x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 51 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 150001 words
  • 153000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 220

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da kallon wannan haɗaɗɗiyar surar tata zata iya zautar dashi.


Turare kawai ta shafa ajikinta, ko sleeping dress batasanya ba, yau kuma da towel takeson kwana, kashe musu wutan ɗakin tayi ta kunna musu na bacci, wanda bashida haske sosai.


A maimakon tanufi gefensa ta kwanta, sai ji yayi ta haye kansa.


"Wayyo mama lutiya zata karyani!" yafaɗi haka aɗan shagwaɓe.
Sake sakar masa duka nauyinta tayi akansa, haɗe da cusa kanta cikin wuyansa.


"Kai nauyinka baisa na karye ba sai nine zan karyaka, ko kamanta kafini nauyi" taƙare maganar tana me manna masa wani irin hot kiss akan wuyansa.


Lumshe idanunsa yayi sosai yaji kiss ɗinnata ya ratsa shi.


"Wai yaushe kika zama haka ne princess?" yatambayeta, don harga Allah kwana biyun nan yana mamakinta.


Cikin rashin fahimtar maganan nasa tace "Bangane ba"


"Naga ne kindaina jin kunyana, sannan kuma nima da nake da kunyan nema kike ki lalatani ki maidani marar kunya"


Cizo takaimasa akan ƙirjinsa, wanda yasanya sa sakin wata ƴar ƙara.


Yana dariya yace
"To ƙarya nayi ai gaskiya nafaɗa, yanzu bakyajin kunyana ko kaɗan, har kaya kike cirewa a gabana..."


Wani cizon takuma kaimasa batare da ta bari yaƙarisa abunda yakeson faɗa ba, da sauri yatureta takoma ƙasansa shikuma yazama yana samanta, yayi mata rumfa da kirjinsa, duka hannayenta yakama yariƙe acikin nasa.


Cikin dariya ta soma ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikinsa don talura cizon da tamai yakeson rama wa.


"Dan Allah kayi haƙuri bazan ƙaraɓa!" tafaɗi haka aɗan tsorace dan ta lura dagaske cizonta zaiyi.


"Ae babu maganar haƙuri yarinya, aƙirji kika cijeni, nima kuma dan haka aƙirjinki zan cijeki" yafaɗi haka yana me warware towel ɗin dake jikinta.


Cikin dariyan data kasa hanashi fitowa tashiga yi masa magiya amma yace sam shi sai ya rama.


Yana ɗaura bakinsa akan ƙirjinta, tayi shiru lokaci guda ta shiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, harwani lumshe idanunta take tsabar daɗin abun da yakeyi mata da takeji, shikuwa dagangan yayi mata haka so yake ya tsokalota sai yayi mata wayo yayi baccinsa, hanunta tasanya ta ɗago kansa, wani irin kallon tayi masa wanda ya rikirkitasa, bakinsu ta haɗe waje ɗaya, atare suka soma sucking lips ɗin juna, shida yake shirin mata wayo sai gashi ya susuce alokaci ɗaya, har yazo yafita ɓuƙata..... Bargo yaja ya rufe musu duka jikinsu, yana kwance akanta bacci me daɗi ya ɗaukesu.....


*****


*_ZAID_*


Tunda aka sallamosu daga asibiti baice da kowa ƙala ba, haushin kowa yakeji, tuƙuƙin baƙin ciki zuciyarsa keyi masa, ji yake yatsani kowa, bayamaso wani yashigo cikin lamarinsa..


Zaune yake a cikin falonsa, dagashi sai 3 guater jeans ko riga baidashi duk da kuwa irin sanyin da ake busawa a gari amma shi haka yake zaune a tuɓe, bawai kuma don bayajin sanyinba taurin kai dana zuciya ne kawai irin nasa ya hanasa suturta jikinsa.


Ƙafansa nakan rug yayinda kansa ke kalllon sama ya lumshe duka idanunsa, sake muskutawa yayi akaro na barkatai, haɗe kuma da ƙara ƙanƙame idanunsa da suke a lumshe, waishi adole so yake yayakice tunanin Zahrah acikin zuciyarsa, amma duk yanda yaso cire tunanin nata acikin ransa ya kasa, hanu yasa ya ɗan bugi kansa da ƙarfi, dai dai lokacin Afrah tafito daga cikin ɗaki daga ita sai wata ƴar ƙaramar riga dake sanye ajikinta, ko guiwarta rigan bata wuce ba.


Wani irin ƙamshin turaren dayaji acikin hancinsa ne yasanya sa buɗe idanunsa, ya watsa su akanta, kallonta yashigayi daga sama har ƙasa. "gatanan dai kamar wata ƴar kaza amma shegiya sai fitinan tsiya" yafaɗi haka acikin zuciyarsa, saboda ya lura kanta yana rawa, nema take ta shigarmai rayuwa taƙarfin tsiya, kuma zaiyi maganinta ne.


Afrah kuwa zuciyartane tashiga dukan uku uku, tsoronsa ne yasake shiganta bama kamar yanda taga idanunsa sun juye sunyi jajur dasu, harta juya zata koma ɗaki, saikuma ta tuno da shawarar da ƙawarta Asma ta bata, Asma tace mata " Zaid ɗan duniya ne yanason mata sosai, saboda haka tayi duk yanda zatayi ta shawo kansa ta hanyar nuna masa surarta a fili, idan ta nuna masa bata da kunya zasu dai dai ta" tunowa da waƴannan kalaman na Asma yasa Afra taji tasamu ƙwarin guiwa.. Sanja takunta tayi zuwa wani salo da ban, direct wajen dayake kishingiɗe ta nufa tana me motsa kowani gaɓa dake jikinta.


Bai taɓa yin zato ba saiji yayi Afra tafaɗo cikin jikinsa kamar wacce aka jefo, baikai ga buɗe idanunsa ba yaji ta saki wani irin munafukin ƙara..


"Wayyo Allah ƙafa ta honey kataimakeni na karya ƙafa ta" abun da Afrah ke faɗa kenan cikin iyayi.


Wani irin kallon takaici Zaid keyi mata, waishi zata gwadawa bariki, tafaɗo kansa da gangan sannan kuma tana yi masa ihun banza wai yataimaketa.


Da sauri yasake maida kallonsa gareta alokacin da zuciyarsa ta ƙitsa masa wani abu akanta.


"Tabbas hakanne ma, sai yanzu yasake lura da ita, amma ba ya gwadata ya gani" yafaɗi haka acikin zuciyarsa..


Da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yaƙira sunanta "Afrah"


Dasauri Afrah dake yashe aƙasa tana kukan ƙarya ta ɗago kanta tana kallonsa jin da tayi yaƙira sunanta. "Kodai Target ɗina yafara aiki ne?" ta tambayi kanta .


"Ba ƙiranki nake ba da bazaki amsa minba!" yafaɗa murya aɗan kausashe.


"Kayi haƙuri honey ƙafa ta ce kemin zafi shiyasa" tafaɗi haka cikin yanayi na shagwaɓa tana wani yayyarfe hannu, ita adole so take ya faɗa cikin tarkonta.


Cike da tsananin takaicin ƙiransa da sunan honey da takeyi yasanyasa rumtse idanunsa da ƙarfi, ji yake kamar yaje ya shaƙeta bazai saketaba harsai yaga bata numfashi, amma akwai abun da yakeson ganowa a tattare da ita dolensa saiya daure.


"Zo muga me yasamu ƙafartaki"


Jiki na rawa Afrah ta matso garesa dama haka takeso yace, tana matuƙar so taganta akusa dashi, haɗa jiki dashi kuma shine burinta batun yau ba.


Hanu yasa ya kama ƙafarta ta, a hankali yashiga shafawa cike da wani irin salo, wayyo Allah Afrah dama haka takeso, ita kanta batasan sanda ta lumshe idanunta ba, wani irin daɗi takeji acikin jikinta, "Gaskiya shawarar Asma tayi aiki" tafaɗi haka acikin zuciyarta, cigaba yayi da shafa ƙafannata ahankali harzuwa wajen cinyoyinta, tuni ta narkemasa ajiki taƙara kusanto da kanta garesa, hanu tasanya akan faffaɗan ƙirjinsa tashiga shafawa ahankali, duk iskanci irin na Zaid saida ya tsaya yana kallonta, tabbas yanzu ya gano abun dayakeson ganowa atattare da ita, wani irin baƙinciki da ɓacin raine suka tokare masa maƙoshinsa.


"Hakan da Afrah keyi masa alamace dake nuna ita babaƙuwa bace a harkan tasan namiji kenan kome?" tambayar da yake tayiwa kansa kenan, shiba ƙaramin ɗan iska bane, yanda Afrah keyi masa alama ne dake nuna cewa tasaba irin haka da wasu mazan. "Kenan ita ƴar iska ce?" still yakuma tambayar kansa. Hanunsa yasanya ya damƙi gashinta haɗe da miƙar da ita tsaye, da fari ta ɗan tsorita amma ganin irin kallon dayakeyi mata yasa taɗanji sanyi acikin ranta, ganin sunnufi hanyar ɗakinsa yasa ta shiga sakin murmushi, daɗi taƙeji yau Allah zai cika mata burinta..


Suna shiga cikin ɗakin yasanya hanunsa da ƙarfi ya yaga ƴar fingilan rigar dake jikinta, take komai nata ya bayyana, hankaɗata yayi kan gado haɗe da soma yunƙurin zare belt ɗin dake jikin wandonsa,, idanu Afrah ta zaro waje amatuƙar tsorace, bata taɓa tsammanin haka daga garesaba ta ɗauka kasheta zaiyi da soyayya amma meyake shirin yi matane haka "Dukanta zaiyi ne ko kuma turmusheta zaiyi batare dayatsaya sunɗanyin romancing juna ba?" waƴannan tambayoyin sune suka cika zuciyarta fal...


(Me Zaid yakeyi hakane🤔 hahhhh da'alama dai yau amarci za'aci agidan Baba Zaid, team Zaid karkuyi nisa saboda nan gaba kaɗan Zaid zai buƙaci taimakonku, yayinda komai ya wakana tsakaninsa da amarya, inaga dole saikun shigo cikin lamarin😂)



*(Thank you my wattpadfans💋 Comment da vote ɗinku suna ƙaramin ƙarfin guiwa sosai, SON SO nake muku)*


*Vote and Comment please😘*


*6/February/2020*




*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI!!*


*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motive the mind of readers}_


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*CHAPTER 107*


Tana ganin yagama zare belt ɗin jikinshi, tasoma ƙyaf ƙyaf ta idanu, kamar wacce aka kamata tana sata, tsoronsa ne ƙarara, ya bayyana akan fuskarta, ganin sa a haka tun farko, ya isa ruɗata, amma kuma dayake bariki ne a gabanta, ya sanya bata fuskanci hakan ba, sai yanzune taga, gaba ɗaya yacika mata idanu.


Cike da tsantsar rashin mutumci irin nasa, yasanya hanunsa ya jawo ƙafarta, zama yayi akan gadon, haɗe da sanya hanunsa akan fuskarta, ya matse mata baki, idanunsa yaɗaura akan ƙirjinta, wani irin murmushi yasake, haɗe da cije laɓɓansa, wai wannan tatsitsiyar yarinyarne, takeson ɗaukar hankalinsa, yaga waƴanda suka fita komai, bai kuma ji wani abu akan su ba, balle kuma ita ƙaramar alhaki, yanaji ajikinsa cewa. "A yanzu ba ayi wata mace wacce zata ɗau hankalinsa sama da Zahrah ba"


Hanunsa yakai kan wuyanta, yashiga shafawa a hankali, tsuru Afrah tayi tana kalllonsa, karo na farko a rayuwarta, da taji wani irin mugun fargaba ya daki zuciyarta, akan abun da ta aikata, "Me zata ce masa yanzu idan har yanemi haƙƙinsa awajenta?" take idanunta suka kawo ruwa taɗago ta kallesa.


Ko kallonta baiyi ba, ya ci gaba da shafa wuyanta, lumshe idanunta tayi, a zahirin gaskiya tana amsar saƙonsa, amma kuma acikin zuciyarta, tsoro ne yayi tasiri.


Ɗayan hanunsa yasanya ya yakice duk wani abu na sutura dayayi saura ajikinta.


Kamar wata mutum mutumi haka Afrah ta tsaya tana kallonsa.
"Tashiga ukunta idan wannan ingarman namijin ya haiƙe mata, batare da ya tsaya yayi romancing ɗinta ba"
ta faɗi haka acikin zuciyarta, bata ida tunanin nata ba, taga yayi off na wutan ɗakin..


Kwanciya yayi akanta, haɗe da sake mata gaba ɗaya nauyinsa, da ƙyar take iya fidda numfashi, sosai yayi mata nauyi, idan ba mugunta bama, taya zai kwanta akanta haka, aiko katifa ce saita lotse balle kuma ita.


Cikin zafi zafi yashiga kissing lips ɗinta. Yi yake kamar zai cijeta, dagani kai kasan muguntane ke cinsa, baƙaramin zafi kuwa hakan keyi mata ba, gaba ɗaya ya taune mata baki, lokacin daya ɗaura hanunsa akan breast ɗinta kuwa, saida tasaki kukan wahala, komai bayayi mata shi cikin nutsuwa, duk wani abu da ƙarfi yake yi mata, abu yake kamar me huce haushi.


Ganin da yayi zata cika masa kunne da kuka ne, yasanyasa sanya hanunsa ya matse mata baki. Yunƙurin ƙwace kanta takeyi amma ina bazata iya ba riƙon Zaid ba wasa ba.


*****


Wani juyawa kansa keyi masa lokaci ɗaya ya firgice, idanunsa ne suka kaɗa sukayi jajur dasu, yayinda jikinsa ke ɓari kamar wani mazari, iya ƙololuwar ɓacin rai a yau Zaid yashigesa, da ƙyar ya iya laluɓawa, ya sauƙa akan gadon, jefa ƙafafunsa kawai yake batare daya koda kalli gabansa bane, yana shiga cikin bathroom ya banko ƙofar da ƙarfin gaske.


Jikin Afrah ne ya ɗauki tsuma, take ta fashe da wani irin kuka me taɓa zuciya.


"Wayyo Allah na, nashiga uku, me zancewa Zaid? kaicona, nakasa haƙuri, gashi yanzu na jawa kaina" abun da Afrah ke faɗa kenan acikin zuciyarta, gaba ɗaya tsoron ma tashi daga kan gadon take, da ƙyar ta iya jan bargo ta rufe jikinta dashi.


Ruwa ne ke dukan kansa, yana tsaye agaban shower kamar wani statue, iyaka ƙololuwar ɓacin rai, yau ya shigesa, baitaɓa tunanin zaiji ciwo acikin zuciyarsa, wai dan yasamu Afrah ba a cikakkiyar virgin ba, sai gashi abun ya juye tunaninsa.


"Ashe dama haka maza sukeji, idan basu samu matarsu a cikakkiyar budurwa ba?" yatambayi kansa.


"ZAHRAH"


itace wacce tafara faɗo masa acikin ransa, take fyaɗen da yayi mata yashiga dawowa cikin kansa filla filla, tamkar alokacin komai ke wakana haka yaji acikin jikinsa, da sauri yasanya hanu ya kama kansa, haɗe da kurma wani uban ihu, yama manta da cewa acikin toilet yake.


Wani irin nadama ne me girma ya ruskesa acikin zuciyarsa, sai yanzu ya tabbatar da cewa bai kyautawa Zahrah ba, yaku ma cutar da ita cutarwa me girma, ya ruguza mata alfaharinta.


"Meyasa yayiwa Zahrah haka? me yasa yarabata da budurcinta? wani irin cutarwa ne yayiwa Zahrah haka?" yatambayi kansa cikin tsananin tsana da ƙyamar kansa.


"I hurt you Zahrah, why do i did this to you? I'am stupid, i dont have sense, meyasa zan aikata haka? kaicona dana cutar da rayuwarki, na gusar miki da farincikin ki, na hanaki mallakawa mijinki budurcinki, na ƙwace budurcinki taƙarfin tsiya, forgive me, i hate my self, because of what i did to you, natsani duk wata rayuwar duniyar nan, rayuwa batamin daɗi Zahrah!!" cikin wani irin murya me haɗe da sautin kuka Zaid ke faɗan haka.


Haƙiƙa yau baida abun da zaice, yasan Allah ba azzalumin kowa bane, sai wanda ya zalunci kansa, gashinan shi ya zalunci kansa, kuma yagani, gashi yanzu Allah ya haɗashi da wata ballagazar mace, wacce ta raba budurcinta ga mutanen titi, yanzu ga abun da Zina ta haifar masa, bayajin son Afrah ko ɗigo acikin zuciyarsa, amma kuma yaji matsanancin ciwon samunta a haka da yayi, to idan dai shi yaji ciwon samunta ahaka, me mijin Zahrah kuma zaice? shida yake so da kuma ƙaunarta.


Jingina kansa yayi da jikin bangon toilet ɗin, yayinda ruwan dake fitowa acikin shower ke dukan bayansa. Rumtse jajayen idanunsa yayi, haɗe da sanya haƙoransa ya danne laɓɓansa, jiyake kamar yata gwara kansa ajikin bango, har sai kan ya rabe gida biyu, koda zaiji salama, acikin zuciyarsa, hanunsa na dafe da saitin zuciyarsa, dake yi masa zafi, yajima a tsaye ruwa na dukansa, har sai da jikinsa yasoma karkarwa kafun ya kashe shower'n....


Buɗe ƙofarsa, yayi dai dai da bugawan zuciyar Afrah, take jikinta yacigaba da karkarwa kamar anjona shocking.


Ko kallon inda take baiyi ba, direct gaban drawer ɗinsa ya nufa, wata farar T-shirt ya ɗauka ya sanya ajikinsa.


Ganin baice da ita komai ba, yasanya ta daɗa firgicewa, batasan me ze mataba nan gaba, cikin muryarta me ɗauke da tarin tsoro, haɗi da fargaba tace.


"Dan Allah kayi haƙur......"


"Get out!!"


yafaɗi haka batare daya bari ta ƙarasa maganar dake cikin bakinta ba.


Cikin kuka takuma cewa


"Dan Allah kayi...."


"I say get out!!!"


yafaɗi haka atsananin tsawace, har sai da Afrah taji ƴaƴan cikinta sun kaɗa.


Gaba ɗaya ta ruɗe ta firgice, yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur dasu, shine abun da yafi komai ɗaga mata hankali, da gudu ta fice daga cikin ɗakin, ko kayanta bata tsaya ɗauka ba, sai blanket ɗin da tayi amfani dashi wajen rufe jikinta.


Kwalbar turaren dake riƙe a hanunsa ya yi wurgi dashi, zuwa wajen wani ƙaton mirror wanda ke kafe ajikin bango, take mirror'n ya fashe, haɗe da tarwatsewa a ƙasan tiles.


Wani irin huci yake fitarwa ta bakinsa, yayinda yasanya duka hannayensa ya kama ƙugunsa, jiyake gaba ɗaya duniyar na juya masa.
"Me ake da irin wannan rayuwa, me ɗauke da takaicin?" yatambayi kansa.


Idanunsa ya sauƙe akan fridge ɗin dake ɗakin, wanda yake a cike da kwalbar wine ɗinsa, a irin wannan halin dayake ciki, wine ce kaɗai zata iya bashi nutsuwa, duk da yasan ba lallaine ta iya ciresa acikin ƙuncin dayake ciki ba, amma tabbas zata iya rage masa damuwa, sai dai kuma bayajin aduniya zai iya ƙara aikata wani abu na saɓon Ubangijinsa, ko a iya nan Allah yaɗauki rayuwarsa, haƙiƙa ya jarabtu, soyayyar Zahrah kaɗai da Allah, yasanya masa, yazamemasa babban jarabawa acikin rayuwarsa.


Zama yayi a bakin gado, haɗe da bin blanket ɗin dake shimfuɗe akan gadon, da kallon takaici, bakomai ne yafaɗo masa arai ba, kamar randa yayiwa Zahrah fyaɗe, haka gaba ɗaya tsakiyar gadon ya ɓaci da jininta, yasamu Zahrah a cikakkiyar budurwa.


"Yayi gaggawa? me yasa bai bari ya amshi budurcinta ta hanyar aure ba?" wasu siraran hawayene suka fito daga cikin idanunsa, suka sauƙa akan ƙuncinsa, sakamakon tunowa da yanda ya farke Zahrah da yayi.


Ahankali ya taka ƙafarsa ya ƙarasa gaban wani tangamemen hotonta, dake liƙe ajikin bangon ɗakin.


Zama yayi agaban hoton haɗe da cewa.
"Kiyafemin Zahrah, a yanzu nayi nadama marar amfani, ni dakaina namiki fyaɗe, nidakaina nasa aka je har ƙofar gidanku aka ya da ke, meye amfanina Zahrah? me yasa nazamo mugu maƙuntaci agareki? nagodewa Allah dayasa baki aureni ba, domin ban cancanci zama miji a gareki ba, ni ban dace dake ba Zahrah, to tayama zan dace dake? ninefa wanda yayi miki fyaɗe, nine azzalumin dana rufe idanuna, na aikata ba dai dai ba akan ki, to taya zaki yarda ki aureni, a'a ko kin yardama ni bazan yarda ba, domin ni dake bamu dace ba, bazan yarda nasake cutar dake akaro na biyu ba, inasonki Zahrah so ba irin wanda kika sani ba, inamiki son da aduniya banayiwa
End Ads