cika ta, cikin farin ciki take cewa, "Yaya, kai ne a garin mu yau?"
Yana dariya yace, "wlh kuwa Hafsah, kin ganmu cikin bazata babu sanarwa."
Dariyan farin ciki tayi, sai tace, "haba dai Yaya, ai babu komai ku shigo." Sai ta kalli Sadiq kuma, bata ce komai ba sabida farin ciki tayi musu iso ciki
Umma Jummai tana ɗaki ta ji shigowar su, shiyasa itama ta fito tayi musu lale marhaban. Tare suka tarbe su aka shimfiɗa musu tabarman kaba, suka zauna sannan aka gaisa
Inna tace, "ga shi kuma Malam ba ya nan, amma yanzu zan sa a kira shi."
Umma tace, "bari Ni in kira sa, zauna Innan Ummi." Ta ƙare maganar tana mike wa da sauri tayi ɗaki
While su kuma suka sake gaisawa, Inna tana tambayar mutanen gida, sai kallon Sadiq dai take yi, sai a lokacin ma ta tambaya tana cewa, "wai wannan SHAREEF ne ko Babanmu? Ni ban gane shi ba."
Dady cikin barkwancin shi yana shafa kan Sadiq ɗin tare da cewa, "ka ganka, ka yi tsawon ƙafa duk sun kasa gane ka, to nema kake ka fi yayyin naka ma Sadiqu."
Baki a washe Inna tace, "wai yanzu Sadiq ne haka? Ikon Allah! Wlh yayi saurin girma, kamar ba sa'an su Bashir ba, Ni wlh in ka bar Ni zan iya cewa a cikin su Baba ko SHAREEF ne."
Dariya suke yi dukkan su. Inda Innan take sake cewa, "Sadiq ka yi girma da yawa, anya baza mu nema maka Mata a nan ba? Kawai ka dawo wurin mu da zama."
Sai dariya yake yi yana sussunne kai, su kuma suna taya sa Inna tana ci gaba da tsokanar sa
A haka Umma ta dawo ta sanar musu, "yana nan tafe."
"Ai da baku kira shi ba, zaku katse mishi hanzari."
"To Yaya ai dole a kira shi tunda yanzu sai magriba shi da ya dawo gidan nan, kuma ai ba nan da nisa bane, gwara ya zo ku gaisa kafin ku tafi."
Abinci suka so kawo musu, amma Dady ya hana, yace, "baza su ci komai ba su bar shi kawai."
Daƙyar ta samu suka sha ruwa, shima Sadiq ne ya sha amma Dady bai sha ba
Babu jima wa kuwa sai ga Baba ya iso. Ya shigo suka gaisa faram-faram cikin girmamawa
A lokacin ma har Umma ta kusa gama abincin rana, shiyasa Baban yace, "a zuba musu su ci gaba ɗaya."
Bayan sun ci sun natsa ne, sai Dady ya kawo nashi bukatun, na son tafiya da Maryamu can Kano ta zauna a wurin sa
Baba dai ya kasa ƙin amince masa, amma yace mishi, "ya fi son Maryamu tayi aure ne gaskiya, saboda har ga Allah ba ya son tayi zurfi a karatu, musamman yanda ita Maryamun halin ta ya fita daban a gidan nan, kuma ka ga akwai ƴar uwanta da suka taso tare za a yi musu auren gaba ɗaya, shiyasa hankali na zai fi kwanciya Maryamu tayi aure, amma ban ƙi ta taka ba Alhaji."
Murmushi Dady yayi tare da cewan, "ai Ni nayi ninyar tafiya da Maryam, tunda naga da alamu tana da buƙatar bin mu, musamman dana kwaɗaita mata komai zurfin karatu zata yi shi, Ni zan ɗauki nauyi, don haka wannan ba wata matsala bace in har zaka bani ita sai in nema wa ɗana auren ta, kafin mu tafi sai a ɗaura mata aure da SHAREEF; hakan zai fi ko?"
[18/01, 9:58 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE11*
Baba ya kasa yin magana sabida jin maganar da Dady ya zo mishi dashi
Sai Dadyn ne yake cewa, "kar ka damu Malam Haruna, ai yanzu mun zama ɗaya, dama ina buƙatar SHAREEF yayi aure a wannan gaɓar, kuma haƙiƙa zan ji dad'i idan har Maryam ta auri ɗaya daga cikin ƴaƴana; sabida hakan zai ƙara ƙarfafa mana zumunci, to na yaba da hankalin Maryam na san zasu dace da ɗana SHAREEF, idan ma kana wasi-wasi ne a kan haɗin, za ka iya faɗan ra'ayin ka ko kuma in turo SHAREEF ɗin ku gana sabida ku san wanda ƴarku zata aura."
"Haba dai? Wlh kar kayi wani tunani a ranka, shirun da ka ga nayi farin ciki ne ya yi min yawa wlh, na san Hafsah zata fi ni farin ciki tunda haɗin zumunci ne babba, Ubangiji Allah ya sanya albarka da alkhairi a cikin wannan auren da zamu ƙulla, gaskiya nayi farin ciki matuƙa." Cewar Baba da rawan murya, yayinda fuskarsa a washe matuƙa da murna
Shima Dady yana murmushin yake cewa, "sai dai alfarman da zan nema shi ne, zuwa gobe zamu tafi Insha Allahu, ko yau ko gobe sai a ɗaura auren su mu wuce da ita."
"To to, ai babu damuwa Alhaji, duk yanda ka ce, Maryamu dai ɗiyarka ce duk yanda kake so haka za a yi, fatana dai a ce mun ƙulla alkhairi wanda zai jawo farin ciki a zukatan mu gaba ɗaya."
Daga haka Dady yace, "a bari zuwa gobe sai a ɗaura auren su wuce, yanzu dai duk a sanar da jama'a tunda ƙurarren lokaci suke dashi".
***
Koda Baba ya sanar da su Umma Jummai zancen auren, haƙiƙa sun yi farin ciki sun nuna murnan su, barin ma Inna domin tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, yau ga shi ƴarta zata auri ɗan ɗan uwanta, dama a koyaushe tunanin ta da damuwar ta bai wuce inda Maryamun zata yi aure ba, sabida halayyarta na rashin haƙuri, ga rashin kunya da tsiwa, wannan idan bata yi dace da mai ƙaunarta ba a lokaci guda zata cika sa ya sake ta, Maryamu tana da ƙarancin hankali da wauta; girman ne kawai a jiki amma sai rashin jin magana, ta san idan ta je gidan ɗan uwanta zasu riƙe ta amana, musamman ma da ta san Momy Mace ce mai matuƙar kirki da kawaici, tabbas Maryamu ta samu gidan dattako, sai dai kawai halin Mijin ne da bata sani ba har yanzu, tunda ba wai zuwa suke yi ba Yaran shiyasa baza ta iya gane halin kowannen su ba, but tana kyautata zaton samun farin ciki mai ɗaure wa ga Maryamun.
Dangi sun yi murna, wasu kuma suna ta mamakin yanda auren ya zo a bakatatan, musamman yanda suke ganin Alhaji Ahmed shiyasa suke cewa, "dama kuɗi ai babu abun da ba ya sa wa, Malam Haruna ya siyar da ƴarsa kawai, idan ba haka ba; aure a rana ɗaya kacal? Ai wannan maganar abun duba wa ne."
Babu dai wanda ya saurare su. Don a ranan ma Sadiq da shi da Bashir da Halliru, tunda sa'annin juna ne, tare suka tafi cikin Zaria suka ɗauko Maryamu
Tun a waya Baba ya kira Iya Samira, ya shaida mata halin da ake ciki, farin cikin Iya ba ya misaltuwa, don har guɗa take ta faman yi tsaban murna
Ita kanta Maryamun har da rawa da Iya Samira ta shaida mata batun. Oh! Yau ga shi ita ce zata auri ɗan masu kuɗi? Tun kafin a je ko'ina burinta zai cika. Ko kaɗan bata damu da sanin wane ne shi ba, amma ta san tabbas shima kyakkyawa ne kamar su Sadiq, ta san ta more tunda gidan masu hannu da shuni ne, shikenan yanzu ta koma ƴar gayu, karatu kuma sai ta ture kenan?
Sai baza ɗuwawu take yi a tsakar gidan tana rawa tana gantsare wa da faɗin, "ah ha! Eh.. eh.. eh... Yau burina zai cika, na zama Amarya, gobe za a ɗaura eh... Eh... Eh.., Shikenan na zama Matar santalelen saurayi, wohh! Ni Maryamu Matar manya, kai dad'i kashe Ni, farin ciki zai kar Ni."
Iya Samira ta taka mata birki tana cewa, "amma ke kam an yi sakaryan yarinya, tsaban rashin kunya a gabana kike rawa kina wannan gantsare-gantsaren? Maimakon ki shiga damuwa sabida rabuwa da zamu yi amma kike murna?"
Dariya ta kwashe dashi tana tafa hannu da faɗin, "Ahayye Iyalle na. Wanne damuwa bayan kina ji aure zan yi gobe? Kuma ɗan guyu fa zan aura ɗan Kawuna, haba dai, ai damuwa ta kau na rantse da Allah, kar ki damu ai ba mutuwa zan yi ba, duk inda na je zanna riƙa dawowa muna gaisa wa, kai Iya ba abun farin cikin ki bane ma ki ganni Nima na zama ƴar masu kuɗi?" Sai kuma ta nufo wurin Iyan tana cewa, "amma Iya gidan su akwai bene ko? Akwai kuma teyes ko?"
"Da Allah ja can, ina ce ba zuwa gidan za ki yi ba? Ki bari idan kin je za ki gani, sakaryan yarinya kawai, ki tashi ki haɗa kayan ki ga su Sadiq nan zasu zo ɗaukar ki."
Tura baki Maryamu tayi tana taɓe shi, ta miƙe tana maganganun ta ƙasa-ƙasa, "ai sai kiyi tayi, Ni dai nayi gaba babu mai hana Ni nuna farin cikina, yo Ni ina ruwana." Ta shige ɗaki tana ci gaba da raira ma kanta waƙa, tana ta rawa da ɗuwawu tana tuttura su
Iya Samira tana jin ta amma bata ce komai ba, sai ta ci gaba da ayyukan ta, tana gama wa ta ɗauki gyale ta wuce gidan su don ta shaida musu auren
Maryamu ma bata san ta fita ba, sai da ta fito tana ta ƙwalla mata kira amma ta ji shiru, sai itama ta saka kai ta fice a gidan
Har su Sadiq suka iso bata dawo ba. Itama Iya Samira har ta haɗa kayanta tace, "zata bi su, su tafi tare, itama ta kwana a can." Duk da ta so sai gobe ne ta taho da sauran dangi da zasu je, amma kuma sai ta canza shawara gwara ta bi su kawai
Ana ta neman Maryamu sai daga baya ta dawo, nan Iya Samira ta rufe ta da masifa tana tambayarta, "ina ta je bayan ta san jiranta ake yi?"
Bashir yace, "ai Iya wannan yarinyar shegen yawo ne da ita, Allah yasa dai baza ta yi halin nata a can ba, don yanzu ba da bane, za ki tafi da auren ki ne, idan kika yi yawo a can babu wuyan an sace ki dan ubanki, sai dai ki ganki a gidan yankan kai kina ƙwalala idon nan kamar robber."
Dariya suka kwashe dashi, daga Sadiq har Halliru
Ita kuma ta zumɓuro baki tana cewa, "ka manta ne kwano ne, haushin rashi dai, kai mu ga naka robbern, da ƙwaƙulallen idonka kamar mazubin ruwa."
Ai kuwa ya biyo ta a guje, ta kwasa bayan Iya Samira tana ihu kamar zata fasa gidan tun kafin ya taɓa ta
"Don Ubanki Ni kike faɗa wa haka? Dama kwana biyu hannuna ƙaiƙayi yake yi ban bugi banza ba, amma yanzu zan fara har ki tafi zan bugi rabo na."
Iya Samira ta ture sa tana cewa, "an yi babban banza wlh Bashari, ƙaton kawai, ka rasa da wa zaka yi faɗa sai da ƙanwar ka? ai kai kake ja take raina ka ma, dalla ja can, idan ka kuma dukan ta zan saɓa maka, baza ka bari ba?"
Sai da ya ƙara ranƙwashin ta a kai, sannan ya haƙura yana ƙwafa tare da cewa, "wlh Iya ba ki san yanda yarinyar nan ta raina Ni bane, Allah yasa ma idan ta je can Yaya SHAREEF ya riƙa jibgar ta kamar Jaka."
Kafin kowa yayi magana, Maryamun ta cafe tana kuka da haki tace, "wlh ba Amin ba, ƙarya kake mugu azzalumi, kuma bakin ka ya sari ɗanyen kashi, mugu azzalumi, luluup! Wowhowho! Yana jin haushi ne dai zan koma gidan masu kuɗi."
Yanda take maganar ne duk sai ya basu dariya
Itama kuma sai kuka take yi babu hawaye, tana ci gaba da tsiwan nata, har da yin ma Bashir ɗin gori, "wai ko ya zo can baza ta bari ya shigan mata gida ba, sai dai ya koma, kuma wlh idan ma ta zo nan itama baza ta nuna ta san shi ba, kashi ma mai ɗoyi sai ya fi shi daraja."
"Haba ƴar ƙanwar mu, ki yi shiru mana haka, mu je kinji ki ɗauki kayan ki mu wuce, kinga dare ya soma yi, ki bar wannan Yayan naki, yanzu Ni ne Yayanki ba shi ba." A cewar Sadiq da ya riƙo mata hannu yana rarrashin ta
Ita kuma sai dage wa take yi tana ƙara ƙwaƙulo kukan nata, sai a lokacin ne ma ɗan ɗiss na hawaye ya fita a idanunta
Bashir sai mata dariya yake yi, yana cewa, "zai kama ta ne, su koma gida ta ga yanda zai yi da ita, banzar yarinya mai kuka babu hawaye."
Iya Samira tace, "ga ka nan ƙaton banza, ka dena tsokanar ta ka zo ka ɗaukar mana kaya mu tafi."
Tare da Bashir da Halliru suka ɗauki jakan kayan nasu. Shi kuma Sadiq tuni ya ja Maryamu sun fita tare zuwa wajen mota. Ya shiga gaba itama ta zauna a gefen sa, su Iya Samira kuma suka zauna a baya sannan suka wuce ƙauyen.
*****
Washe gari kamar yanda aka sanar wa da jama'a, da ƙarfe 07:00am. kowa ya shaida auren Muhammad SHAREEF Ahmad da Amaryan sa Maryamu Haruna, a cikin sadaki ƙalilan domin samun albarkan auren
A lokacin da suka isa, Momy ta gama shirya musu abinci tunda ta san da zuwan nasu, har labarin auren, shiyasa take ta murna, tunda ta ji diran Motan su ta fita ta tarbe su a can, hannun Maryamu ta kama tana murmusawa da cewa, "ƴata sannu da zuwa."
Maryamu na faman washe baki da sunne kai ta kasa amsa wa
Sai Momyn ta kalli Dady tace, "kuma ƴar tawa tubarakalla Masha Allah, I didn't expect to see her like this. so beautiful."
"Allah ko?" Cewar Dady yana dariya
Shi kuma Sadiq cikin farin ciki yace, "Momy sai ma kin zauna da ita, tana da shiga rai, na samu ƙanwa. In fact, I am more than happy that she is with us, I am very happy."
"To ku mu je ciki, mu dena tsayuwa a nan, kai Sadiq shigo da kayan namu kawai." Dady ya furta yana yin gaba
Momy ta bi bayansa hannunta saƙale a cikin na Maryamu
While Sadiq ya tsaya daukar Jakar su. Har ɗaya daga cikin masu aikin gidan ya zo da nufin ɗauka, but sai ya tsayar dashi yana murmushi tare da cewan, "a'a, bar shi kawai zan ɗauka." Ciro Jakar yayi, da nasu dana Maryamu da ta ɗibo kayanta kaɗan a ciki, ya nufi ciki da su
A falo ya tarar da su zaune, Maryamu na kusa da Momy ta manna ta a jikinta tana ce ma Dady, "gaskiya ya kyauta da ya yanke wannan hukuncin, don farin cikin da take ciki baki ma bazai iya misalta shi ba, musamman da ta ga Maryamun zata yi dai-dai da ra'ayin ɗanta; domin sun dace matuƙa, ita farin cikin ta ma yanda aka kawo mata ƴa, don yanzu ta samu ɗiya Mace, ko ba haka ba Maryam?" Ta ƙare maganar tana kallon Maryamu fuskarta cike da fara'a
Kai Maryamu ta ɗaga mata tana ƴar dariya sai wurga ido take yi tana kallon tsarin gidan
"Yauwa, kinga daga yau sai ki riƙe Ni a matsayin Mahaifiyar ki, kamar ƴaƴana ke ma kina kira na Momy ko?"
Sadiq da ya zauna yana cewa, "Ni kuma Momy yanzu na tashi a sahun Auta, ga Auta nan kin samu, don nima yanzu na girma, har Innanta tace zata bani Mata a can."
Baki Momy ta buɗe tana dariyan maganar sa
While Dady yayi masa daƙuwa da cewa, "ka ganka? Ashe baka da kunya kaima? A gaban mu kake furta wannan maganar?"
"I'm sorry Dady, ALLAh wasa nake yi fa."
"Shikenan, amma maganar da zan yi yanzu, ga dai Maryam ta zo gida a matsayin Matar SHAREEF, duk da ban so ta tare a wannan lokacin ba saboda karatu da nayi mata alƙawarin zata yi, but zamu jingirta tarewan ta zuwa nan da kamar 1year in ta saba damu, zata ci gaba da zama a nan batare da kowa ya san Matar SHAREEF bane, don haka kai Sadiq na san halin ka kar ka sanar da ƴan uwanka komai a kai, ka bari idan lokaci yayi sai mu sanar musu har shi SHAREEF ɗin."
"To Dady, bazan faɗa ba Insha Allahu."
Momy kuma ta so tayi magana a kan maganar, sai kuma ta fasa tana cewa, "bari in kai ƴata ɗakin ta idan tayi wanka sai mu ci abincin gaba ɗaya, tashi daughter in nuna miki dakin da za ki zauna ko."
Miƙewa Maryamu tayi bayan ta amsa da to, suka nufi ƙaramin corridor da ke nan downstairs, ɗakin da Momy ta kaita a nan ƙasa yake tunda saman babu wani ɗakin kuma. Sadiq ya biyo su da kayanta ya ajiye ya fita. Ita kuma Momy ta nuna mata komai tana cewa, "duk abun da bata gane ba sai ta tambaye ta, yanzu ta shiga tayi wanka sai ta canza kayanta ta fito suna jiranta."
Su ma su Dady sallah suka je suka yi, tunda a hanya la'asar tayi musu, sannan suka dawo suka zauna a Falon
Jin shiru Maryamu bata fito ba, sai Momy ta leƙa ta ta ganta tana ƙoƙarin saka riga
Da sauri Maryamu ta duƙa tana ɓoye jikinta sabida kunyar shigowar Momyn ta ganta a haka
Murmushi Momy tayi, bata ce komai ba sai tace mata, "har yanzu ba ki shirya ba ashe? To yi sauri ki gama, ki yi sallah sai ki fito ko?"
"To Momy." Ta furta tana zazzare ido still tana duƙe a ƙasa
Murmushi Momy tayi tana fice wa a dakin, ita kanta mamakin yarinyar take yi, ga ta ƙarama da ƙira mai kyau, mamakin saurin girman ta take yi tunda bata manta sanda suka je sunan yarinyar ba, farin ciki ne ya ƙara cika zuciyar Momyn, tana ganin kamar ɗanta ya gama dacen Mata, ƴar kyakkyawa da ita, ko ita Mace ta bata sha'awa bare namiji, wannan idan ta samu gyara ba ƙaramin ƙara direwa da kyawu zata yi ba, "hmm Allah yasa SHAREEF ya so ta." Ta furta a fili tana ci gaba da murmusawa. Wurin