x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 201

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dama idan yayi sex da Zee tofa saitayi masa kuka, na azaba ko na daɗi wannan ne kuma baisani ba,, tsaye yake agaban dressing mirror dagashi sai towel ɗaure a ƙugunsa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan busar da gashinsa da yakeyi da hand dryer, Zee dake kwance akan makeken gadon ɗakin shame shame, kuwa ƙura masa idanu tayi, itakam Allah yasani, Zaid yana matuƙar burgeta, tanajin son gayen har cikin zuciyarta, saidai tasan cewa ko sama da ƙasa zasu haɗe, Zaid bazaitaɓa auren ta ba, saidai tana godemawa Allah ahakan ma daya bata daman raɓansa, domin raɓan Zaid ma sai mai sa'a, kuma sai macen da ta amsa sunanta mace ƴar gayu da aji....


Tsab yagama shiryawa haɗe dayi mawa kansa feshin turare mai daɗin ƙamshi,, Car key ɗinsa ya ɗauka haɗe da wayarsa, hanu yasa acikin aljihun wandonsa, kuɗi ya ciro bandir ɗin ƴan dubu dubu, ya cillamawa Zee akan cinyarta, batare da ya kalleta ba yace " Kada ki tafi sai kin kimtsamin gado na " yanakaiwa nan azancensa, yasakai yafice daga cikin ɗakin bakinsa ɗauke da fito,,, a maimakon Zee taji haushin yanda yamata, saima murmushin da tayi haɗe da lumshe munafukan idanunta, afili ta furta cewa "Allah kamallakamin Zaid amatsayin mijina".....




Tundaga Zauren gidan nasu ta ke jiyo tashin muryan Inna dana Baffa da'alama dai sana'artasu ta kullum sukeyi wato faɗa,, shahada kawai tayi tadoshi cikin gidan, domin dai tasan tana shiga tofa kanta faɗan zai dawo... Aikuwa a rubuce yake tana sawo kai cikin gidan, Inna ta ce "Kekuma uwar gantali saiyanzu aka tashi daga makarantar ?" cike da ladabi Zahrah ta rusuna haɗe da cewa " Baffa ina wuni "...."Daban wuni ba zaki ganni ? nace daban wuni ba zaki ganni ?? Baffa yakuma faɗa cikin tsawa, kai kawai zarah ta girgiza haɗe da nufar ɗakinta,, kwanciya tayi luf akan ƴar katifanta, zuciyarta cike da tunanin halin rayuwa dakuma yau da kullum....




Koda Zaid yabaro guest house ɗinsa bai zarce ko'ina ba sai wani babban Club ɗin dake cikin garin abuja, makeken Club ne mai kyau da tsaruwar gaske, irin Club ɗin nan ne daba kowa ke zuwanshi ba sai wane da kuma ɗan wane, Club ne na manyan guys, da kuma manyan ƴan mata, kamar ƴaƴan shugaban ƙasa da sauransu, amma idan dai har kai ba wani bane kuma ubanka ba kowa bane to fa baka isa shiga wannan haɗɗɗen Club ɗin ba, Zaid kuw yamaida wannan Club ɗin kamar ɗakin baccinsa, domin kuwa zaiyi wuya ace ya kwana ɗaya baijeba...
Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun da aka ƙawata tsakiyar Club ɗin dasu, yana zama wata ma aikaciyar Club ɗin tanufu inda yake hanunta ɗauke da tire na glass wanda samansa ke ɗauke da glass cup guda biyu, da kuma zungureren tsadaddiyar kwalban giya, kasancewa duk wani ma'aikaci dake cikin hotel ɗin yasan, abun da Zaid ɗin ke sha idan yazo wajen... Duk yanda ma aikaciyar Club ɗin nan ke kwarkwasa Zaid baiko ɗaga idanunsa ya kalleta ba, domin shi baimaga macen dazai kula ba kaf cikin Club ɗin, balle kuma ita banza mai aiki.... Cike da nutsawa Zaid yakafa kansa ya kwankwaɗi giya son ransa, saida yayi tatul tukun yabar cikin club ɗin, bayan yayi waya da Asmee ƴar wani minister dake cikin Naija, cewa tazo ta samesa a guest house ɗinsa......


*WAYE ZAID ?*




Zaid tantirin Mazinaci ne kuma ɗan giya, uwa uba baida mutumci ko ƙaɗan, sannan kuma komai kayi masa baka burgesa, Zaid yana da Munanan halayya, Zina shine babban ciwon daya riga yayi mawa jiki da zuciyarsa ƙawanya, Zaid Mazinaci ne na ƙarshe, iskancin sa yake zubawa babu mai hanasa, domin dai iyayensa sunriga da sungama shagwaɓasa, bayajin maganan uban kowa, duk wata haɗɗɗiyar mace wayayya dake cikin garin Abuja babu wacce batasan Zaid ba, domin iskancinsa ya shahara yayi ƙarfi, kasan cewarsa kyakkyawan saurayi mai wanka da naira, yasanya wasu ƴan mata ke matuƙar ƙaunarsa, sannan kuma suke burin mallakansa, amma saidai sama yayiwa yaro nisa babban ma saidai kallo....








*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*




*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*




*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna




*Editing is not allowed 📵*


*Chapter 4*






*Alhaji Ma'aruf Chanji* shine sunan maihafin Zaid, Babban mutum ne da ake da mawa dashi acikin Nigeria, yana da kuɗi sosai, sannan mutum ne mai kyautatawa na ƙasa dashi, bashi da rowa ko kaɗan, matarsa ɗaya *Hajiya Safara'u* kuma itace ma haifiyar Zaid, daga Alhaji Ma'aruf har Hajiya Safara'u shuwa arab ne, Allah yayi musu baiwar kyau ga dukiya, shekaransu biyu da Aure Allah ya azurtasu, da haihuwan ɗa Namiji, wato Zaid, Zaid dai kyakkyawan gaske ne, domin tsananin kyawunsa ke sawa yake shiga ran jama'a, Zaid tun yana ƙarami yataso da wani irin Shu'umanci, ga mugunta, haka zalika baruwansa da shiga harkan kowa, hatta iyayensa kuwa, gaisuwa kawai keshiga tsakaninsu, duk yanda suka so yasake dasu amatsayinsu na mahaifansa, amma abun yaci tura, Sosai Iyayen Zaid ke nuna masa tsananin ƙauna, da tattali, asalin sana'ar Alhaji Ma'aruf shine Chanjin kuɗaɗe, yayi ƙaurin suna a sana'ar, sannan kuma yatara maƙudan kuɗaɗe, ganin harkan nasa natayin gaba dukiyarsa na ƙara yawa, yasanyashi tattarawa yakoma America da zama, can ya cigaba da business ɗinsa, duk ko yanda yaso Hajiya Safara'u tabiyo sa America suzauna ƙiyawa tayi, saidai Zaid yayarda yabi mahaifinsa, inda a can yasoma karatun sa,, Zaid yanada shekaru goma a duniya mahaifiyarsa ta haifa masa ƙanwa maisuna Labisat, Labisat dai kyakkyawar yarinyace suna kama da Zaid, saidai a gaskia Zaid yafita kyau sosai, domin idan kaga Zaid zakai tunanin ba ɗan Nigeria bane,,,, acan America mahaifin Zaid kasuwancinsa kawai yasa a gaba, amma sa'i da lokaci yana zuwa Nigeria duba iyalansa,, Yanayin yanda yake gudanar da kasuwancinsa a America yasanya bashida wani kyakkyawan lokacin da zai kula da ɗansa wato Zaid, kullum Alhaji Ma'aruf idan yafita office baya dawowa sai dare, shikuwa Zaid rayurwasa yakeyi da turawan abokansa, wanda yayisu acikin school ɗin dayake, kunsan dai su turawa, babu wani abun daya damesu iskanci sun maidashi kamar ruwan sha, domin dai dayawansu ba addinin Allah suka sani ba balle su kiyaye, tun Zaid na da shekara 17 yafuskanci abokansa na school suna neman mata, shikuwa sam alokacin mata basa gabansa, duk da kuwa cewa suna kawo masa tallen kansu, amma baya sauraransu, duka abokan Zaid turawa ne, sai mutum ɗaya wato *ABID* Abid cikekken ɗan Nigeria ne cikin garin Abuja shima gidansu yake, sannan babansa shine Minister'n Man Fetur na Nigeria gaba ɗaya, Abid hatsabibin ɗan iska ne kuma tantiri domin kuwa tun yana ƙaraminsa yasan yanda zai jagwalgwala mace, Zaid da Abid a bota suke sosai, domin jininsu yazo ɗaya,, duk da cewa Zaid yana da ƙarfin sha'awa amma bayabin mata, saidai wani zubin yakan ɗan mawa mace kiss da dai sauransu,, lokacin da Zaid yake matakin lavel 2 na degree ɗinsa lokacin yana da shekara 21, Allah ya jefomasa ƙaddaransa kuma Hargitsi mafarin halakarsa,,, wata rana sunje yawon shaƙatawa shida saiɗanun abokansa, ya haɗu da wata ƴar iskan baturiya mai suna Nicky, abun daya fa ra ɗaukar hankalin Zaid game da Nicky shine kyawu da surarta, Nicky irin fitinannun matan nanne, shu'umai wanda idan suka ɗiga tsamansu akan abu tofa sai sun sameshi, tunda Nicky tayi ido huɗu da Zaid gaba ɗaya hankalinta yatashi, domin kuwa Zaid yayi mata hundred percent, bawani ɓata lokaci tabayyana masa soyayyarta a gareshi, Zaid kuwa dake ɗan izza ne saiya soma ja mata aji,, daga ƙarshe dai daya tabbatar da cewa itaɗin bata bibiyar maza sai ya amsa soyayyarta suka cigaba da shan love ɗinsu,,


Watarana Zaid yana kwance a ɗakinsa, sai ganin Nicky kawai yayi sanye da wani irin ɗan iskan kaya wanda yabayyana komai na surarta a fili, ganin da yayi mawa Nicky a haka baƙaramin ɗaga masa hankali yayiba, wata irin sha'awa yakeji mai ɗaga hankali, koda Nicky tafahimci haka saita yi amfani da damanta tasake ruɗa Zaid da irin salonta, jawo Nicky yayi jikinsa yashiga sun batarta tako ina, a rannan sheɗan yaribaci Zaid har yakusanci Nicky, tun da yake a duniya baitaɓa sanin ya daɗin Sex yake ba sai awannan ranan, baisan ya ƴa mace take ba shidai kallon su kawai yake, amma sai gashi yau yasani,, wani irin gamsuwa Nicky tasamu da Zaid a ranan wanda bata taɓa samun irin shi da ga wani ɗa Namiji ba,, tundaga Wannan rana Zaid yazama mashahurin ɗan iska kullum yana tare da Nicky suna aikata Zina, arana sai Zaid yayi Sex da Nicky sau Biyar,


Zaid mutum ne mai ƙyan ƙyami, shiyasa kwata kwata baya neman sauran matan turawa domin yasansu kowa buɗe ma ƙafa suke yashige,, Nicky ce kaɗai abokiyar watsewarsa, itama dan yafuskanci cewa bata mu'amala da kowani na Miji ne, sannu ahankali Zaid yasoma shan giya, koda Abid yafuskanci cewa abokinnasa ya soma baza iskancinsa, sai yasake haɗasa da wasu ƴam mata gangariya, aikuwa Zaid baiƙiba, nanfa iskancinsa yaci gaba da tumbatsa, haryazo ya fi ƙarfin Nicky, Ƙaurin isknacin Zaid har yaɗara na abokansa,domin ko Abid yanzu Zaid yafisa sanin kan mace da kuma iya iskanci,,,, duk wannan halin da Zaid ke ciki Dadynsa Alhaji Ma'aruf baisaniba, yanacan yasa harkan kuɗinsa a gaba, yakuwa mallaki dukiya masu mahaukatan yawa,, akwana atashi Zaid ya kammala degree ɗinsa, cikin ikon Allah kuwa yasamu kyakkyawan result, domin dai yanada ƙoƙari sosai, iskancinsa baisa yadaina karatu ba,, bawani ɓata lokaci Zaid yawuce London domin yin masters ɗinsa acan, hmmmm zuwansa London yaƙara masa iskanci sosai, shima Abid biyosa london ɗin yayi suka ci gaba da zuba iskancinsu acan,, Zaid yazama tantirin shu'umi idan yaga mace matuƙar tayi masa tofa saiyayi sex da'ita,, duk wannan tsawon shekarun da Zaid yaɗauka aƙasashen duniya, sauɗaya tak yazo Nigeria nanma satinsa biyu kacal ya tattara ya koma,,


Kwanci tashi Zaid yakammala Masters ɗinsa, take kuma wani Babban banki dake london suka nemi da yayi aiki dasu, sam bai amince da buƙatarsu ba, domin shi yafiso yayi kasuwanci, maƙudan kuɗaɗe Dadynsa yasanya masa wajen gina masa wani katafaren kamfani a London, shahararren kamfani aka gina masa na ƙera takalma da jakakkuna new styles, masha Allah cikin ƙanƙanin lokaci kamfanin Zaid ya shahara a faɗin duniya domin, kaya masu kyau da inganci suke bugawa,, Zaid yana karatu kuma yana kasuwancinsa harya kammala P.H.D ɗinsa, isakanci kuwa yaci uban na da,, wasa gaske saiga Zaid ya mallaki Company's a ƙasa she da dama, lokaci ɗaya Zaid yayi wani irin mahaukacin kuɗi, baiyi ƙasa a guiwa ba ya dawo Nigeria yakuma gina wani kamfani'n da ake ƙera gyalelluka wato vails, tunda ya dawo Nigeria baisake komawa ko wacce ƙasa ba, domin yaji ƙasar tasa wato Nigeria tayi masa daɗi, company's ɗinsa na ƙasashen waje kuwa, yasanya amintattun mutanensa suna kula masa da su......


Cigan Labari...


Daga Club ɗinnan Zaid baizarce ko'ina ba sai guest house ɗinsa, koda ya isa yasamu tuni Asmee tazo tana jiransa,, tundaga falo Zaid suka soma watsewa shida Asmee,, ........




((Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru, walƙahi wayatace ba charge.))






*13/October/2019*




*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*




*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*




*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna




*Editing is not allowed 📵*




*Chapter 5 то 6*




Haka Zaid da Asmee suka ɓata dare suna iskancinsu, basa ko tsoron Allah mahalicci,, haƙiƙa zuciyar Zaid ta bushe ƙarau, baya ko tuna azabar da Ubangiji zaiyi masa, aduk sanda yaje garesa batare da ya tuba ba.......




Kasancewar yau basu da lecture sai 12 pm yasanya gaba ɗaya aikin gidan itatayi shi, yayin da Inna ke kishingiɗe akan tabarma,, da bala'i Baffa yashigo cikin gidan " Wallahi ni nagaji bazan iyaba ehe, ace akan yarinya kwara ɗaya tol duk inda nagilma mutane zagina sukeyi, to bata saɓuwa, ke Zahrah inakike ne dan Ubanki ?" Baffa yaƙare maganar cikin hargowa, Zahrah dake cikin kitchine tafito jikinta a sanyaye domin tasan kwanan zancen,, "Lafiya kuwa Malam kashigo gida kana ɓaɓatu ?" Inna dake kwance tatambayeshi, " Kema kinsani ai akan wannan yarinyar ce mana Zahrah taƙi fito da Miji tayi aure, tananan koda yaushe cikin bulayin zuwa makaranta, makarantan da ba tsinana mata komai zaiyi ba, to wallahi nagaji, ko ina gulma ake wai nakasa riƙe amanar da ɗan uwana yabani, naƙi aurar da yarinya nasata karatu, bayan nafi kowa tsanar wannan ɗan iskan karatun da takeyi " "Ke Zahrah !!" yaƙira sunan Zahrah da kakkausar murya, batare da yabari ta amsa masa ba yaci gaba da cewa " bazan iyawa zagin mutane ba, nabaki nanda wasu kwanaki ki fito da miji koda kuwa musaki ne na tattaraki nayi miki aure batare da wani kayan ɗakiba, kije can ki ƙarata " Baffa nakaiwa nan a zancensa ya sakai yashige cikin ɗaki, Inna tarufa masa baya,,, ɗaki Zahrah ta koma haɗe da zama akan ƴar yalolon katifarta, " ya Allah gani gareka kafi kowa sanin halin da nake ciki ya Allah kakawomin ɗoki " wasu zafafan hawayene suka shiga sauƙa daga kan fuskar Zahrah, maganar kenan koda yaushe Miji Miji, wai shin ina zata samo mijin da zai aureta ? tun da take a duniya Namiji ɗaya ne yataɓa cewa yanasonta, kuma shima tundaga wannan ranan bata sake sashi acikin idanun taba, tayi imani cewa tana da tsantsar kyau da kuma sura, wanda zai iya janyo hankalin ko wani ɗa namiji zuwa gareta, amma maiyasa babu wani Namiji dake kallonta ballan tana harya furta mata kalman so ? tayi mawa kanta tambayar da bata da amsa,, jin motsin Inna a tsakar gida yasa tayi saurin share hawayenta, haɗe da ficewa daga cikin ɗakin, kuɗi Inna taciro daga kunkuminta, haɗe da miƙamawa Zahrah tace "Ungo maza kaima wa Ladidi mai adashe kice mata ga zubina na jiya " "to" kawai Zahrah tace haɗe da nufar hanyar fita daga gidan, domin dai dama sanye take da hijab ajikinta, al'adar ta ce bata zama babu hijabi, saidai idan a ɗakinta take....


Tafiya take tana kallon ƙasa, yayinda hannayenta ke naɗe akan ƙirjinta, da gudun gaske ya shawo kwanar saura ƙiris ya doketa, Allah ne kawai yasa tayi saurin matsawa gefe,, parking motar yayi haɗe da leƙo kansa waje ta window'n motar " Uh sorry Zahrah ina fata dai bantaka ki ba ?" ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa "A'a baka takani ba" wani irin shu'umin kallo yabita dashi haɗe da cewa "Ina zaki ne haka da tsakar rana ?" " Aika zani " Tabasa amsa a taƙaice,, "Okay shigo na rage miki hanya mana " yayi maganar yana mai yunƙurin buɗe mata murfin motar, "A'a kabarshi kawai nagode" bata jirayi mai zai ceba tasakai tayi tafiyarta,, murmushi kawai Bash yayi haɗe da figar motarsa yayi gaba.....




*Wacece Zahrah ?*


Malam Adamu Muhammad haifaffen ɗan jihar Yola ne, su biyu ne a wajen iyayensu shida ƙaninsa Hayatu, Malam Adamu yakasance mutum mai mutumci da kuma karamci, Matarsa ɗaya Zainab, Zainab, asalinta buzuwar Niger ce fatauci yashigo da mahaifanta Nigeria, Mahaifan Zainab dana Malam Adamu suna da kyakkyawan alaƙa kasancewarsu maƙotan juna, tun Zainab na ƙarama Allah yasanya mata soyayyar Malam Adamu acikin zuciyarta, kasancewarsa kyakkyawan bafulatani, duk da dai tafisa kyau nesa bakusa ba, cikin ikon Allah Zainab nakai lokacin daya kamata ace anyi mata aure, iyayenta suka Aura mata Malam Adamu, zama sukeyi na lafiya da ƙaunar juna,, watarana iyayen Zainab suka shirya don zuwa Niger, ahanyarsu ta zuwa sukai gamo da ƴan fashi, suka harɓesu, sosai Zainab tayi kukan rashin iyeyenta, da ƙyar dai Malam Adamu yasamu ya rarrasheta, akwana a tashi kwatsam ciki yabayyana ajikin Zainab, sosai sukayi murna da samun ƙaruwa da Allah yayi musu, cikin Zainab nada Wata Tara tahaifo kyakkyawar ɗiyarta mai matuƙar kama da ita, saidai ita ƴar harta ɗara Zainab a kyau duk da kuwa kyau irin na Zainab, anyi shagalin suna lafiya inda yarinya taci sunan mahaifiyar Zainab wato *FATIMA* ana ƙiranta da *ZAHRA* Zahrah tataso cikin gata da kulawar iyayenta, saidai muce masha Allah,, watarana ne Malam Adamu yatattara matarsa da ƴarsa suka koma garin Abuja da zama, cikin wata unguwa da'ake ƙira Suleja, yakama musu hayan wani ɗan ƙaramin gida,, sana'ar saida takalma Malam Adamu keyi, yana da ɗan teburinsa a nan yake kasa takalman roba da su silifas (slippers), cikin ikon Allah kuwa,Allah baya hanasa na abinci da kuma na ƴan biyan buƙatun da ba'a rasaba, Watarana Malam Adamu ya tsinci wasu maƙudan kuɗaɗe a ƙasa, daya bincika kuɗin shine yataradda adireshi (Adress) na mai kuɗin acikin jakar daya tsinci kuɗin, a shema wanda ya wurgar da kuɗin, a nan gaba da unguwarsu kaɗan yake kuma yasanshi sunansa Alhaji Umar,
End Ads