yayi ba, har ɗaki suke zuwa su duba Zahrah, sukuma tayasu murna.
Hanyar da Hajiya taga ya miƙa ne yasanyata cewa.
"Wai ina zaka damu ne Sadeeq?"
Da compidence ɗinsa ya juyo gareta haɗe da cewa. "Gidana mana Hajiya"
"Gidanka? to ba gidanka zamuba, gidana zamuyi, hauka kake na ɗauki yarinya da ɗanyen jiki, na baka? wama zai tsaya ya kula da ita? maza juya akalar motarnan" Hajiya tafaɗi haka babu alamar wasa akan fuskarta.
Sam bahaka yasoba, amma babu yanda zaiyi, shikenan shi baza abarsa yaji ɗumin matarsa dana ɗansaba, haka yata ƙunƙuni acikin ransa shi kaɗai, har suka isa gidan Hajiya.
Abinci mai rai da lafiya Hajiya ta kawowa Zahrah, ga kuma gasashshen nama, bayan taci abincin Hajiya dakanta, tasakeyi mata wanka.
Zama tayi agaban mirror tashafe jikinta da manta me daɗin ƙamshi, powder tashafa afuskarta, bata tsaya nanba harda janbaki tashafawa laɓɓanta, ga kuma kwalli da ta sanyawa cikin idanunta, mascara ta ɗauko ta zizira akan eye lashes ɗinta, take fuskarta taƙarayin kyau. Wani riga da sket na material me tsada tasanya ajikinta, take takoma ƴar baby kamar yanda take da, dogon gashinta ta kanannaɗe a bayanta, haɗe da hayewa gado, zataci gaba da bacci, miƙo mata yaron Inna tayi haɗe da cewa "Wani kwanciya kuma zakiyi bayan baki bawa yaron nono ba?"
Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, da ƙyar ta iya ciro nonon nata ta kai bakin yaron, yana kamawa ta runtse idanunta da ƙarfi, saboda wani zafi da taji, haka dai ta ɗan daure, shikuwa yaron sai zuƙeta yake, gajiya tayi dajin zafin ta cire nonon abakinsa, kwantar dashi tayi, itama kana ta kwanta agefensa, baccin gajiya ne ya kuma ɗaukarta...
Idan dai hartaji sauƙan numfashinsa akan wuyanta, to yazame mata dole ne farkawa daga baccin da take, yanzu ma sauƙan numfashin nasa taji adai dai saitin kunnenta, a hankali take ware idanunta harta sauƙesu akansa. Murmushi yasakar mata haɗe da ɗaura kansa akan ƙirjinta.
"INA SONKI!!!" yafaɗa murya a sanyaye....
*(Insha Allah gobe zanmuku update, yau naso nayi da yawa, to wallahi tsoron editing nake, amma Insha Allah gobe kujira sabon posting, maybe ma yanzu kullum zanna baku update saboda mugama book ɗin da wuri)*
*28/February/2020*
*✅OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna
#Love
#Romance
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
*WATTPAD*
@fatymasrdauna
*CHAPTER 115*
"NIMA INASONKA!"
Tafaɗa tana me lumshe idanunta. Iskan bakinsa ya hura mata akan fuskarta, haɗe da sake rungumeta, ɗayan hanunsa yasanya ya shafi kan jaririn nasa, dake ta bacci. Murmushi Zahrah tayi ganin yanda Dr.Sadeeq ya kafe yaron nasa da ido. Hajiya da Inna ne suka shigo cikin ɗakin atare, da sauri Zahrah ta janye jikinta daga na doctor, shima a kunyace ya sauƙa daga kan gadon yana sosa kai.
"Hmmm Allah yashirya, Inna kina gani ko, wai da ahakan yakeso na basa ita" inji cewar Hajiya.
Murmushi kawai Inna tayi batace komai ba. ( Su Inna anzama nitsaljin🤣) Kallon Doctor Hajiya tayi haɗe da cewa "Zo muje inason magana dakai" babu musu yabi bayanta suka fice daga cikin ɗakin.
Zama tayi akan kujera haɗe da maida hankalinta garesa.
"Me dame kake shiryawa sunan nanne? sannan kuma da wani suna kayiwa yaron huɗu ba?"
Murmushi ya ɗanyi haɗe da cewa "Ai nagama shirina tuntuni Hajiya, dama lokaci kawai muke jira, sannan kuma dama tuntuni sunan babanta nake son sawa yaron, dashi kuma nayi masa huɗu ba"
Hajiya tace "Masha Allah, To Allah Ubangiji ya rayasa, hakan da kayi kuma ka kyauta, tashi kaje dama maganan da zamuyi kenan"
Miƙewa yayi haɗe da yi mata sallama yafice daga cikin falon.
Lokacin da Husnah tazo ganin Baby kusan haukacewa tayi, sai santin yaron take wai yayi mata kyau sosai, komai nasa irin na babansa, ga idanunsa kyawawa, itadai Zahrah dariyanta kawai take, saboda itama Husnan tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki.
Akwatuna guda biyu Dr.Sadeeq ya kawo wa Zahrah, ɗaya nata ɗaya na baby'nsa wai kayan barka, kayane masu kyau da tsadar gaske sosai ya kashe kuɗi, wai ahakanma wasu kayan nanan zuwa.
Kulawa Zahrah take samu a wajen Hajiya sosai, idan kaganta ma kamar ba itace ta haihu ba, sosai jikinta ya murje, tasakeyin fresh, hasken fatarta ma sosai ya ƙaru, komai nata ya cika, taƙara kyau akan nada, shikansa Dr.Sadeeq idan yaganta, ko son ɗauke idanunsa akanta bayayi, saboda yanzu tasake zama wata mace ta musamman, duk inda ta zauna kuwa ƙamshi take rabawa.
Ranar suna yaro yaci sunan baban Zahrah wato Adam, za'ana ƙiransa da (Asad) lokacin da labarin sunan da aka sawa yaro yazo kunnen Zahrah sosai taji daɗi, wani irin farinciki taji acikin ranta, girman Doctor kuwa ya ƙaru acikin idanunta, ta tabbatar cewa shiɗin mai so da ƙaunarta ne.
Da sassafe meyi mata meckup tazo ta tsantsara mata ado, sosai fuskarta tasha kwalliya, wani haɗaɗɗen lace orange and milk colour tasanya ajikinta, wanda yaji ɗinkin riga da sket irin 12 piecess ɗin nan, sosai kayan sukayi mata kyau, domin sunja kuɗi wajen sayansu da ɗinkasu, kowa yaga Zahrah da babynta saiyace masha Allah. Saboda sunsha kyau sosai. Hidima sosai akayi tundaga kan abinci da abun sha, har izuwa abubuwan da za'a rabawa baƙi, akwati guda biyu Hajiya tayiwa Zahrah da ɗanta, haka Baffa ma akwati yayi mata Inna ma zagewa tayi tayiwa Zahrah akwati shaƙe da kaya, Auntie Raliya ma akwati ta mata, sosai Zahrah tasha kaya, har rasa inda zata sa kayan tayi, ana cikin haka saiga kayan Dr.Sadeeq sun iso, akwatuna huɗu, biyu natane shaƙe da kaya, sauran biyun kuwa na yarontane, bata gama mamakin irin dukiyar da Dr.Sadeeq yakashe mata ba, saiga Aunty Raliya tana rangaɗa guɗa, hanunta riƙe da key, danƙawa Zahrah key ɗin tayi ahanunta, haɗe da cewa "Ungo amsa kyautace ta musamman daga mijinki, ya baki kyautar gidansa dake cikin asokoro" mamakine ya kusan kashe Zahrah
"Gida kuma Aunty?" ta tambayi aunty Raliya don tayi tunanin ko kunnuwanta ne basu jiye mata da kyau ba.
"Ƙwarai kuwa gida, saima kinga gidan, don gidane me tsananin kyawun gaske, yafa kashe kuɗi sosai wajen ƙawata gidan" Inji cewar Aunty Raliya.
"A'a Aunty gaskiya nikam banaso, wani irin kyautane haka? hidimar da Doctor yakeyi dani tayi yawa, daga haihuwata zuwa yau yakashe kuɗi yafi 3 million fa Auntie, yanzu kuma yace yabani kyautar gida suku tum, inajin tausayinsa Aunti banason nazama rauni acikin arzikinsa" Zahrah tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta.
Murmushi Auntie Raliya tayi haɗe da sanya hanu ta dafa duka kafaɗun Zahrah.
"Kada ki damu Zahrah, shi ɗinfa mijinki ne, kuma kome zaimiki aduniyarnan bazai biyaki ba, kamar yanda kema bazaki iya biyansa duk abun daya miki ba, saboda haka babu wani abun damuwa don yamiki wannan kyautar, kin cancanci hakanne agareshi, don haka amshi makullin gidanki, ke dai kawai kiyi masa godiya, irin wacce ta dace" Aunty Raliya ta faɗi haka tana me damƙawa Zahrah makullin gidan ahanunta.
Kuka Zahrah ta fashe dashi tana jin ƙarin ƙaunar mijinnata na huda mata zuciya, lallai yazama dole agareta taƙara ƙaimi wajen kyautata masa.
Yamma nayi aka haɗa walima me rai da lafiya, bayan malama tazo tagabatar da wa'azine akayi ciye ciye, aka kuma sha drinks, duk wanda yazo sunan kuwa babu wanda baisamu kyaututtuka ba, abun sai dai ace Alhamdulillah, kafun magriba tuni mutane sun watse, gida ya saura daga Hajiya sai Zahrah da kuma Aunty Raliya.
Wanka tasakeyi ta tsantsara ado cikin wani irin meterial me kyau da tsada, wanda yana cikin kayan da Doctor ya ɗinka mata don fitan suna, doguwar riga akayi mata wanda ya matuƙar kama jikinta sosai, dogon gashinta dayasha saloon ta kanannaɗe atsakiyar kanta, ba abun dake fita ajikinta sai ƙamshin humra dana body spray.
Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan wayarta tashiga kan whatsapp, yaronta kuwa tuni dama yana wajen su Hajiya dake zaune a falo suna hira, Sadiya me aikin Hajiya ce tashigo cikin ɗakin haɗe da sanarwa Zahrah cewa wai tayi baƙo yana falo.
Jitayi gabanta yaɗan faɗi, amma saita dake tace da Sadiyan tace da baƙon tana zuwa.
Mayafi ta ɗauka ta yafa ajikinta, kana ta zura flat shoe ɗinta, tafice daga cikin ɗakin.
Su Hajiya tasamu zaune afalon, sai kuma wani, wanda bata ma taɓa ganin fuskarsa ba. Kafun takai ga gaishesa, shiya ɗago mata gaisuwa, amsawa tayi tana ɗan murmushi, gyara tsayuwansa yayi haɗe da cewa..
"Saƙone dama akabani nakawo miki, yana waje, idan ba damuwa muje saiki gani"
Kallon tsoro tashiga yi masa, saboda batasansa ba balle tasan wanene ya aikosa.
"Badamuwa, Raliya rakata sai kuje kuga saƙon ko"
Hajiya tafaɗi haka, don ta lura da tarin tsoron daya bayyana akan fuskar Zahrah'n.
Hakan kuwa akayi tare suka fita da Aunty Raliya.
A compound ɗin gidan suka tsaya gaban wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar mercedes maroon colour, mutuminne ya bubbuɗe ƙofofin motar, take kayan dake shaƙe acikin motar suka bayyana, ɗan makulli ya miƙowa Zahrah haɗe da cewa
"Ranki ya daɗe gashi ni nacika umarnin da aka bani, wannan kyautace daga megida na, yace na ce miki Allah ya raya"
Mamaki haɗe da al'ajabi ne suka kama Zahrah da Aunty Raliya.
"Kyauta daga me gidanka kuma? wayeshi to?" Zahrah tayi masa duka waƴannan tambayoyin cike da son jin amsa, haɗi da kuma mamaki, gani take kamar mutumin baida cikakken hankali.
Murmushi kawai ɗan aiken yayi haɗe da sake miƙo mata makullin motar yace
"Kiyi haƙuri bai bani damar sanar miki dashi ɗin kowaye ba, amma yace dan Allah ki karɓa"
Ta buɗe baki zatayi magana kenan motar Dr.Sadeeq ta kutso kai cikin gidan.
Kasa cewa komai tayi har Dr.Sadeeq yafito daga cikin motarsa, ya ƙaraso garesu, kallonsa Zahrah tayi shima kallonta yakeyi.
"Hajiya ga makullin ni zan wuce" wannan mutumin yafaɗi haka, yana sake miƙa mata ɗan makulli.
"Ko ma waye ya aikoka, kace masa banaso, don bana buƙata" tafaɗi haka tare da juyawa daniyar komawa inda ta fito.
"Zahrah!"
Sunanta da Dr.Sadeeq yaƙirane yasanyata tsayawa cak haɗe da juyowa tana kallonsa.
"Zoki amsa, ki kuma yi masa godiya" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me karantar yanayinta.
Cike da mamaki tace "Amma..."
"Banaso kice komai ki amsa kawai nace" yakatseta daga maganar da take ƙoƙarin yi.
"To" kawai ɗan aiken yace kana ya juya yafice daga cikin gidan.
"Wai meke faruwa ne, waye ya aikosa?" Aunty Raliya ta tambayi doctor, don ta lura kamar yana da masaniya akan wanda ya aiko motar da cikinta ke shaƙe da kaya.
Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa "wani aminina ne dake zaune a Dubai, shine dana gaya masa ta haihu yayi mata wannan kyautar"
Dafe ƙirji Aunty Raliya tayi tare da cewa
"Lallai wannan koma wayeshi yanaji da naira, wannan motarfa zatakai 4million inma bata fi ba, ga kuma kayan dake cikinta, wanda suma kaɗai sun haura 1m, me kenan yake nufi?"
"Babu wani abun da yake nufi Aunty, haka dama shi yake kyautarsa, muje ciki ko" yaƙare maganar yana kallon Zahrah wacce ta daskare a wajen.
Cike da mamakin kyautar abokin Doctor ɗin Aunty Raliya taja ƙafanta takoma falon Hajiya, Zahrah ma jikinta a sanyaye tabi bayanta, shima falon yanufa, yanda yaga tana tafiya asanyaye ne yasanyasa yin murmushi kawai.
Bata tsaya a falon ba direct ɗakin dayake masauƙinta ta wuce, tsayawa tayi a gaban mirror zuciyarta cike da tarin tambayoyi kala kala, sam bataji zuciyarta ta aminta da kyautar nan da'akayi mata ba, kwata kwata batama yarda cewa wai abokin Doctor bane ya bata. Tana acikin tunanin, yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama.
Amsa masa sallaman nasa tayi haɗe da zuba masa idanunta, dagani kai kasan tambayoyine cike a bakinta.
takowa yayi ya ƙaraso daf da ita, hanunsa yasanya ya jawota jikinsa, saida yashaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta, ya sauƙe ajiyar zuciya, kana yace.
"Kinyi kyau sosai"
Murmushi ta ƙaƙalo haɗe da cewa. "Nagode"
Cikinsa yashafa tare da cewa. "Yunwa nakeji sosai, nayi missing sweet cook ɗinki, please ko zaki kawomin abinci?"
"Meyasa kake barin kanka da yunwa? kasan banaso, yanzu me zakaci na kawo ma?" tatambayeshi cike da kulawa.
"Koma me idan kika kawomin ni mai iya ci ne" yafaɗi haka yana me zama a bakin gado.
Harta kusa fita daga cikin ɗakin sai kuma ta tsaya cak, haɗe da juyowa, idanunsu yafaɗa cikin na juna, domin dama shima kallonta yake.
"Waye ne yaturomin da mota? Nasan kasan ko waye, domin zuciyata tafaɗamin cewa, ba abokinka bane ya turo, kamar yanda kafaɗa a baya" tambayar da tayi masa kenan, cike da burin samun amsa agareshi.
"Baki yarda da abun dana faɗa ba kenan?" ya tambayeta yana me ƙara tsareta da manyan idanunsa.
Murya a sanyaye tace "Kayi haƙuri, bawai ina nufin kamin ƙarya bane, kawai dai naji zuciyata ce bata gamsu da amsar da ka bayar ga Aunty Raliya ba"
Murmushi yayi haɗe da cewa "Zuciyarki tafaɗa miki gaskiya, domin kuwa ba abokina bane yaturo kamar yanda na faɗa a baya"
Waro idanunta tayi, duk da zuciyarta ta raya mata cewa ba abokinnasa bane, amma kuma duk da haka bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba.
"Waye?" tatambaya murya na rawa.
"ZAID" yabata amsa ataƙaice...
(Nagaji kuyi manage, idan nasha ruwa zan ɗora daga inda na tsaya)
*29/February/2020/*
*✔️OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna
#Love
#Romance
#One Love My Wattpadians
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Chapter 116*
"ZAID!" ta maimaita sunan abakinta cike da tsananin mamaki.
Yanda yaga jikinta na ɓari shine abun daya basa mamaki, zallan tsoro ya hango kwance akan fuskarta, yayinda cikin idanunta kuwa, suka bayyana soyayyar dake kwance acikinsu, wato soyayyar ZAID, shi yasani ba tun yauba, bakuma zai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah na son Zaid, so ba irin na wasaba, so matsananci, amma kuma babu yanda zaiyi, dayana da iko to daya cire mata son Zaid acikin zuciyarta, amma wannan banasa bane, na Allah Ne, yasan Zahrah tana sonsa, amma soyayyar da takewa Zaid ta dabance, da ace zai iya, to daya danne zuciyarsa, ya miƙata ga Zaid, yasan hakan zai samarmusu da farinciki, ita da Zaid, amma kuma yasan koda yayi hakan to ba mafita bane, domin ayanzu yasan dole idan baya tare da Zahrah tayi kewarsa, yana sane da cewa yakafa mata tutar son sa, wanda bazata ankara da hakan ba, har sai randa yazama baya tare da'ita, baya fatan wata ƙaddara ta rabasu, amma yasani ko mai daren daɗewa sai sun rabu, saboda akwai mutuwa, koshi ko ita, watarana ɗaya dole zai bar ɗaya, yau idan baya raye, baya fata Zahrah ta auri wani namiji idan ba Zaid ba, tunaninsa yayi nisa, baisan da cewa ta ƙaraso inda yake ba, saida yaga ta zube a gabansa, tana kuka, cikin muryar kukan takecewa.
"Kada kamin haka doctor, wallahi ni banason duk wata kyauta da zatafito daga garesa, namantasa acikin rayuwata, banaso kuma nasake tunasa, kamayar masa da kyautarsa, bana buƙata farincikin da kake bani kaɗai ya isheni"
Tunda tafara maganan yake kallonta, ajiyar zuciya yayi, haɗe da kamo hannayenta, cikin murya me sanyi yace. "Kinsani bakyau maida hanun kyauta baya, meyasa to zakiyi haka? mekike tunani akan Zaid?" ɗan dakatawa da maganar yayi, tare dayin wani murmushi, kana ya miƙe tsaye, daga zaunen da yake.
"Kyautace kawai ya miki, ai atunanina hakan ba wai yana nufin wani abubane, bazan tilasta miki ba, amma nasan abundake cikin zuciyarki, don gashi har a idanunki sun nuna, so ba ƙarya bane Zahrah, haka kuma ba laifi bane, don zuciya na dakon so, wannan ma wata ƙaddarace, wanda babu wani wanda ya isa ya kauce mata" yanakai ƙarshen zancen nasa yanufi hanyar fita daga ɗakin.
Da sauri taje ta faɗa jikinsa, kuka take sosai, durƙusawa tayi haɗe da zube guiwowinta a ƙasa, kana ta riƙe rigarsa, kanta tashiga girgizawa, tana kuka tace. "A da na sosa fiye da yanda naso kaina, amma ayanzu baya acikin zuciyata kamar yanda kake tunani, Inasonka da duka zuciyata, bana fatan wata ƙaddara tazo wacce zata rabani dakai, kabani farinciki, kajiyar dani daɗi, kashayar dani zuman soyayyarka, bazan iya watsa maka ƙasa idanunka ba, kai mijinane wanda bayan kai bani da wani tamkarka, nasan kai ɗin me sonane, amma meyasa kayi haka? mai yasa kai da kanka, zaka amince da na karɓi kyautar wanda yazama silar rugujewar rayuwata?"
Durƙusawa yayi agabanta, haɗe da sanya hanunsa ya share mata hawayen dake gudu akan fuskarta, cike da kulawa yace. "Banason kukanki Zahrah, keɗin wata babban jigo kuma mahaɗi ne acikin rayuwata, nasan Zaid ya cutar da rayuwarki, amma kuma hakan bazai hana ki amshi kyautarsa ba, ayanzu kowa yasan cewa ke matatace, saboda haka Zaid bazaiyi miki kyauta da wata manufa ba, kuma kafun ya miki kyautar saida ya tambayi amincewata tukunna, nakuma amince masa, nayarda da Zaid Zahrah, nasan idan duka mutanen duniya zasu taru su cutar dake, to Zaid bazaiyi hakan ba, haka kuma idan ni zan iya cutar dake, to ina tabbatar miki idan Zaid yasan da hakan, to bazai bari na cutar dake ba, Zaid ɗin da kikasani ada bashine wanda yake a yanzu ba, kada kiyi tunanin wai ko zanji haushi akan kyautar da Zaid yayi miki, niba jahili bane Zahrah, haka kuma halina ya banbanta da na wasu mazan, ni mutum ne me saurin fahimta, sannan kuma abune mawuyaci nayiwa wani na mummunan zato, agurin wasu mazan, hakan zai iya zama matsala, amma a wajena hakan ba komai bane, tunda nasan cewa keɗin