Zaid ne saboda dama tuncan yana matuƙar kasheta aduk sanda tagansa sai taji inama dazai zamo nata, sannan kuma gayen akwai kuɗi uwa uba aji, duk da cewa ita ɗinma babanta me kuɗi ne amma baikai na baban Zaid dashi kansa Zaid ɗin ba, lokacin da babanta yazo mata da maganan auren Zaid, daɗine yakusa kasheta ganin irin damar da Allah yabata, ashe bata saniba gidan mutuwa takawo kanta, ita da har jinkanta tasomayi, har ɗagawa takeyiwa ƙawayenta, ita adole ta auri namijin duniya, batasan cewa wahala zata ruska ba, ta ɗauka cewa holewa zatayi, harta fara tunanin ƙasashen da zata sasa yakaita, sai gashi haɗuwarsu ta farko ma da lafiyayyen mari ya tarbeta...
Zaid kuwa yana shiga cikin ɗakinsa yafaɗa kan gado haɗe da lumshe idanunsa, kansa ne yake matuƙar sara mae, tun jiya yakejin ciwon kan, amma yau abun ya tsananta sosai, wata tsuka yaja me sauti, haɗe da sake gyara kwanciyarsa, shi wannan auren ma da aka laƙaba masa kaɗai ya isa ƙara masa ciwon kai, shiba yaro ba, shiba bagidaje ba amma ankama anyi masa auren dole...
******
Tsaye take agaban dinning area, ta kafesa da manya manyan idanunta, yayinda shikuwa baimasan tana kallonsa ba, hankalinsa gaba ɗaya yana ga agogon dayake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa.. Bakomai yasa take kallonsa ba, face kyawun da taga yayi mata, shadda ne milk colour ajikinsa ɗinkin riga da wando, rigar ta tsaya iyaka guiwarsa, yayi kyau sosai yasha hularsa light brown wanda taƙarawa kwalliyartasa kyau.. Yana ɗago kansa suka haɗa idanu, da sauri ta kawar da idanunta daga kansa, haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa.
Murmushi yayi haɗe da takowa yaƙaraso inda take, hanu yasanya ya rungumota ta baya.
"Namiki kyau ne haka kiketa kallo na?" yatambayeta yana me shaƙan daddɗan ƙamshin jikinta.
Ɓata fuska tayi haɗe da cewa
"Namiji kuma dama yana kyau ne idan yayi kwalliya?"
Dariya maganar ta ta ta basa, juyo da ita yayi yazamana suna fuskantar juna.
"Eh mana bakisan maza sun mafi mata kyau ba?" ya faɗi haka yana me ƙarewa fuskarta kallo.
Idanunta ta waro haɗe da cewa "Maza sunfi mata kyau? cab aikuwa nidai baka fini kyau ba"
Dariya yayi haɗe da ɗan jan hancinta.
"Nafiki kyau sosai ma, nifa banasa jan baki, bana shafa powder, bana sa kwalli, bana kumayin jagira, haka kuma bana wani shafa mai wanda zai sa fatata tayi kyau, komai nawa daga Allah ne, ku kuma mata kullum cikin shafawa da gogawa kuke, kinga kenan dagaske munfiku kyau" yafaɗi maganar yana me ɗan ƙara fito da idnunsa waje.
Duk da tana cikin fushi, amma sai da tayi dariya.
"Kafaɗi komai ma, amma nidai bazan yarda cewa wai kafini kyau ba"
tafaɗi haka tana me ƙoƙarin zame jikinta daga cikin nasa.
Sake riƙeta yayi gam haɗe da cewa
"Dagaske namiki kyau? naga har wani kishi na kike"
Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da shagwaɓe fuskarta.
"Idan nayi kyau kaima baka barina nafita, to me yasa kai kakeson yin kyau ako da yaushe? kana tunanin bazanji haushi bane idan wata ta kalleka!" kafun taƙare maganar ma tuni idanunta sun soma kawo ruwa.
"Eh kumafa hakane, harma kintunamin, akwai wata kuwa a asibitin mu, kullum saitace namata kyau, sannan kuma saitace wai ina matuƙar burgeta, gaskiya nima kuma tana burgeni dan a ƴan kwanakin nan harma na fara tunaninta, to mezakice akanta?" yaƙare maganar yana me ɗaga mata giransa ɗaya.
Baki kawai tasake tana kallonsa yayinda wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya. Da ƙarfi ta soma turesa tanason ƙwace jikinta daga nasa.
Ganin haka yasanya yasake riƙeta da kyau haɗe da cewa
"Mekikeyi haka?"
"Kafi kowa sanin abunda nakeyi, inatunanin tsayuwan da kakeyi anan kana ɓata lokacin kane, domin wacce kake muradi tanacan tana jiranka, koba don itane kayi kwalliyar ba? ai bana tunanin ni inada wani amfani a wajenka, ka sakeni kaje tayaba kwalliyar taka banaso na ɓata bata gani ba."
Dagajin yanda take maganar kasan kishine tsantsa kecinta, domin kuwa har hawaye sun gangaro daga cikin idanunta..
Dariya sosai yashiga yi batare daya sake ta ba.
"Kasakeni nace, ai nasan baka buƙata ta!" tafaɗi haka tana me yunƙurin ƙwace hanunta dake cikin nasa.
Da ƙyar ya iya tsagaita dariyan nasa, yashiga dubanta da kyau, yasani dama da sannu zuciyar Zahrah zata nutsa acikin ƙaunarsa sosai, gashi kuma yafara ganin alama tunda har kishinsa ya bayyana acikin idanunta..
Fuskarta yatallafo da tafukan hanunsa haɗe da sanya bakinsa yashiga lashe hawayen dake fitowa daga cikin idanunta.
"Bazan iya jure ganin matata tana kuka ba, ki kwantar da hankalinki kinji me daɗi na, babu wata mace da ta isa ƙwace miki doctor ɗinki, ketawace ni ma kuma naki ne, babu wata kuma danake tunani bayanke kiyarda dani!!" yafaɗi maganar cikin lallausan murya yana me ƙara riƙe fuskarta acikin tafukan hanunsa.
Ajiyar zuciya ta sauƙe wanda harsaida ya bayyana afili, har cikin ranta taji daɗin maganganunsa, amma kuma afili bata nuna hakan ba, ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikinsa tacigaba dayi.
"Nine bakyaso ko? shikenan tunda bakyaso nariƙeki" yafaɗi haka yana me sake ta yanufi hanyar fita daga cikin falon. Da sauri ta je ta rungumesa ta baya, wani murmushi yayi haɗe da juyowa gareta yazamana suna fuskantar juna.
"Dan Allah kada ka ƙaramin irin wannan wasan, gashi duk kasa ma naji natsani komai!" tafaɗi haka a shagwaɓe.
Murmushi yayi mata haɗe da sanya hanunsa yaɗanja kumatunta.
"Bazan sakeba, kiyi haƙuri kinji me daɗi na!"
Da sauri ta cusa kanta acikin ƙirjinsa haɗe da sanya hanunta ta mintsineshi acikinsa. Da ɗan ƙarfi yace "Ahhhshhhh!"
Dariya tayi masa haɗe da yi masa gwalo ta wuce zuwa dinning domin dama abinci take haɗawa.
Biyota yayi kan dinning table ɗin suka shirya abincin atare, acikin plate ɗaya sukaci abinci, gaba ɗaya yanzu doctor yagama shagwaɓata abinci ma shiyake bata abaki, har sai ta ƙoshi, tana ajiye cup ɗin ruwan dake hanunta, ta ɗan saci kallonsa, ta lura tun ɗazu yaketa kallonta.
"Kaima nayi maka kyaun ne, kaketa kallona haka?" ta tambayeshi.
Murmushi yayi mata haɗe da cewa
"Ae ni dama kullum kinamin kyau, ke mai kyauce ai ako da yaushe, amma kuma..." baiƙarisa maganar dake cikin bakin nasa ba yayi shiru.
"Amma kuma me?" ta tambayeshi da sauri domin atunaninta ta zaci zaice amma bata masa kyau sosai ne.
Maganganunsa kunya suka bata da sauri ta sanya hanunta ta rufe fuskarta, jawota jikinsa yayi haɗe da sanya bakinsa adai dai saitin kunnenta cikin muryar raɗa yace
"Bazan iya jurewa ba Zahrah, inaso akullum kina bani kanki sau ba adadi, inason kasancewa tare dake ako wani lokaci" bakinta yashafo da hanunsa haɗe da lumshe idanunsa. "Nayi missing waƴannan lips ɗin amma yau zanyi musu sucking na musamman har ma...." bata jirayi jin ƙarshen zancen nasa ba ta ruga da gudu zuwa cikin ɗaki, bazata iya cigaba da sauraran waƴannan manya manyan kalaman nasa ba. Murmushi kawai yayi haɗe da miƙewa yafice daga cikin falon, dama sabiti zaije.
Tanajin fitar motarsa acikin gidan ta sauƙe ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunta, kwanciyarta ta gyara, tana me tuno kalamansa, itakanta tana tsananin son taji ta ajikinsa, musamman idan fatarsu ta haɗe waje guda hakan na haifarmata da wani irin yanayi me daɗin gaske, kallonta ta mayar ga agogon bangon dake kafe acikin ɗakin. Ƙarfe 11 na rana yau take da lecture saboda haka tana da ɗan sauran lokaci, domin yanzu ƙarfe 10 ma batayi ba, wani English Novel mesuna ( Just A Friend) tajawo haɗe da buɗe chapter'n da take ta soma karantawa, agurin wata ƴar class ɗinsu ta karɓo shi.
****
Ƙarfe 4 na yamma dai dai suka fito daga cikin lecture ɗinsu wanda shine na ƙarshe a wannan ranan, direct library ta nufa saboda akwai wani littafi da takeson dubawa, kasancewar akwai assigment ɗin da aka basu, idan ta samu littafin kuma sosai zai taimaka mata wajen yin assigment ɗin cikin sauƙi. Gaba ɗaya hankalinta naga littafin da take dubawa, sam bata damu da mutanen dake wajenba kasancewar kowa karatu kawai yakeyi. Tana zaro littafin daga ma'ajinsa ta saki murmushi, juyawa tayi daniyar tafiya idanunta suka sauƙa akan shi, waro manyan idanunta waje tayi haɗe da sakin littafin yafaɗi ƙasa. Jikinta ne yaɗauki rawa da sauri ta tsugunna ta ɗauki littafin haɗe da nufar hanyar waje, tsabar sauri har ƙafafunta harɗewa suke, batayi auneba saiji tayi ta buge mutum, da sauri taɗago don ganin waye ta buge, shiɗinne dai tsaye a gabanta yana me kallonta da jajayen idanunsa, da sauri taja baya, haryanzu jikinta rawa yake kamar wacce taga mutuwarta.
"ZAHRAH!"
yaƙira sunanta cikin wata irin murya me matuƙar rauni.
Kusan mintuna uku takasa amsa masa da ƙyar ta iya motsa bakinta,
"I..na..da au..re"
shine kalaman da suka fito daga cikin bakinta awawware batare kuma da ta shiryawa fitowar kalmomin ba.
Rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hanunsa. Cikin murya me ɗaci haɗe da bushewar maƙoshi yace
"Nasani!"
Bazata iya jurewa ganinsa ba da sauri ta bi ta wata hanyar ta wuce da gudu, ko takan littafinta daya kuma faɗuwa batayi ba.
Bayanta yabi da kallo haɗe da tsugunnawa yaɗauki littafin, juyawa shima yayi yafice daga cikin library ɗin. Sai dai ko daya fito, ko ƙyallinta bai gani ba.
Zahrah kuwa tana fitowa daga cikin library ɗin direct wani ɗan corridor wanda mutane basu cika yawan bi ba tanufa, kaitsaye ta tsinci kanta awani fili wanda bakowa acikinsa sai shuke shuke, zama tayi akan wani benci dake wajen, haɗe da fashewa da kuka, tashiga ukunta itakam, wannan wace irin jaraba ne, meyasa Zaid bazai barta ta huta bane, jitayi lokaci ɗaya ƙirjinta yayi mata nauyi kamar anɗaura mata gungumen dutse, wayarta dake ringing ta kalla, Dr.Sadeeq ne ke ƙira amma bazata iya ɗagawa ba, ahalin da take ciki yanzu ma batasan me zata ce masaba idan ta ɗaga. Da ƙyar ta'iya tashi tabi ta ƙofar baya tafice daga cikin makarantar gaba ɗaya, tana fita ta tare me taxi haɗe da gaya masa inda zai kaita, ko ciniki basuyi ba ta faɗa cikin motar haɗe da ce masa yaja suje.
Yana kawota ƙofar gida ta basa kuɗinsa haɗe da ficewa acikin motar ta kutsa kanta cikin gidanta.
Bata damu da duhun dake cikin ɗakin ba haka ta faɗa kan gado ko mayafin dake jikinta bata cire ba.. Zazzaɓine me zafin gaske ya rufeta alokaci guda..
Zaid kuwa yana fita daga cikin library ɗin direct wajen da motarsa ke fake ya nufa, buɗe murfin motar yayi, ya shiga ya zauna, kifa kansa yayi akan steering motar yana mejin zafi da raɗaɗi na ratsawa har cikin ƙwaƙwalwarsa, akaro nafarko daya yardarwa kansa cewa zai haƙura da Zahrah kenan, tabbas yazama dole ya yi haƙuri da ita koda kuwa hakan nanufin mutuwarsa ne, yau Zahrah da bakinta ta faɗa masa cewa tana da aure, maganar dayajita tamkar anwatsa masa tafasheshshen ruwan zafi, bayajin zai iya yin rayuwa idan babu Zahrah, amma kuma ayau yaɗaukarwa kansa alƙawarin cireta acikin zuciyarsa, duk da yasan hakan zai zamo kamar yaudaran kansa ne yakeyi, amma kuma dole zai jarraba....
****
Cikin matsanancin tashin hankali Dr.Sadeeq yadawo gida, yaje makarantar su Zahrah yanemeta sama da ƙasa bai ganta ba, gashi yaƙira wayarta bata ɗauka ba daya ƙara ƙiranta kuma yaji wayar akashe, hankalinsa atashe yake sosai, yana shigowa cikin ɗakin yadanna madannin ƙoyin wuta take haske ya gauraye gaba ɗaya ɗakin, wani irin ajiyar zuciyar dabai taɓa yin irinta ba ya sauƙe, haɗe da lumshe idanunsa, da sauri yaƙaraso gareta haɗe da sona ƙiran sunanta, jin shiru bata amsa saba yasanya yakai hanunsa jikinta, zafi zau yaji jikin nata, take tausayinta yakamasa, shidai yasan hakanan Zahrah bazata dawo gida bata jirasa yazo ya ɗauketa ba, sannan kuma haka nan bazata kashe wayarta ba. Zama yayi akan gadon haɗe da ɗagota ya kwantar da'ita ajikinsa. Mayafin dake jikinta ya zare haɗe da sanya hanu yashiga shafa kumatunta.
"Na'am!" ta amsa masa cikin wata irin murya, dagaji kasan tanajin jiki.
Kanta yashiga shafawa ahankali, zuge mata zip ɗin rigar dake jikinta yayi, haɗe da cire rigar gaba ɗaya daga jikinta, kwantar da ita yayi akan gado, kana ya nufi wajen da ɗan ƙaramin drawer ɗinsa ke aje, maganin da zai sauƙar mata da zazzaɓi cikin gaggawa yaɗauko.
Dakansa ya lallaɓata tasha maganin, abun gwajinsa ya ɗauko yashiga gwadata, cutar dayaga tana damunta shiyayi matuƙar ɗaga masa hankali, wani irin zufane yashiga keto masa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!"
kawai yake ambata acikin zuciyarsa, duk sanyin A.C'n dake cikin ɗakin amma Dr.Sadeeq gumine ke tsastsafowa daga jikinsa.
"Taya akayi Zahrah takamu da wannan ciwon?" tambayar dayake tayi mawa kansa kenan.....
(😲Wani ciwo mun banu🙆♀
Banyi editing ba idan kunga typing error kuyi haƙuri!)
*Thursday 30/January/2020*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
Hanu yasanya akan goshinsa ya share zufan dake tsastsafo masa. Tashi yayi tsaye haɗe da tattara kayan aikin nasa ya ajiye a gefe. Direct bathroom ya shiga haɗe da sakar mawa kansa ruwa....
Tun shiga wankansa har kawo yanzu da ya fito yake shirya kansa tanajin sa,amma idanunta alumshe suke kamar meyin bacci.
Zama yayi akan gadon haɗe da ɗagota ya jawota zuwa jikinsa, kanta ya kwantar akan ƙirjinsa haɗe da soma shafa bayanta a hankali, still ɗaya hanunsa yasanya yana me shafa gashin kanta.
Cikin murya me ɗauke da nutsuwa ya soma cewa.
"Meyasa haka Zahrah? me yasa kika zaɓi ƙuntatawa kanki? tun bayauba nasha faɗa miki cewa ki daina yawan sanya kanki cikin damuwa, na faɗa miki kirage yawan tunani, har acikin zuciyata inamiki wani irin so wanda bansan iyakacinsa ba, bana so nagan ki cikin damuwa, ganin farincikin ki yafiyemin komai aduniyarnan, kinkuwa san meke damunki yanzu? damuwar da kike yawan sanya kanki aciki tahaifar miki da matsala wanda baikamata ace yarinya ƙarama kamarki tana ɗauke da wannan ciwonba, mekika nema kika rasa aduniyar nan? banaso ki ɓoyemin komai inaso kifaɗamin shin azamana dake ina cutar dake ne? ko kuwa inayi miki wani abu wanda ba kya so ne?"
Kanta tashiga girgizawa alamar "A'a" tuni hawaye sungama wanke mata fuska.
"To idan dai har hakane yakamata ki faɗamin damuwarki koda nima zanji sauƙi acikin zuciyata"
yafaɗi haka a gareta cikin tausasawa.
Kuka ta fashe dashi haɗe da sake rungumeshi cikin kukan tace.
"Nakasa daurewa ne, nakasa daure zuciyata, idan dai yana cikin wannan duniyar bazai taɓa barina ba, bazai barni ba harsai yakasheni sannan zai huta, naso namanta dashi amma nakasa, bansan meyasa ba kullum zuciya ta me rauni take kasancewa akansa, dan Allah kayi haƙuri banfaɗi haka agareka don na ɓata ranka ba, kawai dai nafaɗi abun dake zuciyata ne!" taƙare maganar tana sheshsheƙan kuka..
Rumtse idanunsa yayi haɗe da cije laɓɓansa, dama yasani duk duniya damuwarta bazata wuce akansa bane yajima da sanin wannan. Ɗagota yayi daga jikinsa yazamana suna fuskantar juna. Cikin wata irin murya yace..
"Ba iya miji bane ni agareki, ni ɗan uwa ne wanda baki da kamarsa, najima da sanin cewa har yanzu Zaid yana cikin rayuwarki, nasan Inasonki so me tsanani, sai dai kuma duk irin soyayyar danakeyi miki Zaid yafini sonki, da ace zan iya to da najima da mallakawa Zaid ke amma bazan taɓa iyawa ba Zahrah nima masoyinki ne na haƙiƙa kamar yanda Zaid yakejin bazai iya rayuwa ba idan babuke, haka nima nakeji ajikina, batun yauba nasan Zaid yana nan kwance aƙasan zuciyarki, bana yaudaran kaina nakan faɗi abu ne aduk yanda natsaya na fahimceshi, koda kuwa abun dana faɗa bazasuyimin daɗin ji acikin kunnuwa naba, duk da kuwa nina faɗesu, bana ɓoye gaskiya saboda biyan buƙatar kaina"
Kafaɗunta yakama da duka hannayensa. Ci gaba yayi da cewa
"Yanzu zanyi miki magana ne a matsayina na mijinki kuma wanda yake sonki, har yanzu duk da na aureki kina aƙarƙashin ikona bazan taɓa takuramiki ba, inamatuƙar son farincikin ki, idan har kinaji ajikinki cewa bazaki iya rayuwa ba idan babu Zaid shikenan zan iya....." rumtse idanunsa yayi da ƙarfi ya kasa ƙarasa maganar, da sauri ya miƙe yafice daga cikin ɗakin.
Zahrah wanda tun fara maganarsa tayi saroro tana kallonsa, tana ganin ficewarsa ta fashe da kuka.
"Me doctor yake shirin cewa? badai zai haƙura da ita ba?" tambayar da tayiwa kanta kenan, sam haka bazai taɓa yiwuwa ba, wace irin banzace ita? taya ya zata iya jure rashin masoyi kamar doctor Sadeeq? kuka tashiga rerawa me tsuma zuciya, kaiconta tunda dai harta bari Dr.Sadeeq ya iya sanin sirrin dake cikin zuciyarta, yanzu da wani idanu zata kalleshi bayan yasan cewa akwai son wani maƙare acikin zuciyarta? lallai koda ace Zaid ubantane yakamata tayi ƙoƙarin mantawa dashi....
Dr.Sadeeq kuwa yana fita daga ɗakin falo yanufa, yanazuwa ya buɗe fridge haɗe da ɗaukan goran ruwa yakafa a bakinsa, saida yasha ruwan fiye da rabin gora kafun ya kai goran ƙasa, ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa akai akai.
"Meyake shirin aikatawa ne haka?" yatambayi kansa. Girgiza kansa yayi haɗe da ware idanunsa, idan yace zai iya rabuwa da Zahrah to yayi ƙarya, amma kuma idan yazamana bashine zaɓin ranta ba, to fa tabbas yazama dole ne yarabu da ita, badon kowaba saidon samun ingantaccen farincikinta, yasani shima abune me wahala ya iya jure rashinta, amma kuma itama yakamata aduba zuciyarta, yakamata tasamu abun da takeso.
key ɗin motarsa dake aje kan ɗan ƙaramin stull dake falon ya ɗauka haɗe da sakai yafice gaba ɗaya daga