsa tadaki ƙahon zuciyarsa " Sunana JABEER, Idan bazaki damuba, inaso kibani adireshi'n gidanku, sai nazo, domin a matsayinki na mace mai mutumci baikamata natsaidaki a bakin hanya ba " Jabeer yafaɗa hakan yana mai kafeta da idanu,, gaba ɗaya kanta ɗaurewa yayi don haka, batare da tace dashi ƙala ba, tacigaba da tafiya, da sauri sauri,, roƙonta Jabeer yashiga yi akan ta tsaya ta saurareshi, amma ina Zahrah ƙara ɗaga ƙafanta tayi domin ita tsoro ma yabata, ganin da Jabeer yayi cewa bazata tsaya bane yasanya shi ƙyaleta kawai tayi tafiyarta, amma a zuciyarsa ya ƙudura aniyar nemota komai daren da ɗewa ..... Zahrah tana komawa cikin gida kaitsaye ɗakinta tawuce, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa a kai akai tamkar wacce tayi gudu, idanunta da suke lumshe ta buɗe su ahankali, haɗe da da sanya harshenta ta lashi lips ɗinta na ƙasa, Allah yasani gayen ya burgeta amma kuma tanajin tsoro gaskia, domin bata saba tsayuwa da samari ba......






Birgima kawai yakeyi akan makeken gadonsa, kwana huɗu kenan daganinta amma da ya rumtse idanunsa, hoton kyakkyawar surarta yake gani, baisanta ba, baisan wacece itaba, amma wani irin sha'awarta yakeji, tabbas yazama masa dole komawa unguwar Suleja ko Allah zaisa yasake ganinta,, wayarsa dake ringing ne yakatse masa tunanin da yakeyi, DADY shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayara, ɗaukar wayar yayi a kasalance haɗe da karawa akan kunnensa "To" kawai naji yace haɗe da cilli da wayartasa gefe, tashi yayi daga kwancen dayake haɗe da ɗaukan rigarsa yasanya, ya fice daga cikin ɗakin.....


Kai tsaye babban falon Dadyn nasa yanufa, can ya iske Dadyn nasa tare da Mom ɗinsa, zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, fuskarnan tasa babu yabo ba fallasa, yace "Dady gani " Gyara zama Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da cewa " Banaƙira ka bane don muyi dogon magana, naƙiraka ne don na sanar maka cewa zuwa yanzu yakamata ace kafitar da matar aure, kagama karatunka, ga kuɗinan kana samu ba'adadi, to mai yarage maka idan banda Aure Zaid ? a gaskia banajin daɗin zamanka haka ba aure, saboda haka kafito da matar aure "


" Yauwa gaya masa dai Alhaji, tunda ni nayi maganar har nagaji bai ɗauka ba, ga Khausar ɗiyar ƙanwata nan ma, sai ayi tuwona mai na " Mom tafaɗa tana murmushi,,,,


Dasauri Zaid yaɗago yakalli Mom ɗintasa, jin abun da take faɗa, wai Khausar, cab aiko mata sun ƙare a duniya bazai auri muciya da zani ba, yanda yasan mata ciki da bai, yana da tabbacin cewa Khausar tana ɗaya daga cikin irin matannan marassa ni'ima wanda idan kana sex dasu zakana jinsu kamar dusa, babu wani ɗanɗano,,


"Kayi shiru" Dad yakatsesa daga tunanin daya keyi,,


" ka ƙara bani lokaci Dad insha Allahu zan kawota nan bada jimawa ba, amma gaskia maganar Khausar Mom ki barshi, domin kwata kwata ni bana jinta acikin zuciyata " yana kaiwa nan a zancensa yasakai yafice daga cikin falon,, da idanu kawai Dad da Mom suka rakasa, har abada shidai Zaid bamai iya masa sai Allah, duk yanda ka ɓullo zaice ba haka ba.....


Koda yakoma ɗakinsa wanka yayi, haɗe da ficewa daga cikin gidan baki ɗaya,, baizarce ko'inaba sai babban gidan giya dake Abuja, can yaje yacika cikinsa yayi tatul, daganan yasamu abokiyar shaiɗanansa, suka yi watsewarsu.....




Zahrah sunfara Exam, don haka tuni kanta yaɗau zafi, karatu kawai takeyi baji ba gani, cikin ikon Allah kuwa komai nata yana tafiya adai dai, domin dai tana sa ran cewa zata samu kyakkyawan sakamako,,,


Hadari ne yahaɗu sosai acikin garin, yayinda sama tayi baƙi, ruwa ake tsammata yanzu ko anjima, yau amakare suka fito da ga exam, duk yanda Husnah taso Zahrah tashiga su rage mata hanya ƙiyawa tayi dole yasa Husnah ta ƙyaleta, tana fitowa daga cikin makaranta, ruwa ya ɓarke tamkar dama jira ake tafito, duk adaidaita sahun da Zahrah tatare baya tsayuwa, domin ruwan ƙara ƙarfi yake, jikin wata bishiya Zahrah ta lafe, duk da kuwa cewa ruwan baifasa dukanta ba, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe jagwab, ba abun da kayanta suke sai ɗigan ruwa, rigace irin rover gown ɗinnan ajikinta, saikuma rover hijab da taɗaura akan rigan, sanadin jiƙewan da sukayi yasanya, kayan lafewa acikin jikinta, take komai najikinta ya bayyana, hatta shatin breast ɗinta saida yabayyana, domin rigar ce kaɗai ajikinta, batasa breziya ba,, abu kamar wasa haka aka share 1 hour ana tafka ruwan sama, gashi duk bayan minti ɗaya dare ƙarayi yake, sanin cewa tsayuwarta a wajen kan iya haifar mata da matsala, yasanya ta shiga tafiya a cikin ruwan duk da cewa bata ko iya ganin gabanta,, gudu kawai yake shararawa akan titin batare da yayi tunanin komaiba, daidai Zahrah tahau kan tsakiyar titin, dai dai shikuma yaƙaraso wajen,,, wani irin burki Zaid yataka da ƙarfin tsiya, domin ƙiris yarage yabita kanta,, Zahrah kuwa tsabar firgici kasa motsawa tayi daga wajen, hannayenta taɗaura akan kunnenta haɗe da rumtse idanunta gam,, tundaga ƙasanta yasoma kallonta harzuwa samanta, saurin rumtse idanunsa yayi alokcin da idanunsa suka hasko masa shatin nipples ɗinta daya bayyana tacikin hijabinta, " wayyo Allah na !!" yafaɗa a hankali, yayinda ya sanya hanunsa yariƙe bananarsa da alokaci guda tayi wani irin harbawa,, cikin rashin ƙarfin jiki da kuzari yafito daga cikin motar haɗe da nufar inda take,, kallon fuskarta yashiga yi, jin hucin numfashin mutum akusa da'ita yasanyata buɗe idanunta ahankali, sake waro idanunta tayi domin ganemawa kanta shin abun data gani gaskiya ne ko ƙarya, kyakkyawar fuskarsa tashiga ƙaremawa kallo, tamkar taga baƙon halitta, waishin aljanine ko mutum ? tatambayi zuciyarta, kallon kallo Zaid da Zahrah suka shiga yimawa juna, yayinda ruwan sama keta dukansu, tsareshi tayi da idanunta, bata ko ƙyaftawa, ahankali yakai hanunsa zuwa kan fuskarta yashafa kumatunta, saurin ja da baya Zahrah tayi, haɗe da ƙwalalo idanunta waje, abun da wani ɗa namiji baitaɓa yi mata ba aduniya kenan wato taɓa jikinta, saidai ko muharraminta,, wani irin munafukin murmushi daya ƙawata zallan kyauwunsa yayi haɗe da komawa cikin motarsa yazauna, ƙofan dake gefen mai zaman banza ya buɗe, haɗe dayi mata nuni da hanunsa alamar tashigo, tsoro ne yakama Zahrah, amma tabbas bata da wani dama dayawuce tashiga motar tasa, domin idan ta tsaya tofa saidai ta bushe amma bazata samu abun hawaba gashi dare sai ƙarayi yake,, sumi sumi haka tashige cikin motar tazauna haɗe da takure jikinta waje ɗaya,, kallonta yayi tagefen ido haɗe dayi mawa motar tasa key, batare daya ce da'ita ƙalaba suka soma tafiya,, cike da tsananin mamaki take kallonsa ganin da tayi kaitsaye yanufi hanyar Suleja da'ita batare da ya tambayeta ba, saida suka kawo daidai inda yataɓa ganinta kafun yayi parking motar tasa haɗe da juyo da kallonsa gareta wani irin shu'umin kallo yajefeta dashi haɗe da cewa " inane gidan ?" kasa amsa masa tayi saima baki da tasake tana kallonsa kamar tasamu statue (gunki), a hankali ya hura mata iskan bakinsa akan fuskarta, take tayi saurin kawar da kanta gefe, "kabarni anan ma ya'isa nagode " tafaɗa a taƙaice haɗe da yunƙurin fita daga cikin motar, saurin riƙo hanunta yayi haɗe da cewa "Kifaɗamin inane gidan ?" yayi maganar cikin wata irin cool voice maisanya nutsuwa,, "kwanancan ne " tabasa amsa a taƙaice,,, a dai dai ƙofar gidan su yayi parking motar tasa, saurin buɗe murfin motar Zahrah tayi haɗe da ficewa, hartana jin tuntuɓe wajen shiga gida, tsabar sauri,, wani irin murmushi Zaid yayi, haɗe da fito da harshensa ya lashe pink ɗin laɓɓansa, "Sugar Baby !!" yafaɗa in a low voice, yakai kusan 2 minutes aƙofar gidan kafun yaja motarsa yatafi.......






*15/October/2019*


*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*




*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*




*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna




*Editing is not allowed 📵*




*Chapter 8 то 9*



Koda Zahrah tashiga gida bata iske kowa a tsakiyar gidan ba, don haka kai tsaye ɗakinta tawuce, kayanta dake ɗigan ruwa ta cire haɗe da ɗaura zani a ƙirjinta, fita tayi ta shanya jiƙaƙƙun kayan nata akan igiya, kana ta dawo ɗaki, wata doguwar riga mai kauri tasanya domin sosai takejin sanyi a cikin jikinta, zama tayi akan katifarta haɗe da lumshe idanu, saurin ware idanunta tayi, alokaci guda, bakomai yasa hakanba kuma face, kyakkyawar fuskar mutumin ɗazu dake yi mata gizo acikin idanunta, tsikar jikinta ne yashiga zubawa, sakamakon tunowa da yanayinsu naɗazu da tayi, "Yanada kyau !!" tafaɗi maganar a fili, amma anya ba gamo kikayiba kuwa Zahrah ?" zuciyarta taje fomata wannan tambayar, take kuma tsoro yashiga zuciyar Zahrah saikuma tafara addu'a idan Aljani ne ma Allah yarabata da sharrinsa.....


Zaid kuwa daga gidansu Zahrah nasu gidan yayi, koda yacire kayan dake jikinsa kwanciya yayi luf akan makeken gadonsa, yanamai sauƙe ajiyar zuciya, lallai yau yayi gamo da gamdakatar, ashe gaskia Bash keyi da ya ce masa a area'n akwai kyawawan ƴan mata, saidai a yanda ya fuskanta ita ɗin ba ƴar hannu bace, domin ya hango hakan acikin idanunta,, murmushi mai sauti Zaid yayi haɗe da cewa "Kisaurari dawowana gareki My Sugar Baby !!".....


Bayan Sati Ɗaya da haɗuwan Zahrah da Zaid....




Tun randa Zahrah ta haɗu da wannan haɗaɗɗen gayen hankalinta ya kasa kwanciya, ko kwanciya bacci tayi, to fa shike zuwa mata a mafarkinta, dazaran tarufe idanunta kuwa kyakkyawan murmushinsa take gani, duk yanda taso yakice tunaninsa acikin zuciyarta hakan yacitura, saidai ako dayaushe tana mai gargaɗin zuciyarta da ta tsaya a iya matsayinta, kada ta haura matsayin da bata can can ci zuwa ba..


Ɓangaren Zaid kuwa iskancinsa yake bugawa son ransa, zina ƙara yaɗuwa takeyi a cikin jini da zuciyarsa,, yau yashirya cewa zaikai mawa Sugar Baby ɗinsa ziyara,,


Tsab yashirya kansa cikin wasu irin tsadaddun riga da wando, na blue jeans, bakaɗan ba kayan suka amshi kyakkyawan jikin Zaid, yayinda tulin gashin kansa yasha gyara sai sheƙi yake, agogon rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hanunsa, haɗi da baɗe
End Ads