x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - SHAREEF SEXY BOY BOOK 1

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 152447 words

Category: Romance Story +18

Views 366

25 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
sai kuma ta kwashe da dariya tana nuna sa da yatsa

Hakan ne yasa shima ya bi jikin nasa da kallo yana mamakin abun da yasa take mishi dariya. Ganin ta ƙi dena dariyan ne sai ƙara kwashe wa take yi da dariya har da tafa hannaye kamar wata mai kwantaccen kai. Sai yace, "wai lafiya Maryamu? Meyasa kike min dariya?"


Lokaci ɗaya ta ɗauke dariyan tana tamke fuska cikin yanayin ta na rashin mutunci tace, "wlh kana bani mamaki Jamilu, kai har kakai matsayin da zan iya sonka? Ji be ka fa..." Ta ƙara nuna sa da hannu kallon sama da ƙasa, sai tace, "wai tsaya, me ya ba ka ƙwarin gwiwar zuwa wurina?"

Cike da rashin jin daɗin abun da tayi masa yace, "amma ai na san kin san waye Ni a ƙauyen nan Maryamu, sannan na san ke ce Macen da ta fi kowa kyawu shiyasa nima na zo wurin ki saboda dani kaɗai kika dace, ina da yaƙinin za ki so Ni tunda kin san ina fita Birni aiki."

Kama ƙugu tayi da hannu biyu cikin tsiwa tace, "Allah ya kyauta, don kana fita Birni aka ce maka irin Mazan da nake so kenan? To wai ina ruwana da matsayin ubanka a garin nan? Bari ka ji Ni na fi ƙarfin ku wlh, babu Mijina a wannan ƙauyen, ka dube Ni sama da ƙasa." Sai ta juya jikinta a gabansa tana mirza jiki kasancewar Allah ya bata ƙirar jiki, sam babu rama a tare da ita wanda hakan ke ƙara jawo hankalin samari a kanta, kuma duk ƙauyen gani suke yi ta fi ƴan matan kyawu. Sai tace, "to Ni ba sa'an wasan ka bane, kar in sake ganin ka tako ƙofar gidan nan da sunan ka zo wuri na, wlh tallahi ka san hali na bani da mutunci zan shuka maka babban rashin mutuncin da sai ka yi dana-sanin sani na a rayuwa." Sai ta ja dogon tsaki tana juya wa zata shige gida

But sai ya dinga kiran sunanta har yana bin bayanta da sauri

Da sauri itama ta juyo a fusace tana kwaɗa mishi mari, "baka ji mai nace maka ba ko? To wlh ko Ubanka da yake mai anguwa na fi ƙarfin shi bare kai ƙaramin alhaki."

Zallan mamakin abun da tayi masa ne yasa ya kasa motsa wa yana riƙe da kuncin sa, sai da ta shige gidan ya dena ganin bayanta sannan ya soma ƙifta idanu ya dawo cikin tunanin sa, tsaban yanda ransa ya ɓaci ya rasa ma wanne mataki zai ɗauka, ba marin da tayi masa bane; yanda ta ci masa mutunci kuma ta haɗa da ubansa ne ya yi matuƙar ɓata mishi rai tare da mamakin yanda har rashin mutuncin nata ya kai haka ashe, duk zancen Mutane gani yake yi kamar shi ya fi ƙarfin tayi mishi haka har ya iya biye wa zuciyarsa, ashe akwai ranan da zata wulaƙanta sa duk matsayin mahaifinsa a garin, tabbas sai ya ɗauki mummunan mataki a kan yarinyar nan, domin bazai taɓa yafe mata wannan cin zarafin ba, zai nuna mata shi yana da bambanci da sauran Mutanen karkaran, sannan Babansa shi ne shugaba. Juya kai yayi da sauri ya wuce yana gode Allah da babu wanda ya ganshi.



           Ita kuma Maryamu tana shiga gidan sai masifa take yi har da kumfar baki

Umma Jummai ita ta soma tambyarta, "ita da waye zata shigo tana surutu?"

Sai da ta ja tsaki tana tsittar da yawu, sannan tace, "wlh Umma na kusa tayar da bambamin bala'i ga duk ɗan iskan da bai bar zuwa kofar gida kirana ba, don sun raina Ni sai kowanne kare da doki ya zo yace yana sona tunda sun gama raina min wayau? wlh daga yanzu duk wanda ya zo sai nayi mishi abun da ko Uban shi sai yayi dana-sanin haifo sa...."

Bata ƙarisa zancen ba Innarta ta bugo salati tana fitowa daga bayi, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Wai Maryamu kanki ɗaya kuwa? Wato ba ki da mutunci ba ki san Annabi ya faku ba ko? Tam shikenan ki ci gaba da abun da kike yi na rantse da Allah sai na saka Naziru yayi miki mugun duka a gidan nan tunda ba ki da mutunci; banzan yarinya kawai."

Umma Jummai ta karɓe da faɗin, "Ni na rasa kan wannan yarinyar Hafsatu, anya abubuwan da take yi baza a je a duba ƙwaƙwalwan ta ba? Kullum ace ba ta jituwa da Samari sai faɗa da zage-zage wannan abun zai yiwu kuwa? Gwara dai a nema mata magani wlh."

"Ni wlh lafiyata ƙalau Umma. Ya za a yi a mayar da Ni mara hankali bayan baku taɓa ganin na hau iska ba? Ras nake wlh." Tayi maganar tana tura baki tare da wuce wa ɗakin su tana ci gaba da ƙunƙunai

Inda Inna ita kuma tayi ƙwafa tana cewa, "kin gani ko? Iskanci ne ba wai wani abun ke damun Maryamu ba, ta ɗauki burin banza ta ɗaura wa kanta, to a yi mu gani idan wannan hanyar da kika ɗaukar wa kanki zai fishshe ki, kuma dan ubanki ki fito ki wuce Islamiyya tunda kin dawo gantalin naki, kar ki bari in sake miki magana."

"Gani nan." Tayi maganar da ƙarfi daga ɗaki

Su kuma suka ci gaba da tattauna halin Maryamun ita da Umma Jummai, a kan yanda take wulaƙanta Samari, suna faɗa mata, "idan ta ɗauki wannan hanyar wata rana zata yi dana-sani tunda baza su zuba ido su barta babu aure ba, tana ƙauye a tunanin ta wane mutum ne zai zo ya aure ta ɗan birni? Ta ɗauko abun da ya fi ƙarfin ta."

Zurum sai ga ta ta fito tana tura baki da cewa, "Ni fa yanzu ba shine damuwata ba, tunda babu wanda ya isa yayi min aure yanzu dai ina ƙarama ta, na rantse baza a tauye min haƙƙina haka kawai a yi min aure a wannan time ɗin ba, karatu nake so domin sai na cika burina, sai nayi ilmi har na fara aiki in samu daidai ra'ayi na, ku kanku zaku ji daɗi ace yau ga Mijin Maryamu a Mota ɗan gidan masu kuɗi, amma haka kawai na ƙare a ƙauye? Na taso a ƙauye babu ci gaba sai kuma na ƙare a nan? A'a gaskiya bazai yiwu ba."

Inna ta kasa magana don takaici. Yayinda Umma Jummai ta riƙe baki tace, "lallai abun naki ya shahara Maryamu, to ai sai ki jira mai motan ya zo ya aure ki tunda iskancin naki gaba yake yi."

Yaro ne ya shigo a lokacin ya zo siyan panadol

Inna tace, "idan kin gama rashin kunyar ki zo ki amshi mukulli ki ɗauko mishi, kuma kar ki bari in sake miki magana ba ki wuce makarantar nan ba, Allah Maryamu zan mummunar ɓata miki rai."

"Kai Inna! Ni wlh ban san mai nayi miki ba yanzu komai sai faɗa, Ni nace miki bazan je bane? Gaskiya Ni na fi so ma a mayar da Ni wurin Iya kawai in ci gaba da karatu na a can, wlh bari Baba ya zo sai na faɗa mishi Ni dai na fi son karatu."

"Ai gwara ki faɗa ma Baban naki tunda shi ne dai-dai ke kuwa." In ji Umma Jummai tana tashi ta shige ɗakin ta riƙe da kwanon garin tuwo

Ita kuma Inna ta miƙa mata mukullin batare da ta sake ce mata komai ba; ta soma ɗaura alwala

Maryamu fita tayi da yaron; ta buɗe shagon ta ba shi sannan ta mayar mata da mukullin, Hijabin ta ta zura ta fito bayan ta saka takalmi mai tsini tana tafiya daƙyar kamar baza ta taka ƙasa ba

MARYAMU kenan. Yarinya mai tashe a cikin ƙauyen nasu, haƙiƙa tana da farin jini sosai duk da dama ita kyakkyawa ce, ga ƙira mai kyau komai ya ji a jikinta, yarinya ce da bata gaza shekaru goma sha biyar ba, baƙa ce irin Black beauty ɗin nan, Allah yayi mata kyawu ga manyan idanu farare sol, tana da dimples waɗanda suke ƙara mata kyau musamman idan tayi murmushi ko dariya. Ba wata mai tsawo bace ƴar matsakaiciya ce kuma bata da jiki; amma kuma bata da rama ko kaɗan, zubin ta irin waɗanda Maza suke so ne shiyasa suke rushing ɗin ta, sai dai ita ta ɗauki buri ta ɗaura wa kanta, bata da buri sai auren mai kuɗi kyakkyawar saurayi ɗan birni, shiyasa fatan ta a yanzu tayi karatu mai zurfi wanda ta san cewa shine kaɗai zai sa ta samu cikan burin ta, idan tayi ilmi to ta san kowanne namiji zata iya samu

Sai dai tunda suka gama junior secondary ita da Bintu har yanzu basu ci gaba ba, tunda burin Babansu yayi musu aure kasancewar sun kai minzalin aure, kuma a garin yarinya ba ta wuce shekara sha uku bata yi aure ba, kuma yawancin su ba sa karatu, amma dayake shi Babansu ya san daɗin karatun kuma yana barin yaran shi shiyasa su ma ya bar su, Matan ba sa kai wa secondary yake aurar dasu, su Maryamu ne kawai suka gama junior

Kuma a yanzu ita tana burin ta ci gaba duk da zata sha wahala; kasancewar babu senior secondary a cikin garin, dole sai an fita birni. Ita kuma ta matsa a barta ta koma wajen Kakarta Iya Samira tayi karatun ta a can, har yanzu dai Babansu bai yarda ba, tunda tayi masa magana sau ɗaya ma bata sake mishi ba kasancewar yayi mata faɗa sosai a lokacin.
[08/01, 8:25 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*


*Don Allah ina baran addu'a daga bakunan ku masu albarka, ina cikin matsananciyar damuwa, ina neman addu'a gare ku ya Allah ya yaye min abun da ke damuna; da duk wanda ke cikin irin hali na, 😭 innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.*










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE4*
             Bai tashi daga aiki ba, sai kusan ƙarfe shida da rabi, duk da ya saba jima wa but ba ya kaiwa haka, ya kan yi ƙoƙarin tashi by 5 o'clock. Shi yasa gaba ɗaya a gajiye yake jin sa, tafiyan ma daƙyar yake yi fuskarsa a turɓune kamar zai saka kuka, yanayin sa kuma sai ya koma tamkar ƙaramin Yaro abun burgewa ga duk wanda ya kalle shi, shiyasa a koyaushe Mata suke matuƙar ƙaunarsa; domin ta ko'ina SHAREEF ya kai namijin da Mace zata mutu a soyayyarsa. Sai dai kuma babu fuskar da kowacce Mace zata iya tunkurar sa gudun wulaƙanci

Majority Matan da suke aiki a companin babu wacce ba ta yin sa, wasu har ba sa iya ɓoye ainihin abun da ke ransu dole sai sun tunkare shi duk da wulaƙancin da zai yi musu. Shi yasa yawanci suke rasa aikin su, domin ba abun mamaki bane daga kallo ma kaɗai idan bai gamshe shi ba ya kore ka. Companin kowa ya san ba ya wasa bare ɗaukar raini, kuskure kaɗan zai kore ka domin ba ya ma Mutum uzuri. That's why kowa yanzu ya kama kansa yana taka-tsan-tsan kar ya shiga gonan SHAREEF. Domin idan ya yanke hukunci ko Dady ba ya cewa uffan

Yanzu ma Dady ya dena zuwa companin ya danƙa mishi komai shi yake yi, sai jefi-jefi ne yake zuwa ko duba wurin, amma komai SHAREEF ke yi, sai wani lokacin idan Hanif yana gida ya kan zo su yi aikin tare

Sadiq kuwa dama babu ruwansa da companin tunda yace, "babu abun da ya haɗa sa da Kasuwanci." Dayake karatun lauya yake yi. Yanzu haka yana BUK shima ya kusa gama wa ya wuce England

Hanif kuwa, ɗan watanni ne ya rage mishi ya ƙare. So yanzu ma yana gida bai koma ba.



    **** **** ****



             Tunda ya hau motan sa ya soma tuƙawa a hankali; yana yi yana duba wayansa fuskarsa yalwace da murmushi. Wanda hakan ba kasafai yake yin sa ba sai da ƙwaƙƙwaran dalili, yanzun ma chart suke yi da Haseena shiyasa kacokan hankalinsa ya bada gare ta. Sai jefi-jefi yake ɗago kai ya duba hanya a haka har ya ƙarisa gida. Horn ɗaya yayi aka buɗe masa ƙofan ya shige da Motan. A wajen parking space ma sai da ya ɓata time ya ƙi fitowa yana ci gaba da chatting ɗin. Daga ƙarshe kuma ya fito hannunsa ɗaya riƙe da waya, ɗayan kuma ya riƙo Jakar office ɗin sa; inda ya ɗaura suit ɗin sa a saman kafaɗa yana tafe yana duba wayan

Dama already masu aikin gidan sun san halin sa ko gaisuwar su ba ya amsa wa; bare su kawo mishi ɗauki wajen taimaka masa da amsar Jakar, tunda ya hana su yace, "kar ya ƙara ganin wani ya zo inda yake."

Ire-iren halayyar nan na ƙyama da yake nuna musu shiyasa kowa yake jin tsoron sa, a kuma taka-tsan-tsan suke yin komai nasu musamman in yana gida, domin yanzu zai hau su da faɗa yana zagin su. Shi kaɗai ne ya fita zakka a gidan tunda kowa suna jin daɗin zama dasu ban da shi

Falon ya shiga ko sallama babu tunda hankalinsa yana a kan waya. Har ya nufi kan steps zai hau sama sai ya ji kiran Mahaifiyarsa. Yana ɗago kai suka haɗa ido da ita tana zaune a saman kujera tana kallon tashan Arewa24 da ake haska maimacin shirin gari ya waye

"Mom." Ya furta yana ɗan yaƙe haƙora cike da kunyar ganin ta a wurin

Ita kuma sai ta dalla mishi harara tana sake kafe shi da ido ko ƙyafta su ba ta yi

Domin ba abun da yake shakka sama da idon mahaifiyarsa, kasancewarta mai manyan ido shiyasa take yawan hukunta shi da su, domin shi ya sha sanar mata, "yana matuƙar tsoron idanun nan nata." Shi yasa da zaran ta kafo mishi su ya san laifi yayi. Sai ya sunkuyar da kai yana sussune kai, ko kuma ya soma bata haƙuri

Yanzun ma hakan ne, tunda ya yaƙe haƙora ya soma sosa ƙeya kansa a ƙasa

"Zo nan."

Dole ya tako a hankali ya isa inda take. Ya san me take nufi, shiyasa ya duƙa a gefen ta still kansa a ƙasa

Maimakon ta ja masa kunne kamar yanda ta saba, sai ta ranƙwashe shi da ƙarfi yanda zai shige shi, tana kuma ƙara wa da murɗe mishi kunnen

"Oushh! Momy. Da zaafi..."

"Ai zafin nake so ka ji, ba ka jin magana ko SHAREEF? Wai sau nawa zan riƙa maimaita maka magana?"

"Allah Momyna na manta ne, amma da kika kira Ni nayi a zuciyata."

Kunnen ta sake murɗe mishi tana cewa, "au ka yi a zuciya? Haka aka koya maka don ƙaniyar ka? Kana ɗan musulmi zaka shigo mana gida babu sallama bare ma ka ɗaga kai ka kalli Mutanen ciki ko?"

Fuskarsa ya kwaɓe kamar zai yi kuka sai dai ya kasa cewa komai

Sai ta tamke fuska tana cewa, "to kar ka sake bari na kara maka magana."

"To." Yayi maganar a hankali

"Ba to zaka ce ba, ka aiwatar ne, don na gaji da jin to ɗin nan naka amma kullum sai ka ƙara aikata wa, zamu hau sama da kai SHAREEF wlh."

"Ke da Yaron naki ne? Me kuma yayi?" Cewar Dady da ya sauko daga saman benen, yana nufo su da murmushi a kan fuskarsa

"Wlh kuwa, halin nasa ya sake, sai ka yi wa SHAREEF faɗan halinsa sam ba ya jin magana, ban san meyasa yake wasa da addinin sa da yawa ba, kwata-kwata ba ya damuwa da abin da ya kamace shi, yanzu kamar SHAREEF zai shigo mana gida babu sallama?"

"Kullum maganar kenan ai, kai kuma ka ƙi gyara wa har na haddace faɗan nan. Ka yi wa kanka faɗa ka dena saka Mahaifiyar ka magana, ko Sadiq bazai yi abun da kake yi ba." Cewar Dady yana ɗan murmushin sa wanda ba ya rabo da yin sa, domin yawancin sa yana komai nasa ne cikin raha da barkwanci, ba shi da faɗa ko kaɗan, ko faɗan ma zai yi maka baza ka iya ganewa ba tunda yana yi yana saka wasa ne, ko kuma ka ga fuskarsa a sake wanda ba ka iya tantance faɗan ma yake yi, ko kaɗan ba shi da zafi Mutum ne mai sauƙin kai. Shi yasa kowa yake son shi domin ba shi da girman kai irin na masu kuɗi, ga taimakon jama'a kowa nashi ne. "Yanzu tashi ka je ka yi alwala ka ga an kira sallah kar lokaci ya ƙure. Ke kuma Momyn Yara a dena mishi faɗan haka, har yanzu shi Yaro ne wata rana zai dena."

"Hmm kullum haka kake cewa ai."

Murmushi yayi yace, "to ai hakan ne, yanzu SHAREEF ai kai yaro ne ko?"

Dariya yayi yana sosa kansa tare da gyaɗa mishi kai

While Dadyn yace, "yauwa ɗan albarka, to yi maza ka je ka yi alwala kar lokaci ya ƙure. Hanif ma yana ɗaki ka sake koro sa."

"To Dady." Yayi maganar yana wuce wa upstairs

Inda shima Dadyn yace ma Momy, "bari in je Masallaci."

"To sai ka dawo." Ta amsa mishi tana tashi itama ta wuce nata ɗakin domin ɗaura alwala

SHAREEF kuma yana shiga ɗakin, ya tarar da Hanif yana kwance barci ya ɗauke shi a saman kujera, da alamun aiki yake yi tunda ga computer nan a gaban shi tana buɗe

Sai da ya isa bakin gadon su ya ajiye Jakar hannun sa da wayan, ya zare suit ɗin shima ya ajiye sannan ya nufe sa yana kai masa duka a saman kumatu

Lokaci ɗaya kuwa ya farka yana zuba masa idanu

Sai ya harare sa yana cewa, "ka zama mushe ne? Barcin meye kake yi haka?"

Ɗan kwaɓe fuska yayi yana miƙa tare da salati, kana a hankali cikin mayen barci yake cewa, "wlh maganin mura na sha, ban san barcin ya ɗauke Ni ba." Sai ya ɗan ja tsaki sabida jin ana kwaɗa kiran sallah. "yanzu wai har nayi barci da yawa haka?"

"Tun yaushe kake barcin?" SHAREEF ya tambaye sa yana ƙoƙarin zare necktie ɗin wuyansa, tare da koma wa gefen gado ya zauna, sannan ya soma cire Cumbas ɗin sa da socks

Hanif kuma yana basa amsa shima ya miƙe yana ƙara miƙa tare da jujjuya jikin sa, "tun four nake nan barci ya kwashe Ni."

"Da alamu bai ishe
End Ads