x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 38 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 111001 words
  • 114000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 257

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tayi kamar wata statue tana mamakin irin baiwar kyawun da Allah yayi mata, daga riganta har zuwa kan takalminta dakuma ɗan karamin fos ɗin dake rike ahanunta kalarsu yakasance light peach ne, yayinda stones ɗin kayanta suka kasance farare, lokacin da su Husnah sukayi tozali da Zahrah ihu dakuma shewa suka sanya haɗe da tsantsar mamakin irin kyawun da Zahrah tayi, kowa dai yasan Zahrah kyakkyawace amma kuma basuyi tunanin kyawunnata har ya kai hakaba, lallai duk namijin daya samu Zahrah amatsayin mata yayi babban gamdakatar. Take su Husnah suka shiga ɗaukarta hotuna da kuma vedios suna watsawa a instagram dakuma whatsapp, suna cikin buga selfie abokan ango suka ƙaraso don ɗaukar ƙawayen amarya,, duka ƴan matan kowacce da motar da tashiga, yayinda aka bar Zahrah da Husnah sukaɗai saboda Ango yace shi dakansa zaizo yaɗauki amaryarsa... Ƙawaye basu jima da tafiya ba wayar Husnah tasoma ƙara,, murmushi tayi haɗe da kallon Zahrah adai dai lokacin da taɗaga wayar takara akan kunenta, "To ranka shi daɗe gamunan fitowa" abun da Husnah tafaɗa kenan haɗe da miƙewa tsaye hannuwan Zahrah takamo haɗe da miƙar da'ita tsaye..
"Angonki yaƙaraso yace nafito masa dake" murmushi kawai Zahrah tasakar mawa Husnah kana ta sunkuyar da kanta ƙasa.. A hankali Zahrah ke takawa yayinda rigar jikinta kejan ƙasa, babu abun dake tashi ajikinta sai daddaɗan ƙamshin turare,, gaskiya Zahrah tayi kyau sosai ayau ɗin..


Ware idanu Dr.Sadeeq dake zaune acikin motarsa yayi yana me kallon Zahrah, shima yasha ado cikin wata farar gezina me matuƙar kyau da tsada yayi kyau sosai da sosai, kwarjininsa yasake fitowa fili..... Har Husnah ta buɗe murfin motar ta tura Zahrah ciki bai rufe bakinsa ba haka kuma bai ɗauke idanunsa daga kallon da yakeyi wa Zahrah ba, lallai ne godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) daya tsara wannan kyakkyawar halitta, kullum kuma koda yaushe yana kallon kyawun Zahrah amma kuma yau saiyake ganin kyawun nata yafi na koyaushe ƙawatuwa.. A hankali ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunsa,,, Zahrah kuwa tunda tashiga cikin motar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana me wasa da yatsun hanunta,, Motar Habeeb dake bayan ta su Zahrah Husnah tashiga,,, atare motocin suka tashi tafiya sukeyi ahanakali akan titin...


"Zahrah!" Dr.Sadeeq yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi dakuma sauƙar da nutsuwa. Kasa amsa masa Zahrah tayi, hakanan taji wani irin nauyinsa ya lulluɓeta.

"Kinyi matuƙar kyau sosai, sai yanzu nasakejin cewa nayi babban sa'a dana sameki, inasonki sosai Zahrah na, ina fata watarana nima kisoni tamkar yanda nake sonki!"


Sai alokacin Zahrah ta ɗago kanta, haɗe da sakar masa ƙawataccen murmushi, jiyayi gaba ɗaya ta kashesa da salon murmushin nata, a hankali ya matso daf da'ita haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya riƙesu gam acikin nasa, wani irin soyayyartane yaji yana ƙara shiga jikinsa, jiyakeyi tamkar ya jawota jikinsa ya rungumeta kozai sake samun nutsuwa acikin zuciyarsa.... Harsuka iso katafaren hall ɗin daya cika maƙil da jama'a zuwan amarya da ango kawai ake jira, amma Dr.Sadeeq bai ɗauke idanunsa akan abar ƙaunarsa ba, wani abun daya ƙara rikitar da Zahrah takasa cewa dashi komai shine yanayin yanda yake mata magana da wata irin murya me sanyi... Motarsu na'isowa wajen taron, mc yasoma shela cewa ga ango da amarya sun ƙaraso, take guri yasake ɗaukan shewa yayinda kowa yazura idanun ganin ango da amarya, waƴanda suka zo wajen dan gulma suka sake miƙa wuya musamman ma familyn Dr.Sadeeq wanda anriga da angama gayamusu cewa amaryan ƴar matsiyata ne saboda haka suka baza idanuwan ganin ta don kashewa idanuwansu ƙwarƙwata.... Habeeb ne ya buɗewa Dr.Sadeeq ƙofar motar yafito, yayinda shikuma Dr.Sadeeq da kansa yazagayo ya buɗe mawa Zahrah nata ƙofar,,, cikin nutsuwa ta zuro ƙafafunta waje, kafun daga bisani tafito daga cikin motar, hanunta ɗaya Dr.Sadeeq yakama suka soma taku cike da nutsuwa,, wajene yaɗauki shewa masu murna nayi masu baƙinciki ma sunayi, haka masu ɗaukar amarya da ango hoto da vedio's ma duk sunayi,, gaba ɗaya family'n Dr.Sadeeq ƙamewa sukayi ƙam ganin kyawun amarya ya tsoratasu sosai, saboda basu taɓa tunanin haka zasuga amaryan ba, sunyi tunanin zasu ganta wata almajira da'ita amma kuma sai suka ga saɓanin tunaninsu, lallai ba'abanza ba Dr.Sadeeq ya liƙe akan cewa shi dole sai'ita, takai takuma cancanci ayi mata fiye da haka ma... Har amarya da ango suka ƙarasa mazauninsu mutane basu daina yimusu vedio's ba, haka kuma idanu bai ɗauke daga kan suba.........


*(Bazan'iya cigaba da typing ɗinnan ba, saboda banaso ayi bandani domin nima yau zantaka rawa sosai💃💃💃💃 idan kamu ya kammala zan cigaba da typing😜🤣 Team Zaidu muna tare iya wuya😘, Team Dr.Sadeeq kuna cikin ƙalbina asahun farko ma kuwa🤗)*


*12/January/2020*


*Follow me on Whatsapp and Wattpad*



*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*



*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*CHAPTER 86 to 87*


Sunkuyar dakai ƙasa Zahrah tayi gaba ɗaya ita kunyar mutanen dake tare a wajen takeyi, tunda take bata taɓa shiga irin wannan taron ba, sai gashi yau akanta ma akeyin taron, ba abun dake damunta kamar yanda idan taɗaga idanunta take ganin idanuwan mutane akanta kowa ita yake kallo da waƴanda suka santa haddama waƴanda basu santa ba,, matso da kansa yayi kusa da'ita haɗe da kawo bakinsa wajen kunnenta "Anan ma kunya zaki nuna?" ƙasa ƙasa yayi maganar. satan kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi amma kuma batace dashi komai ba, haka dai masu yin vedio suka ci gaba da ɗauka yayinda..... Hmmmm kamu dai yayi kamu yakuma ƙawatar amma kuma sai dai sam amarya Zahrah ta kasa sakewa komai a ɗari ɗari takeyinsa, abu biyune suka haɗe mata kunya dakuma rashin sabo, saboda bata taɓa zuwa irin waƴannan wajen ba, wannan ne karonta na farko, gashi kuma kamun yatara mutane sosai, su Husnah sunyi rawa sosai sun raƙashe Amarya kuwa ae ko taka kafarta bata'iya ba gaba ɗaya nauyi da kunya sun hanata sakat.... sai gab da magrib aka tashi daga kamu kowa yasamu abun arziƙi ankuma cika ciki da abinci na musamman da kuma lemuka... Yanzu kam mota ɗaya Zahrah da Husnah harma da Suhaima suka shiga, yayinda Dr.Sadeeq shikuma yashiga wata motar ta daban... Jingina bayanta tayi da kujera haɗe da kwantar da kanta akan kafaɗan Husnah, duk hiran da Husnah da Suhaima keyi jinsu kawai takeyi, sosai sanyin AC'n dake cikin motar yake ratsata har hakan yaso sanyamata zazzaɓi, haka dama ita take matuƙar ta shiga hayaniya to kanta sai ya ɗanyi mata ciwo, uwa uba kuma idan sanyi yayimata yawa saita ɗanyi zazzaɓi.. Harsuka isa gida Zahrah ko uffan batace ba duk da kuwa yanda su Husnah kejanta da hira, amma iya abun da take iyayimusu shine murmushi... Fitowarta a wanka kenan, sauri sauri ta zura wata doguwar riga me kauri ajikinta,,, kallon ta ta mayar ga Husnah wacce taketa faman chatting a wayarta sai nurmushi kawai take zubawa..


"Wai ke da waye ne haka? a iya sanina dake ke ba mutum bace me yawan chatting da'alama dai munsamu ƙaruwa" Zahrah tafaɗi maganar cikin sigar tsokana... Dariya Husnah tayi haɗe da ɗage giranta sama. "Ƙwarai kuwa tawan, wallahi ɗazu na haɗu da wani guy a wajen kamunki, ina tunanin ya kwantamin arai"


Dariya Zahrah ta sanya haɗe da neman guri ta zauna akusa da Husnah haɗi da kwantar da kanta akan kafaɗan Husna'n....


"Husnah kinsan ya so yake?" tambayar da ta fito daga bakin Zahrah kenan..


Mamaki tambayar da Zahrah tayi mata ya bata amma kuma batasan menene dalilin dayasanya Zahrah tayi mata wannan tambayar ba...


"Eh zan iyacewa nasansa zankuma iya cewa bansan saba, saboda banyi wani zurfi acikinsa ba, amma kuma ke kinsan bana yaudaran kaina Zahrah, duk wasu alamomin so nasansu, saboda hakane ma nayardarwa kaina cewa nakamu da soyayyar Yazeed so matsananci!" Husnah tafaɗi haka tana me wasa da wayar hanunta, da'alama sunan Yazeed kaɗai da ta ambata yasanyata cikin shauƙi..


Ajiyar zuciya me ƙarfi Zahrah ta sauƙe haɗe da ɗago kanta daga kan kafaɗar Husnah, hannayen Husnah takama cikin murya me sanyi tace da Husnah "Wasu irin alamomi ne kesanyawa mutum yagane cewa yakamu da so? sannan kuma inaso ki sanar dani menene hukuncin zuciyar da ta makance har take ƙoƙarin sake son wanda yacutar da'ita, wanda kuma baida wani amfani a wajenta"


Kallon mamaki haɗe da ɗaurewar kai Husnah tashiga yi mawa Zahrah, ƙwarai itakam maganganun Zahrah sun sanyata a duhu me Zahrah take nufi?


"Banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zanfi fahimta idan har kika warware maganar tazama abu guda, amma kuma ni a ganina babu amfanin zuciyar da zata so wanda baida amfani a wajenta, sai dai kuma amma kinsan shi so wani zubin yakan makantar da komai naka ne tahanyar da baka isa kayi yaƙi dashi ba, amma kuma shi so kala kala ne, kowani so da'irin ƙarfinsa haka kuma da irin rauninsa, wani son yana fita, wani kuma sai ahankali zai fita, wani kuwa baya taɓa fita har gaban abada, amma shi wanda baya fita har abada shi ake ƙira da ƙauna, ita ƙauna kuma idan zafinta yatashi ƙona ka, to ƙunan yakan kasance me tsananin zafi da raɗaɗi bakamar na so ba, ina fata dai Ƙaunar Doctor ce tasanya kikamin wannan tambayar?" Husnah tafaɗi haka tana murmushi.. Wasu siraran hawayene suka silalo daga cikin idanun Zahrah zuwa kan ƙuncinta.


"Zahrah kuka kuma?" Husnah tatambaya cike da mamaki domin ita sam bataga abun kuka acikin maganar da sukeyi ba, hasalima ita Zahrah'n ce tafara ɗago maganar ba wai ita ba.


Hanu tasanya ta share hawayenta haɗe da sakin murmushi, "Bakomai Husnah kawai dai idanuna ne tunɗazu sukeyimin zafi, kinsan ban saba da irin wannan kwalliyar da akamin ba, bacci ma nakeji bana ɗan kwanta, idan kingama ki rufe mana ƙofa" Zahrah tafaɗi haka fuskarta ɗauke da murmushin dole..


Har Zahrah ta kwanta Husnah bata ɗauke idanunta daga kanta ba, sosai ganin hawayen Zahrah'n yabata mamaki duk da kuwa cewa tana lure da'ita a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya acikin damuwa take wuni, amma gudun kada ta dameta da tambaya yasanyata sharewa bata tambayeta ba, amma tasan damuwa kam akwai shi jingim acikin zuciyar Zahrah...


Kusan mintuna talatin hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, amma kuma ko kyakkyawan motsi taƙi tayi gudun kada Husnah ta fuskanci cewa batayi bacci ba,, bazata taɓa bari kowa yasan damuwarta ba, ta yarda ta amince zata haɗiye duk wani damuwarta acikin rai da zuciyarta ita kaɗai, koda kuwa damuwartata zata kasheta, tabbas wannan abun da takeji ba abu bane wanda zai ɓoyu ba, amma kuma zatayi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta maidashi ɓoyayyen sirrinta a haka har baccin gajiya ya ɗauketa, tana bacci babu jimawa kuwa ƙiran Dr.Sadeeq yashigo cikin wayarta, ganin ya nace da ƙiran ne yasanya Husnah ɗaga wayar ta shaida masa cewa Zahrah tayi bacci, to kawai yace haɗe da ajiye wayar..
Wani irin tausayinta ne yaji ya dirar masa acikin zuciyarsa, hakanan yaji yau soyayyarta yasake shiga zuciyarsa fiye da ko yaushe yayinda tausayinta yakuma ɗarsuwa acikin zuciyarsa, yaso jin muryarta acikin wannan daren amma kuma hakan baisamu ba, haka yashare yashiga cikin abokansa suka cigaba da sabgoginsu......


Kafe cak idanunsa suke akan haɗaɗɗen zanen POP'n dake mamaye saman ɗakin wanda aka ƙawatasa da ado me matuƙar burgewa, a hankali yake fitar da numfashi me zafi daga cikin hancinsa,, ahalin yanzu ba ciwon da yakeji bane damuwarsa, yafi damuwa da ganin Zahrah'nsa fiye da komai, yanzu kenan saura kwana uku a ɗaura mawa Zahrah'nsa aure da wani bashi ba, rumtse idanunsa yayi da sauri haɗe da haɗiye wani irin yawu me ɗaci daya tsaya masa a maƙoshi, abu kamar wasa saiga ƙwalla suna gangarowa daga cikin idanun Zaid, hanu yasanya yashafa gefen fuskarsa inda yaji sauƙar ɗumin wani abu kamar ruwa,, ruwan hawayen daya fito daga cikin idanunsa ya lakato ahanunsa koda yaga cewa hawayene ke fita daga cikin idanunsa sai yasaki wani irin murmushi me matuƙar ciwo, rayuwa kenan babu yanda bata juyawa bawa, watarana kaga me kyau watarana kuwa kaga mummuna, ƙaddara kenan babu tayanda bata zuwarwa bawa, haƙiƙa SO babban cutane ga bawa musamman idan baka samu abun da kakeso ɗin ba, tabbas ya jarabtu domin ko a iya haka Allah yabarsa ya horasa horo mafi tsanani ma kuwa, tabbas Zahrah itace rauninsa, rasata kuma shine abu wanda zaifiye masa komai ciwo acikin rayuwarsa, baisan wani irin zazzafar soyayya yakeyiwa Zahrah ba, ashe tun dama yaudaran kansa yayi ba sha'awarta yake ba sonta yake, amma kuma saboda wani banzan tunani da kuma banzar hujjan sa yasanya ya kasa yarda da hakan, idan yace zai misalta irin tarin yawan nadaman da yayi kawo daga randa ya yiwa Zahrah fyaɗe zuwa yau to tabbas yayi ƙarya, ya cutar da'ita, ya zalunceta, tabbas yasan bai kyauta mata ba, sannan kuma baiga laifinta da ta ƙishi ba tabbas shida kansa ya san cewa bai cancanci ta sake yarda dashi ba, saurin rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hannayensa da ƙarfi, bakomai ne yasanyasa yin hakan ba face tunowa da yayi lokacin da idanunsa suka rufe ya shigeta da ƙarfin gaske yanajin wani irin ihun da tayi amma saboda bushewar zuciya irin tasa haka bai saurara mata ba,, kansa yashiga duka da hannayensa biyu kamar mahaukaci, ihun da Zahrah keyi masa alokacin da zai keta mata haddine yashiga dawowa cikin kunnuwansa ji yake tamkar alokacin ne abubuwan suke faruwa,,, ihu yashiga yi batare daya sani ba, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu, Mum da shigowarta falon nasa kenan taji ihun Zaid na tashi daga cikin bedroom ɗinsa, cikin sauri hartana haɗawa da tuntuɓe tanufi ɗakin nasa,, kwance tagansa akan gado yaɗaura duka hannayensa akansa yana wani irin ƙara tamkar wani wanda aljanunsa suka tashi..


"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Zaid! Zaid!!" Mom taƙira sunansa cikin matuƙar ruɗewa,, girgiza sa Mum tashiga yi cike da ruɗewa sunansa kawai take ƙira, a tunaninta Zaid ɗin nata ya haukace ne, yanajin muryar Mom ɗinsa acikin kunnensa yatashi a zabure haɗe da faɗawa cikin jikin mahaifiyartasa, abun mamaki saiga Zaid nan na kuka tamkar wani ƙaramin yaro, ita kanta Mum kasa motsi tayi haka ta tsaya kamar statue, wai da gaske Zaid ɗin tane wannan, kuka fa yake, anya kuwa ba aljanune suka shiga mata jikin ɗa ba?.
"Zaid" Mum takuma ƙiran sunansa cikin murya me sanyi domin kuwa itama tuni ƙwalla harsun cika mata ido... "Please help me Mum, i don't want to lost her!" abun da Zaid ke faɗa kenan yana kuka,, mamaki marar misaltuwa ne yakuma kama Mum wannan wace irin masifa ne ya ruski Zaid wace irin tsinanniyar soyayyace wannan datake shirin haukata mata yaro? lallai yazama dole tayi wani abu, bazata taɓa bari tanaji tana gani ɗanta ya rasa ransa akan wata ba, wai dama ashe haka so yake? idan kuwa haka so yake to sai dai muyi fatan Allah yarabamu dayin so me tsanani....


Kansa mum tashiga shafawa ahankali cike da tausayawa tace "Ka kwantar da hankalinka Zaid, kayi haƙuri kasamawa kanka nutsuwa, badai kana sonta ba?"


Kai Zaid ya kaɗa tamkar wani ƙaramin yaro.


"Insha Allahu zata zamo taka, zaku rayu da'ita rayuwa ta har abada, kadaina damun kanka kaji my son!"


Mum ta ƙare maganar cike da lallashi..


Kansa ya kwantar akan kafaɗan mahaifiyartasa lokaci ɗaya yashiga sauƙe ajiyar zuciya irin dai yaro ƙarami yayi kuka ya ƙoshin nan.... Bayansa Mum take shafawa a hankali sai gashi cikin mintunan da basufi 10 ba Zaid yasoma fidda numfashi a hankali cike da nutsuwa da'alama dai bacci ne ya ɗaukesa, Mum tana tabbatar da cewa Zaid ɗin yayi bacci ta tattaro duka ƙarfinta haɗe da zameshi akan kafaɗanta ta kwantar da kansa bisa kan pillow'n sa haɗe da ja masa bargo ta rufeshi, kallon fuskarsa Mum tashigayi cike da tsananin tausayinsa, tajima tana kallonsa kafun daga bisani tayi masa addu'a ta shafa masa akan fuskarsa, cikin sanyin jiki ta tashi tafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni......


*Washe Gari*


Tun safe kwararriyar me zanen lalle wanda Dr.Sadeeq ya ɗaukarwa su Zahrah bayan yabiyata maƙudan ƙuɗaɗe tazo gidan,, zanen jan lalle me matuƙar kyau aka tsantsarawa Zahrah akan hanu da ƙafarta, abunka da farar fata take zanen jan lallen yafito akan fatarta yayi kyau sosai,,, lokacin da ta wanke zanen lallen nata hakanan ta tsinci kanta da sakin murmushi ita kanta sosai zanen yayi mata kyau gashi ya ƙara ƙawata farar fatarta gwanin sha'awa. Wayarta dake ringing ta ɗauka haɗe da karawa akan kunnenta, cikin wata irin kasalalliyar murya taji yace "Amaryata" murmushi tasakar masa me sauti haɗe da cewa "Umm" Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa yagyara zama haɗe da cewa "Ki ɗan bani aron minti 10 daga cikin lokutanki na yanzu inason ganinki" ya ƙare maganar yana wani lullumshe ido kamar wanda yake a gabanta. Ajiyar zuciya Zahrah tayi haɗe da cewa "Gani nan zuwa" tana aje wayar ta ɗauki wani haɗaɗɗen mayafi wanda aka masa ado da fararen duwatsu ta yafa ajikinta yayinda haɗaɗɗen gashinta dayasha saloon ya bayyana kansa
End Ads