Dai dai ta ɗaura hanunta kan handle ɗin ƙofar kenan, aka turo ƙofar daga waje, cikin rashin sa'a ƙofar ya bugeta a goshi, saurin ja da baya tayi haɗe da rumtse idanunta gam, ji takeyi tamkar ta shaƙesa ya mutu, ta tsani ganin kowani irin namiji ne a rayuwarta, musamman ma shi,domin kuwa yanayinsu yana ma ta shige da Zaid, kuma gani take tamkar kowani namiji irin halin Zaid garesa,,
"Ganinki tsaye anan yatabbatarmin cewa guduwa zakiyi, Miye ribarki a rayuwa idan kika gudu daga gaban i yayenki ? nasan duk inda zaki bazakiyi rayuwa mai kyauba, idan kika zaɓi tafiya can wata uwa duniya mai zaki tsinta? ina mai tabbatarmiki cewa babu wani abun da zaki tsinta sai, zallan takaici, dakuma ƙuncin rayuwa, zaman bariki kikeso kiyi? kokuwa zaman kanki kike so kiyi? " da sauri taɗago manya manyan idanunta dasuke cike tab da ƙwalla ta watsa masa wani irin mugun kallo...
"Babu abun daya shafeka da rayuwata, idan naga dama nayi kowacce irin rayuwa ma baishafeka ba, duk ba kune kuka jefa rayuwata acikin matsanancin duhu ba, wallahi na tsani naji koda kalmar farkon sunan kune a cikin kunnuwana, ballan tana aƙira sunan Namiji akusa dani, natsaneku! natsaneku!! " wani irin kukane ya ƙwace mata maicin rai,
"Kacuceni Zaid! Kacuceni! natsaneka tsana mafi muni! mai nayi maka dana cancanci wannan sakamakon a wajenka? mai na aikata maka wanda yasanya ka cutar da rayuwata? bazan yafe maka ba Zaid! kacutar dani, karuguzamin duk wani buri nawa, ka tarwatsamin rayuwata, mai yasa saini kazaɓa maiyasa!!!" taƙare maganar cikin ƙaraji da matsanancin kuka, tamkar wanda takama Zaid ɗin a gabanta..
Wani irin mugun tausayin tane yaji ya daki zuciyarsa, haƙiƙa Zahrah abar tausayice, domin kuwa tanacikin wani hali wanda take buƙatar abokin rarrashi da kuma mai kwantar mata da hankali,,, juyawa kawai yayi yafice daga ɗakin, domin kuwa jin kukanta yake har tsakar kansa.
Nurse yaturo tazo tayi mawa Zahrah alluran bacci, domin idan ba alluran bacci akayi mata ba yana da yaƙinin cewa kwana zatayi tana ruskar kuka..
Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa, hakan ya gagara domin kuwa duk juyin da zaiyi wani irin matsanancin tausayin Zahrah ne ke cika masa zuciya, baisan wani irin tausayawa yake mawa Zahrah ba, amma tabbas yasan tausayinta da yakeyi, yayi ƙarfi a cikin zuciyarsa, da ƙƴar dai yasamu ya yakice tunanin Zahrah, a cikin zuciyarsa ya samu yayi bacci, wanda rabin mafarkansa ya kasance na Zahrah ne...
Wanene Dr S.S. ?
Dr Sadeeq yakasance ɗa na biyu a cikin gidansu, Alhaji KHABEER SARDAUNA shine mahaifinsa, Alhj Khabeer wanda ake ƙira da Alhj Sardauna, mutum ne mai matuƙar karamci da kuma kyautatawa na ƙasa dashi, hakan yasa talakawa suke matuƙar sonsa, kasancewarsa ɗan siyasa, Hajiya Habiba itace mahaifiyar Dr Sadeeq, mace ce itama mai tsananin karamci dakuma kyauta, tana da kyakkyawan hali wanda kowa yashaida hakan, Dr Sadeeq shine ɗa na biyu a cikin gidansu, yanada yaya wacce ake ƙira da Aunty Raliya, Aunty Raliya dai, tana aure ne a cikin garin Abuja, tana kuma zaune a unguwar Wuse Zone 2, bayan Dr Sadeeq a kwai ƙaninsa Samad, Samad dai baya zaune a Nigeria yana zamane a Australia, a can yake da karatunsa, tun Dr Sadeeq yanada shekaru 20, Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, mutuwar da ta matuƙar girgizasu, amma babu yanda suka iya dole su ɗauki dangana domin kowani bawa da kalan tasa ƙaddaran.. yanzu tsawon shekaru biyu kenan Hajiya Habiba tana matsawa Dr Sadeeq, a kan cewa yafito da matar aure, amma abun yagagara, da anfara maganar aure sai abun yalalace, ko daga baya yace baison yarinyar, ko yace bata da nutsuwa, da haka dai magana zata ɓalakuce,, yanzu ne Hajiyarsa ta hura masa wuta akan cewa lallai tabasa nanda kwana kaɗan yafito da matar aure dan bazata ci gaba da zuba masa idanu babba dashi ace bai aje iyali ba....
Washe gari..
Ƙarfe 3 da rabi na yamma Dr Sadeeq da kansa ya rubutawa su Zahrah sallama, domin ya fahimci cewa matuƙar bai sallamesu ba, za a iya nemanta a rasa, bakuma zai so hakan ba.
Koda suka fito daga cikin asibitin, duk yanda yaso Zahrah tashiga cikin motarsa ya kaisu gida ƙiyawa tayi, dole haka yanaji yana gani suka tari mai taxi, baiyi ƙasa a guiwaba wajen shiga motar tasa ya rufamusu baya...
Suna isa bakin ƙofar gida, idanun Zahrah ya sauƙa a dai dai wajen da Zaid yake faka motarsa kullum idan yazo, wani irin muguwar faɗuwar gaba taji, take kuma zuciyarta tayi rauni, kuka ne ya kuma ƙwace mata, da sauri tafice a cikin motar dagudu tanufi cikin gida,, saida Inna suka sallami mai taxi kafun suka lura da Dr Sadeeq dake tsaye a bayansu yana ƙarewa yanayin unguwar tasu kallo, "A'a Likita dama kana biye damune ?" Baffa ya tambaya washe da baki,,
"Eh Baffa ina biye daku, dama gani nayi yakamata ace nasan gidan saboda magungunan ta basu ƙareba, nakuma san basha zatanayiba matuƙar ba'a tilasta mata ba"
"Ƙwarai kuwa likita ai taurin kai gareta, dole saida takurawa, to mushiga daga ciki mana " Baffa yaƙare maganar yanamai yi mawa Dr S.S nuni da ƙofar shiga gidan.. Baiyi musu ba haka yabi bayan Baffa suka shiga cikin gidan,
Inna ce ta baje masa wani ƙaton tabarma ya zauna akai, yayinda ta ɗebomasa ruwa a kofi ta aje mai.
Gyara zama Dr S.S yayi haɗe da cewa "Baffa inaso muyi wata magana ne idan har bazaka damuba "
"Faɗi maganarka kai tsaye likita, kada kaji wani shakku" Baffa yafaɗa yana mai dawo da hankalinsa ga Dr Sadeeq.
"Maiyasa bazaku kai case ɗin Zahrah kotu ba? yakamata ace amatsayinta na marainiya a bimata haƙƙinta, bai kamata ace wani ƙaton banza ya keta mata haddi ba, sannan kuma abarshi yaci gaba da walwala, inaga yakamata ayi wani abu akai" Dr Sadeeq yafaɗa cike da damuwa.
Nannauyar ajiyar zuciya Baffa ya sauƙe haɗe da jinjina kansa, cike da rauni yace "Bazanƙi shawaranka ba likita, sai dai a gaskia bazan ɓoye maka ba, hakan da kake so bazai samuba, domin yanda ka ganmu nan haka muke rayuwarmu, mu talakawa ne, cin yau da ƙyar na gobe da ƙyar, kuma maganan nan ma da nake maka, bansan wanene yayi mawa Zahrah fyaɗe ba, to ka ga kenan babu batun ma ɗaukar fansa"
"Wanene ZAID ?" Dr S.S ya tambayi Baffa.
Washe da baki Baffa yace " shine yaron da Zahrah ta amince dashi, yake zuwa zance wajenta, idan kuma bazaka mantaba ai nafaɗa maka shiɗin yaron kirkine, na tabbatar da cewa baisan haka yafaru da ita ba, da nasan dole zaizo" Baffa yaƙare maganar yana mai jinjina kai..
"Shine yayi mawa Zahrah fyaɗe !" Dr S.S yafaɗa murya a kausashe,
Gaba ɗaya idanunsa Baffa ya zaro, alamar maganar ta dake shi, "Zaid fa kace likita !" Baffa yafaɗa cikin kaɗuwa,
"Ƙwarai kuwa domin kuwa jiya ta ambaci sunansa, nakuma ji da kunne na, amma tunda kace ba zaku kai case ɗin kotu ba, bakomai ni zan wuce" Dr Sadeeq yafaɗa yana mai miƙewa tsaye, bayan yaciro damin kuɗi ya a jewa Baffa kan tabarma,,
"A'a hadda ɗawainiya haka likita? to to munagodiya!" Baffa yafaɗa cike da farinciki,
(hmm mai hali dai baya fasa halinsa)
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Malam hayaƙi, hayaƙi Malam a ɗakin Zahrah !!" Inna tafaɗa cike da tashin hankali, ai da sauri Dr Sadeeq da baffa, suka nufi ɗakin Zahrah'n wanda hayakin haryasoma cika tsakar gidan, dayake ƙofar bata da wani ƙarfi duka ɗaya Dr S.S yayi mawa ƙofar ɗakin tabuɗe, gaba ɗaya ɗakin yaturnuƙe da hayaƙi yayinda wuta kecin wasu kaya dake aje tsakiyar ɗakin, gefe da kayan kuma Zahrah ce durƙushe tana kuka, har wutan yakusa ƙarasowa gareta,
Cikin zafin nama, Dr Sadeeq yasanya hanunsa, ya janyeta daga tsugunnen da take, kai tsaye waje yafito da'ita, domin kuwa hayaƙin yasoma shiga cikin maƙoshinsu, Baffa da Inna kuwa ruwa suka ɗebo suka kashe wutan,
Riƙeta yayi gam yayinda ya kafeta da idanunsa da suka rune tsabar ɓacin rai,
Baisan meyake damuntaba, rashin hankaline ko kuma sangartane baisaniba, yasan cewa tanajin ciwo a cikin zuciyarta, amma abun da take ƙoƙarin aikata mawa kanta, kama yake da taɓin hankali, ƙoƙari yayi wajen danne zuciyarsa, haɗe da saisaita muryarsa, "Maiyasa Zahrah ? bazaki ɗau ƙaddaranki ba ?" yayi mata tambayar cikin tausasa murya, hawayene suke gudu haɗi da ambaliya akan fuskarta, gaba ɗaya jitakeyi duniyar najuya ma ta, dawowanta gida yasake tada mata da mikin dake maƙare cikin zuciyarta, duk da kuwa dama cewa mikin bai wau ya kwanta ba ne,,
Saurin saketa yayi sakamakon ƙarasowar Baffa da Inna wajen, zamewa tayi aƙasa dabas tana mai sakin kuka,
Kallon Baffa Dr Sadeeq yayi, kafun Baffa yace komai Dr Sadeeq yace, "Baffa ni nawuce sai nasake zuwa "
"To Likita mun gode ka gai da gida " Inna da Baffa suka haɗa baki wajen faɗa, da "To" kawai Dr Sadeeq ya amsa musu haɗe da sa kai yafice daga cikin gidan,
Kama hanun Zahrah Inna tayi suka zauna akan tabarma, cike da damuwa Inna tasoma cewa "Maiyake damunkine Zahrah ? sai kace akanki aka fa ra yin fyaɗe? gaba ɗaya duk kinbi kinɗaga hankalinki, muma kin ɗaga mana namu hankalin, a gaskia nida Baffanki munsoma gajiyawa da wannan halin naki, bayan kinso caka mawa kanki almakashi, likita ya hana, yanzu kuma ƙona kanki kikesonyi, wai kina cikin hankalinki kuwa Zahrah?"
"Gaya mata dai Salame, domin nima nan nasoma gajiya da rarrashi, yanzu dakika ƙona kayayyakin daya baki, shiɗin kika ƙona ne? tambayanki nake shiɗin kika ƙona ?" Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa, domin ya lura idan suka biyewa Zahrah tofa bazata taɓa daina yunƙurin kashe kanta ba..
Zuciyar Zahrah ne tasakeyin rauni, " Allah sarki ni, komai nayi, ganin laifina suke, shin bancancanci rarrashi da kulawaba? fyaɗe akayimini amma hakan baiwani shiga jikin kowa ba, natabbata idan da iyayena suna da rai, to tabbas da bazasu taɓa kwantar da hankalinsu ba, kuma nasan dolene sai sun ɗaukarmin fansa, bakuma zasu taɓa gajiyawa daniba, wayyo Allah na mutuwa tayi mini yankan ƙauna daku iyayena !!" maganar da Zahrah take faɗa kenan a cikin zuciƴarta, hawayenta ne suka sake tsananta zuba, sai yau ta tabbatar cewa Maraici bashi da daɗi, sai yau tasake tabbatar da cewa Allah ne kaɗai gatan ta, Zaid ya cuceta, yayi mata babban tabo wanda hargaban abada ba zata taɓa mantawa dashi ba, "maiyasa Zaid ?" tasake tambayar kanta bayan kuma tasan bata da amsa,,
Haka Inna da Baffa suka wuce ɗaki suka barta zaune a tsakar gida tana tsiyayar hawaye, babu mai rarrashi.
Tuƙin mota yake amma gaba ɗaya hankalinsa yanaga yanda yabaro Zahrah, tsantsar tausayinta yakeji, yanason taimaka ma ta amma to tayaya? ta wacce hanya? duk alokaci ɗaya ya tambayi kansa, wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, Zabba'u shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da ɗaukan wayar yakara a kan kunnensa,
"Cike da sangarta Zabba'u tayi masa sallama, amsa sallaman yayi a daƙile haɗe da cewa "Ganinan zuwa" ƙit yakashe wayar haɗe da cillata kan kujeran mai zaman banza, shi sam baisan yanda zaiyi da Zabba'u ba, amma a zahirin gaskia ɗabi'u da tarbiyanta basu masa ba,duk da kuwa cewa ƴar uwa take a garesa.
New York City
Tsaye yake agaban wani tangamemen cupboard paper, wanda yake liƙe ajikin wani abu kamar allo, sanye yake da 3 guater jeans, yayinda yabar gaba ɗaya surar jikinsa a waje, kasancewar baisanya rigaba, babban abun ɗaukar hankali ajikinsa shine lafiyayyun, 6 packs ɗinsa, dake kwance raɗa raɗa akan cikinsa, riƙe yake da wani dogon pen a hanunsa da'alama dai wani abu yake zanawa mai mahimmancin gaske,, ƙayataccen murmushinsa yasake, haɗe da ɗaukan glass cup ɗin da wine ɗinsa ke ciki, yakai bakinsa, saida ya shanye duka wine ɗin dake cikin kufin, kafun ya aje kofin kan wani ɗan ƙaramin table dake kusa dashi,
Hanunsa yasanya akan kyakkyawar fuskar daya zana a jikin cupboard paper ɗin, a hankali yashiga shafa zanen , hanunsa yakai dai dai saitin bakinta, haɗe da shafawa, idonsa ɗaya yakashe haɗe da lasan laɓɓansa,
"Kinkasa barina My Sugar Baby, maiyasa ? " yayi tambayar yana mai tsare zanen dake jikin cupboard papern da ido,
"Bazaki amsaminba ko? fushi kike dani ko sugar baby na?"
Murmushi yakumayi haɗe da matsawa daf da cupboard paper'n bakinsa yaɗaura adai dai kumatun ta yamanna mata kyakkyawan kiss, "Kikulamin da kanki kinji My Zahrah!!" yafaɗi maganar cikin shauƙi,, sai alokacin nalura ashe zanen fuskar Zahrah ne raɗau ajikin cupboard paper'n, bakaɗan ba kuma zanen yayi kyau,, kyakkyawan ƙyalle yasanya yarufe zanen, haɗe da ɗaukar wayarsa yafice daga cikin ɗakin...
Yana fita falo Abid dake tsaye tun ɗazu yana zaman jiransa, ya saki tsuka, haɗe da cewa " Wai don Allah maika tsaya yi ? tun ɗazu fa kasan nakejiranka, amma ka shanyani "
Zama Zaid yayi akan kujera haɗe da jawo kwalbar wine ɗinsa, yashiga shan abunsa, ganin haka yasa Abid sauƙe ajiyar zuciya haɗe da girgiza kai, wato dai yau ƴan halinne suka motsa, gaskia Zaid yanada wuyan sha'ani, bakoda yaushe kake gane gabansa da bayansa ba, duk da kuwa tsananin sabon dake tsakaninsu, amma shi kansa wataran idan Zaid ya juye tofa baya iya gane masa.
"Kana yawan shan wine Zaid, baka tunanin zata iya janyomaka matsala nan gaba ?" Abid ya tambaya cike da kulawa, domin kuwa, shi ko za'a kasheshi bazai iya shan rabin wine ɗin da Zaid yakesha a rana ba,
Dariya Abid yayi, domin kuwa yanzu yatabbatar cewa Shu'umin cin nasa ne ya motsa, "Okay i'm sorry bazanƙara ba, amma yakamata ace musauƙa ƙasa, babes ɗin nan fa suna jiranmu " Abid yafaɗa yana mai duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa,
"Kaje kawai ka sallamesu, nikam bana ma buƙatar ganinsu, mata duk a bubbushe, ba wani diri mai burgewa, sai kace 1, kaje can kata fama idan zaka iya" Zaid yafaɗa cike da ƙuncin rai,
Dariya sosai Abid yayi, haɗe da tashi kawai yafita daga falon, gaba ɗaya kwana biyun nan yarasa maiyake damun Zaid..
Abid na fita Zaid yagyara zamansa, haɗe da lumshe idanunsa, gaba ɗaya fuskar Sugar Babynsa ne yake yimasa gizo a cikin idanun nasa.
Abuja Nigeria
Zahrah ce zaune akan ƴar yaloluwar katifarta, ta tanƙwashe ƙafafunta, yayinda kanta ke kallon sama, ruwan hawayene kawai ke gangarowa daga cikin idanunta, kallo ɗaya zakai mata wata irin muguwar tausayinta yadaki zuciyarka, domin kuwa wani irin muguwar rama ce ta bayyana a jikinta,
Da sallama Khausar tashigo cikin ɗakin, kamar daga sama haka Zahrah taji muryar aminiyarta ta wato Khausar, tana kai kallonta bakin ƙofa taga Khausar ɗin tsaye tayi turus,,
Ai dagudu Zahrah taje tafaɗa jikin Khausar, haɗe da sakin wani sabon kuka mai sauti, duk da cewa Khausar batasan abun dayake faruwa ba, amma tasan cewa ba lafiya ƙawartata take ba, kawai itama sai tafashe da kuka, hakanan taji wani irin tausayin Zahrah'n yacika zuciyarta, rungumeta tayi da kyau a jikinta, ko kaɗan Khausar batayi yunƙurin hana Zahrah kuka ba, saida Zahrah tayi kuka sosai, kafun ta tsagaita, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya,, hanunta Khausar takama suka zauna akan katifar Zahrah'n,,
"Zahrah!" Khausar taƙira sunanta cikin sanyin murya, Zahrah bata iya amsa mata ba, sai ɗago idanunta da suka kumbura suntum tsabar kuka, tayi ta kalli Khausar ɗin,
Zaro idanu Khausar tayi, cike da tashin hankali tace "Zahrah maiyake faruwa ne, tun ranan nake ƙiran wayarki a kashe, nazo gida kuma bansamu kowaba, nazo yafi sau huɗu bana samun kowa acikin gidan, dan Allah ƙawata kifaɗamin maiyake faruwa ?" Khausar tayi maganar cikin damuwa.
"Rayuwata taƙare Khausar, yacuceni,ya yi mini babban illa, dakuma tabo wanda bazai taɓa gogewa ba, ya nakasamin rayuwata, ashe haka ƙaddara zata zomin mummuna? nayarda cewa kowani bawa da'irin tasa ƙaddaran amma ni tawa ƙaddaran tafi takowa muni, danasan haka zata faru dani, dana roki Allah daya kasheni kafun yanzu na...." Saurin toshe mata baki Khausar tayi, cike da ruɗani haɗi da tashin hankali, Khausar tace "Kada kiyi saɓo Zahrah, kinsani acikin duhu, kisanar dani maike faruwa dan Allah, gaba ɗaya kinsani cikin tashin hankali !" Khausar tafaɗa cikin ƙosawa,
"Za..i..d yayi min fyaɗe Khausar !!!" Zahrah tafaɗa tana maisake rushewa da kuka,,
Tamkar anwatsamata ruwan zafi haka Khausar taji ajikinta, lokacin da maganan Zahrah yadaki dodon kunnenta, "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Fyaɗe fa kikace Zahrah ?" Khausar ta tambaya cikin matsanancin tashin hankali, lokaci guda hawaye suka shiga sauƙa daga cikin idanunta, take jikinta yayi sanyi laƙwas,,
"Yacutar da rayuwata Khausar, ashe haka soyayya ta ke? rama alkhairi da cuta, ashe haka duniya take cike da azzaluman bayi? maiyasa yayi min haka Khausar? mainayi masa? yaruguzamin duk wani farincikin rayuwata, wayyo Allah na Khausar ki karɓi wuƙannan ki kasheni dashi ko da zansamu sauƙi da salama acikin zuciyata !!" Zahrah taƙare maganar tana mai miƙomawa Khausar wata wuƙa da ke aje gefenta,,
Matsanancin kuka Khausar tasanya, haɗe da jawo Zahrah jikinta, ta rungumeta ƙam, kuka suka shiga yi wiwi, babu mai lallashin ɗan uwansa...