*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE9*
Kai tsaye cikin Zaria Maryamu ta nufa, tana hawa mota aka sauke ta a Maɗachi, shi ne daga nan ta hau machine ya kawo ta Ƙofan Kibo gidan Iya Samira
Lokacin tana tsaka da ƙulle-ƙullen kayan siyarwan ta, tana zaune a tsakar ɗaki ta ƙure rediyo, sai ganin Maryamun tayi ta faɗo mata daki ko sallama. "Maryamu, ke ce haka? Daga ina?" Tayi mata tambayoyin, bayan ta ɗaga kai ta ganta cike da mamakin zuwan nata
Ita kuma sai ta zauna a gabanta tana mai tanƙwashe ƙafa, fuskarta a kumbure tace, "daga gida mana."
Kashe rediyon Iya Samira tayi, kafin tace, "in ce dai lafiya ba wani abun ne ya faru ba? Ke kaɗai kika zo?"
Kai ta gyaɗa mata tana tura baki ta ƙi cewa komai
"Buɗe baki mana ki yi min bayani, ko wani abun ne ya faru a ƙauyen? Kin ɗaga min hankali."
Sai ga hawaye shaaa a fuskarta, cikin muryan kuka take cewa, "ba Baba bane zai yi min auren dole, shi ne na gudo nan."
"La haula bisha'atil lah! Auren dole kuma Maryamu? Shi Harunan yace zai miki auren dole?"
"Eh mana Iya, Ni kuma wlh tallahi bazan zauna ba, Ni karatu nake so ba aure ba; ana yin abu dole ne?"
"Yo ai laifin nasu ne ba naki ba Mero, in ba don ƙauyen ba taya zai yi miki auren dole tunda kin nuna ba kya so? Maza share hawayen ki babu mai miki aure in har bada yardan ki ba, ita Hafsatun haka aka yi mata? Ina ce nan nayi-nayi da ita baza ta auri Mahaifin naku ba tunda ba kalar ta bane, Mutum ya fito daga ƙauye amma ta nace sai ta aure shi, babu abun da na iya haka na yarda, amma kuma don tsine wa su ba a tilasta musu auren dole ba zasu yi miki? to in ga wanda zai yi miki kina nan baza ki koma ba, karatu kuma ko su baza su saka ki ba Ni zan saka ki, ba dai karatu kike so ba?"
Cikin washe baki Maryamu tace, "eh Iya, na fi so in yi karatu mai zurfi ko don in taimake ku."
"Ai Insha Allah za ki yi sa kuwa, duka-duka nawa kike da za a yi miki auren? tunda zamani ya canza idan an yi wa Yayyinki ai yanzu ba da bane, tunda ke kina buƙata babu mai tauye miki haƙƙin ki, kina nan babu inda za ki koma inyaso Ni zan kira su in faɗa musu na amshe ki, dama ai na fi so ki zauna a nan kusa da Ni. Maza tashi ki ɗibo abinci yana nan a kichen ki ci sannan ki yi wanka ki huta."
Cikin farin ciki Maryamu ta tashi zuciyarta fari tass, domin tunda ta zo nan babu wanda ya isa yayi mata auren dole tunda Iya Samira baza ta yarda ba, musamman yanda take matuƙar ƙaunarta, tun ba yau ba take jelan a bata Maryamun ta riƙe ta amma Iyayen sun ƙi
Matsalar dama daga wurin Mahaifiyar Baba ne, tunda ita tace, "babu inda Yaran sa zasu je domin baza a raba mata kan Jikoki ba, duk rintsi kar ya bar Yaransa su je wani wurin."
Duk da a yanzu ma ba ta raye, kusan watanni goma kenan da rasuwar ta.
*****
A can kuwa gida, duk a tunanin su Inna, makaranta Maryamu ta tafi, shiyasa babu wanda ya damu; har sai da Bintu ta dawo ita kaɗai
Sannan ne Inna take tambayarta, "ina wannan rigimammiyar yarinyar ta tsaya? In ce dai ba nemo mana wata faɗan zata yi ba tunda mai hali ba ya fasa halin sa?"
"Eh ita mana, tunda kika fita ta saka ƙafa ta bar gidan itama."
"To ai kuwa bata je makaranta ba wlh, har Yaya Faisal ma yana tambayana a kan meyasa bata zo ba? Nace mishi bata ji sauƙi bane, shine ya ce to zai shigo gidan, amma wlh bata zo ba."
"Bata zo ba kuma? To ina ta je?" Inna tafaɗa tana al'ajabin maganar Bintun
Umma Jummai wacce ta shigo gidan da sallama, tana yaye mayafin kanta take cewa, "ya naga kun yi cirko-cirko, lafiya?"
Cikin takaici Inna tace, "yanzu nake tambayar Bintu ina Maryamun? Ashe wai bata je ba, duk a tunanin mu fitan da tayi can ta nufa, ashe yawonta ta wuce, ita ta sani ai zata zo ta same Ni kuwa zan ci mata mutunci; tunda yawon ya fiye mata makaranta."
"To Allah ya kyauta, rashin jin magana ce irin na ƴan yau, ke Bintu ki cire Hijabin sai ki je ki leƙa gidan Indo ko tana can, sabida yanzu ma haka daga gidan Ummita nake bata je can ba gaskiya, ko ki zaga inda kika san za ki ganta ki kira ta." Umma ta furta tana yin gaba abun ta
Itama tuni Inna ta ci gaba da aikin ta bata sake bin zancen ba
Koda Bintu ta cire Hijabin, bayi ta shiga sannan ta fito ta rataya gyale a gefen kafaɗanta ta fice. Amma duk inda ta san zata ga Maryamu ta je ba a ganta ba. Bata dawo gidan ba har sai da aka kira sallan magriba, ta dawo ta sanar musu, "duk inda ta je an ce bata zo ba."
"To ina ta je?" Umma ta furta tana kama haɓa
Inna dai bata tanka ba, a lokacin tana tsaka da alwala ne, sai da ta gama ta dubi Bintu da ke zaune tana ci gaba da faɗa wa Umman gidajen da ta je, sai tace, "zo ga buta ki ɗauka ki yi sallah, ita kuma zata gamu da Baban nata bari ya dawo, tunda abun da zata tsiro wa kanta kenan, ki fita tun ɗazu ba a san inda kika je ba?" Sai ta ja ƙwafa tana miƙe wa ta wuce ɗaki.
A haka fa shiru -shiru har su Baba suka dawo Maryamu bata dawo ba. Aka sanar musu shiyasa Baba yake ta faɗa, ya saka su Ashiru su je su duba ta, amma duk inda suka je babu labarin Maryamu. Hankalin su ya soma tashi matuƙa, shiyasa suka jira a fito sallan isha'i su gani ko zata dawo
A gida kuwa Umma ce kawai ta nuna damuwar ta, shiyasa har fita tayi tana duba maƙota ko ta je
Inna kuwa sam ta ƙi zuwa, duk da a cikin ranta sosai ta damu, amma bata nuna a kan fuskarta ba sai harkokin ta take yi.
***
A lokacin Maryamu tana can ta ma manta da wani mutanen gida, ta tasa Iya Samira tana ta faman yin mata tatsuniya, tunda itama shaf ta manta cewan zata kira iyayen Maryamun ta sanar musu kar hankalin su ya tashi basu ganta ba
Sai a lokacin ma ta tuna ta buga salati tana cewa, "Maryamu miƙo min wayata a ɗaki in kira Hafsatu in faɗa mata kina nan, in ba haka ba ai sai hankalin su ya tashi ke kina nan, su suna faman neman ki."
Dariya Maryamun take yi, ta je ta ɗauko tana cewa, "barin ma Baba, don na san sai ya fi tashin hankali, yanzu ki ga yana zagaye bayi."
"Gidan ku, kira min numban shi ko ta Innar taku, ban san shirmen nan naki."
Kiran numban Baba tayi, sai dai bai shiga ba sabida babu kuɗi
"An shige su! ashe babu kuɗi kuma?" Sai ta ja tsaki tana ƙoƙarin miƙe wa tare da cewa, "ina zuwa bari in dubo kamar ina da gudan ɗari a bankaɗen kayana, na san idan ke na aika baza ki gani ba sabida shegen ɓuya da nayi masa."
Babu jima wa kuwa sai ga shi ta dawo da ɗarin, ta miƙa mata tana cewa, "amshi nan, ki fita ƙofar gida ki siyo a shago, tunda an fito masallacin, maza ki siyo wurin Laminu ko Isah a nan bakin gida, ki ce in ji Ni ne zasu ba ki tunda ɗari da goma ne."
Maryamu da ta amsa kuɗin, sai faman juya shi take yi, sai ta soma warware wa tana cewa, "kai Iya wannan kuɗi ta sha ɓoyo da yawa, ji be yanda ta koma."
"Ba dai zata biya mana buƙata ba? Da Allah maza ki je ki dawo kar su ji shiru."
Hijabin Iya Samira ta ɗauka ta zura, sannan ta fice
Bata jima ba ta dawo da katin ta saka a wayan. Sai ta kira numban Baba
Lokacin suna tsakar gida sun yi cirko-cirko ana jimami, sun rasa ma me ya kamata su yi. Sai ga kiran wayan Iya Samira
Haka nan Baba ya amsa wayan muryansa cikin damuwa, bayan ya amsa wayan yake gaishe ta cike da girmamawa
Ta amsa tana cewa, "ya mutan gidan? Ina fatan kowa lafiya?"
Ɗan jim yayi, sai kuma yace, "to Iya kowa lafiya zamu ce..." Sai kuma yayi shiru ya kasa faɗa mata abun da ke faruwa
Ita kuma sai tace, "halan Maryamu kuke ta faman nema?"
"Wlh kuwa Iya, ashe an faɗa miki?"
"A'a babu wanda ya faɗa min, tana nan gidana ta zo tun ɗazu, kuma Ni na manta ban kira na sanar muku ba."
"Iya tana nan wurin ki?"
"Eh ƙwarai kuwa, ga ta nan ma zaune a wuri na, tace ta gudo nan baza ta zauna ba tunda auren dole zaku yi mata, shiyasa ta taho."
"Ikon Allah!." Abun da ya iya furta wa kenan ya kasa ma magana saboda mamaki
"To don haka Jikata dai baza a yi mata auren dole ba, ta dawo wurina da zama don haka baza ta dawo nan ba, Ni zan riƙe ta tunda ku kun gaji da riƙe ta, kuma zan saka ta a makarantar har lokacin da Allah zai fito mata da Mijin aure."
"Amma Iya ban ƙi ta taki ba, kin san yanda mu nan muke aurar da yarinya, kuma mu ba auren dole muka so mu yi mata ba, ita Maryamun ce ba ta jin magana, kawai daga an yi mata maganar ta fito da Miji a yi musu aure tunda ƴar uwanta ta fito dashi, kuma kinga ba karatu suke yi ba tunda sun gama ƙaramar secondary, duk sa'annin su sun yi aure shiyasa Nima zan yi musu, amma Iya ai babu wata maganar auren dole a ciki."
"Eh to babu wata maganar auren dole a ciki, amma ai ita ta nuna bata so; karatu take so, tunda ku baku da kuɗin saka ta ai Ni ban rasa ba, ka barta a hannuna ta ci gaba da karatun ta, zuwa nan da ta gama Sakandiren sai ka ga ta kawo wanda take so, shikenan ma sai a yi auren, kuma ka ga bata ma zauna a ƙauyen ba balle a riƙa gutsiri tsoma, ko ya kace?"
Cike da kunyar ta tunda bazai iya mata gardama ba, yace, "shikenan Iya, yadda kika ce haka za a yi, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi."
"Amin ya Allah, ai karatu da dad'i, ko baka ga yanda Hafsatu ta zama bane a ƙauyen? To itama sai ka barta ta yagi rabon ta tunda haka zamanin namu ya zo, ai an ci gaba har karkaran ba a saurin Aure, Allah ya rufa mana asiri ya bamu dacewa kawai."
"Amin Amin Iya, to mun gode Allah ya saka da alkhairi, bari in sanar da mutanen gida tunda gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake dama."
"Gaskiya kam, ai Ni ce ma da mantuwa, da na kira tun ɗazu da baku shiga ɗimuwa ba, ka gaishe da su sai da safen."
"To Iya, mu kwana lafiya." Ya ƙare maganar yana sauke wayan a kunnen sa tunda tuni ta kashe ma
Sai ya kalli Iyalan nasa, waɗanda suke zaune gaba ɗaya a tsakar gidan, in banda su Yaya Faisal da har yanzu suna can suna neman Maryamu, amma har su Ummita suna cikin gidan, duk da basu ji me Iya take faɗi ba amma kunnen su yana ga Baba suna sauraron shi
A nan ne yayi musu bayanin halin da ake ciki, Maryamu tana can wurin Iya Samira
Sai kawai suka soma murna kowa na furta alhamdulillah, har Inna da tayi nata a zuciya, wacce tana ɗaki a saman darduma, tunda tayi sallah bata tashi a wurin ba cikin tsananin damuwa da tunanin inda ƴarta ta shiga. Amma jin wannan bayanin hankalin su gaba ɗaya ya kwanta
Nan Baba ya aiki Halliru ya je ya kira su Nazirun tunda an san inda take
Sai ga su, su ma sun shigo gidan kowa hankalin sa ya kwanta
Su Ummita, sai suka tashi suka yi musu sallama suka koma gida
Shima Yaya Faisal bai jima ba, yayi musu sallama ya tafi, tare da ɗansa wanda suke tare tun idar da Sallah basu koma gida ba, sai ya ajiye shi a gidan, shi kuma ya tafi ana neman Maryamun tare da shi.
*****
Da safe Iya Samira ta fita ta je gidan su, tunda har sun yanke hukunci ita da Maryamun a kan za a nema mata makarantar nan na Ƙofan Kibo, wato Jama'atu. Shi yasa tace, "da sassafe zata je tayi magana da ɗan wurin Kawunta Shehu tunda Malami ne a can, sai su ji yanda za a yi a samo mata Form."
Maryamu sai murna take yi, domin barci ma ya gagare ta a ranan, sai lissafi take yi tana dariya tare da yi wa Iya Samiran alƙawarukan, "duk sanda ta gama karatu ta zama babba a cikin gomnati, ita zata soma jin dadin ta, albashin ta na farko tayi mata alƙawari ita zata ba."
Itama Iya Samiran sai dariyan shirmen ta take yi, shiyasa ganin yadda ta damu da karatun, safe nayi ta fita ta je ta yi wa Malam Aminu magana. Ɗan Kawunta Shehu da yake koyarwa a school ɗin. Da inda suke da makarantar babu nisa shiyasa Iya Samira ta fi son Maryamu tayi makarantar, ko don sauƙaƙawan wahala
Sai dai an yi rashin Sa'a, Malam Aminu ya sanar mata, "ai kuwa Form ya ƙare, sun rufe ma karɓan ɗalibai."
"To Aminu yanzu kana ganin baza a samu ba? Ko ɗan ciwa-ciwan nan mana kayi mana tunda kaima Malami ne a makarantar, na san baza ka rasa hanya ba."
Dariya yayi da cewan, "ai Iya da ne ake wannan ɗabi'ar, tunda gwamnatin Nasiru El Rufa'i ya hau aka dena, wlh ko ƴar Masu kuɗi ce yanzu sai ta bi ƙa'ida a ƙasar nan take samun gurbin karatu, ai yanzu an ci gaba sosai a kan harkan Ilmi. Ki bari kawai zan yi wa Abokina magana na san baza a rasa a makarantar su ba, sai a nema mata a can tunda da nan da can ɗin duk ɗaya ne, su ma can makarantar Arabia ce tana da kyau matuƙa."
"To ai matsalan, ba na son tayi nesa da gida ne, ka san yanda harkan biyan abun hawan nan yake, shima ƙarin jidali ne."
"A'a kar ki damu Iya, tunda aka sanya ta school ai transport bazai gagara ba, nan Sheikh Ibrahim Arab ne fa, Karau-Karau na hanyar Gaskiya, ashirin ma zai kaita zuwa makarantar. Kinga Hamsin ma ya isa ya kaita ya dawo da ita har da na shan ruwa." Ya ƙare maganar yana dariya
Itama tayi dariyan tana cewa, "to Masha Allah, ai shikenan kuwa, na ji dad'i wlh, Allah yasa a samu, Ni sai in riƙa bata saba'in ma tayi break da sauran, don Allah ka ƙoƙarta min."
"Babu komai Iya, yanzu zan kira sa ma in faɗa masa, duk yanda muka yi dashi za ki ga na zo gidan."
"To Shikenan na gode, bari in je." Ta miƙe da ninyar fita daga ɗakin
Sai ga Matar Malam Aminun, Shafa'atu, ta shigo da Kofin koko da Ƙosai tana cewa, "wai Iya har za ki tafi? Ki bari in kawo miki abun kari mana ga shi."
"A'a wlh Shafa, sai da na karya kafin na fito, ki bar shi kawai, ina Yaran ko har sun tafi makarantar ne?"
"A'a, ai dayake da Babansu suke fita yana sauke su a tasu makarantar, sun shiga cikin gida ne, yanzu za ki gansu."
"To Ni na tafi, sai anjiman ku." Ta fita ta saka takalman ta ta fice daga gidan, batare da ta shiga can cikin gidan ba, tunda dama sashin Malam Aminun a bakin hanya yake, ba sai an zurfafa ciki ba.
***
Kamar yanda Malam Aminu ya faɗa ma Iya Samira ne, sai ga shi ya zo gidan da yamma har da Form ɗin Maryamun an samu, yanzu kawai kuɗi ya rage in an cike Form ɗin sai a maida musu tunda an samu. Shi yasa duk ya faɗa musu abubuwan da ya kamata su yi ko nan da sati ɗaya ne a yi a gama komai, tunda har an fara karatu time ɗin ya ƙure, shima Form Allah ne yasa za a samu don ya ƙare gaba ɗaya sai guda ɗaya
Shiyasa Iyan ta cire kuɗi ta bayar, tace, "ya siyo mata har da kayan makaranta da littafai, abun da bai samu ba ko a hankali sai a siya in har ta fara zuwa."
Maryamu sai murna, tunda ta samu cikan burin ta, karatun shine abu na farko da take buri a rayuwarta, tana son ilmi matuƙa, tana son ta zama ƴar boko wayayyiyar yarinya, wacce ake dama wa da ita a gwamnati. Ta san wata rana sai ta zama ɗaya daga cikin ma'aikaciyar gwamnati tunda shi ne abun da ta fi ƙauna a duk ayyuka, ta ganta cikin office ɗin ta mai sanyi, tana da dogon buri gaskiya a rayuwa, kuma da sannu zata cika sa.