yayi haɗe da kallon Dr.Sadeeq wanda da'alama tunaninsa baya jikinsa.
"Meyake faruwa ne Likita? kashiga kakuma fito da ɓacin rai, ina Zahrah'n takene me yasameta?" cikin damuwa Baffa yayi tambayar domin shi gaba ɗaya kansa ya kulle.
Daure zuciyarsa yayi haɗe da cewa "Tana nan lafiya, gobe da safe zamu zo mu ɗauketa"
Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe me ƙarfi yagodewa Allah da ba wani abun bane yasamu Zahrah, to amma ae da anbarsu sun ganta...
A ƙofar gida Dr.Sadeeq ya sauƙesu haɗe dayi musu saida safe yaja motarsa yayi gaba..
Suna shiga gida Inna ta kalli Baffa haɗe da cewa "Anya kuwa Malam bakaganin cewa akwai matsala?"
"Bawai gani nakeba, tabbas ma nasan akwai matsala Salame, sai dai fatana ɗaya shine Allah yatsare Zahrah, amma tunda Likita yace gobe da safe zamu koma asibitin, saimu jira zuwa goben idan Allah yakaimu"
"To Allah yakaimu" Inna tafaɗa jiki a sanyaye... Da "Ameen" kawai Baffa ya amsa.
Kamar yanda Zaid ya kwana a zaune, haka Dr.Sadeeq yakwana juyi, gaba ɗaya kansa ya kulle, yarasa meke faruwa, baisan waye wannan gayen ba, amma tabbas yaji tsanarsa fiye da misali, amma babban abun tambayar shine me yasamu Zahrah har aka kawota asibiti? sannan kuma meke tsakaninta da wannan mutumin? tambayar dayake buƙatar a amsa masa kenan, amma babu wanda zai amsa masa, tambayar da ta kuma hanasa bacci kenan...
Ƙarfe bakwai na safe Zaid yasa aka turo masa nurses guda biyu, suka zo dankula da Zahrah, saboda yana buƙatar yaje gida yayi wanka.....
Tamkar amafarki haka fyaɗen da yayi mata yasake dawowa cikin idanu da ƙwaƙwalwarta, wani irin nishi tayi haɗe da sakin ƙara mai sauti, lokaci guda kuma ta ware idanunta da suka cika tab da ƙwalla, da sauri nurses ɗin nan sukayo kanta.
Kallon Nurses ɗin tashiga yi, haɗe da soma ƙaremawa ɗakin da take ciki kallo, tabbas idan ƙwaƙwalwarta bata juye ba, zata iya cewa nan ɗakin asibiti ne sannan kuma waƴan nan dake tsaye a gabanta nurses ne.
"Barkanki da tashi, me kike buƙata yanzu a kawomiki?" ɗaya daga cikin nurses ɗin nan ta tambayi Zahrah cike da kulawa...
"Idanunta dasuke zubar da ruwan hawaye, ta ɗaga ta kalli nurse ɗin haɗe da girgiza kanta alamar batason komai.
Hanun nurse ɗin takamo duka biyu haɗe da fashewa da wani irin kuka me ciwo, da'alama wani abu takeson faɗawa nurse ɗin.. Dai dai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, Zaid ne yasha adonsa sai zuba ƙamshi yake.
Tsayawa yayi cak daga bakin ƙofar sakamakon ganin yanda Zahrah take kuka..
"Bamuyi mata komai ba,ranka ya daɗe tashinta kenan tasoma rusa kuka" su duka biyu suka haɗa baki wajen faɗan maganar...
Tamkar wanda aka zuba mata narkakken dalma haka taji sauƙan kalamansa acikin kunnuwanta, rumtse jajayen idanunta tayi, ji takeyi tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta ta fito.
A hankali Zaid yasoma takawa zuwa gare ta.
"Zahrah" yaƙira sunanta dai dai lokacin daya ƙarasa kusa da'ita.. Tunkafun yagama rufe bakinsa yaji sauƙan wani irin gigitaccen mari akan ƙuncinsa, kafun ƙwaƙwalwarsa tagama tantance masa abun dake faruwa, yakumajin sauƙar wani marin aɗaya ɓangaren hagu na kumatunsa..
Kasa koda motsawa yayi saima hangame bakinsa da yayi haɗe da zaro idanu yana kallonta,, Gaba ɗaya marukan nan Zahrah ce ta shararawa Zaid akan fuskarsa..
Yanayin yanda idanunta sukayi ja kace barkono ko attarugu aka watsa mata a ciki.
"Kazone ka sake cutar dani? to gani kacutar dani, gani nace ka cutar dani!!" tafaɗi haka da wani irin tsawa..
Cikin matsanancin kuka Zahrah tasanya hannayenta duka biyu tashiga dukan sa, tako ina Zahrah ke kai masa duka tana kuka, ganin hanu bazai wadarta ba yasanya ta sanya bakinta, tashiga cizonsa a ƙirjinsa, hakama bai mata ba saida ta ɗauki wani ƙarfe dake kusa da'ita tashiga kwaɗa masa a jikinsa tana kuka me tsuma zuciya... Haka Zaid ya tsaya tamkar gunki Zahrah na cizo da yaƙushinsa, gakuma dukan da take kai masa, amma yakasa yi mata komai, yakuma kasa koda motsa hanunsa ne.. dai dai lokacin su Dr.Sadeeq suka shigo cikin ɗakin, turus suma sukayi sakamakon ganin abunda ke faruwa.
"Kasheni zaifi maka sauƙi aduniyar nan, akan ace kabarni da raina, natsaneka, dan Allah ka kasheni!!" Abun da Zahrah ke faɗa kenan tana kuka. Kowa a wajen tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, bakomai ke tashi a ɗakin ba face kukan Zahrah, tun tana dukansa da'iya ƙarfinta har ƙarfin nata yasoma ƙarewa a hankali ta sulale zuwa ƙasa, saboda kuka har shiɗewa take...
"Zahrah" Dr.Sadeeq yaƙira sunanta, cikin wata irin murya.. Jin muryan Dr akunnenta yasa taɗago kanta, tana ganinsa tsaye tatashi a guje haɗe da nufar inda yake da sauri tafaɗa cikin jikinsa haɗi da rungumesa ƙa ƙam,wani sabon kukan kuma ta sanya, haɗe da soma buga kanta akan ƙirjinsa..
Duka hannayensa shima yasanya ya rungumeta..
"Wayeshi?" Dr. Sadeeq yayi mata tambayar acikin kunnen ta..
"Shine wanda yaruguzamin rayuwata, shine yarabani da budurcina, shine yayi sanadiyar lalacewar farinciki na!!" Zahrah ta bashi amsa cikin matsanancin kuka, muryarta ko fita batayi da kyau tsabar kuka...
Iya kaɗuwa Dr.Sadeeq ya kaɗu dajin cewa wai wanda yayiwa Zahrah fyaɗe ne tsaye a gabansa, kallon tsana Dr.Sadeeq yashiga yi mawa Zaid..
Zaid kuwa tuni idanunsa sun rune sun zama jajur dasu, jikinsa har rawa yake, koda sau ɗayane baiji zafin duka dakuma marin da Zahrah tayi masa ba, babban abun da yayi masa zafi, shine yanda Zahrah taje jikin wani ta lafe. Tun da yake a rayuwarsa baitaɓa jin abun da yaji a yau ba... Takowa yashiga yi harzuwa inda suke tsaye ita da Dr.Sadeeq, hanunsa yaɗaga domin ya ciro Zahrah daga jikin Dr.Sadeeq. Da sauri Dr.Sadeeq ya tura Zahrah bayansa, haɗe da damƙe hanun Zaid wanda yakawo daniyar taɓa Zahrah..
"Babban kuskuren da zakayi a rayuwarka shine kayarda hanunka yasake taɓa jikinta, kayi na farko yakuma isheka, saboda haka ka kiyaye! " Dr.Sadeeq yafaɗi haka cikin matsanancin ɓacin rai...
Hanun Zahrah yakama haɗe da janta suka fice daga cikin ɗakin, da sauri su Inna ma suka rufa musu baya, saurin dafe saitin zuciyarsa Zaid yayi, wanda yakeji tamkar zatayi tsalle ta fito waje.. Jingina bayansa yayi da bango haɗe da lumshe idanunsa.. Zafi yakeji a ƙirji dakuma zuciyarsa, take wani irin ciwon kai da zazzaɓi me zafi suka sauƙar masa alokaci guda..
Dr.Sadeeq dakansa yasanya Zahrah a mota, wacce har yanzu kuka take, ataƙaice dai tsabar kuka numfashinta har ɗaukewa yake.... Saboda tsabar gudun da Dr.Sadeeq keyi cikin mintuna ƙalilan suka isa gida, kowa acikinsu yana cikin tashin hankali. Inna ce takama Zahrah takaita ɗakinta. Bayan minti kaɗan Inna tafito daga ɗakin Zahrah da sauri. "Likita temaka numfashinta yana shirin ɗaukewa, taƙi daina kukan" Inna tafaɗa a ruɗe.
ɗago Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da kai kofin ruwan bakinta, sosai tasha ruwan, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya, amma still hawaye na gangara akan fuskarta..
Idanunta dasukayi luhu luhu saboda kuka ta ɗago dasu takalli Dr.Sadeeq, saikuma tasake fashewa da kuka, haɗi da faɗawa cikin jikinsa tarungumesa ƙam, hanunsa duka biyu yasanya shima ya rungumeta, a hankali ya shiga hura mata kunnen ta, saboda hakan zai sa taɗan samu relief, koba komai kukan nata zai tsagaita. Har tsakiyar kansa yakejin kukanta.
Tsawon mintuna 15 yakai yana hura mata kunne, a hankali tasoma rage sautin kukan nata, bayan kamar mintuna 5 yajita shiru, sai sauƙar numfashinta da yake ji akan ƙirjinsa akai akai..
Yana duba fuskarta yaga tayi bacci, hawayene yaji suncika masa idanu, tabbas Zahrah taga ƙaddara a rayuwarta, wani irin tausayinta yakeji me tsanani, tabbas idan ya aureta zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya mantar da ita duk wani damuwa da tshin hankalin da ta tsinci kanta ciki, zai kuma yi iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin yabata farinciki me ɗorewa.
A hankali ya kwantar da'ita, haɗe da sanya hanu ya gyara mata dogon gashinta da ya rufe mata fuska. Yajima yana kallonta kafun daga bisani ya tashi yafita daga cikin ɗakin...
Zaune yasamu Baffa da Inna a tsakar gidan sunyi jigum. Yana fita suka tsaresa da ido da'alama bakinsu ɗauke yake da tarin tambayoyi..
Ajiyar zuciya ya yi haɗe da cewa "Tasamu bacci, kada ayi wani abu da zai tasheta, ni zan wuce office anjima zandawo"
Har bakin motarsa Baffa yarakasa bayan sun tattauna wata magana me mahimmanci....
Zaid ne zaune a cikin falon sa dake guest hause ɗinsa, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa yana cikin tashin hankali, kwalaben giyane zube a gabansa, guda uku daga cikin kwalaben duk ya shanye giyan dake a
cikinsu, ba abun dake gigita masa tunani da ƙwaƙwalwa kamar yanda Zahrah ta nunamasa tsana a fili ƙarara, kallonsa yakai ga hanunsa na dama wanda yake fidda jini, bakomai yajawo hakan ba face ƙarfen da Zahrah ta kwaɗa masa akan hanun,, runtse idanunsa dasuka kaɗa sukai jajur yayi, haɗe da cije laɓɓansa, wani irin zafi yakeji acikin zuciyarsa a duk sanda idanunsa suka hasko masa lokacin da Zahrah taje ta faɗa ƙirjin Dr.Sadeeq, jiyake kamar ya kurma ihu, ko zai samu salama acikin zuciyarsa.... Ahankali yamiƙe tsaye haɗe da nufar ɗakinsa, Da ƙyar yake iya tafiya, saboda abuge yake mankas, kai tsaye ɗan ƙaramin drowern dake kusa da gadonsa yanufa, wani tablet yaɗauko haɗe da ɓarewa kusan guda takwas ya watsa a bakinsa, haɗi da korawa da ruwan swan... Faɗawa kan gado yayi yana me rumtse idanunsa, "Natsaneka" shine kalmar da tafi ɗaga masa hankali aduk cikin kalaman da Zahrah ta faɗa masa. itace kuma kalmar da takeyi masa yawo acikin kansa, cikin wani irin yanayi Zaid yatashi tsaye haɗe da nufar wajen da yake aje kayan shafansa, watsi yashigayi da duk wani abu dake kan dressing mirror ɗin nasa, lokaci ɗaya yayi buji buji da ɗakinsa, yayinda ya fasa gaba ɗaya kwalaben turarensa, har sai da wasu kwalaben suka yankesa a hanu da ƙafarsa, amma don tsabar baƙin kishi ko zafi baiji ba, idanunsa Zahrah kawai suke hangomasa kwance a ƙirjin Dr.Sadeeq. Lokaci ɗaya yaji wani irin juwa ta ɗebesa, harsai da yariƙe bango, a daddafe yaƙa risa kan gadonsa ya kwanta, ji yayi kansa yasoma juyawa, yayinda idanunsa suka soma rufewa, yasoma ganin komai bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan idanunsa suka rufe ruf.....
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*25/December/2019*
*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
Ba'itace ta farka ba sai wajen ƙarfe ɗaya na rana..
A hankali take ware manya manyan idanunta da suka kaɗa suka zama jajur dasu, ba tun yanzu ta farka ba, kawai dai Allah ne be bata daman buɗe idanun nata ba sai yanzu. Tun farkawarta kuwa take cikin tsanani da kuma mamakin mutum mai taurin zuciya irin Zaid, lallai shiɗin yacika ɗan iska kuma shu'umi, duk da irin girman laifin da ya aika ta mata, hakan baisanya yaji ɗar ko kuma shakkan tunkarar ta ba, lallai shiɗin acikin ƴan iska ma daban yake,, haka nan taji gaba ɗaya zuciyarta ta ƙeƙashe takuma bushe, lallai tunda ya nuna mata shiɗin babban ɗan iska ne yakamata ace itama ta nuna masa iyakar iskancinsa, tunda har baiji kunyar tako ƙafa yazo gareta ba, to tabbas itama yakamata tacire kunya, wajen ganin ta koya masa hankali... Sai dai kuma kome zatayi bazata huce ba, saboda iyaka kuma maƙurar cuta Zaid yayi mata, ya mata illa dakuma tabon da bazata taɓa mantawa ba, harta koma ga mahaliccinta kuwa, Zaid ne ya surka mata farincikinta da wani irin mummunan baƙin duhu, ya katse mata jin daɗi da kuma walwalanta, ya lalata mata rayuwa a rana ɗaya, ya ruguza duk wani buri da fatanta, ya gwada mata ƙarfi ya amshi budurcinta cikin yanayi na tozarci, me yafi wan nan ciwo a rayuwar ƴa mace? tasan ƙiyayya amma kuma zafin ƙiyayyar da takeyi mawa Zaid na daban ne, tabbas idan da kisan kai yana da kyau a addinance to haƙiƙa ba abun da zai hanata kashe Zaid san nan kuma itama ta kashe kanta, saboda ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ba'irin ƙuncin nan bane da yake fita, lallai ƙuncin zuciyarta dawwa memme ne, sai dai kawai ta roƙi Allah daya sassauta mata.....
Hawayen da suka fito daga cikin idanunta suka gangaro ta gefen kumatunta ta sanya hanu ta share haɗe da miƙewa zaune, babu amfanin ɓata hawayenta wajen fiddasu, yanzu lokaci yayi da shine yakamata yayi kuka ba ita ba. Kayan jikinta tashiga cirewa, haɗe da ɗaura zani akan ƙirjinta kana ta sanya lufaya....
Tana fitowa daga cikin ɗakin nata, Inna ta kalleta haɗe da cewa.
"Yauwa Zahrah kintashi ko? ya ƙarfin jikin naki de?" alokaci ɗaya Inna tajero mata duka waƴan nan tambayoyin..
"Eh Inna na tashi, ko zan samu ruwan zafi inaso nayi wanka ne, gaba ɗaya banajin daɗin jikina, gashi ina so naje gidan su Husnah" tafaɗi maganar tana me ɗan rumtse idanun ta, saboda wani juwa da taji yana ƙoƙarin ɗibanta..
"Kinkuwa ci sa'a yanzu na ɗaura ruwan abincin rana, gashi can inaga yama tafasa saiki ɗiba, amma idan kin ɗiba ki ƙaramin ruwa acikin tukunyar" Inna tafaɗi haka tana meyi mata nuni da tukunyar abincin dake ɗaure kan murhu...
Sosai taji daɗin jikinta sakamakon wanka da ruwan zafi da tayi, bayan ta idar da Sallan Azahar ne, tayi mawa kanta mazauni akan katifarta haɗe da ɗaukan jakar kayan kwalliyanta, mai kawai tashafa sai kwalli da ta zizara a cikin idanunta, ko powder bata shafa ba...
Doguwar rigar atamfa irin me sauƙin kuɗin nan tasanya ajikinta, haɗih da ɗaura hijab akan kayan nata mai kalar blue, yakumayi shige da atamfarta saboda shima atamfar kalan blue ne dashi (shuɗi). Me kyau de me kyaune ko a yaya kuwa, duk da batayi kwalliya ba kuma fuskarta a kumbure take saboda kuka, amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba....
Kallon Inna dake ƙoƙarin sauƙe tukunyar abinci Zahrah tayi, tana me gyara zaman lufayar jikinta tace.
"Inna ni zan je gidansu Husnah, zuwa yamma zandawo insha Allah"
"Wani irin maganar zuwa gidansu Husnah kuma Zahrah? inace ɗazu ɗazun nan muka dawo dake daga asibiti, har kin yi sauƙin da zaki soma fita yawo?"
(Su Inna anfara soyayya da Zahrah fans, lol)
"Kada ki damu Inna yazama dole ne naje, amma bazan jima ba zandawo, dan Allah kada ki hanani zuwa Inna!" Zahrah ta faɗi haka cikin yanayi na nuna zaƙuwa.
"Shikenan tunda kin matsa, ai de kya tsaya kici abinci, idan yaso saiki tafi"
"A'a Inna banajin yunwa yanzu, idan nadawo zanci" takai ƙarshen zancen nata tana me nufar hanyar fita daga cikin gidan. Da kallo kawai Inna tabita harta fice daga gidan...
Tsayawa tayi tana kallonsa cike da mamaki, yayinda shima kallon nata yake cikin yanayi na mamaki...
Giransa ɗaya ya ɗage haɗe dayin murmushi.... "Ashe ma kinyi sauƙi, dana sani da ban bar aikin da nakeyi nazo duba kiba ae" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me takowa zuwa wajen da take tsaye.
Kunyarsa ne taji yakamata, sakamakon abun da yafaru ɗazu a tsakaninsu, wato rungumarsa da tayi, wanda tasan hakan ba abu bane me kyau haramunne, mace ko namiji su taɓa mutumin da ba muharrami'n su ba, duk da cewa ba'acikin hayyacin ta ta rungumeshi ba, amma tabbas hakan bai dace ba...
"Yade naga kina wani sunkuyar dakai kamar amaryar da aka kaita ɗakin mijinta" Dr.Sadeeq ƴafaɗi haka cike da zolaya.
Sai alokacin ta'iya ɗago kanta ta aika masa da
hararan wasa,,,,, " Yaushe kazo? kuma me yasa ka tsaya anan baka shiga cikin gida ba?"
"Ummm banjima da zuwa ba, dama inaso amin sallama dake ne, kinga bai dace ace koda yaushe ina shiga cikin gidanku kai tsaye ba, amma sai kuma naga kamar keɗin sauri kike zaki unguwa ko?"
Yaƙare maganar yana me leƙa fuskarta wanda ta sunkuyar da ita ƙasa.
Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da sanya haƙorinta na sama taɗan datse leɓenta na ƙasa..
"Yajikin naki?" yatambayeta don yaga bata daniyar basa amsan abun da yatambaya.
"Dasauƙi, dama ni lafiyata ƙalau" tabasa amsa a ta ƙaice..
"Eh hakane kuma dama kinsan wani lokacin, idan lafiya tayi mawa mutum yawa, takan iya sawa ya kwanta a gadon asibiti"
Saurin kallonsa tayi sakamakon jin abun da yace, "Lafiyan?" ta tambaya cike da mamaki.
"Eh itafa lafiyan, to baga example akan ki ba" yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya'isa ya tabbatar maka cewa zolaya ne kawai ke damunsa..
"Hmm" kawai Zahrah tace haɗi da ɗan satan kallonsa, aikuwa karab suka haɗa idanu, saurin ɗauke nata idon tayi.
Hmm yalura sarai kunyarsa takeji, kuma shiɗin ma kusan hakanne, kawai de dauriya dakuma shariya yafita, shiyasa ya share abun, amma shikansa yasan cewa ya aikata ba dai dai ba, saboda da ta rungumesa baikamata ace yabiye mata ba, kamata yayi ace ya ɓanɓareta daga jikinsa, sai de kuma babu yanda ya'iya saboda alokacin tana cikin halin buƙatar taimako, kum san nan shi be rungumeta don yaji daɗi ba.
"Inazakije ne haka, da rana tsaka?" yajefo mata tambaya.....
"Gidan su Husnah zani" ta basa amsa a taƙaice, saboda ba da kowani lokaci tacika son dogon magana ba...
Kallonsa tayi naɗan sakanni, kafun ta rausayar da kanta gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace "Dama kabarni, koda ƙafana ai zan iya zuwa, idan har bansamu abun hawa ba, balle ma