Baki Zahrah taturo gaba haɗe da cewa ...
"Kasan tun ba yauba nafaɗama cewa banaso domin kuwa hidiman da kakemin yayi yawa, mai yasa bazaka bari haka ba!" ta tambayesa cike da sakalci..
"Saboda kina da mahimmanci, kinkuma cancani namiki fiye da haka, amma yanzu dai banso kice a'a ki karɓa kinji" still cikin lallashi yayi maganar.. Badon ranta yasoba haka ta karɓi ledan.
"Saida safe" tace dashi cikin sanyin murya haɗe da juyawa ta nufi hanyar shiga gida.
"Kada kimanta kin ɗauki alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma zaki shiga damuwa ba, kada ki karya alƙawari kinji mai kyau na!"
Murmushi kawai tayi masa haɗe da ɗaga masa kai alamar taji.
Yana ganin shigewarta cikin gida, shima yashiga motarsa haɗe da bata wuta yabar unguwar tasu..
Tanashiga cikin gida, Inna tayo kanta haɗe da fusge ledar dake hanunta, babu magana ba komai ta shiga zazzage ledan akan tabarma, kallonta kawai Zahrah ta tsayayi cike da takaici, sai yanzu take godewa Allah dayasanya ba Inna bace ta haifeta, domin kuwa da Innace ta haifeta to tabbas da nan gaba kaɗan zuciyarta zata fashe, saboda wannan halin da Inna keyi ba hali bane na iyayen ƙwarai, batama tsaya ganin menene acikin ledar ba, ta wuce cikin ɗakinta, domin ita dama ba wannan bane a gabanta, yanzu babban damuwarta shine, yanda zata samo maganin matsalarta.
Ɗaukan kwalin nan da aka kawo mata tayi, haɗe da soma kiciniyar buɗewa, kasancewar bakin kwalin a nane yake da wani gam me kyau..
Tana buɗe cikin kwalin wani tsadadde kuma kyayyawan agogo na mata ya bayya, gefen sa kuwa wani irin awarwarone haɗe da zobe masu kyaun gaske, wanda dagani kasan na gold ne, domin kuwa kyawunsu kaɗai ya'isa ya bayyana haka, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da mai da murfin kwalin ta rufe kamar yanda ta samu, ɗaukan kwalin tayi dukansa, haɗe da ɓoyesa a cikin kayanta, dawowa tayi kan katifarta ta kwanta zuciyarta cike tab da tunanin son gano wanda ya soma
bibiyar rayuwarta...
Hajiya Habiba (mahaifiyar Dr Sadeeq) ne zaune akan kujera gaba ɗaya ta tattara nutsuwarta ta miƙasa ga Baffa Amadu dake zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon...
Baffa Amadu ne yaci gaba da cewa " Banzo nan don na yi miki dole ba, amma Hajiya Habiba yana da kyau wasu lokutan muna ƙoƙari wajen bawa ƴaƴanmu dama akan abun da suka nuna zuciyarsu naso, musamman ma aɓangaren abun da yashafi aure, haƙiƙa Sadeeq yasameni da wannan maganar yakuma min bayani tayanda zan fahimta, Alhmdlh nakuma fahimta, yanzu saura ke, kada kice wai don ƙaddara ya taɓa faɗa mata, ɗanki bazai aure ta ba, kada kiyi haka, domin ita ƙaddara tanakan kowa mai kyau da marar kyau, sannan abu nagaba danakeso kisani, ko da ace alal misali yarinyar ta kasance karuwa ce, addini bai hana masa auren taba, wala Allah saboda auren saiki ga ta shiryu, balle kuma ma bahakan take ba, amma bazan miki dole akan cewa saikin amince ba, ɗan kine kuma kina da iko akansa"...
Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauƙe, haƙiƙa Baffa Amadu yazo mata da magana mai girma.
ɗan nisawa tayi haɗe da cewa "Bawai naƙi aurensa da ita bane, saboda wani abu ba ne, kawai dai inajiye masa yanda tarbiyan yaransa zai kasance ne matuƙar takasance tana cikin gidansa, domin na tabbatar rashin wadataccen tarbiyan da aka bata a gidansu, shiya jawo faruwar haka a kanta, kaga itama bata samu tarbiya mai kyau ba, balle tayi ƙoƙarin bawa nata yaran, haƙiƙa Sadeeq yarone mai biyayya agareni, kuma harcikin zuciyata na ƙudurta aniyar cewa bazai taɓa auren wannan yarinyar ba, amma tunda harka shigo cikin al'amarin shikenan na'amince, amma kuma fa sai dai idan su biyun duka zai haɗasu ya aura, kaga dai Salima ƴar wajen ƴar uwata ne, haka kuma mamarta aminiyata ce, bayanda za'ayi na watsa musu ƙasa a ido, tahanyar cewa Sadeeq bazai auri Salima ba, kuma kaga yanzu saura ƴan satika ne suka rage, har anriga da anfara shirye shiryen biki"
"Ƙwarai kina da gaskiya ta wani wajen, amma kuma bamu iya ja da haɗin Allah, yanzu zansanar da Sadeeq ɗin duk yanda mukayi dake, zan kuma faɗa masa amincewarki, nasan shi ɗinma zai amince da umarninki, amma inaga zaifi kyau ayi bikin nasu a rana ɗaya, domin babu amfanin jan lokaci"
"Shikenan to duk dai yanda ake ciki, zai zo yasanar dake" Baffa Amadu yafaɗi haka bayan yamiƙe tsaye ya gyara zaman garen dake jikinsa...
Cike da mutun ta juna sukayi sallama shida Hajiya...
Zama Hajiya tayi afalon haɗe da yin jigum, tabbas ba'ason ranta ta amince da wannan auren ba, saboda ita gani take tamkar yarinyar ba kimtsatstsiya bace, ta amince ne kawai saboda Baffa Amadu yashigo cikin maganar, kuma tana matuƙar darajasa haɗe da basa girma, domin tana masa kallo ne tamkar marigayi mijinta, amma da ba haka ba da bazata taɓa amincewa ba, yanzu dai kawai sai dai tayi addu'an Allah yabasu zaman lafiya, amma ta wani ɓangare na zuciyarta, tunani take taya zataje ta tunkari ƴar uwarta Hajiya Furaira da wannan maganar, tasan Hajiya Furaira macece mai zafi, bazata taɓa son hakan ba, domin saboda bala'inta da zafin kishin ta, ne ma yasanya mijinta haryau yakasa ƙara aure bawai kuma don baya so ba, to ina kuma da idan taji cewa ƴarta ɗaya tilo zata haɗa miji da wata daban wacce bata da galihu, gaskiya zaiyi wuya ta amince... Haka dai Hajiya tadinga saƙawa da kuncewa daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakinta....
Cikin matsanancin farinciki Dr S.S ke kallon Baffa Amadu sakamakon jin cewa wai mahaifiyarsa ta amince da aurensa da Zahrah, masha Allah ashe dai mafarkinsa zai zamanto gaskia, sai dai kuma farincikin nasa bai zama cikakke ba, domin kuwa sosai maganar haɗa auren Zahrah da Salima ya daki zuciyarsa, saboda shi a tsarin sa baida burin aje mata biyu acikin gidansa.
"Yanaji kayi shiru ne Sadeeq, ko baka amince da sharaɗin mahaifiyartaka bane?" Baffa Amadu yatambayeshi cike da kulawa.
Kansa yashiga sosawa yamakasa ce da Baffan nasa komai..
Murmushi Baffa Amadu yayi domin yafahimci halin da Sadeeq ɗin yake ciki. "Kada ka ɗaga hankalinka Sadeeq, atunanina ka kai namiji wanda zai iya riƙe mace sama da biyu, don haka wannan ba abun damuwa bane, kayarda da sharaɗin mahaifiyartaka, addu'anmu shine Allah yatayaka riƙo, yakuma baka dama da ikon yin adalci a tsakaninsu, yanzu yaushe kakeso muje gidansu ita yarinyar?"
Gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa kuwa jiyayi tayi masa wani iri. "Zansanarda Baffan yarinyar idan yafaɗamin ranan da zakuzo, saina faɗa maka" inji cewar Dr Sadeeq..
"To shikenan Allah yakaimu" daga haka sukayi sallama, Dr S.S yabaro gidan Baffa Amadu zuciyarsa cike da tarin tunani kala kala, yana farincikin cewa Zahrah zata zamo matarsa, amma kuma ta wani ɓangare na zuciyarsa kwata kwata bayajin daɗi. Zahrah tana buƙatar farinciki da kuma kulawa mai kyau, baikamata ace anraba mata farinciki ita da wata ba, to amma "Miye mafita?" yatambayi kansa, bayan yasan baida amsar tambayan nasa, amma koma dai mene ayau zaije yasamu Baffa yasanar dashi cewa yana neman abashi izini yaturo magabatansa don abasa auren Zahrah, yakuma ƙudurta aransa cewa, dakansa zai bada order a Dubai, na kayan lefen Zahrah, domin kuwa zaiyi rawar gani sosai, wajen ganin komai na Zahrah yafita da ban....
Amatuƙar mamakance Alhaji Ma'aruf ke kallon Zaid wanda yafaɗi maganar daya matuƙar basa mamaki.... "Aure fa kace Zaid, dagaske kake, yanzu kashirya zakayi aure?"
"Da gaske nake Dad aure zanyi, kuma inaso kaje da kanka ka tambayamin, banaso auren yawuce nan da sati biyu Dad"
Cike da tsananin farinciki Alhaji Ma'aruf yace "Alhmdlh! naji daɗi ƙwarai da gaske, domin zuwa yanzu yakamata ace ka aje iyali, insha Allah, zan je na tambaya maka aurenta, ƴar wayene kuma a ina take?"
"Ba ƴar kowa bace Dad, talakawa ne ma, amma ni ahaka naji na aminta ina kuma son na aureta" yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa..
Jinjina kai Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da cewa "Zan sa rana sainaje naga mahaifinta"
"To" kawai Zaid yace haɗe da tashi yabar falon Dad ɗinnasa....
Fitowarta amakaranta kenan, tana sauri ta samu abun hawa, don bata son tsayuwa a bakin makarantar, kasancewar Dr Sadeeq aiki yamasa yawa bazai samu daman zuwa ɗauko ta ba...
Wani matashin saurayine yanufo wajenta, hanunsa ɗauke da wani babban kwali wanda aka rufesa da wani irin abu mai kyau, aka kuma ƙawatasa da flower mai walwali..
"Ranki ya daɗe barka da yammaci" saurayin yafaɗa.
"Yauwa barkan ka dai" itama ta mayarmasa amsa cikin ɗari ɗari dashi..
"Saƙo aka bani nakawomiki" yafaɗi maganar yana me miƙa mata kwalin dake hanunsa..
Cikin mamaki Zahrah ta shiga kallon saurayin nan dake tsaye a gabanta..
Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake miƙo mata kyakkyawan gift ɗin dake hanunsa.
"Waye ya aikoka?" tayi masa tambayar cikin dakiya...
"amsar tambayarki duka suna cikin nan" yaƙare maganar yana me nuna mata kwalin dake hanunsa.
Hakanan taji zuciyarta ta aminta da ta karɓi saƙon.. Hanu biyu tasa ta karɓa, batace dashi komai ba tayi wucewarta dai dai lokacin mai taxi ya ƙaraso tashiga.
Tsurawa kyakkyawan kwalin idanu tayi, sosai adon jikinsa yayi kyau haɗe da ɗaukar hankali, gaba ɗaya ta ƙosa, tabuɗe kwalin don ganin ko wanene yake son yin wasa da hankalinta, ta hanyar turo mata da saƙonni, batare da yabari tasan kowaye shiɗin ba.
Tana shiga gida direct ta wuce ɗakinta, ko mayafinta bata cire ba, ta zauna haɗe da soma yaye ledan da akayimawa kwalinnan ado dashi, tana buɗe kwalin tayi arba da wani ƙatuwar ta karda wanda aka naɗeta, cikin sauri ta ɗago takardan haɗe da soma warwareta, amatuƙar razane tayi wurgi da takardan sakamakon idanunta da sukayi mata tozali da zanen hoton dake jikin takardan.
(🤔Ga Zaid ga Sadeeq ko waye cikinsu zai mallaki Zahrah🤷♀)
*17/December/2019*
*Follow me ...*
*Wattpad user name* *@fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Idanu ta ƙara zarowa domin tabbatar mawa kanta cewa abun da tagani gaskiya ne, ko kuwa, gizo idanunta keyi mata.
Tabbas dagaske ne bawai gizo bane, hoton zanen fuskarta ne raɗau ajikin takardan. Hanunta na rawa haka ta durƙusa ƙasa, haɗe da sanya hanu ta sake ware takardan, tabbas itaɗince babu ko kokonto, zanen fuskarta ce kwance ajikin takardan, amma saboda tsananin kyawun da zanen yayi tamkar azahiri haka zaka gani, hanu tasanya ta shafi zanen, cike da fargaba haɗe da ɗaurewar kai.
Lallai yazama dole a gareta tanemo wanda yake aikata mata waƴan nan abubuwan, kusan kwana uku yanzu kenan ana turo mata da saƙonni, bata kuma san daga waye bane.
Bata damu da ta duba sauran kayan dake cikin kwalin ba, ta tattara shi ta ɓoye acikin kayanta.
Zama tayi dirshan akan katifa tana mai da numfashi akai akai, sosai abun yabata mamaki, tabbas ko ma waye ne wanda yake bibiyarta ta tabbata yayi mata farin sani, amma kuma rainin hankalin yayi yawa, dole zataimawa tufkar hanci. Abun da ta ƙudurta kenan acikin zuciyarta domin iskancin yasoma isarta.
Ƙarfe 6:30 na yammaci Dr Sadeeq yayi wa gidansu Zahrah tsinke, bayan yasha adon sa cikin riga da wando na shadda ƴar bugu mai kyau. Zama yayi acikin motarsa yana mai jiran fitowar Zahrah, domin kuwa yamata waya yasanar da'ita cewa gashi nan, a ƙofar gidansu.
Kafeta da idanu yayi domin kuwa bakaɗan ba tayi masa kyau, cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, lallai Zahrah ƙarshe ce wajen haɗuwa dakuma kyau.
Fuskarta ɗauke da murmushi Zahrah ta ƙaraso wajen da motar tasa take fake. Tsayawa tayi ajikin motar, batare da ta buɗe tashiga ba. Ganin haka yasa Dr Sadeeq buɗe murfin motar yafito.
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da juya idanunta. "Eh mana, ko bankai naja aji bane?" itama ta tambayesa cikin yanayi na shauƙi.
"Murmushi yayi haɗe da ɗage giransa sama "Kin isa har kinma wuce, ko bakisan cewa keɗin tamusamman bace?"
Hararan wasa Zahrah ta wurgamai haɗe da kawar da kanta gefe, batare da tace dashi komai ba. Haka take al'adar ta ne, bakoda wani lokaci take bada amsar tambaya ba, domin a cewarta shiru ma magana ne.
"Kona zagayo na buɗe miki murfin motar ne gimbiyata, saboda naga kamar bazaki iya ba ?" yafaɗi hakan cike da kulawa.
"A'a ba buƙatar hakan, ni dakaina ma zan iya" taƙare maganar tana mai buɗe murfin motar, haɗe da shiga tayi mawa kanta mazauni.
Shima komawa yayi cikin motar ya zauna. Bayan ya ɗaura duka idanunsa a kanta.
"Kinyi kyau sosai, fiye da ko yaushe" yafaɗi haka yanamai kashe idanunsa.
Jinjina kansa yayi azuciyarsa kuwa cewa yayi "Lallai Zahrah tana da aji, duk da ta rasa Virginity ɗinta hakan baisanya ta zama wata sakaka da'ita ba, yanason mace wacce ta'iya takunta, wacce bata sakar baki tayita dariya like mental problem, wasu matan da zaran kace dasu sunyi kyau tofa take zasu wage baki suita ƙyaƙyata dariya, babu wani ɗan jan aji ba komai. nima shaida ce irin su Sister Munubiya idan kace dasu sunyi kyau ae har kyautan kuɗi zasu baka tsabar daɗi🤣"
Sake gyara zamansa yayi haɗe da dawo da nutsuwarsa zuwa gareta.
"Zaki'iya zama dani a ko wani irin hali Zahrah?"
Ya jefomata tambayar da bata tsammaci jinsa ba.
Cikin yanayin mamaki Zahrah ta dawo da kallonta garesa, haɗe da cewa "Banfahimci maikake nufi ba"
"Inanufin zaki iya rayuwa dani ako wani irin hali na tsinci kaina? sannan zaki iya yarda na haɗaku ku biyu na aura?" yakuma maimaita tambayar tasa.
Dummm haka Zahrah taji ƙirjinta ya buga, idan da badon kada yace ta rainasa ba, to tabbas da zatace dashi yasake maimaita maganar da yayi. Domin idan kunnuwanta sunjiye mata dai dai, to kuwa bata da amsar da zata basa, domin koda ta basa amsa zata iya faɗuwa, saboda balallai ta bashi amsa dai dai da abun da ya tambaya ba.
Idanunsa duka ya tsura mata, amsa kawai yakeson ji daga bakinta.
Kasa ce dashi komai tayi, domin kuwa haryanzu bata gama haɗa amsar da zata basa ba.
"Nasani dama ba lallaine ki amince ba, Hajiya na ta amince da aurena dake, amma kuma kamar yanda nafaɗamiki a baya, tun tuni akwai zaɓin da tayimin, takuma umarceni da na aureku duka biyu, shin zaki iya aurena a haka, zaki iya zama da wata a matsayin kishiyar ki?" yafaɗi hakan cike da zaƙuwan son jin amsa daga gareta.
Jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, take taji zuciyarta ta karaya, batasan ya'ake zama da kishiya ba, haryanzu ita yarinyace, bakomai tasani na game da al'amarin duniya ba, tanaji a labarai irin illan da kishiyoyi suke mawa junansu saboda kishi, amma ita yanzu ba wannan bane a gabanta, makomarta na gaba take tunawa, shinya zata kasance?" ta tambayi zuciyarta...
"Kinyi shiru kice wani abu mana zahrah ko zuciyata zata daina bugawan da takeyi" Dr yafaɗi hakan cikin yanayin damuwa.
"Bazan taɓa ƙin aurenka ba, sai dai idan har kaine kace kafasa aurena, sai dai kuma inajin tsoro, bansan mene zai kasance dani gaba ba, dan Allah kada soyayyar matarka ta ruɗeka, ka wulaƙantani, banda wani madogari sai ALLAH sai kuma kai" taƙare maganar cikin rawar murya, yayinda idanunta sukayi rau rau dasu, alamar zasu zubda ƙwalla.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, haɗe da sakin ɗan taƙaitaccen murmushi. "Har abada kada kitaɓa tunanin zan wulaƙantaki Zahrah, inasonki da gaske bada wasa ba, namiki alƙwari zan kamanta adalci a tsakaninku, bazan juya miki bayaba insha Allah!" Doctor Sadeeq ya faɗi haka cike da lallashi.
Tuni idanun Zahrah suncika da ƙwalla, amma idan ta tuno cewa bata da zaɓi sai taji gwamma kawai ta daure zuciyarta, haka ta ta ƙaddaran take.
"Kada kiyi kuka kinji My Princess, ina tare dake ako wani lokaci, zankuma share miki dukkanin hawayenki nan bada jimawa ba namiki alƙawari"
Saurin maida hawayenta tayi haɗe da ƙaƙalo murmushin dole ta'aza akan fuskarta, wan nan damuwarta ne ita kaɗai, baikamata ace tabari Dr Sadeeq yagane ba, lallai tun yanzu yakamata ta zama mai juriya.
"Baffa yana gida kuwa?" Dr. Sadeeq ya tambaya.
Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da kaɗa masa kai alamar "Eh"
Kai yajinjina haɗi da cewa "Yanaga duk jikinki yayi sanyi? banace kada kisa damuwa a ranki ba" cikin kulawa yayi maganar.
Cike da shagwaɓa Zahrah ta langwaɓar da kanta gefe haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, "Nibansa damuwa a raina ba" tace haka cikin sanyayewar jiki.
Wani irin kallo maiɗauke da ma'anoni masu yawa Dr.Sadeeq yashiga yi mata, ji yake tamkar yajawota jikinsa ya rungumeta tsam acikin ƙirjinsa, saboda ako da yaushe idan yana tare da'ita wani irin feeling yakeji a jikinsa.