nima inada wasu uzururrukan, yakamata kuna hakuri, amma wasu har baƙar magana su ke ƙoƙarin gayamin don kawai shekaran jiya nayi muku typing kaɗan, hmm wlhy kunbani mamaki, ni bana neman faɗa da kowa, saboda banɗauki duniya komai ba, shekaran jiya a matuƙar gajiye nake saboda naje school, amma haka na lallaɓa nayi muku typing, a she duk da haka wasunku basu godeba, haka sukaita ƙananan maganganu, wata har cewa take wai tagaji da wayon danake yi,koda yaushe sai nace na gaji, yes dole nagaji tun da dai ni ba engine bace, da za'ace bazan gaji ba, kuma ina da abubuwanyi. kuyi haƙuri my real fans na zage inata faɗa, wlhy raina ne yaɓaci wasu komai kamusu baka burgesu.
Nadawo gareku sisters masu cewa Zahrah tasoma basu haushi sbd abubuwan da takeyi, yaka mata ace kufahimceta, bawai inabin bayan tabane, amma yana da kyau ku yi imagine akan ya mace za taji idan har akai mata fƴaɗe?dole za taji matsanancin ciwo, acikin zuciyarta, kuma dole ne abun zai zama babban tabo wanda bazai taɓa gogewa acikin zuciyarta ba, saboda haka kuyi hakuri kuyi mata uzuri. ))
*18/November/2019**
*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written by*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Lovely Brother Khabier (My ƙwarnafi, da mita, lol 😄)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
*Kunayi inajin daɗi team Zaidu 🤣 amma fa iyakune kawai team ɗin nasa waƴanda basa ganin laifinsa, lol, nasu Zahrah kam ba'a magana suna cikin ƙunci😥, saura kuma Dr S.S.😂*
*Chapter 33 to 35*
(Kuyi haƙuri nayi mistake, ƙawar Zahrah sunanta Husnah ne ba Khausar ba, kamar yanda nasa a page ɗin baya, Husnah nakeson sawa, to bestyna saita tsayamin arai nasa sunanta,lol.)
Kuka suka shugayi wiwi babu mai lallashin ɗan uwansa, da ƙyar Husnah ta'iya tsagaita kukanta,haɗe da daidaita nutsuwarta, duk da cewa zuciyarta bata daina bugu ba, tamkar ƴar uwa ta jini haka ta ɗauki Zahrah, saboda haka duk wani abu daya faru da Zahrah tamkar da ita yafaru, domin kuwa abokin kuka shi'ake gayawa mutuwa, wannan abotar tasu tasamo asaline tun suna yara, haka kuma sun ƙulla abotansu cikin gaskia da yarda da juna,,
"Bazance miki kidaina kuka ba, Zahrah domin idan nace miki haka, banyi miki adalci ba, sai dai zan sake tunatarmiki cewa akwai Sarkin sarakuna, mai tausayi ga bayinsa, mai amsa addu'an bayinsa, mai basu, mai kuma hanasu, shi ishashshene akan dukkan komai, yanaji,kuma yana gani, sannan kuma shi ya wanzar da faruwar haka a gareki, tunkafun ya halicceki ya tsara, cewa hakan zai faru a kanki, kada kiyi jayayya Zahrah, domin kuwa babu wani bawa a duniya daya isa ruguza tsarin Allah, Allah baya bacci, yanasane da wanda sukayi cuta, dakuma wanda aka cuta, zaifi kyau ki miƙa al'amuranki garesa, haƙiƙa nasan cewa abun da Zaid yayi miki, abune mafi matsanancin ciwo acikin rayuwar ƳAMACE, amma kashe kai, ko kice a kasheki banaki bane Zahrah, rungumar ƙaddara ita tafi dacewa dake, haƙiƙa nasan cewa har gaban abada bazaki mantaba, amma inaso kiɗauki ƙaddaranki, kimiƙawa Allah lamuranki, da sannu zakiga sakayya, ke ba jahila bace, da iliminki na addini dana zamani, saboda haka inaso kiyi amfani da wannan ilimin naki wajen ɗaukar ƙaddaranki hanu bibbiyu, kada kice na faɗi haka ne don banasonki, wlhy inasonki ƙawata, inajinki tamkar jinin jikina, kawai dai hakan shine mafita !!" Husnah tayi maganar cikin tsananin tausayawa, yayinda ruwan hawaye suka gama wanke fuskarta...
A hankali Zahrah taɗago idanunta dasuyi jajur tamkar anwatsa musu garin barkono, ta kalli Husnah, sosai maganar Husnah yadaki zuciyarta, sai dai yazame mata dole shiga ƘUNCIN RAYUWA, da ace zata buɗewa mutane ƙirjinta suga, cikin zuciyarta, to tabbas da tayi hakan, domin tasan duk wanda yaga ciwon dake mamaye da zuciyarta, to tabbas dole ne zai koka mata, domin kuwa wani irin danƙareren ciwone yabaibaye zuciyarta, wanda batasa ran zata warke har gaban abada,
" Ashe babban kuskurene ɗaukar soyayya ka bawa wanda yafika? menene aibuna dan nafito a mace? me maza sukaɗauki mata ne? a she dan kana talaka shikenan kai bakomai bane? bakuma ka da ƴanci? ya ketamin haddina da ƙarfin tsiya, yanunamin ƙarfi da kuma fifiko, duk dan kawai ina mace, maiyasa ya tsalleke dukkan mata yazo kaina nida banda kowa sai Allah? nayi masa kuka, nayi masa magiya, na roƙesa amma ya toshe kunnuwansa, yacire duk wani imaninsa ya cutar da rayuwata, kigayamin miye laifina dan nafita cikin hayyacina ? ki faɗamin shin bancancanci in haɗiyi zuciya in mutu ba, f...ya...ɗ...e fa yayi mini Husnah!!!" Zahrah tafaɗi maganar cikin matsanancin kuka,
Duk yanda Husnah taso ta sake danne zuciyarta kasawa tayi, kawai sai ta sake sakin kuka haɗe da rungume Zahrah ƙam acikin jikinta,
Saida sukayi kuka sosai, kafun suka soma sakin ajiyar zuciya, take zuciyar Husnah tayi sanyi, amma banda ta Zahrah, domin babu wani sanyi daya ragewa zuciyar Zahrah.
A hankali Husnah tashiga shafa bayan Zahrah, wacce haryanzu sheshsheƙan kuka take,
" Ki tsaida kukanki Zahrah, kuka baya maganin komai, sai dai ya sanyamiki ciwon kai, addu'a ita kaɗai ce magani, nasanki Zahrah, inakuma da yaƙinin cewa baki kai kukanki ga Allah ba, kiji rani inazuwa " Husnah tafaɗa tana me miƙewa tsaye, kaitsaye ficewa tayi daga ɗakin, yayinda Zahrah tafaɗa kan katifa taci gaba da kukanta,,,
Mintuna kaɗan Husnah tashigo ɗakin hanunta riƙe da wasu magungunan da likita ya kawowa Zahrah, wanda takarɓo wajen Inna,,
Ledan da tashigo dashi ta jawo, haɗe da ƙarasowa wajen Zahrah, tamkar ƴa da uwa, haka Husnah ta jawo Zahrah jikinta, cike da tausayi haɗi da rauni tace " Kidaina kuka dan Allah Zahrah, kinga ko na tahomiki da abincin da kikafi so, Shinkafa da Kifi, Mom ce ta dafa " Husnah taƙare maganar tana mai buɗe wni kula, wanda ta ciro a cikin ledan da tazo dashi,
"Nasan bakici komaiba, kuma koda nace kici ma, cemin zakiyi kin ƙoshi, amma dan Allah kici ko kaɗanne zanji daɗi Zahrah, baki da kowa sai Allah, amma kada kimanta nidake tamkar gudan jini muke, damuwarki damuwata ce " Husnah tafaɗa tana mai zub da ƙwalla,
Kallonta Zahrah tashigayi, take kuma zuciyarta ta karye, sai kawai tafaɗa jikin Husnah, tashiga sauƙe ajiyar zuciya,,
Cike da lallami Husnah tashiga bawa Zahrah shinkafa da kifin da takawo, duk dacewa maɗaci yafi abincin daɗi a bakinta, amma hakanan ta daure takeci, badon komaiba sai don Husnah tacancanci tayi mata komai a rayuwarta, itace mace ta farko data fara bata kyakkyawan kulawa wanda tunda abunnan yafaru da ita babu wanda yabata, sai likita..
Duk da cewa bata wani ci mai yawa ba, amma zaiyi mata amfani, domin kuwa cikinta yajima ba'asa mai komai ba a cikinsa,,
Husnah nagama bata abincin, ta ɗauko musu Al'Qur'ani guda biyu, miƙawa Zahrah ɗaya taƴi, haɗe da buɗe mata fejin farko, cemata tayi su karanta a tare, duk da cewa da ƙyar muryarta yake fita amma sosai tayi ƙoƙari wajen karanta Al'Qur'ani,n.
Babu abun da yagagari Allah, Al'Qur'ani littafine mai cike da tarin haske, yana wanke zuciyar maikarantasa, yanasanya nutsuwa ga ma'abocin karantashi, take ƙuncin dake maƙare acikin zuciyar Zahrah yasoma ragewa, sunacikin karatun wani irin bacci ya yi gaba da'ita,, take ta kwanta a wajen tahau bacci,,
Murmushi kawai Husnah tayi haɗe da ɗaukar Al'Qur'ani'n, dake riƙe a hanun Zahrah ta aje gefe,
"Kayafe ma ta ya Allah! domin nasan tsananin tashin hankali da damuwa, su sukayi tasira a cikin zuciyarta, wajen mantar da'ita kai kukanta gareka!" Husnah tafaɗa tana mai kallon sama, gudun kada ta tashi Zahrah a bacci yasanya tasoma karatun nata ƙasa ƙasa...
((Ƙawaye: bawai nishaɗantarwa kaɗai shine amfanin muba, mu mata ne, kuma mu ƙawayen juna ne, yana da kyau, mu ƙaunaci junanmu, tsegumi, ƙyashi, baƙinciki, hassada, duk banamu bane, kamar yanda akace ciwon ƴa mace na ƴa mace ce, yana da kyau muɗauki hakan da matuƙar mahimmanci, du kanmu zamuso ace munsamu ƙawa kamar Husnah, to amma ta yaya zamu samu ƙawa kamar Husnah? dole ne mu tsarkake zuciyoyin mu, mudaina mawa junanmu ƙyashi da hassada, mudaina bawa junanmu mugayen shawara, mudaina zuga wasunmu sukai kansu zuwaga halaka, kada ki bata gurguwar shawara wanda zata cutar da'ita, wai don takawo kanta gareki domin kibata shawara, kada ki zugata akan cewa ta aika ɓarna, idan har bazaki faɗa mata alkhairi ba, to kada ki faɗa mata sharri, dukanmu mata ne, kuma dukanmu zuciyoyin mu suna da rauni, ta yarda dake, saboda kunyi shekara da shekaru kuna tare, hakan yasa ta ɗauki duk wani sirrinta ta zazzage miki, maiyasa tayi haka? saboda ta ɗaukeki ƴar'uwa, tunda ta sanar dake duk wani sirrinta, mai yakamata kiyi? saiki riƙe mata amana, ki tsare mata sirrinta, amma saiki kaje ki ka tona mata asiri a wajen mutanen duniya, idan kikayi haka kincancanci a ƙiraki da suna ƙawa? maiyasa muka ɓata kanmu ? mukaraba kan abotanmu ? saboda bama iya riƙe sirrin juna, kuma bamaso kowa ya ƙaru, ko ya samu buɗi, saimu kaɗai, yana da kyau muriƙe abotarmu da kyau, domin a matsayinmu na mata idan bamuyi abota da junan muba, da waye zamuyi? da maza? suda basusan yanda zasu magance mana matsalolinmuba, sirrin mace fa sai mace ƴar uwarta, please Sisters dan Allah muyi ƙoƙari wajen gyara zuciyoyinmu, domin mukasance abokai na ƙwarai, masu rufa asirin juna.))
Zaune yake a katafaren wajen shaƙatawa dake farfajiyar gidan, sanye yake da riga da wando na jamfa hadda hulansa, bakaɗan ba yayi kyau, kasancewarsa matashi mai jini a jika, sannan kuma dama akwai kyau ɗin tubarkalla, Wayarsace ƙirar iphone Xs Max riƙe a hanunsa yana faman latsawa da dukkan alamu abu mai mahimmanci yakeyi, ƙamshin turarenta ne yafara cika hancinsa, a hankali yaɗago kansa yakai dubansa zuwa gareta, sanye take da doguwarriga na atamfa wanda yakama jikinta sosai, yayinda ta saƙala wani ɗan ƙaramin vail a wuyanta, balaifi tayi kyau, tunda dama kyakkyawace.
cike da takun ɗaukar hankali taƙaraso wajen dayake zaune bakinta ɗauke da sallama,
Amsa mata sallaman yayi yana mai ɗauke idanunsa daga gareta, domin komai najikinta bayyane yake a fili.
Kujeran dake kusa dashi ta ja, ta zauna, cikin sauyawa murya amo tace, "Barka da zuwa Jarumi na"
Kai kawai yaɗaga mata alamar yaji, batare daya Kuma kallon taba, sake lanƙwasa murya tayi, takuma cewa "Yakamata mu'isa falon baƙi ai, sai nake ga kamar zaman mu anan baiyiba, kasan fa kai ɗin maidaraja ne baidace ace nabarka anan ba" taƙare maganar tana mai kaɗa idanunta, alamar yanga.
"Inaganin nan ɗin ma yayi ai basai munshiga ciki ba" Dr Sadeeq yafaɗa yana mai gyara zamansa,
Harara Zabba'u ta ɓallamasa ƙasa ƙasa batare daya gani ba, a zuciyarta kuwa cewa tayi "Inbanda Allah yaɗigamin soyayyarka a cikin zuciyata, da mai zai sanyani tsayawa, har ka wulaƙantani "
Ɗago da kansa yayi ya kalleta, cikin muryan dakewa yace "Ni zan wuce "
"Haba Yaya Sadeeq maiyasa kakemin hakane wai ? ko minti 30 fa bakayi da zuwa ba, amma kuma kace zaka tafi " taƙare maganar tana kwaɓe fuska tamkar wata ƙaramar yarinya, ko kaɗan kuma hakan baimata kyau ba, domin kuwa shekarunta ya wucewa abun da take ƙoƙarin yi, (wannan saimu nida bestyna jikar Hajiya sweet 19,lol)
Hanu yasanya a cikin aljihunsa yaciro kuɗi, aje mata yayi akan table ɗin dake gabansu, haɗe da tashi tsaye yasoma tafiya,, ganin haka yasa Zabba'u daɗa ɓata fuska, cike da ƙuncin zuciya, tarufa masa baya.
Mai gadi na buɗe masa gate yafice da motarsa, Zabba'u naganin fitansa, tasaki tsuka cike da takaici, wai ace kamar ita babbar yarinyar da maza suke mararin samunta, amma wai ita wani ke wulaƙantawa, kwashe kuɗin da ya aje mata akan table tayi haɗe da sakai tayi shigewarta gida...
Zahrah kuwa ba'ita tafarka daga wannan baccin da takeyiba, sai ƙarfe 6 na yamma, lokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, har zuwa lokacin kuma Khausar tananan bata tafi ba,,
Koda ta tashi a baccin, ji tayi gaba ɗaya tayi sakayau da'ita, a cikin kaso ɗari na ƙunci da damuwarta, babu kaso talatin, Allahu Akbar haƙiƙa karatun Al'Qur'ani warakace ga duk wani damuwar zuciya, harma da ta rayuwa.
"Bazan gajiya da faɗa miki ba Zahrah, yin imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, shi'ake so ga ko wani musulmin ƙwarai, kuma Allah baya ɗaurawa bawa abun da bazai iyaba, idan kika ƙara haƙuri ki kaɗau ƙaddaranki, to ina mai tabbatarmiki da zaki samu kyakkyawan sakamako awajen ALLAH, haƙiƙa nasan Zayd ya cutar da rayuwarki, amma Allah bazai barshi ba, da sannu Allah zai saka miki,kimin alƙawari bazaki na yawan kukaba, sannan bazakina yawan damuwa ba, duk da nasan hakan abune mawuyaci, amma idan kika daure zaki iya, sannan kuma kuka baya maganin damuwa, karatun Al'Qur'ani kaɗai zaki riƙa, insha Allahu damuwarki zata gushe, sannan kuma, kinyi kuskure Zahrah kinbari tarin damuwar da kika shiga, ya hanaki kai kukanki ga Allah, kin manta shine maikowa mai komai, dan Allah Zahrah kimin alƙawarin cewa zaki rage sanya kanki a damuwa, duk sanda wani tunani yake shirin zuwa miki, to ki gaggauta ɗaukan littafi mai tsarki, ki karanta hakan zai sanyamiki nutsuwa !!" Husnah tayi maganganunta cikin lumana dakuma son sawa ƴar uwarta ƙwarin guiwa,,
"Bansan mai zance miki ba Husnah, amma haƙiƙa kinwuce ƙawa ke ƴar uwace, kuma koda a cikin ƴan uwanma keɗin ta da bance, namiki alƙawari cewa zan maid komai nawa ga Allah, haƙiƙa rayuwata tana cikin ƙunci da kuma baƙin ciki, amma nasan babu a bunda yagagari Allah, kuma da sannu rayuwata zatayi haske, duk da banda tabbacin hakan !" Hawayene kawai ke tsiyaya daga idanun Zahrah, domin sosai takejin ciwon abun da Zayd yayi mata, yanzu tayarda cewa dama haka Allah yatsara mata, kuma zata rungumi Ƙaddaranta, har Allah yakawo ma ta mutuwarta,, amma dudduniya bata taɓa jin matsanancin tsana ga kowa ba bayan Zayd,,
Sosai Husnah tabawa Zahrah shawara masu amfani, wanda zasu taimaka wajen cireta a damuwa,, saida akayi sallan Isha kafun driver'n gidan su Husnah yazo ya ɗauketa...
Tiryan tiryan Baffa ya ɗebi ƙafa, har ofishin Alhaji Umar, gaba ɗaya abun da yafaru da Zahrah, Baffa ya kwashe ya faɗa masa, bakaɗan ba hankalin Alhaji Umar ya tashi, domin kuwa shi Zahrah tamkar ƴa yaɗauketa, saboda mahaifinta yayi masa taimako sosai, cikin faɗa da hargowa Alhaji Umar kecewa zai kai case ɗin koto, saurin dakatar dashi Baffa yayi, haɗe da yagyara zama, ban baki Baffa yashiga yi wa Alhaji Umar, akan cewa kada yakai case ɗin kotu, domin kuwa yaron yafi ƙarfinsu, sannan kuma idan har aka kai case ɗin kotu, tofa sunan Zahrah ne zai sake ɓaci, wanda basusan an ma ta fyaɗe bama zasu sani, sannan kuma zata rasa mijin aure, domin wasu zasuce ba fyaɗe aka mata ba, ita takai kanta, kuma dole su zasukwan a ciki, domin basu da kuɗi, a yanzu yanda rayuwar duniyar nan take, mai kuɗi shine sarki, kuma mai kuɗi shi kaɗaine mutum, haka wasu suka ɗauka, ko shari'a ake mai kuɗi shiyake nasara,, sosai jikin Alhaji Umar yayi sanyi, domin kuwa tabbas maganganun da Baffa yafaɗa haka yake, kuma yasan duk kuɗinsa bai isa yaja da wanda suka fisa ba, domin shi ɗan ƙaramin mai arziki ne akan wasu...
((Sau dayawa akan cutar damu ƴaƴan talakawa, amma bamu isa mu kai ƙara ba, mune da gaskia, amma mu'ake bawa rashin gaskia, maiyasa ? saboda mu bamu da kuɗi, wanda bashi da kuɗi kuma ba mutum bane a wajenku ko? anacin zarafin ƙananan yara dakuma ƴan mata, amma ba a iya ɗauka musu mataki, saboda kawai wanda suka aikata abun masu hanu da shuni ne, mukuma an maidamu ko'oho, Allah sarki Allah ka'iyar mana, kabimana haƙƙinmu gaduk wani wanda yazaluncemu Ameen.))
*20/November/2019*
*Voted, comment, and share please... Wattpad @Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymerhsardauna
*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*
*🌈Kainuwa Writers Association*
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}