Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, har batasan sanda ta ɗago da idanunta ta kalli Baffa ba.
Baffane yacigaba da cewa "Bansan ko su ɗin suwaye bane, amma ban ɓoyemusu komai ba, nasanar dasu cewa nabada aurenki ga wani, amma mahaifin yaron yace yabani lokaci nayi tunani, saboda hakane ma naƙiraki domin ni bazan miki dole ba, zanbaki dama ne ki zaɓi wanda kikeso"
Take idanun Zahrah suka kawo ƙwalla, sakamakon jin wani baƙon al'amari dayake shirin kunno kansa cikin rayuwarta.
"Kinyi shiru, ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba Zahrah, kema kina da ƴan ci, zan kuma baki ƴancin ki, sai dai abun da nakeson sani shine wanene yaron nasa, saboda bai yiwuwa a haɗaki aure da wanda bamusani ba, amma idan ke kinsan sa shikenan ba damuwa"
"Bansan saba Baffa, kuma ma koda nasansa bazan aminta dashi ba, saboda idan nayi haka ban yi mawa Dr.Sadeeq adalci ba" Zahrah tafaɗi haka cikin sanyayewar murya...
"Adalci, kaji shirmen banza don Allah Malam, wani adalcine yarage miki, wanda yawuce ki kai kanki cikin arziki kicisa yanda yakamata, saidai ko inkuma baƙin ciki kike mana"
Inna ta tsomo bakinta cikin maganar batare da angayyaceta ba...
"Tashi kije Zahrah, idan suka sake zuwa zan sanar dasu cewa hakan da sukeso bazai yi wuba" Baffa yafaɗa, yana mai wurgamawa Inna harara..
Cikin rashin ƙwarin jiki haɗe da ɗaurewar kai Zahrah tabar ɗakin.. Haushin Zahrah da Baffa ne yacika zuciyar Inna, amma ganin yanda Baffa yahaɗe fuska bai bata damar yin ƙorafi ba yasanya itama tafice daga ɗakin tana me ƙananan maganganunta wanda ita kaɗai tasan metake cewa..
Zama Zahrah tayi jigum haɗe da zurfafa tunanin ta, ba'abun dake bata mamaki da ɗaure mata kai, kamar neman aurenta da Baffa yace anzo anyi, "To waye zai zo neman aurenta batare da saninta ba? batare da ta kuma sanshiba, lallai koma waye baisan meyafaru da'ita ba, domin tasan daya sani, da baiyi gigin turo magabatansa nema masa aurenta ba" Haka dai tayita saƙawa da kuncewa har bacci ya ɗauketa......
Cike da tsananin mamaki Zaid yake kallon mahaifinsa, sakamakon ji da yayi mahaifin nasa nacewa "Wai anbada auren Zahrah'nsa ga wani" " Anya kuwa gidan su Zahrah Dad ɗinsa yaje? kodai yayi mistake ne yaje wani gidan amadadin nasu Zahrah?" duk wannan tambayar kansa ya mawa.
"Inaga zaifi kyautuwa kanemi wata My Son, domin kafasan nema cikin nema haramunne" Alhaji Ma'aruf ya faɗa yana me kallon ɗan nasa.
"Inaga ba gidansu kaje ba Dad,
domin ni nasan Zahrah tawace, baza'a bawa wani ita ba bayanni" Zaid yafaɗi haka bayan yayi sipping holandia milk ɗin dake aje cikin glass cup ɗin dake gabansa.
Kallon mamaki Alhaji Ma'aruf, yashiga yi mawa Zaid, sakamakon jin abun daya faɗa.
Baisan me yake shirin faruwa da ɗansa ba, amma tabbas ya hango wata irin soyayya acikin idanun Zaid ɗin me matuƙar zafi, wanda Zaid shikansa baisan da'ita ba...
Murmushi kawai Zaid yayi haɗe da kallon mahaifin nasa...
"Kai mahaifinane saboda haka bana iya ɓoye maka komai, a gaskiya banjin zan iya zama da wata daban, idan ba Zahrah ba, zanyi komai da kaina kawai" yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye... Da kallo kawai Alhaji Ma'aruf yabi sa dashi har ya fice daga cikin falon nasa. Ajiyar zuciya yayi haɗe da cewa "wataƙila idan kuɗi na magani, to zasu maya Zaid, ta hanyar samo masa auren Zahrah"
(hmm bakomai ake nema a samu ba, bakuma komai kuɗi yake iya saya ba)
Kai kawo Zaid yashigayi a tsakiyar tankamemen aljannar duniyar falonsa, gaba ɗaƴa yarasa me yake masa daɗi, shin maganar da Dad ɗinsa ya faɗa masa cewa anbada Zahrah, gaskiya ne kokuwa Dad ɗinnasa ne yayi mistake wajen gano gidan su Zahrah, dudduniya babu wani mahaluƙi daya isa yimasa shamaki da muradinsa, lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyana kansa gareta, baidamu da yanda zata ɗaukesa ba, shidai burinsa kawai shine ya mallaketa amatsayin matarsa, lallai yanzune zai gudanar da babban takunsa, sannan kuma yazama dole yagano bayanshi wayake bibiyan Zahrah, har ake yunƙurin aura masa ita, dole yagano wannan, domin yayi imani cewa Zahrah tasa ce...
***
Fitowarsu daga lecture kenan, wayarta tayi ƙara alamar shigowar saƙo,, ko kaɗan batayi mamaki ba, domin zuwa yanzu tasaba da saƙonnin da'ake turo mata batakuma san waye yake mata hakan ba.
Ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta gama karanta saƙon, yau madai kalamaine masu tsayawa a zuciya, ɓoyayyen mutumin nata ƴarubuta mata, sai dai kuma duk sanda ya turo mata da saƙo, idan takaranta kalaman sukan tsaya mata arai suna kuma yawan yi mata yawo a ƙwaƙwalwarta, koda sau ɗaya ne bata taɓa tunanin mayar masa da amsa ba, amma hakanan taji yau tanason tambayarsa ko shiɗin waye.
"Waye kai?" Abun da tarubuta tatura masa kenan.
Zaid dake kwance cikin wata luntsumemiyar kujera yana sipping wine yaji wayarsa tayi ƙara alamar shigowar saƙo, ɗaga wayartasa yayi yaduba, murmushinsa me kyau yayi bayan yagama karanta tambayar nata..
"Kinason ganina?" shima yamayar mata da tambaya, tahanyar tura mata saƙo.
Zahrah na karanta saƙon tasoma typing kamar haka...."Mezai hana idan zaka bayyana kanka" tana gama rubutawa tayi sending..
"Kishirya ranan friday 8:00 pm zankawomiki ziyara, ina fatan zakiji daɗin ganina, sannan zan taho miki da kyakkyawan surprise" yana tabbatar da cewa saƙon ya isa zuwa wayarta, yayi switch off na wayarsa, sake gyara kwanciyansa yayi ajikin kujeran, haɗe da lumshe idanunsa, jiyake mararsa tana yi masa ciwo, kusan kwana uku kenan da yake fama da wannan ciwon maran, hakan kuma yasamo asali ne da wata irin sha'awa da ta damesa, sai alokacinne ma yake tuna cewa yajima baiyi sex ba, lallai akwai abun da yake damunsa, Zaid ɗin da baya iya kwana ɗaya baiyi sex da mace ba, wai shine yanzu yake iya kwanaki batare da yayi sex ba, shida mace ɗayama bata isan sa, amma sai gashi, yau ɗayan ma, yakasa nutsuwa yakusanceta, lallai yanzu kam yayarda da cewa akwai abun dake damun jiki da zuciyarsa....
Ɗan jim Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon nasa, idan bata mantaba yau Tuesday kenan saura kwana biyu jumma'a tayi, lallai tanaso taga wanene wannan wanda yaɗau lokaci yan ɓata tunaninta, ta wani ɓangare na zuciyarta kuwa, ji takeyi tamkar akwai wani gagarumin abu dazai faru da'ita, yayinda idan ta tuna aurenta da Dr.Sadeeq saitaji ta zama wani iri da'ita, bakuma aurenta da Dr. ɗinne bataso ba, a'a kawai dai tanaji ajikinta kamar basu dace da juna ba ita dashi...
Dariya sosai Salima tashiga yi, sakamakon labarin da ƙawarta kuma aminiyarta Laura tabata yanzun. Wani irin daɗi taji haɗe da sanyi acikin zuciyarta, gaba ɗaya labarin Zahrah Laura ta kwashe ta sanar da Salima, wanda Laura ta samo asalin labarin Zahrah ne daga bakin wata Asma da take unguwarsu Zahrah'n kuma har school ɗinsu ɗayama da Zahrah..
"Dama akan sauran wani Doctor yake wulaƙantani hadda jamin aji, hmm lallai kuwa bazanyi kishi da mai aji bama ballentana marar aji" Salima ta faɗi haka cike da kunfar baki...
"Ae magana taƙare Salima, kamar yanda na faɗamiki, tashi kawai zamuyi muje hargidansu, muci mata mutunci mukuma gargaɗeta da tafita hanyar Doctor Sadeeq" Laura tafaɗi haka cike da son zuga Salima.
"Gaskiya ne nima ina bayan maganarki Laura" wata wacce take zaune gefen Laura ta faɗi haka, tana me taɓe baki..
Kallonta Salima tayi haɗe da cewa "Shiyasa nake sonki ƙawata, bakida wasa, wajen sawa ayi rashin mutumci, idan kinshirya muje gidan nasu yanzu, domin akan Doctor sai inda ƙarfina ya ƙare" Salima tafaɗi haka tana maitashi daga zaunen da take.
Motar Salima suka shiga su duka ukun yayinda Laura ke tuƙasu, domin itace jagoran tafiyan kasancewa har gidansu Zahrah ta sani, saboda tasa Asma ta nuna mata....
Zahrah ce zaune a tsakar gida bisa kan tabarma, kwanon abincine aje a gabanta, gaba ɗaya ta kasa tsayawa taci abincin yanda yakamata domin kuwa yau Thursday gobe ne kuma haɗuwarsu da mutumin dayake ɓoye mata kansa, duka nutsuwarta baya gareta, hakanan takejin babu alkhairi a haɗuwarta da mutumin...
Wani irin bangaja da aka mawa ƙofar gidansu shiyasanyata ɗago kanta takai kallonta zuwaga ƙofar gidan nasu..
Wasu tsalan tsalan ƴan mata su uku ta gani, tsaye ko wacce ta kafa makeken glass akan idonta, yayinda suke taunar cingam cike da iyawa haɗi da salo......
(Manage please👏 rasuwa akai mana shiyasa banyi posting da wuri ba)
*(Wannan page ɗin gaba ɗayansa kyautane a gareku Members na BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION haƙiƙa kuɗin na daban ne, sannan kuma kuna da ƙoƙari sosai da sosai wajen sanbaɗomana comment, muna godia Allah yabar ƙauna)*
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 64 to 65*
Baki da hanci Zahrah ta sake tana kallon waƴan nan ƴan matan da suke tsaye suna me yimawa cikin gidannasu kallon wulaƙanci haɗe da ƙyama..
Cire glass ɗin dake idanunta Salima tayi, haɗe da watsamawa Zahrah wani irin kallo mai ɗauke da mugun tsana, cike da ƙyama ta furzar da yawu, haɗe da kallon Laura "Itace wan nan?" Salima ta tambaya tana me nuna Zahrah da hanunta cike da taƙama.
"Eh itace ƴar matsiyata" Laura ta faɗa tana yanatsina fuska.
"Lafiya kuwa bayin Allah? su waye ku? Zahrah ko kinsan sune?" Inna da fitowarta a ɗaki kenan ta tambaya, Tana me mamakin ganinsu haɗi da aljabi.
"Ba alkhairi bane ya kawomu, saboda baku kai matsayin da zamuzo muku da alkhairi ba, sunana Salima, nazone domin najawa wannan matsiyaciya kuma karuwar ƴar taku kunne, koda wasa Doctor Sadeeq basa'an aurenta bane, saboda yawuce ajin macen da taraba mutuncinta a titi" takawa taci gaba da yi cikin isa harta ƙarasa gaban Zahrah, da ta kasa ko motsi... "Banzo danna cutar dake ba, amma tabbas idan kika sake nakuma dawowa cikin gidan nan to zanyi miki babban illa, rabuwa dashi zai fi miki, idan kuma kika ƙi, hmmmm zakisan cewa bakin rijiya bawajen wasan makaho bane, bake kaɗaiba, hatta tsohon da yake riƙe dake sai ya ɗanɗana" Salima tana kai ƙarshen zancen nata tamaida glass ɗin ta dake riƙe a hanunta, haɗe da kallon su Laura "Muje" tace dasu, babu musu kuwa suka rufa mata baya, suna tafiya suna kareraya...
Sallallami Inna tashiga yi haɗe da tafa hannuwanta duka biyu, "Lallai kuwa wa ƴan nan ƴan iska masu jajayen fuskar suncika marassa ta'ido, rashin kunya har cikin gida" Inna tafaɗi haka cike da mamaki.
Kai kawai Zahrah ta girgiza, haɗe da jawo kwanon abincinta ta ci gaba da ci, batare da ta tankawa Inna da take ta ɓaɓatu ba,, sai dai kuma sosai maganganun Salima suka daki zuciyarta, har wani ɗaci takeji a cikin maƙoshinta.. Tura abincin takeyi amma jinsa take tamkar maɗacin dayafi kowanne ɗaci, har wani zafi takeji a ƙirjinta. Tana gama cin abincin, ta kora da ruwa, haɗe da tashi kai tsaye tanufi ɗakinta.
"Karuwa" sunan da Salima taƙirata dashi yafiye mata komai ciwo, tunda take a duniya ba'a taɓa ƙiranta da sunan karuwa ba, sai a yau ɗin, wasu irin zafafan hawayene taji sunshiga gangarowa daga cikin idanunta, durƙushewa tayi a ƙasa haɗe da soma rusa kuka, filla filla kalaman da Salima ta faɗa mata suke dawowa cikin kanta, koda wasa bata taɓa tunanin za'afaɗi kalma na ɓatanci masu muni irin haka akan ta ba.
"Kacuceni Zaid, Kacuceni, me yasa ka aikata haka agareni, shin koda sau ɗaya ne bakayi tunanin yanda rayuwata zata kasance ba, bazan taɓa yafe maka ba Zaid har kuwa nakoma ga mahaliccina" cikin kuka ta ƙare maganar, domin kuwa sai yau tasake tabbatar da cewa Zaid ya cuceta, takuma ƙara jin matsanancin zafi dakuma ciwo akan fyaɗen da Zaid yayi mata.. Abu kamar wasa haka Zahrah tayita kuka tamkar ranta zai fita, sai gashi cikin mintuna ƙalilan ciwon kai yakawomata ziyara, wanda har sai da yakaita ga kwanciya.. Ƙiran Dr.Sadeeq ne yashigo cikin wayarta amma tanaji tana gani takasa picking call ɗin har wayan ta tsinke, taƙi ɗaga wayan ne kuma don bataso yafahimci cewa tana cikin damuwa. Wani ƙiran nasa ne kuma yasake shigowa, still dai har wayan ta katse, Zahrah bata ɗauka ba, domin har yanzu bata dawo cikin nutsuwarta ba.. Ƙira na uku ne yakuma shigowa cikin wayarta ta, ƙoƙari tayi wajen ɓoye damuwarta haɗe da ɗaukan wayar ta kara akan kunnenta..
Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yasauƙe sakamakon ji dayayi ta ɗaga wayan.
"Wani irin laifi me girma na'aikata haka da aka ƙi amasa wayata?" Dr.Sadeeq yatambaya.
Cikin sanyin murya Zahrah tace dashi "Bana kusa ne shiyasa"
Wata ajiyar zuciya yakuma sauƙewa cike da kulawa yace "Naji muryarki ta sauya ina fata dai kina halin lafiya?" cikin kulawa ya ƙare maganar.
"Lafiya ƙalau" tabasa amasa a taƙaice.
"Yakamata nazo muyi magana domin inaso nasan irin shirye shiryen da zakiyi, idan lokacin auren mu ya gabato, kinsan yakamata ace anfarayin komai akan lokaci, yanzu ina tuƙi ne idan na tsaya zanƙiraki"
"To" kawai ta'iya cewa dashi, har ya katse ƙiran.
Tanacire wayar akan kunnenta saƙo yashigo cikin wayar.
"Nakan ji wani iri a jikina idan har kina cikin wani irin yanayi, ki daina sa kanki a damuwa, saboda zaki iya cutar da zuciyarki, nikuma bazan so haka ba, saboda kece muradina" abun da saƙon yaƙunsa kenan..
Tsuka Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon, haɗe da kashe wayarta ta baki ɗaya, jira take kawai Allah yakaita gobe taga wayane yake raina mata hankali haka, daga goben kuma zata takamawa komaye birki, domin kuwa ko ma wayene bazai taɓa burgeta ba, zuwa yanzu babu wani ɗa Namiji da zaiyi tasiri acikin zuciyarta.
Zaid ne kwance akan makeken gadonsa wanda yasha bedsheet na alfarma, kwanciyar nan yayi irin wanda ba kyau, wato rufda ciki, wata doguwar takarda ne riƙe a hanunsa, wanda take ƙunshe da duk wani abu daya ƙunshi Dr.Sadeeq daga kan sunansa aikinsa har zuwa mazauninsa, dakuma a halinsa, kyakkyawan bincike Zaid yasa a kayi masa akan Doctor ɗin, saboda a cewarsa babu wanda ya'isa ya shiga huruminsa, saboda Zahrah tasace shi kaɗai, saboda haka dole ne zaitakawa Dr.Sadeeq birki..
Murmushine ya bayyana akan fuskarsa bayan yasanya duka hanunsa biyu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa,, shi kansa yaƙosa gobe tayi yaga Zahrah'n sa, duk da kuwa cewa yana biye da duk wani shiga da ficenta, amma kwata kwata baya gajiyawa da ganinta, sam baisan meke damunsa ba, zuwa yanzu yafara kokonto dakuma tunani anya ba wannan abun da yakeji shi ake ƙira soyayya ba kuwa? Idan kuwa harda gaske abun nan da yakeji a game da Zahrah shi ake ƙira soyayya, to tabbas yakamu da so matsananci, sai dai kuma bayida ikon tabbatarwa kansa cewa so yake, hakanne ma ya hanasa gane wanni hali yake ciki, ko da wasa bai taɓa tunanin cewa Zahrah zata ƙisa ba, saboda haka ako da yaushe cikin ƙarawa kansa ƙwarin guiwa yake....
FRIDAY
Rana bata ƙarya, ranan yau ta kasance Friday kuma yaune Ɓoyayyen mutumin ta yayi mata alƙawarin baiyana kansa gareta, sai dai kuma baƙon al'amarin da ta wayi gari dashi yasoma tsinkar mata da zuciya, haɗe da sanyayewar jiki, domin kuwa yau ta tashi tana me jin faɗuwar gaba, haɗe da bugawan zuciya da akai akai, hakan kuwa baƙaramin tsoro yajefata ciki ba, saboda bata taɓa mantawa irin wannan faɗuwar gaban ta dinga ji a ranan da mummunar ƙaddaranta zata rusketa,, sai dai kuma babu abun da yagagari Allah, don haka ta shiga yin addu'o'i acikin zuciyarta, saboda ta samu salama..
Ƙarfe Uku na yammaci de de suka fito a lecture'n ƙarshe da suke dashi na wannan ranan, gaba ɗaya sukuku haka ta wuni a cikin school ɗin, Husnah tayi tambayan har ta gaji, akan ta faɗa mata meke damunta amma tace ba komai, to me zatace mata? ita kanta batasan meyake damunta ba.
Su Husnah ne suka kawota har ƙofar gida, saboda yanzu Dr.Sadeeq aiki yamasa yawa sosai, ga aikin office ga kuma hidiman hada hadan biki, gaba ɗaya baya samun isashshen lokaci, hakan yasa idan sun tashi a school take shiga motar da ake zuwa ɗaukar Husnah su sauƙeta a gida...
Tun azaure take ta kwaɗa sallama harta shigo cikin gidan nasu, amma babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta tabbatar cewa bakowa acikin gidan, har ɗaki ta leƙa amma babu Inna babu alamarta, saboda haka kai tsaye ta wuce ɗakinta. Zama tayi jigum tamkar wacce aka mawa mutuwa, fargaban haɗuwa da ɓoyayyen mutumin nan take, hakanan takeji dama bata nemi ganinsa ba, saboda gaba ɗaya jikinta yagaya mata babu alkhairi a haɗuwarsu, sai dai kuma babu yanda ta'iya tunda ya tabbatar mata da cewa yau ɗin zaizo, ganin da tayi tunani na shirin damunta, yasa ta ɗauko alƙur'ani mai girma tasoma karantawa, saboda hakan yana sauƙar da salama sosai acikin zuciyar wanda yake cikin ƙunci da fargaba....
Tana kai sujjadar ƙarshe ta sallan isha tafashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, hakan yafarune kuma saboda ta kasa control ɗin kanta, sosai faɗuwar gaban da takeji yake tsanan ta aduk bayan wasu mintuna.. Cikin kuka tasamu ta sallame sallan isha ɗin, bayan ta gama faɗawa ALLAH buƙatunta, tana me kuma neman sauƙi a garesa, idanunta da suke cike da hawaye ta ɗaga haɗe da maida kallon ta ga yagalgalellen agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe bakwai da arba'in, saura mintunan da basufi Ashirin ba yaƙaraso kenan, domin ƙarfe takwas yace mata zai zo...
Bugawan da agogo yayi 8:00 pm, yayi dai dai da bugawar zuciyar Zahrah, har