kaɗaiba har ita kanta saida ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi alokacin da zallan fatar jikinsu suka samu haɗewa waje guda. lokaci ɗaya yaji tunaninsa yasoma sauyawa, nutsuwarsa tafara gushewa, haka kuma idanunsa sun soma rufewa,, haɗewar jikin Zahrah danasa jikin baƙaramin feeling me girman gaske ya sauƙar masa ba, tunda yake aduniyarsa yau shine karo na farko, da ya fara haɗa jikinsa dana mace haka, yasan yataɓa rungumar Zahrah amma ba runguma irin wannan ba,,,, Zahrah kuwa baƙaramin jin daɗin jikin nasa tayi ba, jitayi gaba ɗaya nutsuwa yasoma sauƙar mata, sake maƙalewa ajikinsa tayi haɗe da cusa kanta acikin faffaɗan ƙirjinsa har yazamana laɓɓan ta suna gogan fatar wuyansa,, jin yanda take ƙara shigewa jikinsa shiya ƙara taimakawa wajen ƙara masa wutar sha'awarta, hannayensa duka yasanya a bayanta yasake riƙeta gam, numfashi kawai yake fitarwa akai akai shi kaɗai yasan meyakeji acikin jikinsa,, yana cikin wannan irin yanayin yaji sauƙar numfashin Zahrah ahankali yana fita da'alama baccine yakuma ɗaukarta,,, haka yarungumeta ƙam acikin jikinsa yayinda yacusa kansa acikin gashin kanta yana shaƙan daddaɗan ƙamshinta dake ƙara rikitasa,, bakaɗan ba ya yi jarumta wajen ganin ya ƙyaleta baiyi mata komai ba, haƙiƙa bakowani irin namiji bane zai haɗa jiki da mace ace ya iya daure zuciyarsa baiyi mata komai ba, balle ma mace irin Zahrah wanda irinsu basu da yawa acikin mata,, da ƙyar bacci ya'iya ɗaukarsa.......
*(Kuyi Haƙuri idan kunga typing error ina busy ne)*
*18/January/2020*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
Ƙiran sallan asuban fari akan kunnensa,, a hankali ya ware idanunsa akanta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da'alama zazzaɓi da ciwon kan dake damunta sun jima da kama gabansu,, baisan lokacin da murmushi ya ƙwace masa ba, komai na Zahrah me kyau ne, har idan tana bacci kyawunta baya ɓuya, kallon zara zaran eye lashes ɗinta daya kwanto aɗan ƙasan idanunta yayi,, ahankali ya zare jikinsa daga nata jikin, cikin sanɗa yatura ƙofar bathroom yashige, gudun kada motsinsa ya tashe ta daga daddaɗan baccin da take,, saida yafarayin wanka kafun ya ɗauro alwala,, tsayawa yayi yana kallon yanda taketa fidda numfashi a hankali, badon sallah yazama dole akanta ba, to tabbas da babu abun da zai sanya ya tasheta a dai-dai wannan lokacin, zai bartane tasha baccinta ta ƙoshi,, ahankali yashiga girgiza ƙafanta haɗe da ɗan ƙiran sunanta, cikin murya ƙasa ƙasa... Da yake bata da nauyin bacci, ƙira biyu yayi mata ta buɗe idanunta,, da sauri ta sake jawo bargo ta rufe jikinta, kana tasoma raba idanu, murmushi yakumayi mata haɗe da sanya hanu ya shafi gefen kumatunta.
"Kitashi kiyi sallah, ni na wuce masallaci"
Bata iya amsa masa ba haryafice daga cikin ɗakin,, kallon kanta tashiga yi gaba ɗaya gashinta ya watse yayi buji buji dashi, da'alama dai tasha juyi acikin bacci,,, tana shiga bathroom ta haɗawa kanta ruwa me ɗan ɗumi, wanka tayi itama kana ta ɗauro alwala (🤔Yadai dukanku wanka sai kace 🙊)....
Tana fitowa daga bathroom ɗin ta zura wata jan doguwar riga marar nauyi, haɗe da zura hijab ajikinta, kan sallaya tahau haɗe da dai-dai ta tsayuwarta...... Koda ta'idar da sallan saida tayi azkar kafun ta miƙe daga kan sallayan,, harta zauna akan gado, maganganun Hajiya Shuwa suka faɗo mata arai inda take ce mata _"Kada ta sake ƙamshi yabar jikinta, sannan kuma idan tayi sallan asuba kullum tana shafa turare aduk wani lungu da saƙo na jikinta"_ batasan mene manufar hakan ba, amma dai ta ɗau maganar kuma zatayi aiki dashi. Gaban mirror tanufa haɗe da ɗaukan ƴar ƙaramar hand bag ɗinta dake aje kan mirror'n wani ɗan kwalban body spray ta ciro daga cikin jakar, haɗe da fesawa ajikinta, daga kan wuyanta har zuwa bayan kunnenta, sosai turaren yake da ƙamshi, take ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren,, tana shirin maida turaren cikin jakarta, Dr.Sadeeq yaturo ƙofar yashigo bakinsa ɗauke da sallama,, cikin murya me sanyi ta amsa masa sallaman nasa,, direct inda take tsaye ya nufo, batayi tsammani ba saiji tayi ya buɗe hannuwansa ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta,,,, idanunsa ya lumshe haɗe da buɗe hanci ya shaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta cikin wata irin murya yace
"Good morning madam!"
Kunyan sane yakamata, saikawai tayi ƙasa da kanta haɗe da cewa
"Ina kwana"
"Lafiya ƙalau, yajikinki?" ya amsa mata yana me cusa kansa acikin wuyanta..
"Da sauƙi"
Ta mayarmai da amsa cikin ƙasa da murya...
"Ƙamshinki yamin daɗi sosai, kinyi sallah ne?"
Kanta ta ƙaɗa masa alamar "Eh" hanunta yakama yajata zuwa kan gado... Zama yayi kana ya jawota jikinsa,, ɗago fuskarta yayi haɗe da jefa idanunsa cikin nata. Sunanta yaƙira cikin wata irin murya me ɗauke da nutsuwa..
Kanta ta ɗago ta kallesa, ganin idanunsa tsaye cak akanta yasanya tayi saurin meda kanta ƙasa..
"Meyasa kikejin kunya na sosai ne?"
Yayi mata tambayar da bata tsammata ba,, jijjiga kanta tayi alaman
"babu"
Sake matseta acikin jikinsa yayi haɗe da kwantar da kansa akan kafaɗanta.
"Mallakarki danayi wata babban nasara ce dana samu acikin rayuwata Zahrah, inasonki ne da duka zuciyata, dakuma iya gaskiyata, banda niyar cutar dake acikin rayuwar zaman aurenmu, abu ɗaya nakeso kiyi mini shine, ki rage yawan tunani da kuma kukan nan dakikeyi, inajin tsoro kada su haifarmiki da wata cuta, yanzu nasan kina da buƙatar hutu ko, ki kwanta ki huta, kafun anjima sai kiyi break fast"
Miƙewa tayi daga jikinsa haɗe da hayewa kan gadon ta kwanta, amma kuma bata ɗauke idanunta akansa ba, bayan kamar mintuna biyar da kwanciyarta shima yatashi daga zaunen da yake, kan gadon ya hau, har Zahrah taji bugun zuciyarta yasoma ƙaruwa, sai kuma taga ya lulluɓe mata duka jikinta da blanket, agefe da ita ya kwanta haɗe da juya mata baya... Shiru ɗakin ya ɗauka babu abun dake tashi sai sautin fitar numfashinsu,,, bayansa ta kafe da idanu, yayinda a cikin zuciyarta take wani tunani na daban, haƙiƙa duk duniya babu wani namiji daya dace yazamo miji agareta sama da Dr.Sadeeq, ya cancanta ƙwarai, shi mutum ne wanda zaiyi wahala asamu kamarsa, Dr.Sadeeq kuwa lumshe idanunsa yayi bawai don bacci ya ɗauke sa ba,, shima wani tunanin yakeyi daban, baisan meyasa aduk sanda idanunsa zasuyi masa tozali da Zahrah yakejin matsanancin sha'awarta ba, wanda ada kuma ba haka abun yake ba, bazaice da bayajin sha'awarta ba, yanaji sai dai kuma bakamar wanda yakeji yanzu ba, jiya bakaɗan ba ya'iya daure zuciyarsa, amma daba haka ba tabbas da baisan wani irin aika aika zaiyi mata ba, a hankali yaji idanunsa sun soma rufewa da'alama dai shima bacci bai ishesa ba, ae dole ma jiya sunsha gajiya sosai,, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauki ma'auratan biyu, yayinda kowanne daga cikinsu da irin samfurin tunanin dake cikin zuciyarsa....
***
10:00 am dai-dai ta buɗe idanunta, haɗe da waresu akan haɗaɗɗen zanen POP'n da ya cika saman ɗakin, kallonta ta mayar ga inda take tsammanin ganinsa, amma sai dai taga wajen wayam babu shi babu alamarsa. Da sauri ta tashi zaune haɗe da maida kallonta ga wani ɗan madaidaicin agogon bangon dake saƙale jikin ginin ɗakin.
"ƙarfe 10 nakai ina bacci?"
ta tambayi kanta cikin yanayi naɗan mamaki.. A hankali tazuro ƙafafunta ƙasa, haɗe da miƙewa tsaye, ɗakalallen cikinta daya soma mata kukan yunwa ta shafa, haɗi da ɗan yamutsa fuskarta, direct ƙofar bathromm ta nufa, ɗan tsayawa tayi ta kasa kunnenta ajikin ƙofar, koda zataji ƙaran ruwa, amma saitaji shiru da'alama dai bakowa acikin bathroom ɗin, murɗa handle ɗin ƙofar tayi tashige ciki,, ruwan wanka ta haɗa yayinda ta cika turaren ƙamshi acikin ruwan, wankanta tayi cike da nutsuwa... Sanye da wani ɗan madaidaicin towel pink colour ajikinta tafito daga cikin bathroom ɗin, hatta gashin kanta ajiƙe yaƙe, still ƙaramin towel ne kuma riƙe ahanunta tana goge gashin kanta dayake ajiƙe,, daidai lokacin Dr.Sadeeq yaturo ƙofar ahankali yashigo, suman tsaye yayi ajikin ƙofar yana me ƙare mata kallo daga sama har ƙasanta, yayinda ita kuwa batasan ma da zuwansa ba, kanta kawai take aikin gogewa, saboda bataji motsin buɗewar ƙofar ba, shikuwa dama yabuɗe ƙofar ne ahankali gudun kada ya tasheta a baccin daya barta tanayi,, wani yawu ya haɗiye, haɗe da jan ƙafansa a hankali yafice daga cikin ɗakin batare daya bari ta ganshi ba,, yana fita yajingina bayansa da ƙofar haɗe da sauƙe wani irin ƙaton ajiyar zuciya,, lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanunsa acikin tulin sumar kansa yashiga shafawa a hankali,, ashe haɗuwar Zahrah yawuce yanda yake zato yake kuma tunani, wannan wace irin haɗaɗɗiyar surace Zahrah'n sa ta mallaka,, lallai Zahrah mace ce cikakkiya tagaban kwatance,, da ƙyar ya'iya jan ƙafansa ya koma cikin falo, kwanciya yayi akan kujera haɗe da lumshe idanunsa da suka sauya launi lokaci guda...
Zahrah kuwa tana gama goge gashin nata tayi amfani da hand dryer wajen busar dashi mintuna kaɗan gashin yabushe tashafa masa mai,,, wani lotion me ƙamshi ta shafa ajikinta haɗe da murzawa fuskarta hoda da kuma kwalli, light pink lipstick tagoga akan leɓenta, take fuskarta ta tasake yin kyau,, gaban makeken drower'n dake kafe ajikin bangon ɗakin taƙarasa haɗe da buɗewa, kayane jere reras acikin drower'n kala kala sai wanda ranka yaso zaka saka, wata jar atamfa taciro wacce taji ɗinkin pencil gown,, tana sanya doguwar rigan yayi mata kyau haɗe dayi mata ɗas ajikinta, daga kan guiwanta harzuwa ƙafarta atsage yake ta bayan rigan, tanason atamfar sosai saboda tana ɗaya daga cikin kayan da Maman Husnah ta bata, Husnah ce kuma takai akayi mata irin wannan ɗinkin duk da kuwa irin tsadar da atamfar take dashi, kallon kanta tayi acikin madubi, murmushi tasakarwa kanta saboda ita kanta ta yaba da yanda rigan tayi mata kyau ajiki, wani ɗan madaidaicin vail me kalan ja ta ɗauka haɗe da rufe jikinta, duk da kuwa cewa kayan yana da ɗan kwali, sai dai bazata iya tafiya daga ita sai wannan rigan agaban Doctor ba saboda sosai hips ɗinta suka bayyana, ga shi breast ɗinta sun bayyana kansu ta saman rigar kasancewar wuyan rigan yana da ɗan faɗi. Da turaruka masu daɗi ta feshe jikinta... A hankali ta buɗe murfin ƙofar ɗakin tafito, ɗan tsayawa tayi tana kallonsa,, kwance yake akan kujera yayinda idanunsa ke a lumshe, yasha adonsa cikin wata bugaggiyar shadda blue colour. Murmushi tayi domin kuwa yayi mata kyau, sosai kuma hasken fatarsa yasake bayyana acikin blue ɗin kayan. A hankali tashiga takawa har zuwa tsakiyar falon, ƙarewa falon kallo tashiga yi, ita dai haryanzu bata gamsu da cewa wai nan ɗin falon ta bane, koda wasa ma bata taɓa tunanin zata shiga cikin daula irin wannan ba,, bata ankara ba saiji tayi anriƙe mata hanu, da dauri ta juyo don batayi zaton idonsa biyu ba,, Murmushi yasakar mata haɗe da cewa,
Zama tayi akan kujera haɗe da cewa " banjima da tashi ba"
Tashi yayi daga kan kujeran haɗe da kama hanunta, kaitsaye haɗaɗɗen darny area'n dake cikin falon yanufa da'ita, jawo kujera ɗaya yayi daga cikin kujeru huɗu dasuka ke waye wani babban table, zaunar da'ita yayi haɗe da buɗe wani babban food flask, plate ya ɗauka yazu ba mata soyayyen dankalin turawa'n dake cikin kulan (Chips) wata food flask ɗin yasake jawowa pepper chicken ne dayasha albasa, shima zuba mata yayi haɗe da haɗa tea acikin wani cup, turo mata duka plates ɗin dakuma cup ɗin tea ɗin yayi gabanta,, saurin ɗago kanta tayi ta kallesa, kansa ya jinjina mata alamar koma me take tunani hakane, take ta shagwaɓe fuska haɗe da cewa "Bazan iya cinye duka wannan abincin ba yamin yawa"
"Bakomai kici sosai, nasan kinajin yunwa" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin barin wajen.
"Kai kuma fa?" batare da ta shiryawa fitowar tambayarba, saikuma bakinta yayi saurinfurtawa,, tsayawa yayi da tafiyar haɗe da juyowa, murmushi yayi mata haɗe da cewa "Ni bayanzu zanci ba" harya fice daga cikin falon bata ɗauke idanunta daga kansa ba,, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da ɗaukan fork tasoma cakan chips ɗin tana kaiwa bakinta, dama yunwa takeji sosai,, sosai taci chips ɗin saidai tea ɗin sama sama tasha shi, naman kuwa ko taɓa shi batayi ba, domin ita gaba ɗaya naman kaza baiwani dameta ba, tafison gasashshen naman sa, fiye da na kaza, sai da taji cikinta yayi haniƙan kafun ta kimtsa wajen haɗe da miƙewa takoma cikin falon,, haryanzu dai idanunta basu ƙoshi da ƙarewa falon kallo ba, rayuwa kenan wai yau ita Zahrah ce zaune acikin wannan katafaren gida dasunan gidan aurenta, ita da ko gado bata dashi akan zallan ƴar katifa take kwana sai gata yau ta kwana akan haɗaɗɗen gado harda lallausan bargo da ta rufa dashi,, a hankali ya turo ƙofar falon yashigo, wayarsace riƙe a hanunsa yana latsawa,, gaf da'ita ya zauna har kafaɗunsu suna gogan na juna, hanunsa ya sanya ya shafi ɗa kalallen cikinta, "Wannan ɗan ƙaramin cikin baiƙoshi ba"
Murmushi tayi masa haɗe da waro idanunta "Dan Allah kayi haƙuri wallahi na ƙoshi" tafaɗi haka tana me ɗauke hanunsa daga kan cikinta.. Kallonta yashigayi yana me karantar yanayinta yayinda ita kuma tayi ƙasa da kanta, batason haɗa idanu dashi kwata kwata, "taso muje" yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, babu musu ta miƙe, hanunta ya kama suka nufi wata ƙofa dake cikin falon, key ya sanya ajikin ƙofar ya murɗa, tura ƙofar ɗakin yayi, still hanunta na riƙe acikin nasa hanun suka kutsa cikin falo'n, falone ma dai-dai ci wanda aka kewaye tsakiyansa, da wasu kujeru dark purple masu kyau, yayinda tsakiyar falon kuwa aka cike sa da wani ɗan madaidaicin chanies carpet dark and light purple colour, wasu labulaye masu kyau kalan light purpule su suka ƙawata jikin ƙofa dakuma windown falon, wani ɗan ƙaramin plasma ne maƙale ajikin bangon falon, su kenan iya abun dake cikin falon amma kuma duk da haka falon yayi kyau, kasancewar kalan kujeru da labulayen kalane me ɗaukar hankali, ga kujerun sunsha pillow ƴan ma dai-dai ta gwanin ban sha'awa, yana riƙe da hanunta suka kuma shiga cikin wani ɗaki dake cikin falon,, gadone me kyau irin na zamani da drower'nsa me ɗauke da murafe shida, sai kuma su dressing mirror dakuma abun aje takalma da jaka,, kayan furnitures ɗin bawasu masu tsada bane daga kujerun har gadon bazasu wuce dubu ɗari huɗu ba, amma kuma anyi kayan da kyau da kuma inganci,, kallon sa Zahrah tayi alamar tanason ƙarin bayani,, murmushi yasakar mata haɗe da sa hanu ya shafa kumatunta, yace da'ita
"Kayan ɗakin da Baffa yayi miki ne"
Daɗi da farinciki ne suka cika zuciyar Zahrah take tacigaba da wurga idanunta tana kallon kayan, Allah sarki Baffa ashe haka yayi mata ƙoƙari batasani ba, lallai Baffa yafaranta ranta sosai, bata taɓa tunanin zata samu kaya haka ba, ashe dai Baffa yanasonta yana kuma ƙaunar fitar da'ita kunya, lallai wannan kaya sunfiye mata komai, saboda koba komai zata tsallakewa gorin wasu mutanen, wani irin tausayin Baffan nata ne taji ya sake ɗarsuwa aranta,, duk da cewa shiba mawadaci bane amma yayi ƙoƙari ya wadata ta da kayan ɗaki masu kyau dai dai da me rufin asiri, babu abun da zatace da baffanta sai godiya,, kan gadon taje ta zauna tana murmushin jin daɗi, sai taji tafi ƙaunar ɗakin ma fiye da wanda aka kaita daga farko, duk daɗin kyauta dai baikai ace da kuɗinka kacire ka saya ba.
"Yanaga kin wani zauna madam? taso muje nunamiki kawai nayi, bawai nace anan zaki zauna ba" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me miƙa mata hanunsa alamar takama sutafi,,
Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da kwantar dakanta gefe
"Nidai nafison nan please kabarni anan!" taƙare maganar cike da zallan shagwaɓa..
Takowa yayi yazo gaf da'ita haɗe da sanya hanunsa ya ɗago kafaɗunta.
"Nan ɗakin hutawan kine, can kuma ɗakin aurenki ne ɗakin dana zaɓa mana ni dake domin muyi rayuwar auren mu, kodai baki yaba da zaɓin nawa bane? kokuma baki amshi kyautar danayi miki bane?"
Ɗara ɗaran idanunta ta ɗago ta sauƙesu akan nasa idanun, kanta ta girgiza cikin sanyin murya tace " Ba haka nake nufi ba, kuma nayarda da duk inda kazaɓamin zanyi rayuwa aciki, kayi haƙuri idan maganata ta ɓata maka rai ban....."
"Shiiiiii" ya katseta ta hanyar ɗaura hanunsa akan laɓɓanta, jawota jikinsa yayi , haɗe da sanya yatsarsa yashiga zagaye ɗan ƙaramin bakinta,, ƙasa tayi da'idanunta domin kuwa bazata iya jure kallon cikin idanunsa ba, sake matso da fuskarsa yayi daf da tata har numfashinsu na'iya gauraya waje guda, yayinda dogon hancinsa ke gogan nata hancin, atare suka lumshe idanunsu, ahankali laɓɓansa suka sauƙa akan nata laɓɓan, baikai ga soma yin kissing ɗinta ba ƙaran wayarsa ta karaɗe cikin kunnuwansu, da sauri ya sake ta,haɗe da sanya hanu acikin aljihunsa ya ciro wayarsa dake ta faman ƙara, katse ƙiran yayi haɗe da kashe wayar baki ɗayanta ya kuma maidata cikin aljihun rigansa.