x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - SHU'UMIN NAMIJI

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 185824 words

Category: Romance Story +18

Views 227

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
akai akai, bazata taɓa mantawa ba shima da haka yafara, daga ƙarshe kuma ya dasa mata babban tabo acikin zuciya da rayuwarta mai wahalan gogewa, saurin sake kwalin wayar tayi haɗe dayin watsi da kayan da suke zube a gabanta, talauci bahauka bane, bazata sake bari haka yafaru da'ita ba, hawaye ne suka shiga sauƙa akan ƙuncinta, haƙika soyayya bata mata adalci ba, kwanciya tayi lamo akan katifa tana nai sauƙe a jiyar zuciya, jin da tayi zuciyarta na shirin dawowa ɗanyea shakaf ne yasanyata tashi ta ɗauko littafi mai tsarki wato Al'Qur'ani tasoma karantawa domin rage damuwar dake damunta a zuciya....


"Salima kuma Hajiya?" Doctor Sadeeq yatambaya cikin muryar damuwa.


"Ƙwarai kuwa Sadeeq, ko ita Saleema'n tana da wani aibune? ƙwarai nayaba da hankalinta dakuma tarbiyanta, saboda haka nagama yanke shawarata, gobe zanfaɗamawa ƙanin mahaifinku yaje yatambayo maka aurenta, idan ma a so nane banso bikin yawuce nanda wata ɗaya " Hajiya tafaɗi maganar babu alamar wasa akan fuskarta.


Cike da sanyin jiki Doctor Sadeeq yace " Shikenan Hajiya, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma dakin ƙara haƙuri, nan bada jimawa ba zan kawo wacce nakeso"


"Hmmm ai aikin gama yariga daya gama Sadeeq, nagaji dajin wannan zancennaka, koda yaushe haka kake cewa, to yanzu dai nagaji da ƙaululan dakakemin saboda haka natsaida magana,zaka iya tafiya"


Gaba ɗaya hukuncin da Hajiyar tasa ta yanke masa baiyi masa daɗi ba, amatsayinsa na Namiji bai dace ace anyimasa dole akan aure ba, shi sam Saleema ma bata ɗaya daga cikin irin tsarin matan dayakeso, amma yazaiyi tunda dai Hajiya ta kafe, yasanta da wuyar sha'ani, idan tace eh zaiyi wuya kuma tace a'a, jiki a mace haka yafice daga falonnata, kaitsaye ɓangaren sa yanufa, yanashiga cikin falonnasa direct friedge yanufa, goran ruwa mai sanyi ya ɗauko, haɗe da zama akan kujera, saida yasha ruwan fiye da rabin gora, kafun yashiga sauƙe ajiyar zuciya, wayarsa yaciro acikin aljihun rigarsa, kai tsaye lambar sim ɗin dake cikin wayar daya bata, ya danna wa ƙira, saidai yaji saɓanin tunaninsa, domin kuwa cemasa akayi wayar a kashe take, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da aje wayartasa a gefe, "Maiyasa nadamu da'ita sosai ne?" yatambayi kansa, bayan kuma yasan baida amsa,


"Inatausayinta sosai,amma kuma bayan tausayi inajin wani abu na daban a ga me da'ita, menene wannan abun ? yazama dole nasan menene amma tabbas ina da burin inganta rayuwarta " Ƙaran wayarsane ya katse sa daga zancen zucin da yakeyi, ganin da sabon number ake ƙiran nasa yasa bai ɗauki ƙiranba, saima tashi dayayi yawuce cikin bedroom ɗinsa...


Washe gari.


Yau tunda safe takammala shirinta, tayi kyau cikin shigar ta ta atamfa riga da sket, yayinda lufayant dake jikinta ya kasance hot pink colour, sama sama tasha ruwan shayin da Inna ta dafa, tana kammala shan ruwan shayin ta ɗauki jakarta haɗe da nufar hanyar waje. domin batamaso likita yazo yasameta, tafiso tayi tafiyarta, sam bataso yanashiga cikin rayuwarta, takuma yanke shawaran gaya masa yafita acikin rayuwarta, domin sam baikamata tasake bawa wani namiji dama ba.


Turus haka taja ta tsaya, domin kuwa tsaye tagansa ajikin motarsa, yasha ado cikin wata blue ɗin shadda, sam batai tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacinba.


Murmushi yayi mata haɗe da soma takowa harzuwa inda take tsaye.


"Baki tsammaci ganina a dai dai wannan lokacin ba ko?" yatambayeta kansa tsaye yana mai kafeta da idanu.


Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa "Ina kwana"


"Lafiya ƙalau, yakika tashi?"


"Lafiya" tabasa amsa a taƙaice, haɗe da sunne kanta ƙasa, domin hakanan taji yamata wani irin kwarjini.


"Muje kada kiyi latti ko" Doctor yafaɗa yana mai yi mata nuni akan cewa tashige gaba.


Bazata iya musa masa ba, domin kuwa yayi mata kwarjini sosai, don haka cikin sanyin jiki tanufi wajen motar tasa, shikuma yarufa mata baya, gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi, alƙawarin da ta ɗaukawa kanta nacewa zata faɗa masa yafita a rayuwarta gaba ɗaya ya ruguje, domin kuwa tanaganinsa taji bakinta yamutu murus, tana shiga cikin motar ta lumshe idanu, domin kuwa wani irin daddaɗan ƙamshi cikin motar keyi, cike da nutsuwa yake tuƙin nasa, yayinda jefi jefi yake satan kallon Zahrah, wanda gaba ɗaya hankalinta yana ga ababen hawan da suketa hada hada akan titin.


"Maiyasa ki kaƙi kunna wayar dana baki?"


Sunkuyar da kanta ƙasa tayi haɗe da soma wasa da yatsun hanunta, "Babu" tafaɗi hakan cikin sanyi murya.


"Ko kuma dai bakyason kyauta daga gareni ba "


Saurin kallonsa tayi, jin abun da yace, ai kuwa karab idanunsu suka haɗe a waje ɗaya, saurin sadda kanta ƙasa tayi, domin batason haɗa idanu dashi kokaɗan, "Bahaka bane, kawai dai banson rayuwata tasake cutuwa ne" tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.


Kansa ya jinjina haɗe da cizon lips ɗinsa, "Eh ta wani wajenma kina da gaskia, amma ai bada wata manufa na baki ba, amma idan kinaga zaki takura to shikenan saikiyi abun da yadace" shima yayi maganar da iya gaskiarsa.


Daga haka dukansu basu sake ce da junansu komaiba, har suka iso cikin makarantar, yauma har gaban lecture hall ɗin su ya kaita, sai da kuma yaga shiganta cikin hall ɗin kafun yayi tafiyarsa.


Koda aka tashi yauma shiya zo da kansa ya ɗauketa, sai dai tunda suka kama hanya harsuka isa gida babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu.


A daidai ƙofar gidan su ya tsaida motar, haɗe da juyo da kallonsa gareta ƙoƙarin fita tasomayi daga cikin motar, cikin wata irin murya mai sanyi yace "Inason magana dake"


Kallo ɗaya tayi masa ta kau da kanta gefe, "Wace irin maganace ?"


"Maganace mai matuƙar mahimmanci , amma kuma tana buƙatar ishashshen lokaci " Doctor yaƙare maganar yana mai duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.


"Inajinka" Zahrah tafaɗa a taƙaice,


"Bakina jina zaki ce ba, hankali da tunaninki nakeso kibani "


Gyara zamanta tayi haɗe da ɗan satar kallonsa, batare da tace komaiba.


Kwantaccen sajen dake kan kumatunsa ya shafa, haɗe da cewa " No kada kiyi zaton wani abu zance, dama alluranki ne banƙara sa miki ba, kuma akwai matsala idan banyimiki su ayau ba!"


Gaba ɗaya idanunta ta ƙwalalo su waje, yayinda tsoro yacika zuciyarta, "Dan Allah kayi haƙuri wallahi na warke, yanzu banajin komai ajikina!" taƙare maganar lokacin da muryarta ke rawa, alamun zatayi kuka.


"A'a ni gaskia banyarda da cewa kin warke ba, saboda naga kina yawan sanya kanki a damuwa kuma jiya ma dana riƙe hanunki naji zazzaɓi a jikinki, don haka kawai zan ƙarasa miki yanzu" yaƙare maganar yana mai shirin buɗe wani ɗan ƙaramin drower dake cikin motar, take allurai suka bayyana, ai a ɗari Zahrah ta buɗe murfin motar haɗe da rugawa zuwa cikin gida, ko tsayawa ɗaukar jakarta batayi ba.
Dariya sosai Doctor Sadeeq yasanya, hadda riƙe ciki, shi dama burinsa yaga yanayin tsoronta, domin idan tana cikin wannan yanayin tsoron sosai take burgesa, ɗaukar jakar nata yayi haɗe da fita acikin motar kai tsaye yanufi cikin gidan. Yana sallama Inna ta tarbesa da fari'a, haɗe da cewa "Ai dama nasan tare kuke domin daganin yanda tashigo a guje nasan cewa ba ita kaɗai bace" ɗan guntun murmushi yayi haɗe da cewa " waifa dan nace zanmata allurane, shine duk tabi ta ruɗe, kuma yau bazan bar gidannan ba harsai na mata alluran nan, ko yakikace Inna?"


Idanu Zahrah tasake gwalowa jin abun da yake cewa, gaskia ita daya mata allura gwamma yabata magani amma sam batason allura, kuma ita taji sauƙi, amma su sundage akan cewa wai bataji sauƙi ba, kafun ta gama zancen zucin da takeyi taji muryarsa a bakin ƙofar ɗakin yanacewa Inna ta ɗauko masa ita....


(Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru, muna biki ne, yauma a daddafe nayi muku typing bacci nakeji)


*30/November/2019*


*Voted, Comment & Share please....Follow me on wattpad @fatymasardauna



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
Phatymasardauna



*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*


*🌈Kainuwa Writers Association*


{United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*(Ina mai baku haƙurin rashin jina kwana biyu da kukayi, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba)*


*Chapter 44 to 45*



Sake matse jikinta tayi ajikin bango, haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.


"ZAHRAH!" taji muryarsa yana ƙiran sunanta, cikin tsoro da ɗar ɗar, ta buɗe ƙofar ɗakin nata, kallo ɗaya yayi mawa cikin idanunta yakau da kansa gefe, domin kuwa wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, gaskia Zahrah tana da abubuwan ɗaukar hankalin ɗa namiji da yawa a tattare da'ita.


Batare da yakuma kallonta ba, ya miƙomata jaƙarta dake riƙe a hanunsa, da sauri ta fusge jakar haɗe da komawa cikin ɗakin ta,ta kuma datse ƙofar, murmushi kawai Doctor Sadeeq yayi haɗe da girgiza kansa, kallonsa yakomar ga Inna, cikin girmamawa yayi mata sallama, bayan ya cika mata hanunta da alkhairi, cike da farinciki Inna tayi sallama dashi, don tsabar daɗi ma har kusan ƙofa ta rakasa, tana mai zabga masa godiya.


Tafiya yake amma shi kaɗai yake murmushi, sosai Zahrah take burgesa, yanason komai na yarinyar, fushinta, dariyanta, tafiyarta, nutsuwarta, dama duk wani abu nata, tabbas Zahrah tana ɗaya daga cikin irin matar da yake fatan mallaka a matsayin matarsa ta sunna, ko dai zai jarrabane ?" ya tambayi kansa, saurin dukan seterin motar tasa yayi haɗe da cije laɓɓansa, "Ka dawo cikin hankalinka Sadeeq, maikake shirin aikatawa ne haka?" yatambayi kansa a fili.


"No baikamata nayi haka ba, dole zanyi haƙuri !" yafaɗi hakan cikin karyewar zuciya, dai dai lokacin kuma ya iso gaban makeken gate ɗin gidansu, mai gadi yana gama wangale masa gate ɗin ya cusa motar tasa zuwa cikin gidan.


Saida tagama ƙaremawa wayar kallo kafun ta danna madannin da zai sanya wayar ta kawo haske, nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da jingina bayanta da jikin bango, "Yazama dole kikawo sauyi acikin rayuwarki Zahrah, kada ki bari abunda Zaid yayi miki, yazama sanadiyar lalacewar duk wani farinciki dake cikin rayuwarki" zuciyarta ta faɗa mata hakan cike da ƙarfafa mata guiwa, "Amma tayaya hakan zai kasance, bayan banda wani ginshiƙi dazai taimakamin ?" Zahrah tatambayi kanta, sake gyara zamanta tayi haɗe da ɗaukar wayarta, kai tsaye tashiga wajen dazai sadata da apps ɗin wayar, Word Charm shine game ɗin daya ɗauki hankalinta, duk cikin apps ɗin dake wayar, dama tanason game ɗin, don haka kaitsaye tashiga tasomayi, take taji kewa da kaɗaicin da take ji sun soma ragewa, a wannan rana dai Zahrah batayi wani dogon tunani da takura kanta ba, dazaran taji ta takura zata ɗauki wayarta tasoma buga game, idan ta gaji da buga game ɗin kuwa, sai ta shiga Instagram shima sosai yake rage mata kewa (nima haka, lol)..


Tayi kyau sosai cikin blue rover gown ɗin dake jikinta, wata baƙar lufaya ta sanya a jikinta wanda yataimaka wajen ƙarawa shigar tata kyau da armashi, batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, ta dai shafa man leɓe dakuma kwalli, amma duk da haka tayi kyau, dama mai kyau ko baiyi kwalliya ba kyawunsa baya ɓuya.


Kasancewar yau baza su jima a makaranta ba, yasanya bata ɗauki jakaba, sai wasu ƴan littatafai da ta ɗauka a hanunta, sai kuma wayarta, koda ta fito tsakar gidan zaune a bakin murhu ta iske Inna tana tuyan ƙosai, wanda Baffa yace ayi na karyawa.


"Inna ni zanwuce makaranta" Zahrah ta faɗa tana mai ƙoƙarin gyara zaman lufayan dake jikinta.


"Bazaki tsaya ki karyaba Zahrah"
Baffa dake fitowa daga cikin ɗakinsa ya faɗa.


Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da shafa cikinta "Banajin yunwa sosai Baffa, kuma ina tsoro kada na makara!"


"Eh kina da gaskiya, kinga kuwa tun ɗazu likita, yazo yana jiranki, bayanda banyi da shi ba akan yashigo, amma sam yaƙiya, don haka gwamma ki hanzarta, a dawo lafiya " Baffa yaƙare maganar yana mai yunƙurin komawa cikin ɗakinsa.


"Ameen Baffa nagode!" Zahrah tafaɗa cike da farinciki, domin kuwa karo na farko kenan a rayuwarta da taga tsananin kulawan Baffa a kanta.


Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushinsa, ga mamakinsa sai yaga itama ta sakar masa murmushi, wanda yayi matuƙar taɓa masa zuciya, domin kuwa bakaɗan ba tayi kyau, da tana murmushin.


"Saiyanzu ki ka ga daman fitowa? kinshanyani kamar kin aje dutse" Doctor yafaɗi maganar yana mai turo baki gaba, tamkar ƙaramin yaro.


Dariya sosai Zahrah ta shiga yi, domin yanayin yanda yayi maganar yazama dole wanda ya gani ya dara, hangame baki Dr yayi yana kallon yanda take dariyan, abun da bai taɓa gani ba kenan, tun haɗuwar su da'ita, bai taɓa ganinta tana dariya ba sai yau, ashe ma duk kyawunta da yake gani, bai ga komai ba, domin da tana dariyan tafi masa kyau.


Hanunta tasanya ta toshe bakinta, haɗe da tsagaita dariyan da takeyi, kallonsa tayi haɗe da cewa "Bakaga yanda kazama yaro ba dakana maganan nan, tamkar ɗan shekara takwas!"


Murmushi yayi haɗe da jefamata hararan wasa, cikin yanayin da yayi magana ɗazu yakuma cewa "Shine kikemin dariya ko? sai na faɗaki da mamana!" ai kamar yaƙara mata fower'n da riyan nata ne, nan take taci gaba da dariyanta, hadda ɗan guntun ƙwalla a idanunta, wani irin sanyi da nishaɗi yaji yana huda zuciyarsa, tabbas bashida wani buri da yawuce yaga Zahrah tana cikin farinciki Alhmdlh, yau gashi ta sanadiyarsa tana dariya dakuma nishaɗi,


"Kayi haƙuri, bazan sake shanyaka ba, amma gaskia ka iya shagwaɓa da yawa!" Zahrah tafaɗa dai dai lokacin da tayi mawa kanta mazauni acikin motar, haryanzu dariyane kwance akan fuskarta.


"Wato dai yau mugunta kike ji dashi, dariya hadda hawaye!" Doctor yafaɗa cikin nishaɗi.


"Bahaka bane, kai ɗinne dai kawai kabani dariya!" itama ta basa amsa cikin nishaɗi.


"Dagaske kike, saboda ni kike wannan nishaɗin? " Dr ya tambayeta cike da zaƙuwa, duk da kuwa cewa yasan sabo da shiɗinne take nishaɗin.


"Eh mana, saboda kaine, kasan kaban dariya sosai, kuma nasan bama ni kaɗaiba, duk wacce takalleka a irin wannan yanayin dole zatayi dariya"


Ajiyar zuciya Dr ya sauƙe haɗe da murza key ɗin motar, suka ɗau hanyar da zata sadasu da titi.


"Idan kina dariya kinfi ko yaushe kyau ƴan mata na!" Dr yafaɗa cikin muryar nutsuwa.


Saurin maida kallonta garesa tayi, jin abun da yafaɗa tayi kamar wani almara, sai kuma taga yanayinsa tamkar bashine yayi maganar ba.


Yi tayi itama kamar bataji mai yace ba, mai da kallonta tayi ga titi, tana mai kallon yanda ababen hawa suke gudanar da hada hadansu.


"Maiyasa ki ka ƙi cin abinci? ko kinfiso ki zauna da yunwa ne?" Doctor ya jefo mata tambayar da batayi zato ba.


Kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kanta gefe, "Banjin yunwa ne, sannan kuma banaso na yi latti"
tafaɗi maganar a taƙaice.


Baice da'ita komaiba, saima buɗe ɗan ƙaramin drowern dake jikin motar yayi, wani haɗaɗɗen cake dake cikin wani ɗan ƙaramin kwali ya ciro, haɗe da ɗaura mata akan cinyarta, " Kici, kuma banson musu" yanayin yanda yayi maganar zai tabbatar ma da cewa, ba wasa yake ba.


"Nagode, amma zanci idan muka fito a lecture" itama ta faɗa kai tsaye.


"Yanzu nakeso kici, umarnine bawai shawara ba" yakuma faɗi maganar cikin yanayi mai nuni da cewa da gaske yake maganar.


Batason yi masa musu, domin koba komai yayi mata halacci a cikin rayuwarta, a hankali take gutsuran cake ɗin tana kaiwa bakinta, duk da cewa cake ɗin yayi mata daɗi.
Duk abun da takeyi yana lure da'ita, yanayin yanda take tauna abincin shiyafi komai burgesa.


Saida taci cake ɗin fiye da rabi, kafun ta dawo da kallonta garesa, "Naƙoshi" tafaɗa tana mai yatsine fuska.


"Dole sai kin cinye, domin kuwa ni idan nabawa mutum abuna, bai isa yacemin ya ƙoshi ba, dole sai yacinye koda kuwa ya ƙoshin"


Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa "Dagaske nake naƙoshi, amma da alama dole kakeson min"


"Dolen dole ma kuwa" yafaɗa dai dai lokacin da yagama parking motar tasa, domin kuwa harsun kawo cikin makarantar tasu, hanu ta ɗaura akan murfin motar da niyar buɗewa ta fita, tuni ya dannawa ƙofofin luck, saurin kallonsa tayi domin bata fahimci hakan da yayi me yake nufi ba.


"Babu inda zakije, matuƙar baki cinye cake ɗin nan ba" yafaɗi hakan yana me jingina bayansa a jikin kujeran da yake kai.


Ƙwaɓe fuska Zahrah tayi cikin sigar lallashi, tace "Kayi haƙuri, naƙoshi, idan naci da yawa, bazan iya karatu yanda ya kamata ba!"


"Um,Um, naƙi wayon, saura kaɗanne fa please kicinye shi mana Zahrah!" Doctor Sadeeq yaƙare maganar cikin lallashi.


"Um, Um, na ƙoshi, gaskiya idan naci zai cutar dani, zanyi ƙatuwa da yawa, ni kuma banaso nayi ƙatuwa!" cikin zallan shagwaɓa Zahrah tayi maganan.


Dariya sosai Dr Sadeeq ya sanya, domin kuwa maganar Zahrah ta bashi dariya, wai ita bataso tayi ƙatuwa hmm.


"To ai yaune kawai, kuma kinga bazakiyi ƙatuwa ba, nima banso kiyi ƙatuwa da yawa, amma inaso kiyi ƙatuwa kaɗan!" yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya isa sanyawa mutum mutuwar jiki.


Batace dashi komaiba, domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, ɗaukan ragowan cake ɗin tayi, tashiga turawa acikin bakinta, tamkar wacce aka bawa guba.
Dariya Doctor Sadeeq yashiga yi mata ƙasa ƙasa, domin kuwa yanda takecin cake ɗin, dagani kasan dole a kayi mata bawai a son ranta bane. tana cinyewa ya miƙomata goran ruwa, ai kuwa ba musu ta karɓa ta shiga sha, domin dama duk cake ɗin ya shaƙeta.


Cikin yanayi na shagwaɓa da ɓata fuska tace " Na cinye yanzu zan iya tafiya!"


Dariya Dr yayi haɗe da cire luck ɗin da yasanyawa ƙofofin motar "Zaki iya tafiya, amma kikula da kanki sosai, sannan idan kun fito a lecture wani zai kawo miki saƙo daga nine ki amsa"


"Wani saƙo?" Zahrah ta tambaya
End Ads