Bayan an yi sallan isha'i. Duk sun zauna suna hira a tsakar gidan, har da su Baba tunda haka suke yi
Maryamu da Bintu har sun manta da abun da ya faru tunda dama sabon su ne haka, lokaci ɗaya zasu yi faɗa kuma su shirya, sun matsa gefe sai hira suke yi suna ƙus-ƙus
Baba yace, "ku taso ku dawo nan mu yi magana."
Hakan ne yasa suka taso suka zauna a kan tabarman wanda su Baba suke kai
Ya Kalle su yace, "ke Maryamu da ke zan fara, kina da wanda kike so ne?"
"Baba..." Ta furta tana ɗan zare ido
"Ina jinki faɗa min mana? Domin aure zan muku tunda na gaji da shirun ku, ku ba karatu ba sannan ba aure ba, don haka lokaci yayi da zaku fito da Mazajen da kuke so a yi auren ku a huta, inyaso ma sai a haɗa dana su Naziru kawai, Allah zai hore mana domin hakan zai fi sauki."
Umma Jummai tace, "gaskiya ne Malam, hakan ma yayi wlh, nima abun da nayi tunani kenan, tunda zaman kawai suke yi, duk sa'annin su sun yi aure ban da su, karatun nan dai sun yi iya yin su, auren shi ya kamace su."
Tura baki Maryamu tayi tace, "wlh Baba Ni ba na son aure yanzu, karatu nake so, nima ina son in yi karatu mai zurfi."
"Idan ma za a bar wani yayi karatu ai baza a bar ki ba, a wannan halin naki." In ji Yaya Ashiru yana ban ka mata harara
Sai tace, "to Yaya Ashiru me nayi ne Ni? Wlh ba abun da nayi, kuma ban da saurayin ma ai."
"To ai Ni ina dashi tunda ke ba ki dashi." In ji Baba yana kallonta, tare da cewa, "na faɗa miki babu wani karatu da za ki yi, gwara tun wuri ki nemo saurayi tun kafin in nemo miki. Ke ma haka Fatima gaba ɗayan ku ku fito da Mazajen Aure, in Allah ya yarda Allah ya hore za a haɗa auren ku a huta."
Inna da Umma suka haɗa baki wajen furta, "Allah ya tabbatar da alkhairi."
Ita kuwa Maryamu sai faman zumɓura baki take yi kamar yanda ta saba tana ƙunƙunai, amma ta kasa furta abun da ke ranta
Bashir yace, "ya dai Meramu? Akwai magana a bakin ki fa, ko auren ne ba kya so?"
"Ai ko ba ta so sai an yi shi, don nima na gaji wlh, wata rana sai ta jawo mana abun da ya fi ƙarfin mu in dai wannan yarinyar ce, auren za a yi mata tunda haka ta zaɓa." Innar su tafaɗa hakan cike da jin haushin halin Maryamun da ta fita Zakka a gidan nasu
Itama sai ta tashi tana wuce wa ɗaki tare da cewa, "wlh Ni dai har ga Allah ba na son aure, babu wanda zai min aure sai nayi karatu mai zurfi na zama Shugabar ƙasar ma gaba ɗaya."
Sai maganar nata ma ya basu dariya
Baba yace, "ina ruwan mashirmaciya, kya yi a gidan Mijinki amma ba a nan ba Meramu, nima in ɗana irin na Bashir."
Sai dariya suke yi. Haka suka zauna cikin raha suna ta hira. Daga ƙarshe Samarin ne suka soma zame wa suka shiga ɗaki
Itama Bintu tuni ta wuce ɗakin su, lokacin har Maryamu tayi barci, tunda kasa ce, ba ta tsawon hira sai dai ka ji ta tana jan rago. Rufe musu ƙofan tayi itama ta haye nata katifar ta kwanta.
Washe gari bayan su Baba sun tafi wurin aiki. Maryamu ta zauna a tsakar gidan tana ta ma su Inna rashin kunyar, "Alkur'an ba a isa a yi mata aure ba, sai dai ta gudu kowa ma ya rasa."
Inna tace, "to in kin fasa dan ubanki, ko akwai wanda zai neme ki ne? Ki tafi mana yanzu tunda ba a ɗaure miki ƙafa ba."
"Na rantse Inna baza a yi min aure ba, kuma kuna ganin wasa ne sai na aikata abun da nace." Ta miƙe tana ɓata rai tare da cewa, "haka kawai, wlh bazan yarda ba, babu wanda zan kawo bare ma a yi min auren."
Umma Jummai tace, "to wai mu ina ruwan mu da kika zo kika tasa mu gaba kina mana rashin kunya iyee?"
"Ki bar ta don Allah, na kusa karyata a gidan nan, kuma billahil lazi in ba ki yi wasa ba sai na saɓa miki kar ki bari mu saka ƙafan wando ɗaya da ke."
Shiru tayi bata ce komai ba sabida ganin yanda Innar take kallonta, ta san tsab zata ci uban ta. Sai ta wuce ɗakin su bata ma bi ta kan Bintu da ke zaune tana tsintan shinkafa ba, Hijabin ta ta ɗauka zata fice
Amma sai Inna tace, "kar ki fita gidan nan Maryam, wlh ƙafan ki ta fita gidan nan za ki ji a jikin ki."
"To Inna Ni fa ba wani wuri zan je ba, gidan Aunty Ummita zan je, dama tace in zo in taya ta gyaran ɗakin ta."
"Baza ki je ba. Tunda yawon kike so ki zo ki wuce ki ɗauki key ki zauna min a shago."
Babu yanda ta iya haka ta wuce ta ɗauko key ɗin. Tana fita kuwa ta zarce gidan Aunty Ummitan batare da ta shiga shagon ba
Tana cikin tafiya tana rera waƙa. Sai turguɗe wa take yi amma hakan bai sa ta cire takalmin ba. Har ta kusa isa gidan Aunty Ummitan sai ganin Jamilu tayi a gaban ta yana kiran ta. Ja tayi ta tsaya tana cewa, "lafiya? Wannan wanne irin halin karnukanci ne da zaka zo kana shan min gaba? Kana da mind?"
"Halin karnukancin na zo in nuna miki yanzu kuwa, tunda ke ba ki da mutunci yanzu zan nuna miki kin taɓa wanda ya fi ƙarfin ki, zan yi maganin rashin kunyar ki yanzu".
[12/01, 10:08 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE7*
"Hehehe! Uban kutru yayi kaɗan, wlh mai magani na a ƙauyen nan sai ya shirya, Jamilu na fi ƙarfin Ubanka ma bare kai banzan bazara wawa jaki." Tafaɗa cikin tsiwa da rashin kunyar ta
Ai kuwa hakan ne ya harzuƙa Jamilu, ya watsa mata mari tare da ƙoƙarin fincike mata gyalen yana cewa, "daga yau baza ki sake marmarin zagin wani ƙauyen nan ba, abun da kike taƙama dashi da tashen rashin kunyar ki yau zan raba ki dashi."
Sosai Maryamu ta tsandara ihu sabida yanda marin ya shige ta. Lokaci ɗaya suka soma kokawa dashi saboda ganin yanda yake ƙoƙarin fincike mata gyale. Ihu ta dinga zuba wa ta zame ƙasa a wurin tana zagin shi
Ihun nata ne ya fito da Aunty Ummita da Mijinta, tunda babu nisa da wurin, suna jin ihun da ya karaɗe gidan su, da sauri suka fito suka ga abun da ke faruwa. Sai Mijin Aunty Ummitan ya nufe shi da sauri yana kiran sunan sa
Hakan ne yasa Jamilu ya dakata daga abun da yake shirin yi, sai huci yake yi yana haki
"Kai kana da hankali me ya faru da ka kama yarinyar mutane kana jibga haka?"
Tuni Aunty Ummita ta zo ta kama Maryamun da ke ta kuka har da su majinu, cikin tashin hankali take duba ta saboda ganin yanda gyalen ta yayi gefe har ya yaga mata gefen riga
Kafin ka ce me mutane sun taru a Wurin. Saboda yanda Maryamun ta ƙi yin shiru sai ƙara volume ɗin kukan ta take yi, tana yi tana zagin shi tare da bayyana musu cewan, "fyaɗe zai yi mata."
Shi kuma Jamilu yace, "ƙarya ne, rashin kunya tayi masa, har zagin Mahaifinsa take yi, shi kuma bazai iya jure wa ba ya duke ta."
A fusace Ummita tace, "don ta zage ka shine zaka yaga mata riga har ka cire mata gyale? Me hakan ke nufi iyee?"
Ganin abun na son zama rigima babba, shiyasa Lado Mijin Ummita yace, "a wuce kawai wurin mai gari sai a yi sulhu a can."
Tunda sosai Maryamu take kuka tana cewa, "wlh baza ta yarda ba sai an bi mata haƙƙin ta." Sai birgima take yi a wurin
Daƙyar Ummita ta rarrashe ta ta ɗaga ta aka wuce wajen mai gari
Mutanen anguwa sun taru har labari ya je wa su Inna gida
Inna tace, "baza ta je ba, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, tunda ba ta jin magana ta je tayi duk abun da zata yi."
Sai Umma Jummai ne suka fito da su Halliru zuwa ƙofar gidan mai garin
Lokacin har an kira Baba a bakin kasuwa, tunda a can yake kasuwancin sa yana da shagon provision, yanzu ya dena zuwa birni ya buɗe nasa a cikin kauyen su, dama tun farko riƙon shago yake yi a kasuwar tudun Wada, yanzu alhamdulillah Allah ya buɗa mishi ya buɗe katafaren shago, babu abun da ba ya siyar wa a ciki
An taru sosai, aka ce Maryamu ta faɗa abin da ya haɗa su
Tana kuka ta sanar musu cewan, "kawai tana tafiya ya sha gaban ta a kan wai tunda ta ƙi amsar soyayyarsa, sai yayi mata fyaɗe kowa ya guje ta ƙauyen, wai sai yayi maganin rashin kunyanta." Sai ta ƙare maganar tana ɓarke wa da sabon kuka har yanzu babu ko ɗigon hawaye a idanunta
Salati mutanen wurin suka ɗauka har da mai Garin
Jamilu kuma tuni ya soma rantse-rantsen ƙarya ne ba haka bane
Ummita tace, "wlh ranka ya daɗe! Gaskiya ce, saboda tare da Mijina muka fito muka ga yana kokawa da ita, har ta faɗi ƙasa amma bai ƙyale ta ba, ga rigan ta nan ma sheda inda ya yaga mata." Tafaɗa tana buɗe wurin da ya yage
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Yanzu abun kunyar da ka ɗauko mana kenan Jamilu? Wannan wanne irin baɗala ne? Abun da muke yaƙi dashi a ƙauyen shine a gidana za a samu mai yi?"
"Na rantse da Allah Baba ban aikata ba, wlh ban yi mata komai ba." Jamilun ya furta yana hawaye
"Yi min shiru mutumin banza kawai, ai dole doka ta hau kanka, kuma daga yau babu kai babu yarinyar nan, duk sanda aka ce ko magana ce ta haɗa ku zaka ga yanda zan yi maka, hukunci kuma dole zaka amshi sakamakon ka tunda baka fi kowa zane ba." Sai ya dubi Maryamun yace, "ki yi shiru kinji? Insha Allahu zamu ɗauki mataki a kansa hakan bazai sake faruwa ba. Malam Haruna muna roƙon afuwar ka a kan abun da ɗana ya yi wa ƴarka, a yi haƙuri don Allah."
"Babu komai ranka ya daɗe! Dama Yara ka haife su ne baka haifi halin su ba, idan da laifin Jamilu har da laifin Maryamun." Sai ya ɗan ja numfashi tare da cewa, "amma Allah ya ƙara tsare gaba."
"Amin ya Allah." Dattawan wurin suka amsa baki ɗaya
Kana aka sallami kowa aka watse. Inda Mai gari ya sanya a shiga da Jamilu ɗakin horo a hukunta shi
Ummita tuni ta kama hannun Maryamu; sun wuce da su Umma Jummai zuwa gidan su. Baba na biye da su a baya yana kaɗa kansa
Da shigan su, tsumagiya Baban ya ɗauka ya soma dukan Maryamun
Nan da nan ta kure gidan da ihu da kururuwa tana neman agaji
Ransa a ɓace yace, "wlh Ni baza ki ja min abun kunya a garin nan ba, uban me ya kaiki inda yake da wani abun zai haɗa ku? Maryamu ke ba kya jin magana ko? Kina son ki fi ƙarfin mu tunda kinga ina ƙyale ki ba na ɗaukar mataki a kanki." Haka yake dukan ta ya riƙe ta gam ya ƙi sakin ta, sai da ta bugu lilis sannan ya ƙyale ta
Su Umma suna tsaye cirko-cirko babu wanda yayi ƙoƙarin ƙwatan ta
Shi kuma yana gama wa ya fita gidan ransa a ɓace
Inna itama sandan ta ɗauka ta nufo ta tana cewa, "shegiyar yarinya mara jin magana, gwara da yayi miki dukan tunda ke ba a isa a saka ki a hana ki ba, kin fi so ki gagare mu a gidan, ba a taɓa yin yarinya kamar ki mara jin magana ba, ko ke kaɗai ce yarinya a gidan da kullum sai kin ɗauko mana magana iyee?" Tafaɗa tana maƙure ta sosai tana jan mata gashi
Duk da kuka da ihun da Maryamu take yi but ta ƙi sakin ta
Su Ummita suka zo ƙwatan ta amma Inna ta ƙi sakin ta, sabida ta kaita maƙura, fushi sosai Inna tayi sai jibgar ta take yi kamar an aiko mata da jaka. Daƙyar su Umma suka ƙwace ta
Da gudu Maryamun ta miƙe ta shige ɗakin su ta saka saƙata tana ta gunjin kuka
"Ai wlh sai na karya ki a gidan nan tunda kin ce abun da kika tsirfo wa kanki kenan, har in hana ki zuwa inda kika yi ninya amma ki nuna min ban isa ba, zamu zuba kuwa." Innar take faɗa cikin ɓacin rai saboda ba kaɗan ba ranta yakai ƙololuwa da ɓaci. Musamman da ta ji abun da ya faru, "yanzu da ace ƙaddara ta afka yayi miki wani abun ya zamu yi? Shikenan kin gama zubar mana da mutunci bamu da sauran ƙima a garin."
Daga Ummita har Umma Jummai haƙuri suke ba wa Inna, saboda basu taɓa ganin ta ɗauki zafi a kan Maryamun ba duk da rashin ji irin nata, kullum da akwai abun da take janyo musu, yau kuwa da alamun ta kaita maƙura tunda ta shaƙa sosai
Ƙarshe dai Ummita tafiya tayi ta bar Innar a haka tana ta masifa, sun kasa bata haƙuri tunda a tunzure take
Ita kuwa Maryamu tana ɗaki tana ta kuka tunda ba kaɗan ba ta bugu a hannun su, daga ƙarshe ma barci ne ya kwashe ta a wurin kasancewar ta mara wahalar Barci, sai lokacin ne ma ɗis-ɗis na hawaye yake zuban mata a kunci, duk wannan kukan da ta sha basu fita ba sai yanzu a karan banza da hofi.
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆
Jikin SHAREEF da sauƙi sosai kamar ba shi ba, har ma ana shirin sallaman sa, Likitan ne yace, "ya ɗan zauna na kwana biyu su ga yanayin jikin." To Alhamdulillah musamman ma yau ya tashi da kuzarin sa sosai
Yanzu ma suna zaune dashi da Hanif, suna ɗan taɓa hira. Yake ce masa, "ina wayansa?"
Hanif yace, "ai tun jiya na kashe na ajiye ta, yau ma har na fito na koma na ɗauko maka, maybe you need it."
"Yeah. Miƙo min." Ya furta a hankali yana ɗan gyara zamansa ya zauna sosai
Ciro wayan Hanif yayi daga aljihun wandon sa ya miƙa masa. Sannan ya miƙe ƙafafun sa sosai yana saka earphone a kunnen sa ya mayar da hankalin sa a kan wayan sa
Shi kuma SHAREEF tuni ya kunna wayan yana jiran ta gama daidaita. Kafin wani lokaci saƙonni sun soma shigowa cikin wayan sa. Na Haseena ya soma duba wa yana kallo yana murmusawa, duk ƙorafin ta a kan rashin ɗaukar wayanta da bai yi bane, and kuma daga baya da ta kira sai ta ji wayan a kashe. Cije leɓen sa yayi yana ɗan lumshe kyawawan idanunsa, tare da buɗe su ya zuba wa Hanif su yana cewa, "meyasa ka kashe min waya?"
Ɗan ɗago kai Hanif yayi shima yana kallonsa, sai ya ware idon yace, "to me yasa zan bar shi a kunne tunda za a neme ka?"
Numfashi ya ja yana kawar da kan nasa. Kana ya soma ƙoƙarin danna wa Haseenan kira
"Oh! I forgot, na ga sweetheart ta kira, so ban san me zan ce mata ba that's why na kashe wayan, maybe sabida ita kake min ƙorafi?" Ya ƙare maganar idanunsa ƙir a kansa
Shi kuwa SHAREEF taɓe baki yayi batare da yace mishi komai ba, saboda ganin ta ɗauki wayan, sai ya kara a kunne yana sauke ƙafafun sa a ƙasa tare da zama sosai a kan gadon, That's why he turned Hanif
Daga can ɓangaren Haseena ita ta soma magana cikin tsantsan shagwaɓa; wadda alamun kuka take yi tana faɗin, "Why did he turn off the phone all this time when she was looking for him and did not see him?"
"I'm sorry sweetheart. Wayan bata hannu na."
Kuka ta fashe dashi tana cewa, "No. Kana son juya min baya ne dai, and tun kafin in yi nisa ka soma canza min, meyasa zaka kasa nema na after ka san cewa kiran ka kaɗai nake jira? Kowa ya kira Ni but ban da kai, and I called you but you hung up on me?"
Shiru yayi ya kasa magana sabida yanda yake jin kukan nata yana ratsa shi, sosai yake jin ciwo sabida ganin tana kuka, ko kaɗan ba ya jin daɗi ya ga tana cikin damuwa, yana shiga matsanancin tashin hankali. And kuma a yanzu ɗin ya kasa magana bare ya rarrashe ta
Hakan ne yasa ta ci gaba da kukan nata tana kiran sunan sa but ta kasa cewa komai
"I'm sorry sweetheart. Bani da lafiya ne... That's.. why." Ya ƙare maganar cikin ɗaiɗai tare da jan numfashi
Lokaci ɗaya sai ta rikice ta tsayar da kukan tana cewa, "shi ne baka sanar min ba? Me ke damun ka don Allah ka faɗa min kar zuciyata ta buga?"
"Realise sweetheart. Na ji sauƙi, babu komai ciwon ciki ne kawai, amma na fi son ki yafe min don ba na son ranki yana ɓaci haka."
Cikin shagwaɓa tace, "ai tun farko idan na san baka da lafiya bazan yi maka ƙorafi ba, at least ko text sai kayi min ba wai ka bar Ni a haka ba, dole hankalina ya tashi."
Murmushi yayi cike da ƙaunarta yace, "to shikenan, nayi kuskure amma bazan sake ba, ya school ɗin?"
"Alhamdulillah. Amma ka ji sauƙi ko? Ba na son komai ya same ka hankali na ya tashi."
"No. Ba abun da zai same Ni Sweetheart, na ji sauƙi sosai, and ko dambe zamu iya yi da ke tunda na fi ki lafiya a yanzu."
Dariya take yi sosai yana taya ta
Sai ta soma mishi shagwaɓa tana cewa, "ita wlh tana jin garin babu daɗi, fuskarsa kaɗai take son ta gani ko hankalinta zai kwanta, tunda ta sauka ta kasa samun