zuciyar Maryamu tayi ba, kai ba ita kaɗai ba, har su Momy sai da suka bi SHAREEF ɗin da kallo kamar wani TV. While Maryamu kamar an saka mata glue an nane ta a inda ta tsaya, zuciyarta wani irin buga wa take yi yayinda nan da nan jikinta ya soma tsuma sabida wani irin abu da ya dunƙule mata a ƙirji, tuni zuciyarta ta hasaso mata abun da ke faruwa a wurin sabida maganganun su da suke yi a yanzu, wanda ta kasa jure wa har ƙafafun ta rawa suke yi, take wani karfi ya zo mata bata san sanda ta bar wurin ba da sauri tana shigewa dakin ta, da gudu ta ƙarisa gefen gadon ta sulale a ƙasa ta zauna, duk da ta fahimci me ke faruwa amma ta ƙi yarda da cewan ƴan Matan SHAREEF ne a wurin, bata yarda cewa da gaske abun da ta fahimta budurwan sa ne ya kawo ba, "wlh bazai yiwu ba, Ni kaɗai ce Matarsa, su wane ne wadannan?" Ta furta da rawan murya, sai kuma ta matse kanta a cinyoyinta ta fashe da kuka gunun tausayi, yanda jikinta ke rawa da kuma abun da take ji a zuciyarta ita kanta ta kasa jure wa, baza ta iya ba, wani irin kishi ne ya tabaibaye ta, sosai take kukan tana ci gaba da matse kanta
Momy ne ta shigo dakin; ta ganta a haka, da sauri ta isa wurin ta tana kiran sunan ta
Itama sai ta ɗago kanta a firgice tana kallonta, nan da nan ta saka hannu ta soma share hawayen still jikinta na faman rawa sosai
"Maryam, mene ne kike kuka? Wa ya taɓa ki?"
Girgiza kanta ta soma yi duk da wasu hawayen ne ke zubo wa, sai dai ta kasa magana sabida ɓarin baki da take yi
"Faɗa min mana mene ne kike kuka? Ko wurin ciwon naki ne ke miki zafi?"
Wani kukan ne ya taho mata domin ta kasa jure wa, sai ta kifa kanta a kafafun ta ta fashe da sabon kuka
Hannu Momy ta sa tana ɗago mata kanta, sosai Mom hankalinta ya tashi sabida ganin halin da Maryamu take ciki, cike da kula wa da damuwa a face ɗin ta take kara rarrashinta tare da ci gaba da tambayarta
Daƙyar ta iya furta mata, "Momy Yaya SHAREEF, wata ya kawo gidan nan zai aura?"
Shiru tayi tana kallonta, "wai dama duk don shi kike wannan kukan? Wa yace miki auren ta zai yi? Ba na son sakarci ki share hawayen nan naki tun kafin in ɓata miki rai, tashi ki cire kayan bari in kawo miki abincin ki da maganinki ki sha, kar kuma in ƙara ganin kin zubar da hawaye."
"Amma Momy..."
"Shiiii! Ba na son ji, lafiyar ki ta fi komai a yanzu, ki share hawayen nace ba na son ganin su." Tayi maganar babu wasa a tare da ita
Dole Maryamu tayi abun da tace, amma kuma wasu hawayen ne suke gudun tsere a kan face ɗin ta don ta kasa tsayar da su, yayinda zuciyarta take mata zafi sosai; ga wani irin buga wa da take yi kamar zata faso ƙirjin ta
Momy bata sake cewa komai ba ta fice a ɗakin
Ganin haka sai ta sake fashe wa da wani sabon kukan tana dafe gefen zuciyarta, "don Allah Yaya SHAREEF kar ka auri wata bayan Ni, Ni ina sonka... Na.. na fi koowa sonnka wlh.." ta ƙare maganar a ɗai-ɗai sabida yanda numfashinta yake sama-sama kamar zai ɗauke,
Duk yanda ta so ta jure amma ina, kuka sosai take yi har da su majinu, shikenan gani take yi ta rasa SHAREEF tunda yana da wata budurwan, ga shi har ya kawo ta gidan su
A haka Momy ta zo ta tarar da ita a wannan mawuyacin halin, numfashi ma daƙyar take yi tsaban jaraban kishi ya ci ranta, lokaci ɗaya har ta fita a hayyacinta
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Maryam, me kike son ki ja wa kanki ne? Kina so mu ɓata ne? Ba kya jin magana ko? Baza ki share hawayen ba?"
Yadda ta daka mata tsawa babu wasa a tare da ita, shiyasa dole Maryamu tayi abun da tace, da sauri ta share hawayen nata tana shashsheƙa gunun tausayi jikinta sai faman rawa yake yi
"Ɗauki abincin ki ci, Allah zan saɓa miki idan kina kuka a kan SHAREEF, Mutum bai damu da ke ba amma duk kin gama ƙwallafa rai a kansa, har yaushe kika san soyayya haka Maryam? Abun naki ma gaba yake yi ko? To bismillah ki ci gaba, common ci abinci ki sha maganin ina jiran ki."
Babu musu tayi yanda tace, haka take tusa abincin daƙyar kamar zata yi amai
Ita kanta Momy tausayi ta bata, musamman yanda ta ga sai faman rawa jikinta yake yi, hakan ne yasa ta buɗe baki tace mata, "kinga Maryam, ba na son kina tayar da hankalin ki a kan SHAREEF. SHAREEF Mijin ki ne already kin rigada kin zama Matarsa, kuma waɗannan Matan da kika gani koda ya kawo su ba hakan yana nufin zai auri yarinyar da yake so bane, yanzu haka ma mun yanke hukuncin za ki tare a ɗakin Mijinki, don haka duk wani tunani ki ajiye shi a gefe ke ce Matar SHAREEF ba wata ba, Dadyn ku na dawowa zamu zauna mu faɗa masa gaskiya sabida mu danƙa ki wurin Mijin ki."
Da sauri Maryamu ta ɗago kanta tana kallon Momy, yayinda wani sanyi da farin ciki nan da nan ya tabaibaye ta
Murmushi Momy tayi mata tace, "Oh! Maryam ko kunya ba kya ji ko? Ba kya jin nuna soyayyar ki a wurin mu?"
Saurin rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana dariyan farin ciki, wani irin dad'i ne ke ratsa ta saboda jin abun da Momy tace
Ita kuma sai ta ja numfashi tana miƙe wa tare da furta, "bari in je in sallame su, ki gama cin abincin sannan ki cire kayan makarantar."
"To Momy." Ta amsa da sanyin murya har yanzu tana jin farin ciki a ranta
Momy kuma ta fita zuwa falo, a can ta tarar da su har sun taɓa abincin; SHAREEF ya saka su dole sai da suka ci, duk da basu so ci ba, har sun tashi ma zasu tafi SHAREEF zai kira Momy, sai ga ta ta fito. Shi yasa ta ɗan saki fuska suka yi sallama, sai tace, "su jira ta tana zuwa."
Ɗakinta ta shiga ta ɗauko musu turare guda uku ta saka musu a leda sannan ta kawo musu, tace, "su gaishe da iyayen su."
Tare suka fita da SHAREEF har mota ya kaisu, Haajara ta shiga Motan ta bar su a nan a tsaye
While SHAREEF cike da farin ciki yake cewa, "yanzu ba ki ji wani irin farin ciki da nake ji ba, Finally yau dai Iyayena sun san da ke, sai kuma maganar auren mu." Sai ya kira sunan ta kuma cikin kwantar da murya yana tsare ta da ido
Yayinda itama ta kafa mishi idanun tana sauraron mai zai ce mata tunda ta ji ya ambaci sunan ta
Hannunta ya kamo ya haɗa da nashi yana ɗan matsa mata cikin wani irin salo, yayinda ya zuba mata narkakkun idanunsa masu ƙara mata tsananin ƙaunarsa a ranta. "you know I love you, a wannan lokacin nake so mu kawo ƙarshen matsalar mu Haseena, ina tsananin bukatar aure ke ma kin sani; kuma ke ma na san haka ne, i know baza ki watsa min kasa a ido ba sabida akwai shawaran da na yanke." Sai ya ɗan ja fasali tare da ƙara wa da faɗin, "since you will have holiday in two months na yanke shawarar zamu yi aure a wannan lokacin, idan na faɗa ma iyayena sun yarda zasu nema min auren ki, inyaso sai ki ci gaba da karatun ki ban damu ba, Ni dai burina a ɗaura mana aure a wannan lokacin, sai na riƙa zuwa har can ina duba ki hakan zai kawo mana sauƙi a lamurran mu."
Bata taɓa tunanin zata ji wannan maganar daga bakin sa a yanzu ba, shiyasa tayi shiru ta kasa furta komai sai kallonsa da take yi, while fuskarta ta sauya alamun kamar bata amince da zancen nasa ba
Hakan ne yasa ya ƙara riƙe hannunta tare da sake rarrashinta cikin kwantar da murya da nuna fuskar tausayi, yana ƙara bata baki da nuna mata muhimmancin auren nasu a yanzu, shi ya yarda kowanne irin karatu tayi in har za a ɗaura musu auren, daga baya sai ta tare after ta gama karatun, auren kawai za a ɗaura
Duk da haka ta ƙi amince wa, sai ta langaɓe mishi itama ta nuna masa, "zata yi shawara, kuma zata sanar da Abbanta in ya amince, ko mene ne sai ta faɗa masa."
"Please try sweetheart, I need to marry you now, hankalina zai fi kwanciya."
Ya furta yana ƙara mannewa a jikinta kamar zai rungume ta
Ɗan waro ido tayi kaɗan tace, "nan gidan ku ne fa, we will pass and sai mun yi waya dear, don't worry I will try to talk to Abba."
Dad'i ya ji sosai, sai da ya ɗan sakar mata kissing a hannu before suka sake yin sallama ta tafi, yana sanar mata, "zuwa goben in zata tafi zai zo su je airport tare."
Sai da suka tafi sannan ya shiga gida.
***
_____Ko kusa Momy bata yi wa SHAREEF maganar Haseena ba. After Dady ya dawo ta zayyane mishi komai
Shi kansa yayi mamaki saboda dukkan su basu yi zaton yana soyayya ba,
Shi yasa bayan sun gama cin abinci sai Dadyn yace, "su zauna gaba ɗaya yana da magana."
A tunanin SHAREEF maganar Haseena za a yi tunda yana tunanin Momy ta sanar da Dady, sai faman murmusawa yake yi. Saɓanin haka sai ya ji abun da ya girgiza shi har ya tashi tsaye a kan ƙafafunsa yana zaro ido, take ya soma jin wani irin gumi yana tsatstsafo mishi lokaci guda
Su kuma suka tsaya suna kallon yanda ya nuna firgicin sa kamar wanda aka faɗa masa mummunar abu
Da mamaki Momy tace, "ya haka da firgici sai ka ce abu mummuna ake sanar maka? Ka zauna mana."
Hannu ya ɗaga yana nuna Maryamu da yatsa, cikin sarƙewan murya kamar zai yi hauka yace, "wai kuna nufin wannan abar ce zata zama Mata ta? Noo! Impossible wlh, ba na sonta! Ba na ƙaunarta! Bazan taɓa zama da ita ba, i hate her so much! Wlh ku canza tunani Momy bazan taɓa zama da ita a matsayin Matata ba, never."
Tsawa Momy ta daka masa, "kana da hankali kuwa SHAREEF? Kanka ɗaya?"
Da idanunsa jawur yake kallonta cikin ƙunan rai yace, "Momy da hankali na, taya ya zaku yanke wannan hukuncin ba tare da sanina ba? Me zan yi da wannan yarinyar? Wlh bazan taɓa zama da ita ba, ina da wacce nake so."
Miƙe wa Momy tayi ta kifa masa mari tare da daka masa tsawa, "shut up! SHAREEF ko in baka mamaki a nan wlh, har kai ka isa ka riƙa faɗa mana magana irin wannan? Ashe baka da kunya? Mu kake fada wa magana haka?"
"Bar shi ya ci gaba Deejah, ai zai nuna mana shi ya haife mu bamu muka haife shi ba."
Kallon Dady yayi, sai hawaye ya soma zubo mishi shaaa, da sauri ya bi hanyar steps da gudunsa ko sauraron su bai yi ba, duk da yana jin kiran da Momy take mishi
While Maryamu tuni ta soma kuka sabida ganin yanda SHAREEF yake yi, musamman da ya nuna ba ya sonta bazai zauna da ita ba, yanda take ganin tsantsan tsanarta a wurin sa bazai taɓa ƙaunarta ba. Sai kuka kamar ranta zai fita, lokaci ɗaya numfashinta ya sarƙe ta zube a wurin sabida kasa jure halin da take ciki
Su kansu su Momy basu ankare ba sai da Sadiq ya kwaɗa kiran Maryamu ganin bata numfashi, dayake yana kusa da ita ya taɓa ta ya ji ba ta motsi, shiyasa ya dinga kiran sunan ta hankali a tashe
matuƙa hankalin su ya gama tashi, musamman yanda suka zuba mata ruwa amma ina ta ƙi farka wa
Dole Dady yace wa Sadiq, "ya dauko key su kaita asibiti."
Da gudu ya wuce ɗaki domin dauko key din Motan,
While Dady shi ya saɓa ta a kafaɗa ya fita da ita
Dukka suka tafi asibitin gaba ɗaya hankali a tashe. After sun isa ba ɓata lokaci aka amshi Maryamu; since yawancin doctors ɗin asibitin sun san waye Alhaji Ahmed
Kafin ma a yi mata wani taimakon har ta farka, sai dai kuma yanda take ta kela amai kamar zata zubar da ƴan hanjin cikin ta; gaba ɗaya ta gama fita hayyacin ta, Likitan da ke duba ta shi ya saka wata Nurse yace, "ta gyara ta, sai ta ɗibi sumfurin jininta ta je ta gwada; ta kawo mishi result ɗin office."
Sannan ya fita zuwa office suka wuce tare da su Dady a can suka zauna, yayi musu bayanin, "yanzu za a kawo result, ta farka ma but amai take yi, dole sai an gwada ta sun tabbatar da me ke damun ta."
Hakan ne ya ɗan sa hankalin su ya kwanta tunda sun ji ta farka. Suna nan suna jira; Likitan ma tuni ya bar su a cikin office ɗin ya koma wurin ta
After an yi gwaje-gwaje sakamako ya nuna ciki a jikin Maryamu, shi kansa Likitan ya ɗan yi confused kasancewar cikin bai fi two to three weeks ba, duk da ciki yana iya bayyana a wannan ƙanƙanin lokacin, to bai sanar musu ba sai da ya ƙara saka wa aka yi mata duk wasu gwaje-gwaje da zai ƙara tabbatar musu, har fitsarin ta sai da aka ɗiba, daga nan aka saka mata drip tunda duk ta galabaita a ɗan ƙanƙanin lokaci tamkar ba ita ba, sai nimfarfashi take yi idanunta sun kaɗa sun yi jazur sun fita a hayyacin su tana ta sambatun magana, that's why har alluran barci sai da aka yi mata, amma kuma hakan bai sa ta ɓingire da barcin ba, sai surutai take yi kamar na zafin ciwo, kamar kuma ba ta cikin hankalin ta
Almost ten minutes before su ga ta dena motsi, alamun barci ya ɗauke ta,
Sai Doctorn ya bar Nurse a wurin ta, yace, "ta kula da ita yana zuwa."
Office din ya koma ya zauna before ya sanar musu da result ɗin abun da suka samu, ɗan cikin da suka samu a jikinta
Kalman cikin suka maimaita a tare suna kallon junan su cike da tsananin mamaki da al'ajabi
Sadiq da ke tsaye a gefe, shima sai da ya ɗan zare idanu yana maimaita cikin a ransa a rikice
"Ƙwarai ciki ne a jikinta, binciken mu abun da ya nuna mana kenan, kuma bai fi sati Uku ba, abun da yasa ma muka daɗe sai da muka ƙara mata duk wasu gwaje-gwaje da zai sake tabbatar mana da hakan, kuma tabbas ciki ne."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...!" Abun da ke fitowa daga bakin Momy kenan tana ɗan shafa fuskarta
To wane ne ya yi mata ciki? Sun fa rikice sosai tunda basu san ya zasu ɗauki maganar ba
Dady ne ma yayi ƙarfin halin faɗin, "zamu iya ganin ta Doctor?"
"Eh zaku iya ganin ta, amma mun yi mata allura tana barci, mun ƙara mata ruwa ma, Insha Allahu komai normal ne zata samu lafiya da yardan Allah, Allah ya bata lafiya."
"Amin." Suka amsa da sanyin jiki zuciyoyin su na tsinkewa
Sannan ya tashi yace, "su je ya kaisu ɗakin."
Duk yanda suka so su cire damuwar abun da ke ransu but sun gaza, abun da ɗaure kai, to ta ya ya Maryamu ta samu ciki after all SHAREEF bai taɓa sanin ita Matarsa bace? Sannan ma taya ya zasu zarge sa bayan sun san zaman da ke tsakanin su; SHAREEF ba ya ƙaunarta.
Dole akwai rikitar wa, amma ko ma dai mene ne ita Maryamu zata iya faɗa musu wanda yayi mata cikin
Ganin yanda Momy ta nuna damuwarta fiye da nasu har da ɗan guntun hawayen ta, shiyasa Dady ya sake kwantar mata da hankali sosai
Amma ita gani take yi kamar har da laifin ta, yarinya tana wurin ta tayi ciki ba tare da sanin ta ba? To wanne sakaci suka yi da har hakan ta kasance? In fact ma har Sadiq sai da ta kawo zargin ta a kansa, sai dai furta wa ne bata yi ba amma kaifafan idanunta suna kansa, but babu wani abun zargi a wurin sa
Dole ita Momyn ta zauna da ita; su kuma suka tafi gida since dare yayi sosai,
Ƙarshe kasa runtsa wa tayi ta zauna ta buga uban tagumi tana ta kallon Maryamun da ke kwance tamkar matacciya, babu inda ke motsi a jikinta,
Har garin Allah ya waye Momy tana zaune digir-gir bata runtsa ba, kuma har wannan lokacin itama Maryamun bata motsa daga yanda ta kwanta ba,
Sai kusan ƙarfe biyar da rabi time ɗin Momy tana zaune ta gama nafila zata gabatar da sallan subhi da ake ƙoƙarin shiga,
Bata san Maryamu ta farka ba har ta tayar da Sallan,
Sai ta soma jin sambatun ta tana kiran sunan SHAREEF, hakan ne yasa ta ɗan taƙaita sallan before ta idar; ta miƙe ta nufi wurin tana kama ta tare da kiran sunan ta
Ashe ma idanunta a rufe suke, sambatun kawai take yi bata gama farfaɗo wa ba
"Sannu Maryam, kin tashi?" Tayi maganar tana riƙe da dantsen hannunta
Buɗe ido Maryamu tayi tana kallonta, sai kuma ta soma tunanin abun da ke faruwa da ita since bata gama dawowa cikin hayyacinta ba, sai kallon ɗakin take yi kamar wacce take neman wani abu
Ruwa Momy ta ɗauka ta buɗe goran tana kaiwa bakin ta after ta tallabo ta
Kamar dama ta san tana jin matsanancin ƙishi, sosai bakin ta ya bushe wanda har saman laɓɓanta sun yi ƙamas sun fitar da fata
Sai da ta bata ruwan sannan ta sake tambayarta jikin nata?
Maryamu da ke dubanta tace, "Momy me ya kawo Ni nan?"
"Kwantar da hankalin ki, yanzu babu abun da ke damun ki ko kina jin wani ciwon a jikin ki?"
"A'a Momy."
"To bari in kira Likita ya sake duba ki. Ina zuwa."
Sai ta sake ta tana ajiye ruwan before ta fita da sauri
Lumshe idanu tayi tana ɗan kama kanta da ke faman sara mata kamar zai ɗaɗɗake, kwata-kwata bata tuna abun da ke faruwa da ita ba har ta zo nan, in fact ma bata fahimci a asibiti take ba duk da ta ga hannunta an saƙale shi da